*GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 1 & 2 An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ NA *ZAINAB HABIB (MOM ISLAM)* Free page *Gargaɗi! Gargadi!!! Ban yarda wani ko wata su juyamin littafi ba ta kowace siga ba haƙƙin mallakarsa nawa ne abi doka a zauna lafiya*! Bismillahir rahmanir rahim da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai . Ina godiya ga Allah daya bani aron rai da lafiya da kwanciyar hankali har nakai ga fara rubuta wanan littafi mai suna GUGUWAR ZALUNCI ya Allah ina roƙonka ka tsaremin hankali na da basirata gurin rubuta alkairi ya Allah ka tsaremin alƙalamina da rubuta abinda zai tarwatsa rayuwar jama’a ya Allah ka ƙara mana lafiya ka nuna mana ƙarshe littafinnan lafiya kamar inda ka bani ikon farashi cikin ƙoshin lpy amen y Allah. Wattpad momislam2020 Facbook mom islam mon islam Email: Zainabhabibu@gmail.com Whtsapp: 08141799224 *BIRNIN TARAIYYA ABUJA WUSE TWO.* Anguwa ce mai cike da manyan masu kuɗi ga kuma tsararun gidaje kamar a ƙasar turai . A cikin anguwar akwai wani ƙeraren gida mai kyan gaske gidane daya sami ƙwararun magina masu aiki da ilimi , tun daga wajen gidan zaka gane mai gidan hamshaƙi ne wato Alhaji Sani ana kiransa da Alherin Allah , babban ɗan kasuwa ne sananne a kowace ƙasa kuma kowane fanni yanada kamfanoni da dama dakuma motoci wanan kenan. daga gefe ɗakin mai gadi ne can kuma gefen kudu da arewa shuke shuke ne na wasu kyawawan flowers gwanin sha’awa , ga wasu ɗawisu da suke kaiwa suna komowa guwanin birgewa . Iyalan gidan ne zaune a palon da za’a iya kiransa da aljannar duniya iya tsaruwa ya tsaru nera tayi kuka musamman ma danƙara danƙaran kujerun da suka mamaye palon ,wata farar mata ce zaune a ɗaya daga cikin jerin kujeru sai wasu ƴan mata su biyu masu kama da ita amma sun fita haske matashiyar matar ce ta dubi ɗaya daga cikin ƴan matan tace “Diyana zakuyi dare fa kinga har yanzu dadynku bai fito ba , Wace aka kira da Diyana ce ta taɓe baki tare da lumshe fararen idanunta masu ɗauke da zara zaran gashin gira tace “mom ni dama bason zuwa ƙauyen nan nakeyi ba dady ne ya matsa mini wai nice banison zuwa duk cikinmu , Budurwar dake gefe ce ta dubi momy fuskarta da alamun ɓacin rai tace ” mom village ɗinnan ya cika sauro gakuma rashin tsafta , Diyana ce tace ” good Afreeda ashe kin gane ,jin maganar tasu zatayi yawa ne momy tace ” shiii alamar suyi shiru dan tajiyo takun mai gidan nata , ƙarasowa yayi da shiga ta alfarma a jikinsa shadda ce gezna fara wace tasha aiki , momy ce take ƙare masa kallo da murmishi a fuskarta shima mayar mata yayi tare da kallon su Diyana da Afreeda da hankalinsu ke kan wayar dake hanunsu , Dady ne yace ” to nagama so ke nake jira rau rau Diyana tayi da ido tana kallon mom ganin batace mata komai ba yasata miƙewa tana bubuga ƙafa Afreeda na dariya ƙasa ƙasa , Dan tasan ita zata iya jure wuyar ƙauyennan amma Diyana kam tana tausaya mata, dady waje yayi dan shima ba mai son yawan magana bane kamar mom , Hand bag ɗinta Afreeda ta ɗauko mata tare da wata jaka mai kyau da alamu itace jakar kayan nata , mom ce ta miƙe ta nufi step ɗin dake tsakiyar palon bata ɗau lokaci ba sai gata ta fito da wato leda fara ƴar baba ta miƙawa Diyana , buɗewa Diyana tayi taga su man shafawa ne masu tsada dakuma takalma harda atamfa itama mai tsada kana ga turaruka , taɓe baki Diyana tayi tace “mom wanan kayan wa za’a kaiwa granny ɗinku taɓɓ hmm Diyana tasa kai ba tare da takuma cewa komai ba , Jerowa sukayi tare da Afreeda idan kaga yanayin tafiyarsu kai kace ƴaƴan sarakuna , Fuskar Diyana babu fara’a kasancewar dady na cikin mota yana waya hakan ya basu damar yin magana , Afreeda ce tace “Anty Diyana saifa kin daure da mutanen village ɗinnan dan lokacin da mukaje wlh cemin sukeyi anyi jar fata tashigo ƙauye kokuma sudinga bina suna kallo na , Dafe kai Diyana tayi kana tace ” nashiga uku nikam nima haka zasuyimin ? har Afreeda zata yimata magana dady ‘ ya katsesu zo mu tafi , dady na back side ita kuma ta shige gaba dan batason zama kusa dashi kasancewar ba tun yanzu ba ya hanasu chart eyepice tasa a kunnen ta kana ta jingina kanta da kujera ta lumshe ido driver na shiga suka ɗauki hanyar ƙauye . *KANO. ƘAUYEN SHAFA* Ƙauye ne mai gidaje jifa jifa dakuma mutane iri iri yawancin gidaje nasu duk rufin ɗakin anyishi ne da jinka basu damu dayin katangu ba wasu kuma sunayi kana babu ginin siminti sai a wani gida dake gefe shi kaɗai . Bacci mai daɗi ne ya ɗauki Diyana dady kam hankalinshi na hanya dan sun shiga kano a halin yanzu ma hanyar ƙauyen suka dosa , wata irin gargada suka shiga wace tayi nasarar farkawar Diyana a tsorace ihu ne kawai bata kurma ba ga mumunan faɗuwar gaba , Ƙarewa ƙauyakun kallo tashiga yi tana salati badai nan ne kauyen ba taɓɓ gashi dady yace ” 5 days zanyi ina bazan iya ba , duk cikin zuciyarta take wanan maganar jin anyi parking yasata ɗago kai tare da juyawa ta kalli dady dake tattara wayoyinsa a kan siddin motar dady har mun iso ne ?” yes daughter yau zakiga granny ɗinki , yana maganar da murmishi a fuskarsa, driver ne ya fito ya buɗewa dady mota kana ya buɗewa Diyana , a tare suka fito daga motar hanunta riƙe da wayoyinta guda biyu tabi bayan dadyn , Daga bakin ƙofa dady yai sallama jin muryar wata tsohuwa yasa Diyana waro ido dan ganin wacce mata ce zata fito ?”. Wata tsohuwar mata ce fuskarta taɗan tamushe haƙoranta sunji jiki tsabar cin goro tasa riga da zani dakuma ɗankwalin yadi barka da zuwa Alhaji tanata faɗaɗa fara’arta ywwa Hajiya , Hajiya ce tace ” to kuzo mushiga jikalle ansha hanya ta dubi Diyana , Yamutsa fuska Diyana tayi batare da tace ” komai ba suka shige ciki . Tsakar gidan da yaji siminti fess yake a share ko tsinke babu amma hakan bai sa Diyana dena yatsina fuska ba tana tattare kayanta wai karsu ja ƙasa , shiga cikin ɗakin sukayi da yake malale da leda babu kujera sai ƴar tuguno Hajiya ta miƙawa Diyana batare da tayi magana ba ta karɓa ,Hajiya ce tace ” Alhaji a ina ka samo wanan ƴar gwallin ?”dan naga kamar ba wannan bace da ta taɓa zuwa shekarun baya ?. Kawar da zancen dady yayi ta hanyar durƙusawa yace ” Hajiya bamu gaisa ba ina wuni washe baki Hajiya tayi tace” lafiya lao Alhaji ya aiki ya hidima yakuma Faɗimatun buɗe baki Diyana tayi cikin zuciyarta tace ” waye Faɗimatun komai sai an ɓatawa mutum suna mom ce Faɗimatu taɓɓ , Dady ne yace ” tana gaisheki Diyana ce ta kalli driver tace ” kaje motor ka ɗauko wata farar leda ka kawo min , to driver yace ” cikin rawar jiki ya fice Hajiya ce ta miƙe ta fita sai gatanan da kwanon fura da nono a wani baban kwanon silba da suga a leda dakuma ludayi , Tunda Hajiya ta shigo da nonon Diyana take keɓe baki dan inba na kanti ba batashan wanan , driver ne ya dawo hanunshi riƙe da ledar ya durƙusa yace ” ranki shi daɗe gashi karɓa tayi ta ajiyesu gaban Hajiya batayi magana ba , kallonta kawai Hajiya takeyi dan a bisa dukka halamu jininsu bai haɗu da Diyana ba , dady ma ya lura da rashin sakewarta dama yasan halin abarsa ko anyi abinci a gida bataci inba tayi ra’ayi ba drinks sune kayan shanta sai cake da shauransu . Alhaji nayima magana a inaka samo wanan yarinyar mai kamada aljana kayimin kunen uwar shegu ko ? dady ne yace “Hajiya Diyana ce fa ko kin manta ta yayar Afreeda ,kaji ai kusawa yara sunan mutunci bazaku sa ba sai wani suna mai kamada na biririka ,dariya ce taso kuɓucewa Diyana amma ta make , miƙawa dady haɗin furar tayi kana ta miƙawa driver dake zaune can gefe a tabarma takuma ajiyewa Diyana a gabanta yatsina fuska Diyana tayi kana tace “I dont like this thing dady ta miƙe tana tari , la haula wala ƙuwata illabillah Hjiya take ta mai maitawa tana tafa hannu ta dubi Alhaji tace ” mudai bamu ɗauko wanan mugun halin ba gaskiya ɗayar ƴar uwarta tafi daɗin sha’ani , Nikam yaushe zamu jitu da wanan mai kamada zabiyoyin chaɓɗijan , Diyana dai na zaune dan hankalinta na kan wayarta maganar da taji dady nayi ne yasa ta juyo a tsorace ” zaku jitu ita da zata yimiki sati , Washe baki Hajiya tayi tace “aiko dana sami ƴa suka haɗa ido da Hajiya Diyana ta sakar mata harara , Dady ne ya kalli Diyana yace ” wai kin mance gurin wacce nace miki zanzo ne ?” wanan fa da kike gani mahaifiyata ce walh zan saɓa miki , Diyana dai kanta na ƙasa ba ma’abociyar surutu bace , wata yarinya ce ta shigo da gudu tana cewa kaka yau bazakije itacen bane ? Hajiya dake shan rahowar furar da dady ya rage tace ” nayi baƙi jeki cewa mamanki Alhaji yazo to yarinyar tace ” kana ta fice da gudu . Da isarta gidan nasu dake zagaye da dangar kara tafara ƙwalawa mahaifiyar tata kira tana cewa ” Talatu ki fito wanan yayan naki na bini yazo wlh harda baturiya kiyi sauri , Talatu dake ɗaki tana fere rogo ta leƙo tare da cewa da gaske kike yi tinene eh ? yasin kizo zaki ganhi harda baturiya , Yafo gyale talatu tayi jiki na rawa ta saka takalmin ta ‘ ta fice ta kwashi sauri dan tasan yau ta warke . Kasancewar basuda nisa sosai dan danan sai gata a ƙofar gidan ganin sabuwar mota ne yasata tabatarwa ,tinene ce ta biyota da gudu tana cewa ” Talatu kinga zahiri ko ga motarhi nan , ƙarasawa sukayi tayi sallama Hajiya ce ta amsa gimbiya Diyana na sallah a sallayar da ta ɗauko a mota , Harkin iso Hajiya tace tana washe baki yayanki ne yazo kuma yau ze wuce shine nace “tinene ta kirawo ki , Talatu na fama da susar kai tace ” ai ganinan Inna ina yaje ne ? Hajiya ce tace?yaje sallah ai ba jimawa zaiyi