GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 19 & 20
Zune yake a cikin mota fuskarsa rufe da farin gilashi ba ƙaramin kyau yayi ba,
Wace mota ce ta shiga gabanmu ?” tambayar da ya watsawa securities ɗinsa kenan drivern sa ne yace ” wata yarinya ne a cikin motar inaga batasan ko waye a cikin motar bane yasa basu kauce ba ,
Kamill da ransa ya fara ɓaci yace ” maxa sha gabansu mu wuce waye ubanta ,
Da gudu drivern Kamill ya wuce su Diyana Masifar da take yiwa drivern su ne yasa shi gogar motar Kamill batare da ya lura ba , wani wawan birki drivern Kamill ya doka yana salati ,
Ba shiri Kamil ya buɗe mota ya fito ya nufi gurin motar su Diyana ,
Kai waye dahar zanzo wucewa kasha gabana .
Cikin tsiwa Diyana ta zuge glass ɗin mota zatayi magana taga Kamill ,saida gabanta ya faɗi tayi ƙarfin halin cewa ” kai ɗin waye dazaka tarewa mutane hanya ,
Yana shirin buɗe motar tasu ya figota wani mutum yazo yana cewa ” haba babban yaro ba girmanka bane ka ƙyaleta pls , juyawa Kamill yayi ransa a ɓace tareda ƙwafa ,
saida ya wuce su Diyana suka wuce lol.
suna isa ƙofar gidan da momy ta aikosu ta fice daga motar babu wanda ta kula , bubuga get ɗin tayi ba’a ɗau lokaci ba sai ga mai gadi ya buɗe , cikin sauri ta shige gidan tana sallama kamar ansata dole sai tayi,
mom Khady da yanzu ta fito ta iske Diyana zaune a kan kujera tana kuka ,
Shigowar Afreeda ne yasata maida kallonta ga Afrredan tace ” ƴata mai ya sami kyakyawa ne naga tana kuka ? dariyar yaƙe Afreeda tayi dan ita duk budurin da Diyana keyi a titi dariyama ya bata , momy ƙila batada lpy ne , Afreeda tace ” tana shirin zama akan kujera ,
Driver ne ya shigo da bag a hanunsa ya gaida momy ya miƙawa Afreeda ,
Miƙawa momy Afreeda tayi tare da cewa inji momy tace abaki , oky mom Khady tace tare da karɓa ,
Tayimin bayanin komai .
Diyana ce ta miƙe tare da cewa mom muntafi , haryanzu idanunta basu dena fidda hawaye ba ,
Janta momyn Khady tayi suka nufi bedroom ɗinta ,
zaunar da ita momyn Khady tayi a bakin bed ɗinta, itama ta zauna , fuskantar Diyana tayi kana tace ” daughter na nasan problem ɗinki momynki tayimin bayanin komai so insha Allah zamuyi iya bakin ƙoƙarinmu gurin ganin kin sami farinciki ,
A gidan auranki , share hawayenki .
Share hawayenta tayi tace ” momy na gode ,
Yanzu saura 29 days bikin zaki dawo gidannan nanda 1 week zan fara haɗa miki magani , kinji ?”
Tom Diyana tace ” ta miƙe batare da momy tace ” jeki ba ,
Da kallon tausayi momy ta bita tana girgiza kai .
Bayan Diyana ta dawo palo ta sami Afreeda da Khady a zaune sunata hira cikin farinci ,
Zama Diyana tayi nesa dasu ,
Khady ce ta miƙe ta nufi gurin Diyana , kasancewar sa’ar Diyana ce amma da yake su ba ƙawance sukeyi ba ƴan uwantaka suke ,
Khady ce tayiwa Diyana magana a kunne bansan mai tace mata ba naga Diyana na dariya .
Afreeda ce tace ” sis zomu tafi okay Diyana tace ” ta miƙe Khady tace ” barin kira momy ,
Bayan momy ta fito sukayi sallama tace ” zata kira momy suyi magana.
