GOJE 23 and 24
FREE PEGE
23&24
Biyu da rabi na sulusin dare!
Cikin firgitaccan yanayi ta tashi zaune tana kiran sunan Allah! hakan ya janyo farkawarsa dama can bashi da nauyin bacci, zaune ya tashi kafin ya rike hannunta dake wani irin rawa, yace.”Menene Aysha.”? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta rungumeshi tana girgiza kai da fadin.” Zinat ce ranka ya dade yarinyar nan na cikin mugun yanayi Allah ya nunan hakan a mafarkina.”
Sake rungumeta yayi a jikinsa cikin sigar rarrashi yace.”Aysha mafarki ba gaskiya bane kada ki gazgata abinda ki ka gani, bana tsammanin cewa mafarkinki zai tabbata, jikina yafi bani cewa yarinyar nan tana a raye kuma daf take da ta dawo garemu da ikon Allah.”
Kallonshi tayi hawaye na tsere a saman fuskarta tace.”Ranka ya dade koda Allah ya nufa yarinyar nan ta dawo gida bai zama lallai a sameta da cikakkiyar lafiya ba ka san dai yanda duniyar nan ta lalace da rashin gaskiya wannan shine babban tashin hankalina.”
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin.” Kada ki fadi haka Aysha! zuciyarki ta dinga halarto miki alkairi akan yarinyar nan! adduarki a gareta karbabbiya ce a gurin Allah, kada ki yarda zuciyarki ta yarda da wannan mafarki ki dauka cewa k’anzon kurege ne, a yanzu abinda zakiyi ki faranta min shine ki tashi kije ki dauro alwala ki gabatar da nafila a gaban ubangiji kana ki mika masa kukanki.”
Ta sauke ajiyar zuciya da jin sassauci acikin zuciyarta, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga gadon ta nufi toilet domin daura alwala.
Tana fitowa shima ya tashi ya shiga ya daura alwalar ya fito, lokacin har ta tayar da sallar, jallabiya da gajeran wando ya sanja kana ya gyara dadduma shima ya tayar da tashi sallar.
Tun bayan daya sa’ba ta a kafad’a suke buga artabu a tsakanisu, rikon tsauri! yayi mata yana gudu tare da tsallake manya-manyan dutsina da ita a kafadarsa! tayi duk wani kokari gurin ganin ta ceci kanta abun yaci tura! domin mutumin mugun basamude! ne wanda cizo da yakushi basa shigarsa! dukansa take tana cizo duk ta dauke masa fata amma ko ajikinsa, ya riketa katamau! yana gudu! burinsa kawai ya kaita gaban ogansa ya san hakan zai faranta masa rai.
Hakan ne ya kasance kuwa, Ogan nasu yana cikin bacin rai! mai tsanani sakamakon rashin samun nasara! bai ta’ba fuskantar irin hakan ba sai a wannan lokacin, kai kawo kawai yake gurin ya rasa abinda yake masa dadi! …………Amma zuwan babban yaron sa da yarinyar ya faranta masa rai! mutuka, sai kawai ya kwashe da wata ‘yar iskar dariya kafin yayi wani irin tsalle! da juyi na jin dadi, ya zuba mata kwala-kwalan idanuwansa!
Bakinsa kawai yake lasa, jikinsa na wani irin tsuma! komai na yarinyar yayi cif da cif! bata da makusa, cikakkiyar mace irin wacce ya jima bai kwanta da irinta ba!
Gurin ya tsit! gabad’aya yaransa sun zagayeta motsin kirki ta kasa, kanta ne ma yake juyawa a gurin, dishi-dishi! take kallonsa har ya karaso inda take zube!
Ya tsugana kusa da ita, sai tayi saurin janye jikinta, ya sha kunu; tare da matsawa jikinta, ta sake janyewa tana watsa masa mugun kallo!
Mahaukaciyar dariya yayi! ya cigaba da lasar lebansa, yana bin sassan jikinta da wani irin kallo na tsantsar sha’awa! Hannu ya kai jikinta, a zabure! ta fitar da hannu ta bashi kyakykyawan mari a fuskarsa! ko gezau! beyi ba sai dai yaransa da suka zabura! sukayi kanta!
Ya daga musu hannu da basu umarnin matsawa baya.
Suka matsa can nesa suka bar shi da ita, zaman dirshan yayi a gabanta ya mika mata tafkekiyar fuskarsa dake cike da kasumba! yace. ” Idan hakan yana miki dadi ki sake aikatawa.” Ya fada yana sake tura mata fuskar.