ba yanzu zai dawo, Talatu ce ta cire mayafin kanta tare da cire ɗankwali tasa hanu biyu tana sosa kanta , Hajiya ce ta dubeta tace ” wai talatu har yanzu baki sawa ƙwarƙwatar magani bane ?dagudu Diyana ta miƙe ta daka tsalle sai gata a waje , shigowar dady ne yasata sunkuyar da kai tace “sannu da dawowa dady ywwa daughter lafiya na ganki a nan ?” kafin tayi magana Hajiya tace ” uwarta Talatu take gudu dady ne yace ” to maiya faru ? Diyana idanunta cike da hawaye tace ” Dady ka tafi dani wlh bazan iya zama a nan garin ba , Kinci gidanku dady ya cewa Diyana , ya shige ɗakin Hajiya washe haƙora Talatu tayi tace ” yaya hannu da zuwa kunsha hanya , wlh kuwa ya yara ? lafiyansu lau Alhaji ya hidimomi mungode fa , babu komai Alhaji yace ” yana kallon tinene wanan ƴar gurin waye ?, Hajiya ce tace ” ɗiyar Talatu ce fa gatanan kamar ka kifeta da kwando ga guru gurun idanuwa kamar na waccan ta wajen , Kwashewa da dariya sukayi Alhaji ya miƙe yace “toni zan tafi Diyana kiramin driver kokuma kice ya kwaso kaya a mota oky tace ” ta fice tare suka shigo da drivern hanunsa ɗauke da buhunnan shinkafa da katan ɗin taliya da jarkar man gyaɗa da maggi da gishiri , dubu arba’in dady ya miƙawa Hajiya ita kuma Talatu ya bata dubu ashirin ai kamar an jefata a aljanna tahau zuba godiya tana ƙarawa , Dady ne yace “hajiya nanda wata ɗaya zaki dawo ABUJA dan wlh kina kusa abin zai fi ,zaro ido Diyana tayi tana nazarin irin zaman da zasuyi da wanan tsohuwar mai bala’in sa ido amma babu komai da ƙafarta zata nemi ta dawo ƙauyensu , hajiya na kuka tana sanyawa dady albarka tare da duk abinda yasa gaba , Shigewa cikin palon Diyana tayi tare da ɗauko jakarta ta dubi dady zan bika bazan iya zama a nan garin ba cikin ɓacin rai dady yace ” anan na girma komai nawa anan yake kaf cikin ƴaƴana kece mai tsananin ƙyamar jinina ,to dole ki zauna har sati ya zagayo saboda zumunci abu ne mai ƙarfi , kuka Diyana takeyi kamar ranta zai fita da ajinta da komai ta zauna a wanan banzan gidan wanda ko ɗakin zuba shararsu bai kai ba wajen kyau , niko nace wanan gida da kike rainawa shine ƙurewa gurin kyau a wanan ƙauyen , 20k dady ya bata yace ” to mu mun tafi Hajiya najin duk dramar da sukeyi taƙi kulasu Talatu ko tsabar murna har yanzu murmishin fuskarta bai ɗauke ba, dady 20k is to shot tana bubuga ƙafa 5k ya ciro ya daɗa mata yana bata haƙuri akan zai turo driver ya zo ya ɗauketa , Hajiya ce ta matso tana cewa maganar sai kace ta munafurci da wani yare kukeyi dan kar ajiku ko , wlh Alhaji ka sakalta ƴaƴanka da kashe kuɗi , dariya dady yasa dan inya biyewa Hajiya bazai tafi yanzu ba , shigewa mota yayi yana ɗaga musu hannu , Tinene dake gefe tana ƙarewa Diyana kallo gaskiya kaf cikin ƙauyenan bata taɓa ganin mai kyau irinta ba gaskiya ƴan binni sunji daɗi ko kaushi basuyi bare faso, Hajiya ce tace ” baiwar Allah taso mu higa gida yamma tayi Talatu ce tace ” Hajiya nikam nayi gida yau zamu hyarɓi jar miya yasin yaya Sani ya jiƙani da nera ai wlh ko Ado bazan nunawa ba dan yana ƙyala ido to zai rabani dasu , Hajiya ce tace ” harkin gama abincin ne ? a’a wlh ina cikin gyaran rogo he ga tinens tazo kirana wai Alhaji yazo inafa zan gama tinene ce ta kwashe da dariya kana tace ” wayaga kaka a binni yasin sai sun koroki , Hajiya da haushi ya ɗebeta tace ” cin uwaki niɗin bzan iya zama a can ɗin bane to kikasa wasa ma dake zani , Diyana ce takuma cika a zuciye ta shige tabarsu anan sunata surkulllen maganarsu….! Kubiyo ni dan jin cigaban labarin ya rayuwar Diyana zata ƙare a ƙauye biya 200 ki karance shi cikin kwanciyar hankali . [31/05, 12:39 am] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 3&4 NA *ZAINAB HABIB (MOM ISLAM)* Wattpad momislam2020 Facbook mom islam mon islam Email: Zainabhabibu@gmail.com Whtsapp: 08141799224 Mangariba ta sako kai Talatu ta wuce gida itama kamar ba mai son mutane ba dan kamar batasan Diyana yarinyar Alhaji bace kodan yangar da taga tanayi ne oho , Tinene da bata wuce gida ba ta dawo gidan Hajiya ta zauna a bakin kofa , Hajiya ce tace ” tahi karki janyo mana fitina kina sane almuru tayi ,tinene ce ta harari Hajiya kana tace ” wlh sa ido yayi yawa ƴar birninnan da wuya ta iya zama dake wataran sai tayi kamar zata gudu ga ki da gani babu ƙyalewa , Tafa hannu Hajiya tashiga yi tana salati tare da cewa” au ni zakiyiwa cin mutunci wlh Ado kika yiwa ba niba hyahya hya kawai wanan kalmar tabawa Diyana dariya dan duk ɓacin randa take ciki sai da ta dara , Tinene ce ta miƙe tare da karkaɗe zani tace ” ha muzo muyi daka tsami dan yasin bazanyi wanka ba ko kallonta Hajiya batayi ba da alamu anyi faɗa kenan . Wayar Diyana ce tafara ring cikin farinciki ta duba number dan tun ɗazu take ta neman network babu , Da sauri ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta tace ” hello Afreeda yakike ?” daga can ɓangaren Afreeda tace “sis kina jina kuwa ? alamu dai na rashin network babu ya ɗauke , Diyana rasa me zatayi kawai tahau kuka tana kiran ta shiga uku harda shure shure gata ƙatuwa , Da gudu Hajiya tayo ɗakin har tana shirin faɗuwa ta sameta a zaune kan jakar kayanta tana shure shuren ƙafafunta , Nidai naga ta kaina yanzu waccan mai kamada bulaliyar ta gama gayamin magana yanzu kuma ga wanan mai kamada yan ruwan aljanunta sun motsa Hajiya harda ƴar kwallarta wai ta tausayawa Diyana hhh, Batasan ciwon rashin network bane ya motsa ,ƙwalawa tinene kira ta farayi tinene dake goge kaushi da dutsen goge ƙafa taƙi kulata , can kuma tace “ashedai mutum yanada rana eh naji koma mai zakice zoki kirayo min malam fari ya duba yarinyar nan , Diyana ji takeyi kamar ta ɓarar da Hajiya saboda tun farko jininsu bai haɗu ba rasa inda zatayi ta hukunta hajiya tayi can wata dabara ta faɗo mata aikuwa ta tuntsire da dariya , wanan karon saura kaɗan Hajiya tasa ihu , tinene ce tace ” toshi malam farin me zaiyi miki wlh kincika fitina , Hajiya ce tace ” kice inada mara lafiya a gidannan ni dare ma nake tsoro wlh, Ficewa tinene tayi tana tafiya tana mita da isarta gidan ta ganshi zaune akan wani dutse yana alwala ina wuni tace ” lafiya lau ƴar budurwa , tinene ce tace ” wai kazo inji Hajiya tanada mara lafiya a ɗakinta , Subhanllahi wacece ?” malam fari ya tambaya, Wata baturiya ce wlh kazo zaka ganta, washe baki malam fari yayi kana yace ” bari a fito sallaj kice mata ganinan zuwa yanzu , To tinene tace ” ta koma gidan ta samu Hajiya na sallah ta koma waje ta kwaso kwandan soso ta shige cikin uwar ɗakin Hajiya da murmishi a fuskarta , Hajiya na idarwa ta zabura tayo uwar ɗakin tana cewa ubanme zakiyimin wlh ban yarda dake ba kitafi gidan ubanki ni banison shishigi yanzu ma badan dare yayi ba wlh dana watso miki kayanki kin wuce tunda ni yanzu kin rainani , Hajiya nata banbamin faɗa itako Tinene na shafa mai ko a jikinta dan inda sabo ta saba baya damunta , Ko uffan batace wa Hajiya ba sai ma waƙa data kamayi . Sallamar malam fari ce tasa Hajiya fitowa tana washe baki suka gaisa yake tabyarta ya mai jiki da sauƙi Hajiya tace ” amma fa bata dena kukan ba , Malam ne ya matso kusada Diyana yana tambayarta maiya sameta , Wani azababben tsami dataji yana tashi ta gefensa yasata ficewa da gudu tana kuka , Hajiya ma fitowar tayi ta riƙota Diyana na ƙwacewa dan kaf mutanen gurinnan ɗaukar ƙazamai take yimusu har Hajiyan ma , Samun kujera Diyana tayi ƴar tsuguno ta zauna amma fa a dole tacigaba da kuka , takalmi malam yasa kana ya sami kujera shima ya zauna dan bai fahimci mai yasa ta gudu ba ya ɗauka aljanunne tunda basa tsoron adu’a ko kaɗan. Tinene tunda taji anfara artabu da Diyana ta daka tsalle tana dariya kujera ta taka ta janyo wani ƙaton kwanon silba mai cike da soyayyen nama da cincin tasan koda yaushe Hajiya bata rabo dashi wanan zuwan na dady ma sai da ya kawo mata wani na yau kam ta cika baƙar leda tam dan ledar ma daga mararta take . Hajiya ta mance Tinene na ɗaki saboda ta ruɗe malamin ne yace ” baiwar Allah maiya sameki ?”da kamar Diyana bazatayi magana ba can kuma tace “nifa lafiyata ƙalau rashin network ne yasani kuka , Hajiya ce ta mai maita newak ? no am say network shima dai malamin ba fahimta yayi ba amma yafi bada ƙarkin abin cine kokuma abin sha miƙewa yayi jiki babu ƙwari garin kallon Diyana ya bige da bango , Fitowar Tinene daga ɗakin Hajiya ta dubeta tace ” kakalliya nayi kyau kuwa ? yaufa haladu zai zo kinga ya kamata na tsara kwaliya tana fari da ido , Diyana ce ta ɗago kai ta kalli Tinene fuskar nan tasha jar hoda ga farin janbaki ƙamshim man ma da ta shafa bai yiwa Diyana daɗi ba dariya Diyana tasa kana ta miƙe tabar Hajiya a gurin, Hajiya na tsaye kamar gunki har yanzu bata yarda Diyana batada aljanu ba . Tinene dataga Hajiya taƙi kulata tayi hanyar waje zuciyarta farinciki dama a gidansu daga sallah sai cika ciki suke cin nama , Diyana ce ta ciro hijab a cikin kayanta ta fito batare da ta kula Hajiya dake tsaye tun ɗazu ba itako Hajiya wanan abun yafara yimata ciwo amma tabari duk lokacin da Alhaji yakuma zuwa zasuje gurin wani malami mai aganin Aljanu. Fita tayi batasan ina zata nufa ba tafara tafiya tana dube dube wani yaro ne yazo wucewa da alamu aikansa akayi , Diyana ce tace ” kai dan Allah innane ake siyarda Swan water tsayawa yaron yayi yana kallon ta tunowa tayi da maganar sis tanta , tace ” am sorry to ko kasan shagon da ake siyarda ruwan gora ko ruwan leda ? eh yaron yace ” wancan hyagon ne can zani ok to nagode , Yana gaba tana binsa