Suna fita suka shige mota driver ya kaisu gida kasancewar titin babu yawan motoci ,
Alhaji Safiyan ne zaune shida Amena yana waya , bayan ya ajiye wayar ne Amena ta dubeshi tace ” Alhaji maganar kayan auran Kamill lokaci ya ƙarato , gyara zama Alhaji yayi kana yace ” aikuwa wlh inason ayi kamar akwatuna dozin biyu , riƙe baki tayi tana jinjina kai , a ranta tana cewa sai kace zai auri ƴar shugaban ƙasa , Alhaji ne yace ” menna naji kinyi shiru ,
Dariyar yaƙe ta ƙaƙalo kana tace ” to yaushe za’a fara siyayyar ? gobe insha Allah Alhaji yace ” yana washe haƙora ,
Zansa ayau ɗinnan a tanadi komai gobe kawai sai mu wuce london a jirgi , farinciki fall zuciyar Amina sbda koba komai itama zata yagi rabonta .
after 2 weeks Diyana ta koma gidan mom Khady acan ake yimata gyara kama daga tsumi na gargajiya haɗin turaruka da shayin amare tare da kaji ga dilka da halawa da ake yiwa Diyana , abinka da farar mace sai ta koma kamar baturiya .
Wata ranar juma’a suna zaune ita da Khady , Khady na bata labarin wani novels da take karantawa a wattpad suna dariya , taji kira ya shigo wayarta, batasan mai kiran ba hakan yasata ɓata rai ,ta ajiye wayar gefe,
Khady da ta tsaya da karatun ta ɗaga wayar lokacin anyi kira na biyu , ta danna receive ta karawa Diyana a kunne ,
Mai kiran baiyi magana ba haka itama batace komai ba , jin Diyana tayi shiru yasa Khady ƙara volume ɗin wayar ,
Saida aka ɗauki mintuna mai kiran yace ” barka dai amarya bakya lefi zaro ido tayi tanason tuno mai muryar ta kasa tayi iya tunaninta amma takasa tunowa ,
Waye kai??” Diyana tace ” cikin sanyin muryarta .
Mijinki ne .
A ina ka sami number ta karka ƙara kiran wanan layin dan wanan baiyi kamada mijin da zan aura ba ta katse wayar.
Iya ƙolokuwar ɓacin rai Kamill yayi wani uban ƙara yasa wanda yaja hankalin masu tsaronsa dakuma masu yimasa hidima , suka shigo da saur, lpy oga ? suka tambaya a tsorace , idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ya kallesu kana yace ” karku damu kowa ya koma gurin aikin sa zan nemeku anjima,
Haka suka fice jiki babu ƙwari dan kwana biyunnan basajin daɗin ganin shugaban nasu haka .
Yanzu burinsa kawai yaga ankawo masa Diyana a matsayin mata Allah ne kaɗai yasan hukuncin da zaiyi mata , Ya miƙe tare da zagaye ko ina na ɗakin ranshi a ɓace .
Biki ya ƙarato shiri akeyi na musamman fanin momy da dady dakuma fanin iyayen ango ,
satin Diyana ɗaya a gidan momyn Khady yau ta dawo gida , kowa ya ganta sai yai sha’awarta .
Momy ce ta jata zuwa ɗaki , Diyana . momy ta kira sunanta
Na ‘am Diyana tace ” momy ce tace ” shi mijin naki ya taɓa kiranki kuwa ?” a’a momy .
Diyana tace ” kanta a sunkuye , momy tace ” bare har akai ga maganar kuɗin anko taɓɓ , Diyana dai batace komai ba taci gaba da wasa da gezar rigarta , fashewa da kuka momy tayi tana salati , wanan aure shine ake kira da auran dole.
shigowar dady ne yasa momy saurin share hawayenta ta ƙaƙalo murmishin ɗole , tace ” barka da dawowa Alhaji , ywwa dady yace ” ya nemi guri ya zauna ,
Kalon diyana yayi tare da cewa kibamu guri daughter.
Dama abinda takeson ji kenan dan zaman ɗakin ya isheta kasancewarta ba mai son yawan surutu ba ,
Tana shiga bedroom ɗinsu taga Afreeda a zaune tanata kuka ƙara tashi hankalinta yayi ,
Da sauri ta iso kusada ƙa nwar tata tayi ta rungumeta , meya faru ne my sis ? wani kukan Afreeda takuma saki tana cewa ” sis yanzu kin yarda ki auri wanan mutumin sis tafiya zakiyi ki barni , hawaye masu zafi ne suka zubo daga fuskar Diyana ,
Takuma rungume Afreeda sunata kuka .
