GOJE 7 and 8
FREE PEGE
7&8
Banyi tsammanin rubuta wannan littafin a kusa ba, asali ma nayi wa kaina alkawari cewa na daina sakin littafi sai na kammala, amma cikin ikon Allah ya nufe ni da fara rubuta wannan littafin ba tare da nayi tunanin hakan ba, ina rokon Allah ya bani hakuri da juriyar rubuta abinda za’a amfana dashi, sannan ina mika godiya ga dubbanin masoyana wanda na sani da wanda ban sani, hakika duk wanda Allah yayiwa baiwa ta jama’a dole ya gode masa, babu abunda zance da masoya sai godiya da fatan alkairi, sannan a cigaba da hakuri da yanayi na rayuwa, koda zanyi wa wani laifi a bisa rashin sani to ina neman afuwa馃檹馃徎 d’an adam ajizi ne, ina fatan zaku bibiye ni a wannan littafin nawa mai suna a sama, ku bani hadin kai sannan ku bini a sannu a hankali domin isar da sakon dana dauko, #500 kacal zaku biya domin karanta cikakken labarin.
WANNAN NAKI NE
(AUTAR MANYA)
A cikin marubuta ke ta dabban ce a gurina馃馃徎馃グ
Jin kukanta yake har tsakiyar kansa, koda can baya son ganin tana zubar da hawaye ballanatana yanzu da ta riga ta zama garkuwa a tare dashi.
Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo tare da rike kafad’unta, hannu yasa ya share mata hawayen dake zuba a saman fuskarta, ta rike hannunsa da fadin.” Ka bari nayi kukan domin shi kadai zanyi na samu sassaucin abinda nake ji a cikin zuciyata.”
Ya girgiza kansa da fadin.” Ke kin san bana son zubar hawayenki Aysha me zai sanya ki kara tayar min da hankali bayan wanda nake ciki.”
Ta tsira masa idanuwanta wanda suke cike da ruwan hawaye ” Me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa ka dauki laifi kacokan ka dora a kaina bayan idan adalci a za’ayi kaine babban mai laifi dangane da faruwar wannan al’amarin.”
Girgiza kansa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin zafi da k’yar ya iya magana.” Bani da laifi Aysha ba zan haifi d’a a cikina na lalata shi ba, ba zan gaji da fadi miki cewa tarihi ne yake maimaita kansa.”
Ranta ya ‘baci da jin furucinsa, a duk sanda zai fadi wannan kalmar akan wannan al’amarin sai taga kamar akwai rashin adalci a cikin maganarsa.
Tana kokarin magana, Safa ta shigo da sallama a bakinta, suka amsa tare da bin ta da kallo har ta karasa inda suke tsaye. fuskarta kadai zai nuna maka cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tare da ita, ba ita ta haifi Yarinyar ba amma tafi kowa shiga tashin hankali da rashinta.
A raunane ta kalleshi da fadin.” Ranka shi dade har yanzu babu wani labari ko.”?
Kanshi ya daga da fadin.” Babu wani labari Safa watakila ma yarinyar nan bata raye domin duk iya binkice anyi amma ba’a samu wani labari mai dadi ba.”
Kuka ta fashe dashi, ta nemi guri ta zauna tare da rufe fuskarta da tafikan hannayenta.
Ganin tana kuka yasa Aysha da sauri ta kama hanya domun fita bata so duk su lalace a gurin koke-koke domin mutukar tana kallon kukan Safa to itama zata iya taya ta.
Karo sukayi da juna, Aysha kanta a kasa yake shiyasa bata ga shigowarta ba, Maijidda ce matar mijinsu, da ya aureta bayan shekara masu yawa da suka wuce.
Kasancewar basa shiri da juna yasa tayi saurin kauda kanta ta wuce, ita kuma hamshakiyar ta bita da wani irin kallo kafin ta ta’be bakinta cikin wata irin tafiya ta isa da ta’kama tayi sallama a falon.
Shi kad’ai ne ya amsa sallamar Safa har yanzu kuka take yana tsaye ya gaza rarrashinta shima da zai samu yayi kukan da yaji sassauci a zuciyarsa.
Wawan kallo takewa Safa kafin tace.”Ke a ganinki hakan kauna ce? kullum baki da aiki sai kuka uwar data haifi yarinyar ma har ta fiki dauriya Safara’u kuka bashi ne mafita ba.”
Safa ta dago kanta tana kallonta da mamakin furucinta, za tayi magana kenan, Yace.” Abinda nake ta so su fahinta kenan yanzu ita kanta Ayshan ta gama nata ta fita, na fada masu cewa addua itace abinda ya cancanta.
A tausashe tace.”Hakane ranka ya dade shiyasa ko kadan ban zubar da hawaye na akan wannan al’amari ba, abinda nayi shi ya cancanta, ya kuma kamata, tun ranar da al’amarin ya faru na sanya almajiran mahaifina suyi saukar al’kur’ani na tsayin sati guda, da izinin Allah yarinyar nan tana hannu nagari za kuma ta dawo gida cikin aminci.”
