GOJE

GOJE 9 and 10

Ya dauki rigarshi data cillar masa ya rufa mata a jiki, baya so yana ganin abinda zai tayar masa da hankali.

Ai da sauri ta cire rigar ta cillar da ita can tana ya mutse fuska, zaune ta tashi tace.”Idan zaka kwana kana rantsuwa cewa kai ba dan ta addah bane ba zan yarda ba wallahi.”

“Ke baki isa nayi rantsuwa a kanki ba, kuma idan kika sake kirana da wannan sunan zan nuna miki ta’addanci na.”!
Yanda yayi maganar shi ya tsorata sai tayi shuru amma bata fasa yi masa kallon banza.

Ya dauki rigarsa data jefar yana girgiza kansa ya rasa wace irin yarinya ce me manta alkairi ina laifin wanda ya suturta ka.

Rigar ya sanya a jikinsa, can kasan makoshi tace.” Kazami kawai.” Yaji abinda tace amma be tanka mata ba, ya juyo, tayi saurin dauke kanta, janyeta yayi kan daddumar ta fadi kasan gurin, ba tare da ya saurareta ba ya bar gurin da daddumar a hannunsa.

Ta ciji yatsa tana bin bayansa da mummunan kallo.

Daya daga cikin yaransa ne ya karbi daddumar ya wanke tas ya shanya kan wata bishiya.

Ya umarcesu da suyi shirin fita shima tare zasuje don baya tsammanin zai zauna da yarinyar tana ‘bata masa rai bayan masifar data jefashi a ciki.

Be saurareta ba ya hada kan tawagarsa suka fice ba tare data sani ba, hankalinta ya kai kololowa gurin tashi, lokacin data fahimci ita kadaice a cikin dajin sai ta raina kanta da wayonta, tana kuka ta kama hanya ta cire tsoro da fargaba kokarinta ya za’ayi ta fitar daga kanta daga cikin masifa.

Aikuwa kanta ne ya juye! a maimakon tayi baya sai ta dinga gaba, tana kutsawa cikin dogwayen bishiyu na kuka da tsamiya nan ta dinga arba da manya manyan birai iyaye da ‘ya’yansu, hankalinta ya tashi, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, gwagwgwan biri! ido sukayi da wani kato ya tsufa sosai! yana zaune duguzun-duzugun jikin wata narkekiyar bishiyar kuka!

Da baya da baya ta farayi kafin ta juya a sukwane tana falfala gudu hade da kiran sunansa GOJE!! shi kuwa Gwaggon birin nan dariya yayi da ya fahimci tsoronsa take sai ya kudiri aniyar tsokanarta, ya fara bin jikin bishiyu yana tsalle yana mata dariya har ya dura a gabanta.

Zubewa tayi tana daga masa hannu yawun bakinta ya bushe “Don Allah kayi hakuri! wayyo Allah na wayyo na shiga uku kuka ta dinga yi hawaye da majina sunyi kaca kaca da fuskarta.

Daya bayan daya suka kewayeta iyaye da kakanni! da alama sassaninsu ta shigo bata sani ba.

Kanta ne ya dinga juyawa a gurin kafin ta fadi, suma tayi, ba tare da bata lokaci ba wannan dattijon birin ya dauketa yasa a kafada, kataf-kataf ya fara tafiya da ita iyalinsa suka rufa masa baya.

Dabaru irin nasu sukayi mata ta dawo hayyacinta koda ta bude ido ta ganta a tsakiyarsu, sai ta mayar da idonta ta rufe jikinta sai karkarwa yake, su kuwa suna zazzaune sai cin manya manya ayaba sukeyi suna gurnani da alama zantuka suke a tsakaninsu.

Sai gefin magariba suka dawo, hankalinsa ya tashi lokacin daya duba sama da kasa be ganta ba,

Dajin ya shiga yana yana sasssare mattatun itatuwan da suka cika gurin, ya fito da sarewa yana busawa tare da cigaba da ratsa cikin dajin.

Zumbur! ta tashi zaune jin busar sarewar na kusanto gurin da suke, daga can nesa ya tsaya yana hango tawagarsu tana tsakiyarsu sai kace ‘yar tsana saboda kankanta.

Kai tsaye gurin ya nufa yana cigaba da busa sarewar dake bakinsa, tsakiyarsu ya shiga yayi wani irin tsugo gaban dattijon birin nan yana me cigaba da busa abinda ke bakinsa,

Murmushi yayi ya dora hannunsa me cike da gashi da farata zako-zako a hannunsa a saman kansa, kafin ya cire ya nuna masa ita, yana gurnani!

Kansa kawai ya girgiza ya nufi inda take, hannu ya mika mata ta mike tsaye kafafunta sai kyarma! suke a haka suka bar gurin.

Saboda fargaba da mutuwar jiki yasa gabadaya kafafunta sukayi sanyi da kyar take iya jansu, bakinta ya mutu murus! tsabar tashin hankali binsa kawai take duk inda yaja ta, b’angaransa kuwa yana sane yaki goya ta saboda tayi bala’in bashi haushi, ya tabbata idan wata dabbar ce sai yasha mutukar wahala kafin ya samu damar fito da ita daga cikinsu idan sun barta da rai kenan.
Wannan Gwaggon birin sun saba dashi sosai duk sanda zasu shigo farauta dajin basu da matsala dashi da iyalinsa, wani sa’in ma har kyautar ayaba mai yawa suke basu.

Cikin mawuyacin hali suka karasa gurin da suka yada zangon ya jefar da ita ta fadi kasan gurin, zaune ta mike tana kallonsa ya juya mata baya gabadaya jikinta yayi sanyi domin ba tayi tsammanin zata cigaba da rayuwa ba.

Cikin wani irin amo! taji maganarsa. “Kada ki kuskura ki sake barin gurin nan dana ajiye ki domin kuwa yin hakan na barazana da rayuwarki, babu inda yake da tsaro a cikin dajin nan fiye dana nan gurin, idan kika sake fita yawo to ba zan sake yunkurin ceto rayuwarki ba, yau kwananmu biyu sai kuma munyi sati guda kafin mu koma gida don haka ki kiyaye rayuwarki kibi umarnina kuma mutukar kina bukatar cigaba da rayuwa.”

Kuka ta fashe! dashi ra rarrafa ra rike kafafunsa, ” Kada kace haka mana! ka tausaya min a matsayina na mace mai rauni ka fitar dani daga wannan dajin ni ba zan iya sati a guda a cikin wannan tashin hankalina ba, wallahi komai kake bukata mahaifina zai maka ka taimakawa rayuwata.”

Yanda take kuka tana rokonsa sai ku dauka mutuniyar kirki ce, haka take dama a duk lokacin da zata ganta cikin wata ukubar takan gigice ta saduda amma daga an kwana biyu sai ta koma baya.

Kafafunsa ya cire ba tare daya ce mata komai ba ya bar gurin, Hakan da yayi ya ‘bata mata rai! sai kawai ta kullaceshi a ranta, ta kuma kudiri aniyar wani abu a ranta zata tayar masa da hankali wanda zai daga
Masa hankali dole ya kaita gaban iyayenta……..

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button