GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

Zaune momy suke a dining kowa da sakwara a gabansa da miyar egusi da naman kaza gefen kowanen su shayi ne mai kauri gakuma bredi da wainar ƙwai .
Hajiya dake kan kafet a zaune ita da Tinene ta dubi dady tace ” Alhaji gobe in Allah ya yarda zanje gidan wanan zabiyar in dubota , to Hajiya dady yace ” yaƙara da cewa ” Allah ya tsare hanya driver zai kaiki , dady nima zani cewar Afreeda Allah ya tsare dady yace ” musu momy kam tunda ta tashi takejin jikinta babu daɗi tanajin kamar akwai abinda ke faruwa da Diyana kasancewar ta mai zurfin ciki yasata yin shiru batare da ta gayawa dady ba .
Haka dai suka gama breakfast ɗinsu kowa ya watse .
yau kwanansu biyu da aure ko leƙowa bai yi ba ,a iya kwana biyu Diyana ta rame sosai fuskarta babu wani farinciki kana ganinta zaka gane .
Sallamar su Hajiya ne yasata amsawa cikin fara’a niko nace aure mai gyara hmm .
Guri Hajiya da Tinene da Afreeda suka nema tare da kallon Diyana dake zaune da remote a hanunta , bayan sun gaisa Hajiya tace ” ƴarnan mai yaja miki rama haka ? kinfara nuna masa halinki na ragwanta da raki ko ?” sunkuyar da kai Diyana tayi dan bazata iya sanar da wanan tsohuwar damuwarta ba , miƙewa Afreeda tayi ta koma kusa da ita suka rungume juna , tashi ki kawo musu wani abin akwai drinks a fridge ɗauko musu kiduba kitchen akwai cin cin.
Riƙe baki Hajiya tayi tare da cewa kinci gidanku ta watsawa Diyana daƙuwa , waye yace “miki yanajin yunwa kokuma kawo ko bazanci ba sai naci ehe ,Diyana ba surutun Hajiya ne a gabanta ba hakan yasa ta gyara kwanciya a doguwar kujerar da take zaune tayi matashi da cinyar Afreeda .
Riƙe baki Hajiya tayi bata ƙara cewa komai ba , ta miƙe tare da juye abinda Afreeda ta ɗebo a gaban hijab ɗin Tinene ,to kitaso mu tafi inkuma kinzo zaman ɗaki ne sai muji , Hajiya tace tana shirin ficewa , miƙewa Afreeda tayi idanunta sun ciko da hawaye tace ” my sis sai munyi waya .
Kasa magana Diyana tayi saboda kukan da ya ƙwace mata , tanaji tana gani suka tafi suka barta a gidan da shida kurkuku duk ɗaya.
Yau kwaanta uku a gidan bayan tayi sallahar Azhar ta jingina kanta da gado tun tana wani tunani daban har bacci yai nasarar ɗaukarta , jin an watsa mata ruwa mai kamada na ƙanƙara yasata saurin buɗe ido ta miƙe cikin tsoro , Kamill ne tsaye yana sanye da shadda fara tasha aiki kannan yasha hula sajens luf luf ba ƙaramin kyau yayi ba , wayabaki lokacin bacci a gidana ? cikin tsiwa Diyana ta taɓe baki kana tace ” inbanyi bacci ba mai kakeso nayi ? ke karki kuskura kiyimin rashin kunya dan ni da kike ganina ina hukunta marasa kunya so ki kiyaye kisan ko da wa kike magana , taɓe baki takuma yi a karo na biyu tace ” mtsw har ya ɗaga hannu zai kai mata mari ko mai ya tuna oho sai ya fasa ya fice daga ɗakin
[22/06, 3:30 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ????????
*GUGUWAR ZALUNCI*
Page 23 & 24
Part ɗinsa ya wuce ya watsa ruwa kana ya fito ya shafa mayukansa masu ƙamshi ya nufi drower ya ciro gajeren wando da farar singlet ya sanya , ɗaukar wayoyinsa yayi kana ya sauka ƙasa , yana sauka yaji wani ƙamshi mai daɗu ya bugi hancin sa , leƙe ya shiga yi ta ina ne jin ko ta ko ina ƙamshin ke fitowa yasa shi nufar ɗakin Diyana cikin ƙasaita ,
samunta yayi a kwance kan gado hawaye sun bushe a fuskarta keee…! tashi ki dafamin indomie Diyana da takejin maganar kamar a mafarki ta kuma juyawa tana gyara kwanciya , fincikota yayi tare da cewa ” gidanku babu manya ne ? karki manta yazu daga ni sai ke a gidannan so kuma kinsan matsayina a gurinki ko kin mance my blood ɗinne yau ? kuka Diyana ta fara mai sauti tana cewa “wlh ka cuceni Allah sai ya sakamin danasan kai ne zaɓin da iyayena sukayi min wlh bazan amince ba , zama gefe gado yayi tare da janyota yana riƙe da bakin maganar yace ” sai kuma gashi kin yarda kuma inyi abinda nakeso dake , runtse ido tayi tana tuno irin tsanar da tayi masa tabbas bazata taɓa son sa ba koda nan gaba.