a baya cikin salo da iya taku har suka iso shagon , Jitayi yaron yace “Idi abani ƙarago da garin kwaki zaro ido tayi badai shine zai ci ba ? a zuciyarta take maganar , Yaron yazo wucewa ta kira shi ta miƙa masa ɗari biyar kallonta yayi yace ” me za’a sawo miki ?”Diyana sai da taɗan lumshe ido dan ɗabi’arta ce hakan tace “nabaka ne , cikin murna ya hau yimata godiya Idi ne yace ” wlh kazo mu raba dan idona yagani abinka da basusan zasu samu ba suka raba ɗari biyu da hamsin kowannen su , mai shago kabani ruwan leda bag ɗaya dakuma Faro in akwai , Idi ne ya dubi Diyana da sai yamutsa fuskarta takeyi yace ” Hajiya akwai ruwan leda amma banida jakar saka miki ,Diyana taso yin dariya amma ta fizge tace ” duka ledar cikin rawar jiki ya ɗauko ya bata , kana yace ” ammafa babu ruwan gora ,okay Diyana tace ” bani canji yaron da tabawa kuɗi ne yace” kawo in kai miki , badan kayan sunyi mata nauyi ba da bazata bashi ruƙon ɗaukar leda ba kasancewar duk ƴan ƙauyen ƙyamarsu takeyi, haka dai ta barshi ya ɗauka bayan ta karɓi chanjin ta suka wuce gida . Hajiya na tsaye a bakin ƙofa tayi zugum tana jiran shigowar Diyana tsoronta ɗaya kar ƴar mutane tabi wani ƙauyen , Jin sallamarta yasa Hajiya washe baki tace ” ina kika higa ne ƴar albarka ?” Diyana ce ta taɓe baki kana tace ” naje siyo ruwa ne ,yaron yana ajiyewa ya fita . Salati Hajiya tahau rafkawa tare da cewa”au yanzu duk tsaftatacen ruwan dake tuluncan be i’heki ba saikin siyo ruwan bature ? dont worry Diyana tacewa Hajiya , A’ lallai kuwa wlh Alhaji ya ɗauko hanya marar ɓulewa amma zai kuma dawowa wlh bazata saɓu ba , Ita dai Diyana tama wuce abinta ta ɗauki ruwan alwalah tana idarwa ta tada sallah janyo jakarta tayi ta ɗauki cake ɗin da momy tayi mata tafara ci da nutrimilk , ƙara duba wayarta tayi chaji saura 20% gashi tunda tazo bata sami lambar momynta ba sunfara waya da Afreeda network ya ɗauke , dafe kanta tayi tana tunanin anya zamanta zai yi a ƙauyen nan, Bayan sallahar isha’i Hajiya ta zubowa Diyana tuwo miyar kuka da man shanu tunda Hajiya ta shigoda tuwon tafara jin tashin zuciya da sauri ta kawar da kwanon tana toshe hanci , wata uwar harara Hajiya ta wurga wa Diyana dan yau ta ƙureta , Hajiya ce ta kama ƙugu tace ” ke ƴarnan banison kinibibi wlh inbaki fita idona ba zan dakaki , dariya ma tabawa Diyana aikuwa tahau ƙyaƙyatawa dukda ita ɗin ba mai son yawan dariya bace , aikuwa Hajiya ta ƙara ƙuluwa ta kuma girgiza ƙugu niko nace kamar muciya lol Diyana kam zanyo blanket ɗinta tayi ta shimfiɗa a palo ta yi filo da jakar kayanta , tsabar bakinciki da ya isheta ma waƙa ta kunna ta toshe kunenta , mita Hajiya taci gaba dayi kamar zata ari baki oh ni Hafsu naga ta kaina indai birni ne wlh Allah wadai nikam tayi uwar ɗaki tana kakaɓe zaninta , tana zama tayi bakin gado tana lilo da ƙafarta ,kasancewar gado mai rumfa , juyawar da zatayi taji cizo innalilahi to mai ya sameni ?” hango cinnaka tayi yana tafiya ta gefenta sai yanzu ma tafara jin cizon , abinka da jikin tsohuwa yaji jiki tafara susa lalubar ƙarƙashin filo tayi koda zataga man zafi gurin harya kwaile tsabar susa tana ganin man tahau sharɓawa aikuwa tasha zafi ƙaramin hauka ne batayi ba, Diyana tana jiyo surutunta tayi shiru tana bin waƙar Hamisu breaker mai taken Jarumar mata anan gurin ma Hajiya tana jiyo saurin muryarta dan taƙi jinin tayi magana ayi kunnen uwar shegu da ita ,tofa da alamu dai Hajiya bazasu jitu da Diyana ba .. Diyana kuwa cikin ranta cewa takeyi ai tunda kince sa ido ne aikinki to wlh nafiki bari dare yayi sosai zaki gane . Bayan wasu mintuna bacci ya ɗauki Diyana bata samu tayiwa Hajiya hukunci ba . Washe gari da asbha Hajiya ce tafara tashi sai da ta idar da nafil filinta tazo ta tashi Diyana ganin taƙi tashi yasa Hajiya fara sana’ar tata wato mita komawa tayi ta kwanta tunda ta tasheta taƙi tashi , Saida gari yayi haske misalin ƙarfe bakwai Diyana ta motsa lokacin Hajiya ta kuma tashi tana gaban murhu ɗumama tuwo , Sannu Diyana tacewa Hajiya kanta a ƙasa , Yawwa ƴar albarka Hajiya tace ” shigewa banɗakin da ya zame mata dole tayi bayan ta fito ne ta sunkuya zatayi alwalah taji Hajiya na masifa Diyana ce tace ” shidai mutum kullum cikin masifa yake , ashe Hajiya ta ji, aikuwa takuma ɗorawa tana cewa yanzu ban isa nayi ajiya ba sai anyimin sata ankwahe nama ankwahe abinnan da akeyi da fulawa to yau zanci uwar ɓarawon nan bari Tinene ta shigo ƴar kan uba datanada gaskiya da asubar fari zaka jiyo sallaɓarta tazo cin ɗumamen tuwo . Diyana dai bata sake magana ba tana gamawa taje ta fara sallah tana idarwa tayi adu’oin ta, ɗibi ruwa a randa badan ranta yaso ba ta koma ɗakin ta ɗauki soso da sabulu tashiga wanka , ta daɗe tana wanka kasancewar jiya bata samu tayi wankan dare ba , Tsaye Hajiya take tana jiran shigowar Tinene ganin ta shafe mintuna bata shigo ba yasa Hajiya komawa ɗaki tafara cin tuwonta , sai da rana tayi sosai har anyi azhar Tinene ta kwaɗo sallama , gyan gyaɗi Hajiya takeyi a kan kujera amma dake tasa abin a ranta a zabure ta miƙe tanajin Tinene ta shigo ta cakumo ta tare da cewa yanzu kin kyauta kenan? ” Tinene ce tahau borin ƙarya tana cewa wlh kaka kidena ƙalamin sata nice kaɗai a ɗakin ? Hajiya ce takai dubanta ga Diyana dake tsara kwaliya tana shirin sa kaya tace ” to wazan ƙalawa inba keba waccan mai kamada zabiyoyin ba komai takeci ba bare nace ita to wlh zan haɗaki da Talatu dan bazan yarda ba, haka dai Tinene tasamu ta zulle dama ba yau suka fara ba . Kwanci tashi asarar mai rai yau kwanan Diyana shida a ƙauyen SHAFA babu abinda ya sauya na daga ɗabi’unta sai dai takanci abinci intaga yayi mata . Diyana ta gyara kayanta sbda basuyi datti ba ta ninkesu ta saka a jaka a ƴan kwanakinnan suna ɗan magana da Hajiya , Gobe takesa ran driver zai zo ɗaukarta wayoyinta babu caji duka sbda garin babu gurin caji tun tana baƙincikin hakan har tazo ta haƙura , A daren yau ne Diyana ta shirya yiwa Hajiya mugunta . 7:pm na dare bayan Talatu tazo sunɗan taɓa hira da Hajiya har Diyana ta gaishe ta ,ta jima a gidan sanan ta tafi yau dai tunda Tinene ta tafi gida bata shigo ba gashi dare yayi sosai lokacin ƙarfe tara da rabi , Diyana ce ta ɗauko bredin da Hajiya ta bada aka siyo mata da madara kasancewar yanzu dai ƙyan ƙyamin ba kamar da ba amma fa akwai , yanzu damuwarta ɗaya Allah yasa kar ace za’a tafi da Hajiya dan tanada yaƙinin zata dinga haɗasu faɗa da dadynsu amma daga yau zata fara tsorara ta ta , Hajiya tagama gyan gyaɗin da tasaba akan kujera ta miƙe tacewa “Diyana ƴar albarka sai da safe, Allah ya tashemu lpy Diyana tace ” yaukam bacci babushi a idanunta duk akan za’ayiwa Hajiya hukunci . Ƙarfe goma da rabi kamar an tsikari Diyana ta miƙe ta juya ta ciro wani farin hijab nata mai niƙab dogo har ƙasa da ‘ alama na sallah ne , Shiga cikin uwar ɗakin tayi tana ƙarewa jeren ɗakin kallo taɓ wasu ɗakuna ma sai ƙauye wai yazuma anan gidan a dol gidan masu kuɗi kenen ko uhm , Tunowa tayi da abinda ya kawota , tsinken tsintsiya tasamu tafara shafo fuskar Hajiya dashi kana ta ɗauko kujera ta zauna tanata bin fuskar da tsinken tsintsiya , jin anyo ta wajen kunnen Hajiya yasata farkawa a zabure tana cewa yauma shazumamun ne suka kuma shigowa bayan na rannan dana kwashe , Bata lura da Diyana dake gefe ba sauya murya Diyana tayi tace ” nazo tayaki kwana ne nice yarinyar Aljani ɗan kutub wata uwar durowa Hajiya tayi ganin farin abu, babu fuska kamar likafani…! Kubiyo mom islam dan jin cigaban labarin akwai cakwakiya a gaba biya ɗarinki biyu ki karanta . [31/05, 12:40 am] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 5&6 NA *ZAINAB HABIB(MOM ISLAM)* Wattpad momislam2020 Facbook mom islam mon islam Email: Zainabhabibu@gmail.com Whtsapp: 08141799224 Dan Allah kuyi haƙuri kuji tausayin bil adama wata uwar dariya Diyana ta saki badan tasan tanada babbar murya haka ba, tsumar jikin da Hajiya takeyi ne ga ɓurma mmen baki gaskiya comedy.com taci dariya ita da bata dariya sosai , Girgiza kai Diyana ta fara yi da farin hijab ɗin da ya rufe mata fuska , itako Hajiya ta haɗe hannuwa biyu tana cewa kuyi haƙuri nidai bansan laifin danayi muku ba tunda kwana biyu ba higa jejin nakeyi ba bare kuce naje na yimuku wani abin , Wata uwar ƙara da Diyana ta saki ne yasa Hajiya zabura zatayi palo dosota Diyana tafarayi kana tace ” kwanta kuma da safe mukaji kinyi maganar mu sai mun juya miki baki gefe maza ki kwanta Allah sarki Hajiya an maidata kamar baby . Ta koma ta kwanta tare da runtse ido Diyana ko yin alamun kamar mai fita tayi ta shigo a hankali ta kwanta . Washe gari Hajiya a makare ta tashi lokacin ma anyi sallar asbha tunda ta tashi yau ko mita babu juyawa tayi taga inda Diyana ke kwance taje kusa da ita tace ” ke ƴar albarka tashi gari ya waye , tom kawai Diyana tace “jiki a sanyaye Hajiya taje ta haɗa wuta ta je yin alawalh kafin taje sallah wutar ta kama ta ɗora ruwan kunu ta je sallah tana idarwa ta koma uwar ɗaki ta riƙe baki tana mamakin abinda ya faru da ita jiya gashi ance karta gayawa kowa , girgiza kai tayi tana nazarin inhar Alhaji yazo yau to bazata zauna a garinnan ba sbda tunda aka fara yimata haka to gaba ranta za’a nema ta miƙe tayi waje , Diyana na lura da yanayin Hajiya jitayi kuma taɗan bata tausayi wata zuciyar tace ” ai da bakiyi mata haka ba da tana nan tana mitar da tasaba . Tinene ce ta shigo tana kiran kaka ! kaka ! jin Hajiya taƙi kulata yasata ƙarasowa tace ” kaka lafiya kuwa ? Hajiya ta sako tuwo a kwano zatakai ɗaki tace ” ke ni kauce kibani gu , kaucewa Tinene tayi ganin yau babu masifa kuma babu alamun wasa . ƙarfe goma na safe driver ya iso ƙauye lokacin Diyana ta shirya shi kawai take jira ai tanajin horn ɗin mota ta miƙe tana cewa to Hajiya a yafemu , Hajiya dake ɗaki tanayi walha sallamar ta kenan ko adu’a batayi ba ta taso tana mita , “Saikace ina cizonki ai kyabari in fito ke ga ganɗoki ko kokuma mun gundureki ne ?”