GOJE 7 and 8
Washe gari ta hada kayanta kaf ta koma sashen Safa, itama anan din bude mata wuta tayi ta nuna mata kuskuranta, kafin ta bar sashen sai da tayi mata rashin kunya tasa wata baiwa ta daukar mata akwatin kayanta ta nufi sashen Maijidda, a maimakon ta nuna mata kuskuranta, sai ta hau rarrashinta ta nuna mata cewa itake da gaskiya kuma ba zata bari ayi mata auran dole ba, a takaice dai da sanya hannun Maijidda komai ya lalace! itace kuma ke daure mata gindi tana iskanci iya son ranta.
To wannan dalilin yasa ita Ayshan take ganin harda sa hannunsa dana matarsa gurin lalacewar yarinyar, amma tun sanda al’amarin ya faru ya dauki laifi ya dora mata, kullum idan zai budi baki magana daya yake fada (Tarihi ne zai maimata kansa) tana jin bala’in haushin wannan magana, ta san a lokotan baya tayi sharafi amma abinda tayi be kai wanda ita yarinyar keyi ba, dalili iyayenta da tayi rashinsu a halin yanzu a tsaye suke a kanta, abunda tayi be kai wanda ‘yar cikinta keyi a yanzu ba, ita dashi suka san hakan, amma idan ya tashi magana saboda rashin gaskiya a gaban kowa fadi yake abinda yarinyar take gado ne don haka itace sila akan faruwar al’amarin.
Ta kalli Safa bayan fitar yaron nasu, tace.”Duk ranar da Maijidda ta sake magana al’amarin nan sai tayi data sani domin duk irin abinda take aikatawa ina fahinta na gane itace ke zugashi yana daukar laifin yana dorawa a kaina.”
Safa ta girgiza kai da fadin.” Eh ba zan hana ki ba ni kaina zan tayaki cin mutuncinta domin ta kai ni bango abin mamaki kuma har yanzu laifinmu yake gani, akan hakan ta shigo ta sameni cikin halin damuwa tana min maganar banza ya goya mata baya, ta kaini karshe duk sanda ta sake min katsalandan a gabanshi zan taka mata burki sai dai duk abinda zai faru ya faru.”
Tace.”Safa ba zaki iya dasu ba, ki kyaleni ita dashi duk zanyi maganinsu, nagaji da wannan abun zanyi magani.”
Zuciyarta tayi sanyi da jin furucinta, ba tun yau ba, ta san halin Aysha ba kanwar lasa bace da sannu za tayi maganinsu gabad’aya.
Lokacin data farka garin yayi duhu, kuma bai kunna fitila ba tun bayan daya gabatar da sallahr isha’i sai ya kishingida a gefenta, saboda ita ya sanya bai jagoranci yaran sa farauta ba, sai kawai ya turasu daga shi sai ita ya rage a gurin, sai kuma kukan ‘kananun dabbobin dake tashi.
Cike da tsananin tsoro! da firgici! ta mike zaune tana lalube a gurun, masifaffan tsoro ne da ita, rarrafe ta fara ko’ina zata oho! yana kokarin tashi zaune ta afko kansa, fuskokinsu suka hadu, bakinta ya hadu da nasa, lokaci guda numfashinsu ya had’u! da sauri ta kautar da fuskarta, ta danne kirjinsa da hannu tana kokarin barin jikinsa, ba tare da wata manufa ba ya zuba dukka hannuwansa kan kwankwansonta, gefe guda ya ajiyeta, ta sake yunk’urin barin gurin domin kan ciyayi a ajiyeta tana kuma jin tsoron wani mugun k’waron ya cijeta, kafarta daya ya rike, can kasan makoshi yace.” Ki samu nutsuwa.”! kafarta ta fizge, da rarrafen ta lalubi daddumar ta zauna tana ya mutse fuskarta, gabadaya cinyoyinta sun dauki kaikaiyi da azabar zafi.
Fitila ya kunna yana kallonta, sai yamutse ya mutse take, mikewa yayi ta kalleshi, yana kokarin barin gurin, da sauri tace.” Ina zakaje.”?
Bai juyo ba domun ji yayi tambayar tayi kama data rainin hankali sai kace uwarsa tana masa magana gatse-gatse! Ya cigaba da tafiyarsa ba tare da ya amsa maganarta ba, kallonsa ta dinga yi tana mamakin girman jikinsa dogo mai garin jiki yana yanayi da jarumin kasar hindu ( Parbahs bahubali) idonta a hanyar da yabi gabanta sai faduwa yake, can taji wani irin kukan dabbah! a bayanta, a zabure! ta juya tana zare ido! jin kukan na kara kusanto inda take yasa ta kurma ihu! sai ta fara jan gwiwa tana waiwayenta bayanta.