Ƙara matsowa yayi kusa da ita suna jin nunfashin juna yace ” baby tashi ki dafamin indomie kuma wlh nabaki 3mins zaro ido Diyana tayi dan wanan lokacin yayi kaɗan , tunowa tayi to inma bata dafa ba uban me ya isa yayi mata , yana ficewa ta koma ta kwanta,kamar daga sama taji saukar bulala mai tsafi , innalilahi ta ambata cikin muryar kuka .
Mai nayi maka ? jaka aka kawo maka? to wlh ka kuma dukana ka gani, duk wanan maganar da Diyana takeyi idanunta a rufe , janyota Kamil yayi haɗi da cigaba da janta har hanyar kitchen , haka tadinga jin zafin janta da yayi a step ga kurjewa da tayi bugu da ƙari ƙarfinsu ma ba ɗaya ba , tayi iya yinta gurin ganin ta ƙwace amma abin ya citura , babu tausayi ko imani ya wurgata kitchen yana mayarda nunfashi tare da gurnani kamar zaki , oya ki wuce ki dafamin ko inyi miki abinda yafi haka , babu shiri Diyana ta miƙe bakinta da guwai war hanunta duk ya ƙuje ta kuna gas kana ta ɗora ruwa yana tafasa tasa komai tare da mangyaɗa da sauransu , sai da ta juye a plet ganin baya kallonta ta zabga gishiri a ciki ta miƙa masa , banza kalmar da ta fito daga bakinsa kenan , sai da Diyana ta ruga da gudu tace ” ai ba’a banza ɗaya sai dai biyu ta shige bedroom tana cigaba da kuka tare da murɗa key ɗin ƙofar.
Ƙwafa yayi dan yasan bakinta ba mutuwa zai yi ba , dining ya nufa ya zauna tare da ɗaukar cokali ya fara juya indomien lomar farko yaji ɗan karen gishiri kamar iya shine a abincin , Diyana ….bazaki fito ba wlh yau sai kin gane bakida wayo uban wa yace miki haka ake girki ? shiru batare da ta amsa ba ya sashi ƙara tunzura yana huci ya haura up step , kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya faɗa gado zuciyarsa nayi masa saƙe saƙe , ring ɗin wayarsa ne yasa shi ɗago kai ya nuba mai kiran nasa Abba ne , Kamill yace ” tare da ɗaukar kiran ya kara a kunne , Aslamu alaikum Abba barka , cikin farinciki Abba yace ” dafatan kuna lafiya ya ɗiyata ? tana lafiya Kamill yace ” to masha Allah ka nutsu my son yanzu kayi aure fa .
To insha Allah Kamill yace ” daga nan sukayi sallama .
Kwanciya yayi kansa na kallon sama yana tuno kalar muguntar da zai sake yiwa Diyana a karo na biyu , daga haka bacci mai nauyi yayi nasarar saceshi , jinshi shiru yasa ta buɗe ƙofa ta fito saɗaf saɗaf tayi kitchen flaks ɗin ruwan zafi ta ɗauka kasancewar tunda masu kawota suka cikashi da tafasashen ruwa batayi amfani dashi ba , ɗibo kayan haɗa tea tayi da duk wani abinda zata buƙata harda ragowar cake ɗinta da butter duk ta kawosu ɗakinta ta jeresu kan bedsite ɗinta kana takuma dannawa ƙofar key , haɗa shayinta tayi mai kauri tanasha tana gutsirar cake , da haka har ta ƙoshi sosai , ajiye cup ɗin tayi tare da gyatsa ta lumshe idanunta , tunowa tayi rabonta da waya da momyn ta tun safe dan haka ta ɗauki wayarta ta danna number my mom , ring ɗaya momy ta ɗauka cikin farinciki tace ” my daughter dafatan kina nan lafiya ? eh ina lafiya momy ya Afreeda dakuma wanan tsohuwar ? dariya momy tayi tace ” duk suna nan lafiya amma babu wata matsala ko ? naji muryarki babu daɗi ? uhm babu komai Diyana tace ” akwai fa naji muryarki ta sauya ni mahaifiyarki bazaki sanar dani ba ko to wa zaki gayawa ? kuka Diyana ta fashe dashi dan zuciyarta ta tsinke da kalamin momy.
