GOJE

GOJE 21 and 22

Hakan ya janyo hankali d’aya d’aga cikin yaran uban daba wanda yake shawagi a gurin………..Gurin ya shiga yana zazzare ido! ita kuma ganin b’akuwar fuska yasa ta sake rikicewa! shi kuwa murmushin farin ciki yayi ya nufeta da saurin gaske!

Hannunta ya fizgo! ta turje! tana rirrike itaccen dake katange da gurin, kuka take tana rokonsa yayi hakuri, ya d’auke fuskarta da mari! da tafkeken hannunsa!! a take hancin ya fashe! ya dinga tsiyayar da jini!

Janta yake tana turjewa da bashi hakuri cewa bata da laifi itama sato ta sukayi, ya sanya kan k’otar lafceciyar wu’kar dake hannunsa ya dinga bubbuga mata a gwiwa, lokaci guda ta galabaita! ta zube a gurin! d’aukarta yayi ya sa’ba a kafad’a ya fito da ita. kai tsaye mafarkarsu ya nufa da ita a kafad’arsa………….

Tashin hankali kenan! lokacin daya hangeta sa’be a kafardar gardi! sai da wukar hannunsa ta subce! ta kusa fad’uwa amma yayi muzzakaracin riketa da kyau a hannunsa!! Wani uban ihu! ya kurma! wanda ya razana! abokan fad’an nasa suka ranta ana kare, amma ina! basu samu nasara ba, sai da ya kama su, ya sanya wata narkekiyar igiya ya daure musu hannuwa da kafafu!

Gabad’aya gurin ya hargitse! sakamakon bomb din da ya tashi, yayi sanadiyar kona biyu daga cikin yaran shi, suna kwance magashiyan! rai a hannun Allah…… Duk da cewa sune suka samu nasara amma beso wata matsala ta afku da yaran sa ba..

Ya kallesu gabad’aya kammaninsu ya sauya hatta da fuskokinsu sun rine! da baki! sakamakon tashin bomb din, wannan ce hanya mafi sauki da abokin hamayyar ya samu nasara a kansa!

Ya kallesu da fadin.” Yayi imani! da cewa idan ya tunkari inda muke da wu’ka ko wani abu makamancin haka ba zai samu nasara akanmu ba, wannan shine dalilin daya sanya shi jefo mana bomb! ba tare da munyi tsammanin hakan ba, to Alhamdullhi duk da hakan be samu nasarar da yake bukata akanmu ba, yanzu kalubalan dake gabanmu tunkarar sansaninsa domin gwabzawa a tsakanimu, babu yanda za’ayi mu tafi mu bar masa wannan yarinyar da yayi nasarar dauke mana ita, duk da cewa tsintar ta mukayi akan hanya bamu san daga ina take ba, hakan ba zai sanya mu bar masa ita ba, duk yanda za’ayi sai mun samu nasara a kansa.”

Da yawa daga cikinsu sun tausaya mata, amma wasu sun kalubalanci maganarsa! bai ta’ba sanya kara sun tsallake ba, amma da alama akwai wa’inda za suyi masa tawaye a cikinsu.

Ya dinga kallonsu yana nazarin yanayinsu, yace.” Babu wanda zan tursasa! cewa ya take min baya! a cikunku. zan iya tunkarar sansanin ni kadai! ba tare da kowa ba! saboda haka wanda yake ganin zai bi bayana bisimillah.” Yana gama maganarsa sai yayi gaba, wasu suka bi bayan shi da sauran karnukan! dake raye, wasu kuma suka tsaya suna surutai da mai da magana a tsakaninsu!

Free pege ya kusa karewa a daure a biya kudin karatu馃檹馃徎 don Allah idan kin san ba siyan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button