. Lumshe ido Diyana tayi batace komai ba , hakadai Hajiya tayi ta gama tayi shiru . Driver ne ya fito daga mota ya shigo gidan Hajiya durƙusawa yayi har ƙasa ya gaisheta cikin fara’a ta amsa tana tambayarsa yasu Alhaji da Faɗimatu ?”., duk suna lpy suna gaidaki driver yace ” ya miƙe tare da kallon Diyana ya gaisheta a yangace ta amsa dama ɗabi’arta kenan, Kana yace ” inkin shirya hajiya sai mu tafi ai kafin yakai ga ƙarasa magana Diyana tace ” nafa shirya dama kai nake jira Hajiya dai taga ikon Allah wata ƙatuwar leda tabawa driver ya bawa momy zasu fita kenan sai ga Talatu ta shigo , Ina kwana Diyana tace “da fara’a Talatu ta amsa da lpy yaune tafiyar ne ? eh Diyana tace suka ɗunguma sukayi waje , back side ta shiga suka kuma yin sallama Diyana ce ta kalli Hajiya kana ta ɗan yamutsa fuska tace ” ina wanan yarinyar ? washe baki Talatu takuma yi tace ” ai na aiketa hyagon Haliru 1k Diyana ta bawa Talatu ta ajiyewa Tinene aikuwa sun sanya mata albarka . Motar na shirin tashi Hajiya tace “to ƴar albarka sai Allah yayi zuwanmu killer small Diyana tayi kana tace ” saikin zo driver yafara tafiya . Shunyi tafiya mai nisan gaske kana suka ɗauki hanyar Abuja Diyana takan tuna rayuwarta ta ƙauye jifa jifa tayita murmushi musamman farin hijab ɗunnan data sawa Hajiya yana matuƙar sata nishaɗi , Jin horn da driver yakeyi ne yasata ɗago kai Alhmdulilh tace cikin ranta ,mai gadi na wangale get ta Hango momy da Afreeda suna tahowa da murmishi a fuskar su hawaye ne suka zubo mata tarasa na miye , Mai gadi ne ya buɗe mata murfin mota ta fito da gudu ta faɗa jikin momy ta saki kuka , Afreeda ganin kukan sistan ta yasata fara kuka , Momy ce ta hausu da faɗa tana cewa ” meye kuma na kuka bayan Allah ya dawo dake lafiya , Diyana batayi magana ba suka ɗunguma zuwa palo zama sukayi a kujera momy sai kallon ɗiyar tata takeyi ga wata muguwar ramar da tayi kuma jikinta ta gefen fuskarta ga cizon sauro nan, jinina kai momy tayi batare da tace komai ba , Tunani ta fara batada ikon hana Alhaji tafiya da Diyana ƙauye . Jin hirarsu ce ta dawo da ita daga duniyar tunani Diyana tace ” momy mai kuka dafa ne ? Afreeda ce tace ” tuwon shinkafa miyar shuwaka , Yamutsa fuska tayi kana ta ƙara da shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace ” acan ma mutum baiji daɗi ba , anan ma bazanji ba ?” momy dai batace komai ba sbda rigimar Diyana tafi ta ɗan yaye wani time ɗin , Diyana ce ta miƙe tana fushi ta nufi fridge hango fanta tayi mai sanyi hakan ya sata ɗaukowa ta ciro ragowar cake ɗinta a hanbag tafara ci kamar an aikota , Niko nace su Diyana an daɗe ba’a haɗu ba . Saida ta shanye babbar kwalba kana tayi gyatsa ta maida kanta ga kujera ta jingina , Momy da Afreeda banda kallonta babu abinda sukeyi , Afreeda ce ta ƙunshe dariya tace ” sis yaushe rabon da kisha fanta ?”. Shigowar dady ne ya hana Diyana bawa Afreeda amsa . Momy ce ta miƙe tayi masa barka da dawowa tare da karɓo wata takarda dake riƙe a hanunsa , Diyana da Afreeda ma sannu da dawowa sukayi masa , Cikin farinciki ya amsa yace ” daughter ansha ƙauye ina kika baro Hajiya ?” Diyana ce tace ” ai tana gaishe ka wai sai tazo , Madallah dady yace ” ai takusa zuwa ma nanda two weeks insha Allah , sunkuyar da kai momy tayi dan batada ta cewa a wanan gaɓar haka dai suka dinga hira da dady . Afreeda ce suka haɗa ido da Diyana tayi mata alamun ta, taso akwai labari da sauri sukayi ciki suka bar momy da dady a palo suma tashin sukayi kowa ya watse akabar palon shi kaɗai . bayan sunyi sallahr magrib Afreeda ta gyara zama ta dawo kusa da Diyana tace ” my sis kinsan me ? nayi sabon saurayi a bikin Hindu da naje shekaran jiya , Diyana ce ta dubi Afreeda kana tace ” sis karfa ace soyayya zaki fara a ƙarancin shekarunki yanzu fa kina 18 years ne amma kike maganar soyayya . Ɓata rai Afreeda tayi tace ” haba sis mai yasa aduk lokacin da na kawo miki shawara sai kin nemi hanani yin abu , Afreeda tafara kuka. gyara zama Diyana tayi ta rungumo Afreeda tace ” my little sis ina sonki banison ta sanadiyar soyayya karatunki da brain ɗinki su shiga wani hali , so yanzu dai kibari zuwa tomorrow zamuyi magana karki damu . Haka dai suka bar zancen sai zuwa gobe amma ran Afreeda ya ɓaci bata bari sistern ta ‘ ta fahimta ba kasancewarta mace mai fushi sosai. Kawar da ɓacin ran tayi ta hanyar cewa ” sis ya kikayi da zaman village ? naga kin rame sosai kuma kinyi baƙi . Hmm kedai bari wlh nasha wuya ko a mafarki bana burin sake zuwa wanan ƙauyen sbda wlh ni nasan halin da na shiga ga tsohuwar nan masifa tayi mata yawa , Diyana ce ta kwashe labarin bidirin da tayiwa Hajiya aikuwa suka dinga dariya . Afreeda ce ta riƙe haɓa tace ” sis ashe wanan tsohuwar zata dawo gidannan ? gaskiya tana dawowa mun shiga uku . “hmm ai bakisan wani abu ba wlh inhar tadawo saita gwammace dan wlh momy zata dinga sawa ido , muma dai ba barinmu zatayi ba aikuwa zata gwammace kiɗa da karatu dan wlh duk dare sai na horata dariya suka sa kana ko wacce taje toilet tayi wanka Afreeda saida ta fita sbda cikinta baya jurar yunwa ,tasami abinda zatasa a bakin ta suna ƙarasa salolinsu kowa ya kwanta . 9am kow yayi sallahr asbha ya koma bacci kasancewar yau weekend sai 11:am suke breakfast , Ƴar aikin su na kitchen tana ta haɗa musu abinci , Afreeda ce ta fara motsawa brush ta shiga toilet tayi kana ta nufi kitchen dan cikinta baya yimata uzuri , Diyana kam anata sharar bacci anji katifa mai laushi lol, Ƙarfe sha ɗaya kowa ya hallara a palo kan dining momy dady Diyana dakuma Afreeda kowa yai wnka da shiga ta alfarma a jikinsa , bayan sun gaisa ne kowa ya maida hankali ga cin bincinsa saɓanin Diyana da takecin soyayyen dankali da shayi , Dady ne ya kalli momy yace ” Hajiya fa gobe zata zo Fatima , momy ce tace “Allah yasa muga goben lfiya Alhaji amen dady yace ” Diyana da Afreeda suka haɗa ido kowacce ta buɗe baki basu bari dady ya gansu ba kowacce ta maida hankali ga plet ɗin gabanta , suna gamawa dady ya miƙe ya shige ciki binsa momy tayi kasancewar tun jiya ya gaya mata sunada meeting a office . Diyana ce tace ” wlh dady yasa wanan tsohuwar a rai bai san inhar ya kawota aiki zata basa ba hmm , haka dai suka dinga hira wacce duk ta Hajiya ce dakuma abubuwan da zau shirya mata . gari na wayewa dady ya fara ƙwalawa driver kira da azama ya ƙaraso ya durƙusa gaban dady, Dady ne yace “inason ka ɗauko Hajiya ne amma karka bari ta kwaso komai iya kayanta kawai, Angama Alhaji driver yace ” kana ya miƙe . Lokacin da ya ɗauki hanya ƙarfe tara na safe sai dai muyi masa fatan isa lafiya , Da isarsa yai sallama Hajiya na girka daddawa gidan ya gurme da wari ya durƙusa ya gaisheta amsawa tayi tana cewa” lalle lale da ƴan binni barka da zuwa ,yawwa driver ya amsa Hajiya . Wanke hannu tayi tace ” to shiga ɗakin man, da shigarshi Hajiya ta miƙo masa kwanon fura da nono aikuwa driver yayi murna sosai dama yana abota da fura da nono ita kuma Hajiya bata rabo dashi , sai da ya cika cikinsa dam sanan ya dubi Hajiya dake zaune hankalinta na kan kalwarta yace ” Alhaji ne yace ” inzo in taho dake , hajiya ce tace ” har satin ya zagayo ne dahar zai turoka , driver ne yace ” to yadai ce inzo in tafi dake , jinjina kai Hajiya tayi tace ” leƙa ƙwar gida ka kiramin yaro to driver yace ” ya miƙe yana fita yayi sa’ar ganin wata yayarinya tana doso gidan , ina wuni tace masa ‘amsawa dtiver yayi da lafiya lao , Nan gidan zaki shiga? Eh yarinyar tace ” okay suka shiga a tare , tun daga tsakar gida Tinene tafara wankawa Hajiya kira ,kaka kizo Talatu ta aikoni wai ki hammata gihiri , Hajiya na mita ta fito tana cewa Tinene kiyi maza ki hirya yau binni zamu kwana ki gayawa Talatu ta haɗo miki kayanki , Driver dai komawa mota yayi yabarsu a gurin. Wani uban tsalle Tinene ta doka harda taka rawa tace “hikenan zamu zamo ƴan binni tafara tafiya tana yarfe hannu tasa dariya , takuma canza tafiya wai zatayi kalar tafiyar Diyana . Hajiya dai tashige gurin shirya kayanta , Kamar wacce aka zabura tayi waje da gudu driver dake mota ya hangota dariya yasa yace ” ƴan matan ƙauye hhh. Tinene na isa gida tafara wankawa Talatu kira fitowa tayi tafara yimata faɗa akan wanan kiraye kirayen da takeyi tun daga ƙofar gida , to albishir zan yimiki yau kaka zata binni , Da sauri Talatu ta ajiye ledar gyaɗar da take ɓarewa tace ” kai dan Allah ?” wlh kuwa to zomu tafi gidan Tinene ce tace ” a’a nidai kayana zan tsaya shiryawa Talatu bata jira ta saurari Tinene ba tayi waje , a ƙofar gida ta ƙarasa sa mayafin. Tana shiga tasami Hajiya a tsakar gida ta fito da buhu , cikin azama ta ƙarasa tace ” inna wai yau zaku tafi binni ? gashi kuma kina gani , ina tace tana ciciɓar buhun , Talatu ce tace inna yanzu tafiya zakiyi ki barni ?” kuka Hajiya tasa tana cewa ” zan dinga zuwa karki damu nima ba ason raina zanyi tafiyar nan yau ba ,ina Tinene tazo ta kawo buhun nata in haɗa da nawa Talatu ce ta share hawayen da suka kwaranyo mata tace “inna inkika tafi wazai dinga