BAYAN KWANA BIYAR.
Zaune yake kan ƴayataccen bed ɗinsa da yaji tsadden zanin gado , idan nayiwa yarinyar nan haka banyi mata adalci ba koda yake ta wula ƙanta ni , amma duk da haka kamata yayi nayi ruwa biyu , sai tashigo in tada mata da GUGUWAR ZALUNCI na shi kaɗai yaketa zancen zuci , yaci gaba da cewa” iyayenta zasu fahimci wani abun fa…
janyo wayarsa yayi ya danna lambarta da yai seven da no. ring ɗaya ta ɗauka cikin sanyin murya , kwanciya yayi tare da cewa ” barka da wanan lokacin ƴan mata , ywwa dawa nake magana , ƙara duba number tayi tanajin kamar ta gane mai muryar amma tarasa inda tasanshi , fatan masoyinki ne mijin da zaki aura , zatayi magana ya katseta da cewa ” ayimin haƙuri nasan nayi laifi dahar saida lokacin bikinmu ya ƙarato nafara kira ,
Diyana da taji wani sanyi ya mamaye zuciyarta tace ” babu komai karka damu ta lunshe ido kamar yana ganinta , janyo fillo Kamill yayi tare da rungumewa ya daɗa kashe murya , yace ” ya shirye shiryen bikinmu ni yanzu burina inganki kusa dani saboda in nuna miki zallar soyayya dakuma farinciki , Diyana da tayi nisa cikin love ta gyara kwanciyarta dama a kujerar palo take kwance , batasan Hajiya na gefe a tsaye ba tun ɗazu .
Gaskiya nayi sa’a nima ina fatan hakan amma meye na zumuɗi , dole nayi sbda muryarki nasani bansan kyawunki ba koda yake inada tabbacin kyanki shima ƙarshe ne, dariya tasa marar sauti sosai tace ” kaima hakan ai , to yanzu dai nawa kikeda buƙata sbda a halin yanzu zanbar ƙasar sai ana gobe ɗaurin aure zan dawo , cewar Kamill .
Lumshe ido Diyana tayi kana tace “duk abinda ka bada yayi .
Kamill ne yace ” 3 hundred thousand yayi ? eh tace ” cikin farin ciki .
sallama sukayi kana ta miƙe waigowar da zatayi sukayi ido biyu da Hajiya , ko kallon inda Hajiya take Diyana batayi ba , jiyo maganar Hajiya tayi tana cewa ” gulma da ance ba’aso yanzu kuma anzo ana kwarkwasa , wucewa Diyana tayi zuwa bedroom ɗinsu batare da ta kula Hajiya ba jin son lovely ɗinta takeyi kamar zai fasa zuciyarta , shigowar Afreeda yasa Diyana faɗaɗa fara’a tace ” sis yanzu my husband ya kiranj , murmishi Afreeda tayi cikin zuciyarta tace ” hmm ƴar uwata har yanzu bakisan wa zaki aura ba ina tausaya miki dakinsan Kamill zaki aura nasan da kina nan kina rusa ihu inma ba’a kaiki asibiti ba da sauƙi , sis sis me kike tunani a firgice Afreeda ta waigo idanunta cike da hawaye tace ” banason rabuwar mu my sis , Diyana dariya tasa tana cewa inajin kamar nafi kowa sa’a a duniya sbda mijin da Allah yai min zaɓi, hmm Afreeda tace ” tare da kwanciya a gefen Diyana .
Kamill ya turo wa Diyana kuɗi , bayan ta ciro a p o s kasancewar yanzu bata cika zuwa bank ba , dama sunsi komai karɓar kuɗin momy tayi tabata 50k ta riƙe a hanunta , ƙanwar momy data zo daga kano ta tsarawa Diyana haɗaɗen lalle baƙi da ja , ga gyaran gashi da sukaje jiya , ɗinkuna akalla tayi sunkai kala ashirin kuma duba babu marar tsada .
a ƴan kwanakin nan tayi ƙiba saboda kulawar da take samu daga gurin Kamill , suna tsaka da waya yace ” amma baxa’ayi wani event ba ko dan har yanzu ban dawo nigeria ba , my lovely babu abinda za’ayi karka damu cewar Diyana killer smile Kamill yayi yasan yafara sata a layi kafin ya goce ta .