Safa ta watsa mata wani irin kallo na zargi kafin ta tashi tare da kama hanyar fita.
Sunanta ya kira ta juyo tana kallonsa babu walwala ko ta kwabo a fuskarta.
Yace.”Kada ki cigaba da wannan kukan bashi da fa’ida ko kadan addu’a zakiyi kinji ko.”
Ba tace masa komai ba ta fita ta basu guri, kai tsaye sashen Aysha ta nufa, ta sameta tare da babban yaron su wanda suke kiransa da magajin Sarki.
Tana shiga ya mike tsaye yana mata barka da zuwa, ta zauna kusa da ‘yar uwata kafin ta bashi umarin zama.
Ya zauna kasan kafafunsu, a nutse yace.” Mommah don Allah ku kwantar da hankalinku bana so naga daya daga cikinku na zubar da hawaye ni nayi imani da Allah da manzon Allah yarinyar nan tana hannu nagari da yardar Allah zata dawo gida cikin koshin lafiya.
Aysha bata iya magana ba, Safa tace.”Babana ina mamaki idan naji kai da mahaifinka kana maganar mu kwantar da hankalinmu, ta ina hankalinmu zai kwanta? a cikin wannan yanayin yarinyar nan sace ta akayi kuma akwai sanya hannun makusanta bana shakka a cikin maganata.”
Yace.”Hakan tana iya kasancewa amma Mommah kada ki manta fa yarinyar Zinatu bata jin maganar kowa kuma a daran da al’amarin nan zai faru gabadaya sai da kuka hanata fita amma saboda rashin tarbiya ta tsallake maganarku to me zai sanya hakkinku be bibiyeta ba.”
Shuru sukayi domin kuwa babu mai bakin magana a cikinsu, abinda ya fada gaskiya ne, yarinyar ta fita zakkah a cikin zuriarsu, sai kuma Allah ya jarabcesu da tsananin sonta, shi kansa maimartaba wato mahaifinta baya son laifinta, ko kad’an duk da ya san abubuwan da take na rashin kyautawa a masarautar duk zafinsa baya iya tsawatar mata, sai ‘yan uwanta mata dake gidajen auransu suke tsaye a kanta, wani sa’in su din ma bata saurara musu rashin kunya take musu kuma ta kwana lafiya, babu wanda take shakka sai shi Magajin sarkin, shima a bayan idonsa zaginsa take tana fadin be isa ya hana rayuwar jin dadi tun bayan dawowarta daga kasar waje bayan ta kammala karatunta ta dawo da mugayen dabi’u irin na turawa, duk wanda ya nuna mata kuskure akan abinda take cewa zai shafi masarauta da martabar mahaifinta sai ta d’aura gaba dashi, halin da ake ciki shi kansa Magajin sarkin ba tayi masa magana saboda yana tsawatar mata akan abubuwan da take na rashin tarbiya, jin kade – kade sanya matsatsun kaya bayan baiwar da Allah yayi mata na qira, yawace-yawacen pary cloub club babu inda bata shiga tayi b’arna da kudi da famkama da manya motoci ta fito babu abunda ya dameta.
Da yawa mutane ba sayi mata kallon cikakkiyar mace saboda mummunan dabi’unta. Don akwai lokacin da wani babban malami ya nemi ganawa da maimartaba akanta, suka tattauna sosai maimairtaba ya fahimceshi ya san me kaunarsa shine zai zo har gabanshi ya fahimtar dashi abunda ya shige masa duhu, a lokacin ya tashi tsaye a kanta, kuma ya gargadeta kan cewa mutukar bata sanja hali ba to zaiyi mata aure duk wanda yayi ra’ayi, hakan ya tsorarta da ita, tayi sanyi na kwana biyu amma kwanaki suna turawa ta cigaba da abinda take, Gabadaya sai ya dauki al’amarin ya jinginashi a matsayin jarabta, abin na damunsa mutuka amma ya rasa me yasa baya son bacin ran yarinyar, Dan uwanshi, Abbas wanda yake Waziri a gareshi ya bashi shawara kan cewa aurene kadai abinda zai daidaita nutsuwar yarinyar saboda haka shi zai umarci babban yaron sa domin yazo su fahimci juna, maimartaba yaji dadin shawarar dan uwansa.
Koda Taufiq ya sameta domin bin umarnin mahaifinsa rufe ido tayi taci masa mutunci harda zagi kamar ba jininta ba, aikuwa ya fusata! ya gaggaura mata mari hade da farfada mata mumunan magana, “Bani da ra’ayi auran mace mara tarbiya irinki umarnin mahaifina nabi har nazo neman auranki saboda haka wallahi ko ba dazi rasa mijin aure ba zan aureki ba shashaha mara hankali kawai “
Bata saduda ba tana kuka tana zaginsa, Magajin sarki ya samu labarin abinda tayi wa abokinsa ya shiga har dakinta ya zaneta da belt ya fito yana huci! Gimbiya Aysha na zaune a falo yazo ya wuce ba tace masa komai ba.