bani wani abin idan na nema , Hajiya ce ta kunce ɗaurin zaninta kana ta ciro kuɗi a lalitarta, sunkai dubu goma ta miƙawa Talatu da keta share idanunta da mayafi , Cikin farinciki ta karɓa tana godiya . Hajiya tasan wuyar da Talatu kesha a gidan mijinta wata rana baya bada kuɗin cefane kokuma yace” ta auni masara ta kai niƙa babu kuɗin girkawa hakan yasa Hajiya take matuƙar tausaya mata amma bata cika nuna mata a fili ba sbda gudun wata rana , Hasali ma shine yasa takeson ɗaukar Tinene duk da ta zamo budurwa dan a ƙalla zatayi shekara goma sha huɗu , Hajiya nada tabbacin kakar baɗi ubanta zai ce aure zaiyi mata kuma gidansu haɗin zumunci sukeyi . Hajiya ce ta ƙara kai kallonta ga Talatu tace ” inada buhun masara a ɗaki dana wake kuma ga shinkafa nan rabin buhu akwai mangyaɗa , duk ranar da bakida kayan awo ga mukulli nan kizo ki buɗe , Wani sabon kukan Talatu ta ƙara fashewa dashi tana tunanin kowa ya rasa mahaifiya yayi kuka tabbasmahaifiya itace abin alfahari ga kowane ɗa kuma itace take sanin ɗanta yaci ko bai ciba dazarar taga bai ciba zata fasa cin nata ta miƙa masa , haka dai sukayi sallama jikinsu duk a mace Tinene kam murna ta cika zuciyarta burinta taje birni ta waye tadinga kalar tafiyar Diyana dan komai na Diyana birgeta yakeyi . Hajiya na kulle ƙofar ta miƙawa Talatu mukulli takuma ce mata akwai dambun nama a kwallah ki ɗauka mukan mun fito. [31/05, 12:42 am] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 7 & 8 NA Wattpad momislam2020 Facbook mom islam mon islam Email: Zainabhabibu@gmail.com Whtsapp: 08141799224 To Inna Allah ya saukeku lafiya cewar Talatu , Hajiya ma dauriya takeyi haka dai akasa abubuwan da takeso suka shiga mota , Tinene ta ƙwalawa Talatu kira , tana matsowa tace ” Talatu dan Allah ki gayawa Bashiru nayi tafiya , maketa Talatu tayi kana tace ” bakida kunya ne kifa kintsu Tinene rayuwar binni ba irin tamu bace ki nitsu ina gaya miki , sallama suka kuma yi motarsu ta tashi zuwa garin shugaban ƙasa wato Abuja , Basuyi wata tafiya mai nisa ba dan basu fita a kano ba Hajiya ta tsayar da driver tana cewa” kai baka tsayawa mutane suyi fitsari ne ? ko kuma so kakeyi yarinya tayi a wando , Ayi haƙuri Hajiya driver yace yana parking ɗin motarsa a gefen titi fita sukayi tare da wani galan da suka ɗuro ruwa a cikinsa, Hajiya ma fitsarin tayi suka dawo mota . Fitarsu Kano keda wuya Tinene ta hango mai gasa masara shirin kuka tahau yi tana cewa Hajiya itafa yunwa takeji , Shidai driver badan uwar mai gidanshi ya ɗauko ba babu abinda zai hana baiyi musu magana ba , Hajiya ce tace ” kai tsaya a siya mata wani abun tasa a bakin salati , Driver ne yace ” Hajiya nan basu siyar da komai fa , Tinene ce ta karɓe da cewa ga mai masara can wlh ko ita nasamu ai ƴaƴan cikina sa barni na huta , Hajiya ce ta ciro nera ɗari tace ” driver ya siyo musu ƴan uku hamsin , driver yasan babu hakan yasa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa mai masara dan yasan inhar yakoma bai siyo ba Hajiya zata iya tsigaleshi , yana miƙa musu ,ya tada mota . Sunyi tafiya mai nisa sbda sun wuce garuruwa da dama , jin motar tayi shiru yasa shi leƙa wa ta mudubi , hamdallah driver yayi ganin mai damun mutane tayi bacci , cikin ikon Allah sai gasu a Abuja har sunkusa layin su , Hajiya ba taɓa zuwa tayi ba shiyasa tayi gum da bakinta , Horn ya shiga yi , mai gadi ne ya wangale get ɗin yana ɗaga musu hannu , Hajiya ƙarewa gidan kallo takeyi badan ta ɗan yarda da drivern nan ba da zata iya cewa gidan ƴan yankan kai ya kawota amma bari ta zuba masa ido tagani , Yana parking ya fito tare da buɗewa su Hajiya , Tinene tayi bacci Hajiya ce ta ɗaka mata duka a razane ta tashi takalli Hajiya sanan ta kalli ina suke , mutsuke ido tayi tace ” alkur’ani da gaske ne nayi mafarkin gani a wata sabuwar duniyar Hajiya ce ta sharara mata mari kana tace ” zaki fito ko zaki zauna ni gaba zanyi dan inama tunanin kamar ba gidan Alhajin ya kawomu ba sbda babu ko wulƙawar mutane sai tsintsaye , Tinene ce ta fito tana shafa kumatunta , Ta nufi gurin mai gadi , gaishe sa tayi kana tace ” muna neman masu gidannan , mai gadi ne yace “ciki zaku shiga bazasu jiku daga nan ba amma kuzo muje , Sai da ya kaisu har bakin wata ƙofa mai glass kana ya ƙwanƙwasa , Da sauri ta fito jikinta sanye da kayan bacci da alamu bugun ƙofar ne ya tasheta , Tsawa ta dakawa mai gadi kana tace ” waye ya baka izinin shigowa nan ?” durƙusawa yayi har ƙasa yana bawa Diyana haƙuri saboda kaf cikin ma’aikatan gidan tsoronta sukeji sosai , Kasancewarta mace mai wani irin hali wato ƙasai ta bugu da ƙari kwarjini , Hjiya ce tayi saurin leƙowa tana cewa ” waye yake mgna Diyana da bata gane ko wacece ke magana ba kasancewar Hajiya na can baya mai gadi kuma yana kusa da ƙofar ,Tinenuwa kumatanacan gurin tsintsaye tana kallonsu , Diyana tace ” nice nan Diyana , Ai da sauri Hajiya ta matso tana cewa kauce kibani guri iyayi yayi muku yawa ,in mutum zai shigo har sai an tambaya , tunda Diyana ta tabbatar Hajiya ce ta iso tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta Allah ne kaɗai yasan irin abinda zuciyarta ke shirya mata, Kutsawa Hajiya tayi tana tana sana’ar tata wato mita , shikam mai gadi ya wuce tuni . juyawar da Tinene zatayi taga babu Hajiya ai da gudu ta ƙara taje ta tura ƙofar ta shige , Samun su Hajiya da momy da Diyana da Afreeda tayi suna zaune a kujera anata gaisawa , samun guri tayi itama ta zauna tare da cewa ” ina wuninku , lpy momy da Afreeda sukace banda Diyana daketa yamutsa fuska , Hajiya kam anbaje akan kujera anata zubawa momy labari , Tinene ce ta kalli Diyana ta nunata da yatsa tace ” kaka wanan ce tazo gidanmu hekaran jiya ko ?” eh Hajiya tace ” ai wanan da kike gani bansan gadon waye tayo ba , sam batason mutane . Momy ce tayi dariya kana tace ” ai wlh Hajiya nima ina tunanin hali irinna Diyana amma inaga halitta ce kawai , Hajiya ce ta gyara zama tace” inason Alhaji yazo muje gurin wani babban malami ƙila tanada matsalar aljanu dan naga kamar ba ita kaɗai bace , Tuntsirewa da dariya Afreeda tayi tana kallon bakin Hajiya sai kai lomar shinkafa takeyi ita da Tinene , Kuma kai wata lomar Hajiya tayi tace ” tun lokacin da tazo gurina naga take taken hakan , momy ce tac” to Allah yabasu haƙuri , amen suka amsa banda Diyana da haushi ya cikata , Cikin ranta tace wato wanan tsohuwar tun yanzu zata fara ɓatamin rai ko ?” to wlh mu zuba zata gane batada wayo ta miƙe tayi bedroom ɗinsu, da yamma bayan la’asar kowa ya shige ɗaki Hajiya da Alhaji ne a zaune sai Tinene dake ƙasa a gefe tana kallo a tv hango wani mutum tayi yana kuka da alamu wani abinne ya sameshi a shirin film ɗin ai itama tahau share hawaye tana cewa” Allah sarki hankalinsu Hajiya bai kai gurinba sai da taji anja mata ƙafa tayi ƙasa ,wani wawan ihu Hajiya tasa tana riƙe da gurin ,Tinene da tayi abun hankalin na gurin tv tana kuma kaiwa Alhaji shirin naushi , Kaucewa Alhaji yayi yana tunanin anya wanan yarinyar mai lafiya ce kuwa ?. Sannu Hajiya dady yace ” yana kallon ƙafarta , Fitowar momy da Diyana da Afreeda ne yasa dady cewa zoki ɗaga Hajiya da azama momy ta ƙaraso tana cewa mai ya sami Hajiya ? abinda ya faru dady ya gayawa momy , ji sukayi an kwashe da dariya ,juyawa sukayi dukkansu harda mai kallo , ba kowa bace sai Diyana da ta riƙe ciki tana dariya , dady ne ya ɓata rai kana yace ” ke Diyana kinci gidanku dan bakida kunya Hajiyar ce abin yiwa dariya kina gani tana fama da ƙafa wanan sakaran takuma jibga mata naushi , Da gudu Diyana tayi ɗaki saboda wata sabuwar dariyar ce takuma kawo mata ziyara, riƙe haɓa Hajiya tayi tace “Faɗimatu kingani ko kinga abin da nake gaya miki ko ?” to Alhaji tun wuri kayiwa tufka hanci tun kafin suyi mata illa , dady da bai fahimci abinda Hajiya take cewa ba yafara tambayar mai ya faru ,mayar masa Hajiya tayi kana ta ƙara da cewa ” a gaggauta wlh . Itadai momy batada bakin magana sai eh da eh , dady ne yafara yiwa Tinene faɗa yake gaya mata mutanen tv ba fitowa sukeyi ba kuma basujin mutane , shiru tayi kai kace ba ita ta aikata ba , Miƙewa Afreeda tayi ta nufi bedroom ɗinsu tinda comedy ya ƙare , da dare yayi bayan isha’i mai aiki ta jera musu abinci a dining , Hajiya tunda taga anan za’aci abinci tace ” bata yarda ba a kawo mata nata ƙasa , babu mai yimata musu kaf ɗinsu momy ta sauko mata dashi akan faranti , Diyana bata fito cin abinci ba sai Afreeda da ta zuba farfesun kifi tana ci , ina daughter ?”dady ya tambayi Afreeda , Afreeda ce tace ” tana bedroom tunda tayi sallah ta kwanta , Buɗar bakin Hajiya tace ” ba dole kaga mutum kamar muciya ba babu auki saboda baici abincin gidansu ya ƙohi ba, Kai lomar tuwon shinkafa tayi tana mita , Tinene dake zaune da shinkafa da miyar kifi a gabanta tace ” Allah sarki Talatu ko taci hinkafar da kika barmata oho , Hajiya ce ta dubi Tinene tace ” maza kiyi kici kije ki kwanta , Faɗimatu ki nuna mata ɗaki karta cika mutane da surutu , Miƙewa dady yayi ya yiwa su Hajiya sallama ya shige ciki . Washe gari takama laraba Diyana da Afreeda zasuje bikin wata classmate ɗinsu ko wacce burinta tayi kwaliya ta kece raini kasancewar yarinyar wani babban ma’aikaci ne amma bai kai dadynsu Diyana kuɗi ba, Kar mai karatu ya ɗauka shima mahaifin amaryar talaka ne , no yanada kuɗi sosai kuma babu wanda bashida labarin mahaifin amaryar harnyanzu ana damawa dashi , Sai dai shi mahaifinsu Diyana wani attajiri ne wanda ko shi bai san