GOJE 23 and 24
Wani irin nishi! yake yana zazzare idonsa! shi kansa yayi mamakin al’amarin, yana da suddabaru! iri-iri! ya akayi har yaron ya samu damar ganin inda yake tare da samun damar harbinsa da kibiya!!
Sai kawai ya fasa ihu!!! ya dubi abunda ke daure hannunsa yana wasu irin surutai! ya sake murza abun! yana sambatu! gurun yayi tsit! babu mai kwakwkwaran motsi a cikinsu, domin sun shiga rud’ani da faruwan wannan al’amarin!!
Sautin muryarsa ne kawai yake tashi a gurin, yana wasu irin maganganu!…………..Can kuma sai haushin karnkuna! ya maye gurbin maganarsa, Tsit! yayi gabansa na wani irin fad’uwa!!
Hankalinsu ya kai kololowa gurin tashi!! duk suna tsaye sun kasa tabuka! komai ya zabura! da karfi yace.”Tsayuwar me kuke ba zaku ba zama ba har sai ya cimma na.”
Da sauri suka rarrabu a cikin dajin suna neman inda yake..
Yana tsaye! a gurin sai kace dasashe! har yanzu kuma hannuta yana rike a hannunsa ya rike tamau!!
Haushin karnukan! suka cigaba da kusantowa inda yake! da saurin gaske ya fara kokarin janta tana turjewa! kawai sai ya dauketa ya sa a kafad’a, ya riketa da kyau! da niyyar neman mafaka! taku daya yayi yaji saukar wata kibiyar! ya gantsare! tare da sakin ihu!! amma duk da haka bai sauketa ba.
“Ni ne GOJE!!! mugun! makangari sai kuree! Ni cinkun! naci garina kuma ni ke zuwa garin wasu yaki!! kandagarki kurmar dutse! mugun makangari sai kureee!
Sautin maganarsa ya cika dajin gami da kunnuwansu.
Ya juya gabas kudu yamma arewa! domin hasashen inda maganar ke fitowa, bashi da tabbacin gurin, kawai sai ya umarci sauran wa’inda ke tare dashi cewa su tashi bomb a kowanne sassa na gurin!
Hakan ne kuwa ya faru tashin bomb! sukayi a gurin kowane sassa a dajin ya rikice! da hayaki! wannan damar ya samu yayi dirar mikiya! a gabansa! alokacin da yake kokarin neman mafaka.
Kallon kallo aka fara! Zinat kam ganinsa ya sanyata sauke ajiyar zuciya ta shiga godewa Allah!!!
Ido ya tsirawa! hannunta dake cikin nasa. wata kibiyar kishi ta sokeshi! cikin hargagi! yace.”Sakar mata hannu ko na sheka da kai barzahu”!!
Ya tsira masa jajayen idonsa kafin ya fashe! da dariya ya sake rike hannunta da kyau! Yace.” Kai ne dan iskan da kake ganin ka isa kayi gogaggaya dani ko.!
Yace” Eh ni ne UMARU! kuma ni zan kawo karshen ta’addancinka.”!!!
Kaifaffar wu’kar dake rataye a jikinsa ya cire ba tare da zato! ba ya datse! masa hannu wanda yake rike da nata! hannun tun daga kafada har kan yatsu ya fadi a gurin yana wutsil-wutsil, jini kuwa sai tsartuwa yake! ya durkushe! a gurin, yana wani irin ihu!!!!!!
Kafin kice kwabo! kaf! kowa ya hallara a gurin, ganin ogansu a durkushe! babu hannu ga jini na zuba ya zaburar dasu! sukayi kansa! sai yayi gaggawar soka wu’ka a wuyan ogan nasu!!! Uban daba! ya sake rikicewa! domin bai shirya mutuwa ba, da hannu yayi wa yaran sa alama cewa su ajiye makaman dake hannunsa, sukayi yanda ya umarcesu!
Ajiye makamansu keda wuya suka fara jin jiniya alamun jami’an tsaro sun shigo gurin!!!! Uban daba! hankalinsa ya sake tashi, babu shakka ya san ya shiga hannun hukuma k’aryarsa ta kare! sai kawai yayi kwance-kwance ya shammaceshi! wani wawan duka ya sakar masa a gwiwarsa!. dukan ya shigeshi! sosai yayi taga-taga! zai fadi wannan damar ya samu ya k’wace! daga hannunsa a sukwane! ya bar gurin cikin wani irin gudu na ceton rai! sauran yaransa suka rufa masa baya………..!
Zubewa yayi k’asan gurin ransa a masifar bace! kwata-kwata bai so hakan ta faru ba, amma ba komai tunda har ya samu nasar raba shi da hannunsa guda, watarana zai samu babbar nasara a kansa!
Tsinin bindiga! yaji a saman kansa! da sauri ya bude idonsa sai kawai yayi arba da zaratan! sojoji da ‘yan sanda! sun zagaye shi kowanne ya saita shi da bindigar dake hannunsa……….”Babban cikinsu shine yayi magana .”You under arrest.”! Hannuwansa ya daga sama cikin bin umarni, suka d’aura masa zabgegiyar tsar’ka! kafa da hannu suka sa key suka kulle, kafin su mikar dashi tsaye….!