Jin ihunta ya tashi hankalinsa da saurin gaske yasa bakin kokon dake hannunsa ya kamfaci ruwan dake gudana ya juyo da saurin gaske, me zai gani ita ya hango a gigice! tana rarrafe tare da d’aga masa hannu, haushi ta bashi, bega abun gudu a gurin ba, tuntuni sun saba yada zango a gurin, babu wata dabbah mai cutarwa da ke zuwa gurin. saboda su kansu dabbobin sun gane gurin, basa tunkarar zuwa sun san idan sun shiga basa fitowa cikin dadin rai.
Koda ya k’arasa inda take sai kawai ta rike masa kafafu tana karkwarar jiki, “Allah yasa tsakanina daku azzalimai macuta.” Kalmomin da suka futo daga bakinta kenan ta nayi tana dukan gwiwarsa harda cizo.
Gabadaya ta kanainayeshi, tana dukansa, kuka take sosai! bece mata komai ba har sai da ta gaji da kukan ta cikashi, ta daga kai tana kallonsa, ya cije baki kamar yanda ya saba idan zaiyi magana “Na fahimci duk gidan da ki kaka fito babu tarbiya, bana shiri da mara kunya ba kuma na san raini! meye laifina anan? ina iya kokarina akanki kina zagina saboda kina takama da mulki da sarauta ko.”?
Hannu ta daga masa da fadin.” Kaga malam ya isa haka kawai ni ka daukeni ka bar gurin nan dani.”
Ya girgiza kansa kamar koda yaushe idan zaiyi magana yace.”Ba zaki samu hakan ba, yanda kika rarrafo da gwiwarki hakanan zaki biyo bayana.” yana gama maganarsa ya fizge kafafunsa ya barta a gurin.
Da kyar tayi yunkurin tashi tsaye, ta daga masa hannu da fadin.” Don Allah kada ka tafi kayi hakuri ka dawo kafafuna sunyi tsami ba zan iya tafiya mai tsayi dasu ba.”
Yana jin maganarta be juyo ba ya cigaba da tafiyarsa, yana so ya fara koya mata hankali tunda ya fuskanci bata da mutunci.
Takawa take tana ciccije baki, hawaye kuwa sai karakaina yake a fuskata, abubuwa da yawa sunyi mata dabaibayi, ciwo! tsananin fargaba da tashin hankali bakar azaba da yunwa ta rasa da wane bala’i za taji.
Tun tana hangensa har ta daina, ta dinga tafiya cikin ciyayi tana jin saukar kwarika a kafafunta, ta riga ta saduda ta barwa Allah da wannan masifar da take ciki gwara wata dabbar ta cinyeta.
Ya kai minti ashirin da isa amma shuru babu labarinta, a jikinsa yaji akwai wani abu tunda babu wata tazara mai tsayi tsakaninsu da bakin kogin.
Bayanta yabi yana haske fitilar hannunsa, yaci tuntube da ita, kwance kafafunta sun rufta cikin wani rami da alama na wasu dabbobin ne, sai kici-kici take tana kuka, hannunsa ya mika mata, ta rike da kyau! yasa karfi ya fizgota!
Ajiyar zuciya suka sauke a tare, be jira komai ba, ya sunkuya tare da juya mata baya, kafira!馃槀 bakin rashin kunya ya mutu, tana zazzare ido ta haye bayansa ya mike tsaye da ita, hannunta tasa sosai ta matseshi, sai ajiyar zuciya take, shi kam cakumar da take masa ta sanyashi shiga tashin hankali wanda sai yayi shekaru be shiga irinsa ba, huci kawai yake yana cizan lips dinsa,
cikin mawuyacin hali suka isa gurin,
Yayi gaggawar sauketa, tayi kwance a gurin tana fitar da numfashin wahala, shi kam can gefe ya matsa tare da juya mata baya, matsalarshi guda a yanzu halin da ya shiga, shigarsa a wahala amma fitarsa nada wuya yakan yi kwana da kwanaki kafin yanayin ya bar jikinshi.
Ga wa’inda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu biya 1k domin samun damar karanta littafi biyu
#500 via 0543282124…Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number… 07084653262……..Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number….