iya adadin dukiyarsa ba , kasancewar sa mai kuɗish sosai , Kayane anko suka ɗinka kala uku uku kowane ɗaya zaiyi 50k ɗinki kuwa anyi masa na 5k atamfa da less da material babu na kushewa a cikinsu , Yau akeyi ɗaurin aure , in suka tafi yau sai gobe zasu dawo . Diyana ce ta kalli Afreeda tace ” sis yanzu mai zamu kaiwa amarya a matsayin tamu gudun mawar kinsan dai in muka bata kuɗi ba karɓa zatayi ba , Afreeda na saka skirt da ƙyar tace ” sis yanzu dai gurin momy zamu dan wlh nima kaina yayi zafi burina inganni a gurin bikinnan , ƙarfe huɗu duk sun gama shiri Maltina Diyana ta ɗauko a fridge kaɗan tasha ta riƙe ragowar a hanunta suka nufi bedroom ɗin momy . Samunta sukayi tana sa kaya ,zama Diyana tayi a bakin gado ita kuma Afreeda ta zauna a kan stool dake gaban mirror , Kallonsu momy tayi da fara’a tace ” harkun shirya ne ?” eh suka ce Diyana ce ta shagwaɓe fuska tace ” mom munrasa abinda zamu kaiwa Khairat a matsayin namu kyautar , riƙe baki momy tayi kana tace “karku damu ga wani haɗin humra da turaren wuta da nasa aka yimin haɗinsa tun daga maiduguri so ku tafi dashi kawai duka inyaso zanyiwa Hajiya Falmata magana ta ajiye min in tanada ragowa , rungume momy sukayi suna godiya , Afreeda ce tace ” momy bakice munyi kyau ba , dariya momy tasa tace ” ai wanan kwaliyar taku ko maƙiyi , sukasa dariya dukkansu lokacin da suka kammala shiri ƙarfe biyar na yamma , sunyi kyau kamar ka sacesu ka gudu Diyana ce ta ɗora baƙin glass ɗinta a ido kasancewar ta ma’abociyar son sakashi amma Afreeda bata damu da sanyawa ba, ƴar aiki suka aika kiran driver , sai gasu sun dawo a tare Diyana ce tace ” driver sabuwar mota zaka fito da ita , kafin ta ƙarasa magana driver yace ” to Hajiya angama insha Allah , fitowar momy taci karo dasu sai ga Hajiya nan ta ɓullo tana ɗingishi , wayar Diyana ce ta fara ring ko kallon Hajiya bata yi ba ta ɗaga wayar , Khairat ce take magana kamar zatayi kuka , Haba sis kufa ake jira a gurin reception ɗinnan pls kuyi sauri , Hajiya ce ta gyara tsayuwarta tace “yau naga duniya yara su koma kamar zabiyoyi jibeku ko kyau bakuyi ba , Afreeda da hankalinta yayi gurin shagali tace ” bye momy Hajiya bye tana ɗaga musu hannu , ganin cikinsu babu wacce ta kulata yasata cewa ” ke zabiya zoki tafi da Auta itama taga gari , Ai da gudu suka fice, Suka shige mota sai gurin biki , sunyi tafiya mai nisa kana suka iso ƙawataccen gurin da idan ka ganshi sai ka rantse a ƙasar waje ne , iya tsaruwa gurin yayi, suna sauka a mota na hango wata budurwa batada jiki tana sanye da doguwar riga fara ta yafa mayafin rigar a kanta , da gudu tayo gutinsu Diyana tana faɗin barkan ku sists wato munce bamuson let sai da kukayi ko ? ga anty Khairat can taƙi sakin jiki wai dan babu anty Diyana , lumshe ido Diyana tayi kana tace “am sorry amaryar mu tayi haƙuri ganinan na ƙaraso , Afreeda ce taja budurwar mai suna Siyama sukayi gefe ita kuma Diyana ta shige ciki , Da shigarta kallo ya dawo kanta kowane saurayi mai ji da kansa ita yake kallo hatt MC ma ita yake kallo , Gashi dai kayane da kowa na gurin yasan tsadarsa da kyansa kuma ba wata fayattaciyar makeup tayi ba amma hakan bai sa sundena kallonta ba , Cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da gurin zaman amarya, Tun daga nesa Khairat tafara fara’a da dariya ɗauke a fuskarta , Diyana ma maida mata da dariyar takeyi tana tafiya , Batasan da mutum a gabanta ba ta bigeshi wayarta ta faɗi ƙasa ta watse gefe , A, zuciye ta ɗago kai ta waysawa wanda ta bige harara kana ta ƙara masa da mari , Baice komai ba sai shafa gurin da yayi kafin kace me hankalin kowa ya dawo gurinsu bodyguard ne guda uku suka yi kana da shirin duka , Matashin saurayin ya dakatar dasu yana huci . Durƙusawa Diyana tayi ta cire sim ɗinta tabar wayar a gurin , ta ƙarasa gurinsu Khairat da taketa zubda hawaye tana kallon Diyana , zama Diyana tayi takai dubanta ga Khairat da idanunta sun fara ja tsabar kuka , “afuwan amaryar mu cewar Diyana , Kamill wato ango da yanzu ya dawo gurin zamansa , kasancewar yaje bawa babban amininsa haƙuri ya dubi Diyana , yace “amma Diyana kinyi ganganci maiya kaiki kula wanan bawan Allahan?”, Lumshe ido Diyana tayi tace ” Kamill sanin kanka ne bana ɗaukar raini shiɗin waye waye babansa ? shiii!!!, Kamill yace ” karki ƙara magana , Ƴan matan dake gefe sai kallon Diyana sukeyi masu gulma nayi kowa yana ganin Diyana batada tarbiya wasu kuma daga can gefe , suna cewa ai gara da tayi masa haka , Maganin mutumin da bai ɗauki ɗan adan da daraja ba kenan , Shigowar Afreeda kenan taga anata nuna Diyana , kai dubanta tayi gurin da Diyana take zaune , ganin fuskarta babu walwalah yasata ƙarasawa da sauri , Ruƙo hanun Diyana tayi tace ” my sis maiya faru ?” kiyi haƙuri kinga na daɗe ko ?” munje duba wata abaya ne da za’ayi yayi wanan sallahar , lumshe ido Diyana tayi kana takuma buɗesu tace ” karki damu sis damuwata da ban kizo ki zauna , Khairat itama jikinta duk yayi sanyi , haka dai aka kira abokan ango da ƙawayen Amarya , farko sunan Diyana aka fara kira na biyu kuma babban aminin ango wato Kamill , sai da gaban Diyana ya faɗi , komawa gurin Kairat tayi ta raɗa mata a kunne cewar sis bazan iya rawa da wancan banzan ba…..! [31/05, 12:43 am] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 9 & 10 *AREWA WRITERS ASSOCIATION* Sa sauta murya Khairat tayi kana tace ” pls kiyi haƙuri kije na lokaci ɗaya nefa , Badan Diyana taso ba ta wuce ta nufi gurin da aka tanadar musu na rawa , Mc ne yasa mutanen gurin tafa musu , ya fara kwararo musu yabo , kaga matashin saurayi mai ji da kansa ƴan mata ma wawarka sukeyi , kai ku tafawa Alhaji Kamill ɗa ɗaya tilo a gurin mahaifinsa wato Alhaji Safiyan gidan kuɗi . A zabure Diyana ta ɗago kai takai dubanta ga Kamill da shi hankalinsa ma ba a gurinta yake ba ta kawar da kai , innalilahi ragowar ta maƙale mata ma maƙoshi , tasani ubansa ba sa’an ubanta bane yafi ubanta dukiya hatta mahaifinta yana girmama Alhaji Safiyan kuma yafi mahaifinta suna kasancewar sunansa ya zaga ƙasashe da dama harda na ƙetare , Duk da shima ubanta sunanshi ya shahara amma ko kwatan na uban Kamill bai yi ba , Jiyo maganar Mc tayi yana cewa ” an gaisheki babbar ƙawa aminiya kyakyawa kuma kuma fasihiya a fanin iya kwaliya kai kubata tafi , kowa yakama raf raf hankalin mutanen duk ya dawo gurinsu , mc ne ya bada umarni aka sanya waƙar da akayi ta biki , Kamill rawa yakeyi tsakaninsa da Allah matsowa kusa da Diyana yayi yace ” ƴan mata ki taka man karki bada manyan mata har video akeyi fa , wanan sunkuyowar da Kamill yayi yana yiwa Diyana magana wasu abokan Kamill suka fara ɗaukarsu hoto aikuwa sun bada kala , Ɗan takawa tafara a hankali jikinta a sanyaye amma tanajin inhar Kamill ya kuma ɓata mata rai babu abinda zai hanata ci masa mutunci koda komai zai faru , tsayar da kiɗan akayi mc yace suje su huta , ran Diyana ya ɓacci sosai musamman da zasu sauko Kamill yakuma sunkuyawa yayi mata magana . Khairat ce ta janyo Diyana tace ” nagode sis nasaki abinda bakiso ko am sorry , rufe mata baki Diyana tayi da cewa ” a’a sis karki damu wancan banzan ne ya ɓatamin rai badan haka ba da komai zai tafi normal, ƙarfe 8pm an tashi anyi su yanka cake da hotuna, Afreeda ce ta kamo hanun Diyana tana cewa sis momy na kira wai mudawo gida okay Diyana tace “. Bayan sun bawa ƙanwar Khairat abinda zasu bata sukayi sallama , kasancewar Afreeda ta kira driver yazo ya ɗaukesu , suna fitowa sukaci karo da Kamill yana waya yana murmishi , tsaki Diyana taja kana ta janyo Afreeda sukayi mota , wani killer smile Kamill yayi ya zura hannayensa cikin aljihun shaddarsa , ganin motarsu na shirin tashi ya koma gefe ya tsaya tare da ciro wayarsa , numbar bodyguard naga ya dannawa kira ko 3 mins ba ‘ayi ba sai gasu nan sun taho sun tsa tsaya a gabansa tare da sunkuyar da kai , sukace barka prince yawancin abokansa da sunan suke kiransa amma ba kowa yasan da wanan sunan ba ,saboda wasu dalilai , haɗe rai yayi yace ” kunga waccan motar maza kubita karku bari su gane okay sukace , cikin hanzari suka shige mota , Sukabi motar da yanzu ta fice daga harabar gurin. Tafiya drivern nasu yakeyi cikin ƙwarewa ba kowa zai san yanabin wata mota ba kasancewar ko kwana motarsu Diyana batayi ba . Tunda Diyana ta shiga mota tafara tuno abinda ya haɗasu da kamill a zahiri itama tanada laifi amma sam batason raini hakan yasata yimasa rashin mutunci ,sai huro hanci takeyi . Afreeda ta lura da yanayin sis ɗin nata amma bata kulata ba kasancewar tasan halinta inta fiya shiga harkarta a time ɗin da take cikin baƙin ciki sukan iya ɓatawa su kuwana ma basu shirya ba , A haka suka isa gida babu mai cewa komai , Bata jira driver yazo ya buɗe motar ba ta fice zuciyarta nayi mata ƙuna , ko sallama batayi ba ta shiga palon ganin Hajiya da Tinene a palo yasata yamutsa fuska ta wuce bedroom ɗinta , Hajiya dake zaune ta riƙe haɓa tana jinjina lamari irin na Diyana , A fili tace ” nikam wanan wace irin yarinya ce batasan darajar mutane ba , Tinene dake zaune gefen Hajiya tace Hajiya sufa ƴan binni basu damu da sallama ba , Hajiya ce ta ranƙwasheta kana tace ” badai duka ba ita wanan mai zuciya kamar faɗa wuta bansan gadon wa tayo ba, Sallamar Afreeda ce ta katse musu zance suka amsa tace ” sannu Hajiya , Washe baki Hajiya tayi kana tace ” ywwa ƴar albarka kun dawo lafiya ?” lafiya Afreeda tace” ta wuce ciki . Kai tsaye bedroom ɗin momy ta wuce , da sallama