Tsaki mai tsayi taja! ta matsa nesa dashi! ya rarrafa kan gwiwarsa ya cimma inda take! kafafunta dake daure da takalmi ya tsirawa ido, babu abunda yafi tafiya dashi irin shara’ban kafafunta, ya kai hannunsa gurin yana shafawa da lumshe ido, janye kafarta tayi da fadin.” Allah ya isa!!
Ya bude idanuwansa da suka rikice! da zazzafar sha’awarta!
“Ni kikewa Allah ya isa.”? yafada yana nuna kirjinsa.
Ba ta amsa ba, wani irin kallon banza take mai, ya lumshe idonsa ya bude da fadin.” Ina sonki saboda kinyi min, ban ta’ba amfani da mace na maimaita ba, amma gani guda da nayi miki naji cewa kece zaki zama mahadin rayuwarta, shekaru sun ja ya kamata ace nima na ajiye k’wai a duniya kece zaki zama uwar ‘ya’yana, kinzo hannuna babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake.”
Maganganunsa suka dinga amsa kuwwa! a kunnanta, ta tsira masa ido tana mamakin furucinsa, kallonsa kawai take ta rasa yanda zata fasaltashi, shi ba mutum ba ba aljan ba.
Ya mike tsaye a kanta! saurin kauda kanta tayi gabanta na lugudan duka!
Blet din dake daure a kugunsa ya fara kokarin kwancewa, tayi saurin tashi tsaye! dariya ya fashe da ita, kafin ya cire blet din ya jefar dashi ya zame wandon…………”Innalillahi- wa’ina ilahi raji’un! abinda ta ambata kenan, ta rintse idonta da karfi! tunda take bata ta’ba ganin tsaraicin namiji ba sai a kansa, yanda yake mara fasali to hakama gabanshi yake tamkar na mahaukacin doki!!
Wandon ya mayar jikinsa, yana kyalkyala dariyar hauka kafin ya fizgo kafadarta! fuskarta ya rike a cikin tafin hannunsa, ta rufe idonta gam! bata son kallon mummunar fuskarsa.
“Ina fatan kin shirya zama tare dani! masoyiyata nayi miki alkawarin baki dukkan wani jin dadi na duniya! gwarzo ne ni akowane fanni! na tabbata cewa ba za kiyi nadama da kasancewarki a tare dani ba.”
Zuciyarta ta dinga tashi sakamakon warin bakinsa, fuskarta ta fizge! da karfi ta matsa can gefe tana numfarfashi! yawu ya cika mata baki! yana zuwa gurin da take ta fesa masa yawun a fuskarsa!
Ya sanya hannu ya shafo yawun yana lashewa! amma kuma fuskarsa ta rikide da alama yaji haushin abinda tayi masa.
Sai da ya lashe yawun tsaf! sannan ya kalleta, ta tsorata da yanayinsa, sai ta sunkuyar da kanta, a kausashe! yace.” Wannan shine na farko kuma shine na karshe kada ki sake maimatawa idan ba hakaba zan ladabtar dake.
Ta cire tsorosa da fadin.” Wawa!! kafara ladaftar da kanka kafin ka ladaftar da wani.”
“Wawa!! kalmar tayi mai ciwo! sosai a ransa sai kawai ya dingi maimaita kalmar a fili yana zagayeta, ta dinga binsa da kallo duk inda yayi, ya shammaceta yasa mata kafarsa ta fadi a kasan a gurin! turmusheta yayi ya danneta iyakacin karfinsa! bakinta yake kokarin sumbata tana kautar da kai yana bin duk inda ta nufa, be fasa maimaimata maganar ba! suka dunga bugawa! domin duk yanda yaso hada baki da ita ya gagara! ta gumtse bakinta gam!!! sai ya zama kamar mahaukaci sai rawar jiki yake babban burinsa yaji yana shan bakinta……………..Ba zato! ba tsammani! yaji saukar kibiya a gadon bayansa!!
Ya gantsare! tare da zabga ihu!! a zabure! ya mike tsaye! ya fizge! kibiyar ya jefar jini ya fara tsiyaya! tashin hankali kenan! waige-waige yake a gurin yana mamakin yanda akayi hakan ta faru.
Cikin zafin nama! ya mikar da ita tsaye sai numfarfashin wahala take, ya rike hannunta katamau! yana sake dudduba gurin!………………!
Wani abu dake daure a hannunsa ya murza! kafin ya kirayi yaran sa! kaf! suka kewayeshi! sai dai ganin jini na tsiyaya a bayanshi ya firgitasu! a garin ya akayi hakan ta faru!
Ya akayi ogansu ya bari aka cimmasa irin haka? a tarihin rayuwarsa kaf babu wani mahalukin da ya ta’ba fitar masa da jini sai zuwan wannan matashin saurayin lallai akwai wani abu da yake shirin faruwa!