Labarai

NDLEA ta kama kasurgumin mai safarar kwayoyin da ke da alaka da Abba Kyari

Hukumar NDLEA da ke yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi da ke da alaka da DSP Abba Kyari, dan sandan da aka dakatar daga aiki bisa zargin rashawa.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Litinin, ta ce jami’anta sun kama Cif Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wanda shi ne shugaban kamfanin Mallinson Group, bisa safarar tramadol ta naira biliyan uku BbcHausa ta rawaito.

Sanarwar, wacce kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya sanya wa hannu ta ce an kama Mr Ukata ne a filin jirgin saman Legas a kan hanyarsa ta tafiya Abuja.

“Bayan ya kwashe wata da watanni yana zille wa kamu, an kama Ukata, wanda shi ne shugaban rukunun kamfanonin Mallinson Group, a filin jirgin saman Lagos da ke Ikeja a cikin jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja ranar 13 ga watan Afrilu,” in ji sanarwar.

Bincike ya nuna cewa shi ne babban mai safarar miyagun kwayoyi nau’uka daban-daban musamman tramadol hydrochloride mai nauyin kilogiram 120, da 200 da 225 da kuma 250 wadanda aka haramta, a cewar sanarwar.

NDLEA ta ce Ukata yana da kamfanonin yin magunguna da kuma na robobi da yake amfani da su wajen yin safarar miyagun kwayoyi.

Muna ci gaba da sabunta wannan labarin…

 

 

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button