ta shiga ta gaida momy , kun dawo sai yanzu ko ? momy ta jerowa Afreeda tambayoyi , am sorry mom wlh matsala aka samu amma yanzu komai yai normal , Momy dake kallon fuskar Afreeda tana nazrin ta tace ” ina Diyana ?” tana bedroom , Kiramin ita, Tom Afreeda tace ” Afreeda na fita momy tashiga tunani tasan duk lokacin da ran Diyana ya ɓaci bata wai wayar kowa har ita ma to yau kuma maiya faru ?” batada mai bata amsa yasata zama gefen gado tana jiran shigowar Diyana , A’ ɗakin Diyana Hajiya ce tsaye a bakin ƙofa tana balbale Diyana da masifa akan rashin ladabi , kuka Diyana tasa mai sauti dan a halin yanzu babu abinda zatayi zuciyarta tayi mata daɗi sama da kuka , Tafa hannu Hajiya tafara tana salati tace ” to sharri zakiyimin ? shigowar Afreeda ne yasa Hajiya yin shiru ta juya bata ƙara magana ba . Dafata Afreeda tayi kana tace ” my sis momy na kira pls ki share hawayennan karki ɗaga mata hankali , To kona share hawaye mezan ce mata banison tasan irin target ɗin da na shiryawa wancan jakin dan wlh tunda yasani zubar da hawaye nima sai na wulaƙantashi , Afreeda ce tace ” sis wai kina nufin Kamill ?” eh Diyana tace tana girgiza kai alamar tabatarwa , Wani marayan nunfashi Afreeda ta sauke kana tace ” sis ki janye wanan maganar bazaki iya da Kamill ba mahaifinsa yafi dady komai hasali ma dady zai iya zama ɗan aikensa…..! wani mahaukacin mari Diyana ta sakarwa Afreeda tare da nuna mata hanyar waje, why zaki ƙara ɓatamin rai kinada hankali kuwa ?” Afreeda ficewa tayi tana kuka a ranta kuwa cewa ” tayi da badan tunda suka taso bata taɓa yiwa Diyana rashin kunya ba , Da yau sai sunyi dambe , ficewarta shine mafita, Fitowa tayi daga sashin ta rufo door ɗin , mai gadi na hangota yafara miƙo gaisuwa dan jininsu ya haɗu da Afreeda kasancewarta batada wulaƙanci , Yanata gaisheta amma ko saurarar shi batayi ba , bai damu ba yasan hakan tana faruwa in tana cikin fushi bata cika magana ba , Gurin furannin gidan ta nufa tanata tsinkarsu tana jefarwa , miƙewa tayi ta dawo cikin gida , Samun momy da ƴar aiki tayi sunaya jera abinci a dining saita nutsuwarta tayi , kana tace ” sannu da aiki momy, murmishi momy tayi kana tace ” to ayi magrib azo aci abinci food is ready , sunkuyar da kai Afreed tayi tace ” okay momy ta shige ciki , jinjina kai momy tayi dan taji faɗansu na ɗazu amma ba komai nasu take shiga ba tunda daga sunyi faɗan suke shiryawa kamar ba suba , Kai tsaye Bedroom ɗinsu Afreeda ta wuce , Samun Diyana tana sallah yasata shiga toilet tayi alwalar itama ta ɗauki sallaya tafara sallah , bayan sun idar dukansu, Diyana ta rungume Afreeda tace ” am sorry my sis kiyimin afuwa karkiyi fushi da sistanki tana buƙatar taimakonki , Sauke ajiyar zuciya Afreeda tayi tace ” karki damu komai ya wuce momy na kiranmun, Afreeda tayi hanyar waje zata fita Diyana ta riƙo mata hannu , haɗe hanuwanta Diyana tayialamun neman alfarma tace ” my sis pls karki sanarwa momy abinda ke fariwa kinsanta da saka abu a ranta,oky dont worry i promise bazan faɗa ba zomuje kici abinci yau abinda kikeso ne akayi, Menene shi?” Diyana ta tambayi Afreeda, plantain and egg Afreeda tabata amsa da sauri suka nufi dining kowacce fuskrta a sake, Sannu momy , Ywwa daughters harkun fito ?”. Eh momy . Hajiya dake gefe a zaune a kan kafet itada Tinene tace ” to sabon salo uwar waye bazaku cewa hannu ba , yara sai kinibi bin tsiya to ba mutuwa zanyi ba , Tinene dake gyara zani tace ” kaka wanan abin yayi daɗi aɗan ƙaramin asamin kabejin da yawa , momy ce ta ƙwalawa Nana ƴar aikinsu kira tace ” ta daɗowa Tinene kabej kasancewar Hajiya ce tace ” dole ayi mata kwaɗon kabeji da ƙuli kuli , Aikuwa basuci abincin kirki ba sai kabeji , Afreeda ce ta ƙunshe dariya yanda taga Hajiya na kwasar kabeji to Allah ya kyauta . Suna gama ci momy tace ” in akayi isha’i tanason ganinsu , Hajiya ta miƙe tana dogara ƙafa ta nufi ɗakinsu , Sanda Tinene tayi fam da kabeji sanan itama tabi bayan Hajiya ,dan bataga alamar gidan suna wasa da yara ba shiyasa takejin tsoronsu , Bayan isha’i Diyana da Afreeda suka shigo ɗakin momy kowacce na jiran taji metayi , dubansu momy tayi kana tace ” gaskiya kuna shirin bani kunya , Kunga tsohuwar nan duk ranat da ta haɗaku da dadynku wlh zakuji babu daɗi tunda yana amfani da duk abinda ta gaya masa to wlh ku kiyaye , Kuma batun gaisuwa kowacce daga cikinku tadinga zuwa da safe tana gaisheta Afreeda banida matsala dake amma Diyana yakamata ki rage abubuwan da kikeyi ke mace ce fa gidan wani zaki, Haƙuri suka shiga bawa momy da alƙawarin bazasu sake ba lol nidai nasan gimbiya da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa , Allah yayi muku albarka kuje saida safe , miƙewa sukayi kowacce da abinda take saƙawa a ranta . Tunda suka shiga ɗaki , Diyana taketa ƙwafa tana tsaki zama tayi a gaban dress mirror kan wata ƙujera mai kyau ta dubi Afreeda tace ” wanan tsohuwar tafara kaini maƙura, cikin sauri Afreeda ta ƙarɓi zance tare da cewa wlh kamar kin shiga zuciyata dan dazarar dady ya dawo zata iya haddasa mana fitina, Diyana ce tace ” zokiji , banji mai sukace ba naga sunyi dariya harda tafawa , Dare yayi sosai kowa na gidan yayi bacci bakajin ƙarar komai sai na AC da fridge , Diyana ce ta farka dan har bacci ya ɗaukesu tashin Afreeda tayi suka farashirin abinda yakamata suyi , wani jan ƙyale Diyana ta ɗauko kana tace ” Afreeda ta ɗauko mata teddy , tana ɗaukowa suka fara kiciniyar sanyawa teddy janbaki da jan ƙyale , kana suka ɗauko wata hoton fuska , wace suke sawa in zasuyi wasa a school lokacin suna secondary , Nice zansa wanan kekuma ki ɗauki farin hijab ɗinnan kisa ki riƙe teddy ki tabbatar da kin rufe fuskarki…….!. [31/05, 12:44 am] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* 11&12 Afreeda ta sanya farin hijab wanda ya rufe mata fuska ko ina kasancewarsa kamar mai niƙaf , ta ɗauki teddy ta rungume . Sanya fuskar Diyana tayi ta kalli kanta a mirorr ta kwashe da dariya tana cewa yau zamu birkito musu kabej lol. Fita daga ɗakin nasu sukayi suka nufi ɗakin da aka bawa Hajiya , A buɗe ƙofar take hakan yasa basu sha wuya ba suka kutsa kai ciki , Hajiya na kwance ansami katifa mai laushi sai gwarti take kwasa, Tinene na gefenta itama bacci takeyi yau na gangarowa , Afreeda ce ta shafa fuskar Hajiya tana cewa munzo ne muji dalili , Buɗe idon da Hajiya zatayi ai taga kammanni kamar na aljanu ta tashi ta zauna dama ɗakin ba wani hasken kirki sbda tunda suka shigo Diyana ta rage Hasken , mai kuma yau nayi muku bayin Allah ?” Maƙale murya sukayi dukkansu sukace , wayace kizo birni ?” bakisan mun maida ɗakin ki na ƙauye turakar babanmu ba ?” a razane Hajiya ta runtse ido tana shirin kurma ihu , rufe mata baki sukayi da hanunsu dake sanye da hand globe , kikayi ihu zakisha mamaki zamu tafi da jikarki , Tinene da tun ɗazu ta tashi taƙi ɗago kai dan itama Allah ya zuba mata tsoro, Hajiya duk jikinta rawa yakeyi kasancewarta matsoraciya ba ta wasa ba , haɗe fuskarsu Diyana tayi tanata zaro ido cikin fuskar nan jin fitsari yana ɗiga ta gefe yasa Diyana cewa , shine aka jiƙa mana ƴaƴanmu to tun wuri ki kwashe shi kokuma yanzu mu tafi dake ƙasarmu , Hajiya na kuka tana tsane fitsari da zaninta sbda akwai sikel ɗin ciki a jikinta , tagumi ta zuba tana magana , duk inda naje sai kun biyoni?” a ‘garin namu ma baku barni ba ,haka anan ma bazaku barni ba ?” . Hajiya tasa kuka tace ” wlh kakanmu ya cucemu da yabar mana gadon aljanu wayoo mun higa uku , nanfa Diyana da Afreeda suka fara kwasar rawa suna takawa kai kace aljanun gaske , Jiyo tari sukayi ta gefen Tinene , Afreeda ce ta ƙarasa gurin tace ” idan baki tashi ba saimun maidaki akuya , ai da gudu ta miƙe jiki na rawa kan kace me ji kake ɓirrr tana shirin sake musu kashi , Waro ido Diyana tayi tace ” kifito kizo yanzu birnin mu zamu kaiku , Cikin azama Hajiya ta sakko ta durƙusa gaban Afreeda kasancewar tafijin tsoron teddyn hanunta , tace ” kuyi haƙuri yarinya ce batasan komai ba kuyi mata aikin gafara dan Allah , nasanku kunfimu haƙuri to ku ƙara , Afreeda ce ta kece da dariya marar sauti sosai ta dubi Hajiya da ta jiƙe da zufa dakuma hawaye , jitayi tausayinta ya shigeta ta dubi Diyana tafara yimata wani irin yare , gani nayi Diyana ta girgiza kai alamar a’a . Matsowa Diyana tayi tace ” nan ɗakin na uban ubanmu ne yatafi misira kuma yabamu ajiyarsa to kufice kokuwa musa a ɗagaku sama , Tinene da taƙi fitowa daga bayi , Afreeda ta ƙwanƙwasa ƙofar tace ” kigama muna jiranki, ku bakwa ganin mutane a gefenku a kwance zaku shigo mana ɗaki koku bar wanan ɗakin ko gidan gaba ɗaya kokuma mu ɓatar daku daga duniyar …..! kafin su ƙarasa magana Hajiya ta buɗe bayi ta janyo Tinene dake tsaye babu ko wando kasancewar in zatayi kashi saita cire wando , suka nufi palo babu ko magana, Tafawa sukayi Afreeda tace ” zamu gudu , raɓawa sukayi ta gefe suka wuce batare da kowa ya gansu ba , dama momy na can sama sukuma suna ƙasa , Suna shiga bedroom ɗinsu suka fara tsalle sunata dariya , Duba wayarta Diyana tayi lokacin ƙarfe biyu da rabi na dare, kowacce ta nemi gurin kwanciya asuba ta gari. Washe gari da safe kowa na gidan na bacci kasancewar weekend ne sai shaɗaya 11am suke breakfast, Tun shida Hajiya ta tashi taje ɗakin Nana mai aiki ta tasota , Sata ɗora ruwa tayi da abinci , babu shiri tafara kiciniyar abinda Hajiya ta sakata , Da farko dai ruwan wanka aka miƙowa Hajiya cikin sauri ta karɓa tana sakawa Nana albarka , tashin