HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

*RANAR ƊAURIN AURE*
Da safe misalin ƙarfe bakwai ƴan uwan momy suka sata gaba wai gashi biki na ƴar fari amma babu wani wasa da akayi , momy da ta jiyosu tace ” ku ƙyaleta karku damu Allah dai yabasu zaman haƙuri kowa ya amsa da amen .
Zuwa ƙarfe goma angama tsarawa Diyana kwaliya ta haɗe cikin material less mai tsada anyi mata ɗinkin riga da sikel ba ƙaramin kyau tayi ba ,
wasu magunguna aka dinga ɗura mata da turaruka momy da momyn Khady suka faɗa mata inda zatayi dasu ,
Zuwa sha ɗaya Kamill ya kirata ya sauka a garin kano , wani irin farinciki takeji na daban , iskar ma da take kaɗata ta ranar ta daban ce ,
[15/06, 6:43 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ????????

*GUGUWAR ZALUNCI*

Page 21 & 22

A yau dubban mutane suka sheda ɗaurin auran Kamill Safiyan da amaryarsa Diyana Sani , ɗaurin auran da yasami halartar manyan mutane ta kowane ɓangare musamman ma ɓangaren mahaifin Kamill , kowa ya sanyawa auran Albarka , Kamill kam bai sanarwa yawancin abokansa ba a cewarsa wanan auren nasa auran hukunci ne sbda yanason tada GUGUWAR ZALUNCIN sa bayan amarya tazo , mahaifinsa duk bai fahimci hakan ba , kayan lefen da aka kawo gidansu Diyana ya girgiza mutane tabbas nera tayi kuka duk cikin kayan babu na 50k momy ma tasha mamaki amma ba’a mamaki da ikon Allah yasata jan bakinta tayi shiru .
Hajiya da tinene sunsha ɗinkin atamfa riga da zani suma ba ƙaramin kyau sukayi ba amma Tinene na gefen Hajiya bata bari tayi nisa da ita .
Bayan sallahar magrib Diyana da Afreeda na hango manne da juna sunata kuka kowacce idanunta fal da hawaye , momy da ta shigo kiran Diyana ta gansu a haka , itama kawar da kanta gefe tayi tana share hawayen daya zubo mata daughter kizo dadynku na nemanki , daga haka momy ta fice , sakin juna sukayi Diyana ta tafi kiran dady .
Da sallama ta shiga palon dady kanta a sunkuye , kallon tausayi dady yayi mata yasan tayi masa biyayya kuma shima yana son ya kwatanta kyautata mata ,
Dady gani , ywwa daughter abinda nakeso kisani aure ibada ne yinayi bari na bari karki maida gidan auranki gurin cin kasuwa kokuma filin faɗa da miji karkiga dan bai baki kulawa kina waje kice inkin shiga ciki bazaki bashi kulawa ba , kizamo mai tausasa murya ga mijinki kizamo mai tausayinsa kizamo mai faranta masa kamar inda kika yimin biyayya Allah yabaki ƴaƴa masu albarka masu biyayya , cikin muryar kuka Diyana tace ” dady ka yafe min.
Dagani kasan ƙarfin halin magana yakeyi yace ” na yafe miki Diyana .
yayi mata umarni da ta tafi , tana tafiya tana kuka wata yayar momy ta jata zuwa part ɗin momy , nan ma nasiha suka yimata mai ratsa zuciya kowa tausayinta yakeji kasancewar labarin auran da akayi mata ,
9:pm motar ɗaukar amarya ta ƙaraso tayi wanka ankuma shiryata jikinnan kamar anyi ɓarin turare , duk inda ta zauna ƙamshi ke tashi sai ta barmusu tsaraba ,
rabuwa da momy ba ƙaramin kuka tayi ba sbda sabo turken wawa , Afreeda gata ga amarya suna riƙe da hanun juna , Hajiya cewa tayi bazataje ba sai daga baya zataje taga gida a nutse ,
sunyi tafiya mai nisa sosai sanan suka shigo anguwar da dadyn Kamill ya siya masa gida , tun daga nesa suka hango gidan shi kaɗai , gashi ba wani ƙato sosai ba amma nera tayi kuka , horn drivern nasu yayi aka buɗe masa get ya shige dasu , yana parking wata ƙanwar momy tace ” fito da ƙafar dama kiyi bismillah , tana fitowa itama ganin tsaruwa da kyan gidan yasata sunkuyar da kai gefen zuciyarta tanajin tayi sa’ar miji , mai kula da ita ,
rungumeta sukayi kai tsaye suka kutsa cikin gidan gaskiya inhar nace zan tsaya misalta kyan gidannan bansan irin misalin da zanyi muku ba ku ƙaddara gidannan kamar irin ginin turai bedrom aka shige da ita aka zaunar da ita akan gado , cigaba sukayi dayi mata nasiha sanan suka sata tayi wanka ta sauya kaya , suka feshe mata jiki da turare sukabi ko ina na ɗakin da turare mai sanyin ƙamshi ,
Sallama sukayi mata , a lokacin ta gane lallai aure ya wuce tunanin mai tunani , Afreeda da ta kwanta jikinta taba kowa tausayi janta sukayi tare da cewa ” yanzu ba’a kwanan gidan amarya kiyi haƙuri kizo muje kiyimata adu’ar zaman lafiya kawai , haka aka janye Afreeda tana kuka suka fice daga ɗakin , kasancewar batada wasu ƙawaye .