Bankaɗo ƙofar da taji anyi ne ya hanata gayawa momy halin da take ciki , bata ankara ba taji an fizge wayar daga hanunta , Aslamu alaikum momy ya gida ya aiki yakuma lil sis , dagajin muryar tasan mijin Diyana ne , washe baki momy tayi tace ” lafiya lao ya ƙoƙari Allah yayi muku albarka Allah ya albarkaci rayuwarku , amen Kamill yace ” tare da cewa mun gode momy muna nan zuwa gobe insha Allah, momy ta mance da maganar su da Diyana cikin farinciki sukayi sallama da Kamill .
wurgo mata wayar yayi Allah ya temaka bata faɗi ƙasa ba , tare da cewa ” wlh duk ranar da naji kin gayawa wani yanayin zaman mu sai na illata ki , lumshe ido tayi batare da ta kalli inda yake ba , sai da ya gama surutansa sanan ya fice .
Washe gari bayan sallahar ashba garin ya tashi da sanyi mai shiga jiki kwance Diyana take a bed ta ƙudun dune da blanket sai kwasar baccinta takeyi .
Tunda Kamill ya dawo daga masallaci yake jinsa cikin wani yanayi , ɗakinsa ya wuce yana rawar sanyi , idanunsa sun kaɗa sunyi jawur dama a dai dai wanan time ɗin yakeda buƙatar mace ” a duk lokacin da gari yai sanyi to baya cikin kwanciyar hankali ,ga gararsa kwanciyar tayi ya dawo palo ya kwanta yana rawar sanyi , haƙoransa babu inda baya rawa ga wani wahalalen nunfashi dayake sauƙarwa .
Kamar an tsikari Diyana ta miƙe tare da buɗe ƙofa ta fito palo ko me take nema oho , jiyo sautin sauƙar wahalalen nunfashi ya sata ƙarasawa da gudu domin taga waye , Kamill ne kwance jikinsa nata ɓari , abinka da mace mai tausayi sai ta tallafo kansa ta gyara masa kwanciya tare da miƙewa ta nufi ɗakinta ta haɗo masa shayi mai zafi ta kawo masa , tashi kasha , jiki na rawa Kamill ya fara shan shayin cikin ikon Allah zufa ta fara keto masa ta ko ina yadena jin sanyin , tunda Diyana ta tabbatar ya dawo hayyacin sa ta janyeshi tare da cewa ” kaci darajar tausayin da Allah yasa min amma badan haka ba babu dalilin da zai sa in temakeka taja tsaki.
Kamill dai jiki babu ƙwari dan haka bai kulata ba ya maida kansa ya kwanta ,
Zuwa ƙarfe goma da rabi yaji sauƙi sai ciwon mara dake ɗan damunsa , haka dai ya haura zuwa ɗakinsa yai wanka ya sauya kaya sai ƙamshi yake zubawa dole duk macen da ta gansa sai ta yi sha’awar ya kasance mijinta , fararen kayane a jikinsa ta baƙar hula mai adon farin zare ga tsadaden agogon sa da takalminsa fari , sakowa yakeyi a hankali kamar ba shine mai rashin lafiya ba , direct ɗakin Diyana ya dosa ya murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa’a ta buɗe , zaune ya sameta tana makeup itama fa tayi kyau sosai ta haɗe cikin baƙin leshi mai adon jan flawoyi tagama shafa powder tana shafa pink ɗin janbaki ɗakin ya game da ƙamshi , tsayawa Kamill yayi yana ƙare mata kallo cikin zuciyarsa yana cewa ” gaskiya da auran soyayya mukayi da na more wanan mai zan so a jikinta mtsw ya kauda tunanin da ɓacin rai ,
Baiyi magana ba ya fice itako tun shigowar sa tana kallonsa ta mirorr bata kulasa ba , ɗage kafaɗa tayi irin ko a jikina ɗinnan .
Ba’a jima ba taji ƙarar tsayawar motarsa tasan shine ya dawo , kuloli ne masu kyau a hanunsa guda biyu ya nufi dining dasu ya jere su tare da ɗauko su fanta da 5alive da sauransu ya ajiye , kuma komawa ɗakin Diyana yayi wanan karon harda sallama , amsawa tayi cikin siririyar muryarta , zama yai a gefen bed tare da cewa am sorry mata ta kiyi haƙuri da dukkan laifukan da nayi miki nasan ban kyauta ba , nan danan zuciyar Diyana ta karaya kasancewar ta mai saurin fushi dakuma tausayi uwa uba ga son a risina mata, bakice komai ba my Diya? sharesa tayi tana ƙoƙarin miƙewa , janyota yayi ta faɗa jikinsa suna jin ninfashin juna ya kai fuskarsa kan tata tare da cewa nayi miki magana tare da bada haƙuri kinƙi kulani ko kinason Allah yayi fushi dake ? tuno nasihar su momy da dady tayi cikin karayar zuciya tace ” na haƙura wata irin runguma ya kai mata tare da manna mata kiss a kumatunta , munada baƙi fa , waro ido Diyana tayi tare da cewa ” mai za’a dafa musu ? no nasiyo kawai inason ki zama cikin shiri , oky Diyana ta faɗa da murmishi ɗauke a fuskarta.