Bata gama tsorata ba sai dataga mutane sun watse ita kaɗaice a gidan hankalinta ya fara tashi , miƙewa tayi ta murɗa handle ɗin ƙofar toilet , alwala ta ɗauro sbda batayi magriba da isha ba , tana fitowa ta shimfiɗa dar duma ta tada sallah , bayan ta idar ta kwararo adu’oi ta shafa , lumshe idonta tayi tana mai godiya ga Allah ta ninke dardumar ta koma kan gado ta kwanta kamar wata baby , jin shiru har ƙarfe 10: yasata janyo wayarta ta lalubo lamar Kamill da tayi seven da my blood danna kira tayi , jin tana ring ba’a ɗaga ba tafara tunanin ko lafiya tunda bai saba yimata haka ba .
Ƙara danna kira tayi a karo na biyu nanma shiru ba’a ɗaga ba , ajiye wayar tayi tare da fashewa da kuka dama idanunta sun kuɓbura daƙyar take buɗesu , shiru shiru har ƙarfe sha biyu na dare , lokacin ma bacci mai nauyi yayi gaba da ita sbda gajiyar biki.
Zaune yake a guest hause ɗinsa dake kano , tofa masu karatu ango baya Abuja yana ma kano .
bacinsa yake shara hankalinsa a kwance kamar ba ango ba bashi ya farka ba sai wajen asbha lokacin anata kiraye kirayen sallah daga ma ban bantan masallatai , kasancewar akwai masallaci a gidan yasashi nufar masallacin .
Har akayi sallahar asbah Diyana na bacci ba ita ta tashi ba sai ƙarfe bakwai na safe , a firgice ta sako daga gado tare da nufar toilet tayi brush ta ɗauro alwalah tafara sallah tana idarwa ta koma ta kwanta inka ganta abin tausayi .
Kogin tunani ta shiga to ina my blood tamayar da take yiwa zuciyarta kenan , babu mai bata amsa yasata janyo filo ta rungume tare da share ƴar kwallar data zubo mata.
Wayar ta ce tafara ruri cikin sauri ta janyo wayar ta ɗauka Kamill ne mai kiran hakan yasata gyaran murya , tana duba fuskar wayar taga my sis cikin ƙarfin hali ta kara a kunne tare da cewa” ƴar uwata yakike ? ya momy da dady , Afreeda dake dariya tace ” kowa lafiya dafatan dai amarya na cikin ƙoshin lafiya , normal sis ina lafiya yaushe zaki zo ? zaro ido Afreeda tayi kana tace ” kema kinsan ba barina fita za’ayi ba amma karki damu inanan zanzo cikin satinnan , daga haka sukayi sallama .
tashi tayi tafara zagaya ko ina na palon babu laifi nera tayi kuka kuma ko ina ƙamshi ke tashi ga kayan kallo nagani na faɗa , haurawa step tayi tana mai ƙarewa fentin kallo kai kace ƴar ƙauye , ɗakuna uku ne a saman,
Na farkon tafara buɗewa wani fitinannen ƙamshi ne ya daki hancin ta batasan lokacin data kutsa kai ciki ba ,
Hoton da tagani ne yasata faɗi jugub cikin firgici da tashin hankali tafara nuna hoton da yatsanta tana cewa ” kardai shine , wayo nashiga uku na lalace badai shine mijina ba dady bakuyimin adalci ba inhar shine baku sanar dani ba , kuka takeyi tana matse kanta lokaci ɗaya ciwon kai yayi mata sallama , amma har yanzu bata dena kallon hoton Kamill ba .
ƙara nuna hoton tayi a karo na biyu tare da cewa ” natsaneka na tsaneka bana sonka bana ƙaunarka takuma fashewa da kuka mai ban tausayi , jan ƙafafunta tayi da suke neman ƙin ɗaukarta ta nufi ƙasa nata riƙe da kai , bata sami damar ganin sauran ɗakunan ba tayi gamo da ɓacin rai, gado ta faɗa zuciyarta fal baƙinciki inta tuno maƙiyinta shine mijinta lallai akwai aiki tasan auran hukunci yayi bawai na tsakani da Allah ba , tabbas shine mai kirana a waya tabbas shine , magana takeyi kamar zararriya tana riƙe da kanta har yanzu .
Bayan tagama juye juyenta bacci mai nauyi yai nasarar ɗaukarta , baccinta takeyi cike da mafarkai iri iri duk na Kamill dakuma yanayin zamansu .
sai ƙarfe ɗaya ta farka tana tashi yunwa tayi mata sallama , kitchen ta nufa cikin sanyi jiki ta buɗe handle ɗin ƙofar ,komai akwai a kitchen ɗin babu abinda babu , in baku manta ba dama ba gwanar cin abinci bace , fridge ta buɗe shima cike yake da lemu kala kala , nutrimilk ta ɗauka mai sanyi ta koma kitchen ta ɗauko cake ta ɗora kan plet ta dawo palo tafara ci , bawani daɗi yake yimata ba amma saboda yunwar data addabeta yasata maida hankali ga ci .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button