Tinene tayi tazo tayi wanka yau a garinsu zasu kwana , Tinene dake bacci mai daɗi cikin bacci , tace “Kaka ni kibarni nayi bacci kina ganin jiya gudawa tasani gaba , tsabar haushi da ya cika Hajiya tace ” uban gudawa , dan uwaki ni zaki gayawa kinyi gudawa to tun wuri kitashi muje kiyi wanka , dan yau sai Shafa ƙauyenmu , a zabure Tinene ta miƙe ta riƙe ƙugu tace ” wlh babu inda zani , Kaji kaka dai da wani zance , muna hyan hyayi da burodi kice mutafi to yasin ko dafani akeyi nan naga gurin zaman dan haka kima canza tunani , Riƙe baki Hajiya tayi tana tunanin kodai Tinene ta mance halin da suka shiga jiya take batun zama, to bara inje inyi wankan in fito wlh saikin bini bazakisa ubanki ya tambayeni ina kikaje ba , Wucewa Hajiya tayi ta nufi ɗakinsu da ya zame mata abin tsoro tashiga da adu’a tana cewa ” wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir rahim, tashige ta surka ruwan , Bayan tayi wanka ta fito ta , tattara kayanta a buhu ta shafa manta da farin kwali ta sanya kaya ta fito palo. Baccin kuwa ta koma hankali kwance da mamaki inna ta hamɓareta tace ” wlh kitahi kokuwa insa masu gadi su ɗaukeki , da sauri ta tashi tayi ɗakinsu , tana shiga aljanun jiya suka faɗo mata ihu tafara kurmawa tana ƙarawa , a na biyun ne ya tashi mutanen gidan dukansu da sauri momy ta fito tana tambayar lpy kuwa? Hajiya da yanzu take shirin shiga ɗakin dan tsoro ya hanata tace ” leƙa kigani faɗimatu ko aljanu ne , aljanu kuma ? momy ta mai maita , Eh leƙata , Hajiya ta kasa taɓuka komai sai cewa leƙata, shiga momy tayi ta leƙa bedroom ɗin ganin tinene na wanka tana tsala ihu yasa momy shiga tafara tambayar anya lpy kuwa Tinene ? , nan ma hankalin Hajiya yakuma tashi taƙara tattaro kaya tana cewa wlh aljanu sun samu a gaba a gidannan , inna zuwa ƙauyenmu bazan sauka ko ina ba sai gidan malam fari ,dan wlh dole ya yimin istahara akan aljanun gidan Alhaji , Duk da nima na gidana basu barni ba dole naɗau mataki , momy dai jin hajiya takeyi dan ba abokiyar yinta bane , Amma su da basu taɓa jin hayaniyar komai ba amma ace wai gidansu da aljanu , kodai rikicin tsufanne ya motsa , to Allah ya daɗa karewa momy tace ” ta fice , Diyan da Afreeda suna zaune a palo kowacce ranta fess Hajiya zatabar gida , amma basu nuna a fuskarsu ba , Ganinsu a palo yasa momy cewa ” ku bakusan abinda ke faruwa bane ?” yamutsa fuska Diyana tayi tace ” good morning momy , bata amsa ba sai ƙara jero musu tambayar taƙarayi , langwaɓar da kai Afreeda tayi kana tace ” momy munji ihu ne mafa ya tashemu wlh “mai ya faru ne , kuje ku tambayi Hajiya , daganan momy tayi gaba , suna ganin momy ta wuce suka tafa suka miƙe kowacce ta koma gado , Ɓangaren Hajiya tagama shiri tsaf Tinene take jira , itama Tinenen tunda Hajiya tace mata inhar bata zo sun tafi ba to babu ruwanta , Ko ta mance da takarar da aljanun jiya sukayi na cewa zasu ɓatar damu , aikwa babu shiri Tinene jiki na tsuma tace ” zan biki yasin bazan zauna ba , Amma fa zamuyi kewar ruwan hyayi mai madara , Ke dalla can marar tunani lafiyar mu tafi hyayi dan haka mutafi kawai , basa bibiyar ƴan gidan sai baƙi to dole na nemowa Alhaji magani wataran mutan gidan zasu nema , Nafito ina zaure kisameni a can , Tinene dake ɗaura zani tace ” ganinan . Kamill ne zaune a wata ƙayatacciyar kujera ita kanta kujerar abin kallo ce bare wanda ya zauna akan kujerar , dogo ne fari , yanada manyan idanu inka ganshi kamar balarabe , Gashin kannan nasa luf luf kamar wanda ake shafashi ga baƙin sajen da ya ɗan kewaye bakinsa yana ɗauke da pink lips , Yanayin jikinsa kaɗai ya ishi mai kallonsa yasan cewar kuɗi yazauna bai taɓa neman abu ya rasa ba , idan kuɗi yakasa samar masa yakan sa basira , Idan basira ma bata samo masa ba yakansa ƙarfinsa domin ya mallaki abinda zuciyarsa takeso , iyayensa suna zaune a kano unguwa uku , gidansu ya fita daban da shauran gine gine amma shi ba mazauni bane, haka mahaifinsa Alhaji Safiyan gidan kuɗi baya rayuwa a Nigeria , kasancewar sa hamshaƙi , bare uban gayya wato Kamill . Ɗai ɗai garin da bai mallaki gida ba saboda hutawa aure baya gabansa hakan yasa iyayensa zuba masa ido yakeyin abinda ranshi yakeso, Juyi yayi a kujerar ya kalli bodyguard ɗin dake zagaye dashi yace ” kun gano min gidan su wanan yarinyar ?” yes oga mun ganshi mahaifinta shine Alhaji Sani alherin Allah , buga ƙasa Kamill yayi tare da furzar da isa daga bakinsa ya katse mai maganar da cewa ” wato ubanta bama kowa bane amma ta takani , to wlh bazan barta ba saina tozarta ta dole tayi hankali koda a gaba akace ta yiwa wani haka bazatayi ba , Miƙewa yayi ya nufi ciki daga bakin ƙofar flowers ne suketa haska ko ina , shiga yayi yana takunsa na ƙasaita ya zauna a kan wata fitinanniyar kujera ,wanan ɗaki na Kamill faɗar kyansa bazai rubutu ba, Kasancewar ya tsaru shi kansa palon kai kace ɗakin mai mata ne , ga wani ƙamshi dake tasowa ta jikin wasu flawoyi dake manne a bango, ɗaukar apple ya ɗauka yakai bakinsa , kaɗan ya gutsura ya ajiye tare da cewa , natsaneki!!!!. Ya riƙe kansa dake yimasa wani irin ciwo kasancewar sa inhar yasa damuwa a ransa to sai yayi zazzaɓi , wanan karon ma hakan ce zata faru , tashi ɗaya jikinsa yai zafi , babu inda ya iya bare ya kira bodyguard ɗin nasa su temaka masa sbda ya hanasu shiga part ɗinsa muddin ba shine ya turosu ba , Baccin wahala ne ya ɗaukesa sai wajen ƙarfe uku na rana ya farka , Jikin yayi masa sauƙi sosai miƙewa yayi ya zauna kan bed tare da janyo bed side ya ciro maganinsa ya ɗauki ruwa a fridge yasha , Jin wayarsa na ring ya dawo kan kujera ya ɗauki wayar , cikin muryar tasa da duk wanda yasansa yasan babu lafiya , yace ” Aslamu Alaikum Abba . Wa’alaikumussalam ɗan albarka ya kake , Kamill ne yace ” lpy lou Abba yaushe zaka dawo ?” gobe insha Allah mai kakeso ?” dariya Kamill yasa kana yace ” Abba akwai kyakyawan albishir wlh Allah dai ya dawo dakai lafiya , kodai mafarkina na ne zai tabbata zan sami suruka , dariya kamill yayi yace ” saidai kazo ɗin sukayi sallama.Ce ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 13&14 Hoton fuskar Diyana ne keyi masa yawo da wata shu’umar dariya yayi ya miƙe toilet ya nufa ya ɗauro alwala yafito domin zuwa masallaci. Da wani buhu Tinene ta fito da alamu buhun kayansu ne , Nana tazo wucewa Hajiya ta kirata , durƙusawa tayi tace ” gani hajiya , Hajiya dake mamular goro tace ” ina abincin namu ?” da sauri Nana ta miƙe tanufi kitchen ta fito da shinkafa , da cokula guda biyu dakuma faranti , Bajeshi Hajiya tayi, suka fara ci jin abincin yayi daɗi Tinene ta turo baki tafara shura ƙafa tana cewa” gaskiya kaka inhar na yarda na biki to yasin nayi asara , Innalilahi bina hine asara?” Ƙara kai lomar shinkafa Tinene tayi tana cewa wanan ai hine kaga samu kaga rahi any zan iya bin Kaka kuwa , 11am momy da iyalanta sun hallara a dining yau kam sun gaishe da Hajiya , breakfast momy da Afreeda sukeyi banda Diyana da ruwan lifton takesha sai juya cokali takeyi a ciki alamar akwai abinda ke damunta, babu wanda ya kulata , Wayar momy ce tafara ring ganin sunan dady yasata ɗagawa tare da gaisuwa , Ganinan shigowa ma ina bakin get , masha Allah momy tace ” Allah ya shigo dakai lafiya , Hajiya da ɗan ƙullin buhunta da Tinene suna zaune , Sukaji sallamar Alhaji , Washe baki Hajiya tayi tace ” hannu dai Alhaji , ywwa Hajiya munsame ku lafiya ? Lpy lou Hajiya tace ” tana daɗa gyara ɗaurin bakin buhunta , Hajiya mekuma muka samu ?” Diyana da Afreeda ne suka karɓe zancen da cewa barka da dawowa dady , kafin ya amsa Hajiya tace ” gida zan wuce bazan ƙara kwana a gidanka ba kaji na gaya maka , Sunkuyar da kai momy tayi dan wanan al amarin yafi ƙarfinta da tana ganin abin kamar wasa yanzu ya wuce tunaninta , gara taja bakinta tayi shiru inyaso insun gama ta tofa nata , Gyara zama dady yayi yace ” Hajiya kina nufin wai ƙauye zaki koma ?” eh Hajiya tace ” maiya faru da zaki ɗago tafiya haka yanzu da bayau zan dawo ba sai dai inji ta tafi kenan , Hajiya ce ta nuna momy tace” laifin matarka ni babu ruwana ehe tafiya zanyi gidanka duk aljanu hatta ɗakin da muke ma saida suka jamana kunne , Miƙewa tayi tare da janyo hanun Tinene tace ” tahi karmuyi dare, momy da sai yanzu tayi magana tace ” kayi haƙuri dan Allah , Da’ na ɗauka ba tafiyar zatayi ba , shiyasa ban gaya maka ba . Hanyar fita Hajiya take shirin yi dady yasha gabanta tare da durƙusawa yace ” Hajiya dan girman Allah kiyi haƙuri ki zauna babu komai a gidannan , Zan kira ayiwa gidan sauka yau ɗinnan dan Allah karki tafi , Tausayi ɗa da uwa Hajiya ta juyo ta zauna kan kujera tana cewa ” to wlh tun wuri ka kira malamin dan jiya a rumfa muka kwana , Dady baiji daɗi ba sam amma baice komai ba , Sama ya haura zuciyarsa babu daɗi , Bin bayansa momy tayi tana jiran abinda zai biyi baya , Salama tayi ta samesa yana cire maɓallin rigarsa , Ciki ciki dady ya amsa bai ko kalleta ba , Zama momy tayi a gabansa tare da janyo hannayensa ta zaunar dashi , haba mijina mai nayi da zakayi fushi dani ?” Inhar maganar Hajiya ne to kayi haƙuri naɗauki lefin dan girman Allah , duk da haka bai kulata ba saima shirin shiga toilet ɗin ɗakinsa daya fara yi , Da sauri momy taje ta tara masa ruwan wanka ta tsaya a toilet ɗin tana jiran shigowarsa , tasan mulki da isa irin tasa , Har ace gadon wa Diyana tayi hmm , momy taji shiru bai shigo ba , tana fitowa ta samesa a zaune yayi shiru yana bubuga ƙafa, ɗumin hawayen da yaji ne yasa shi ɗago fuska a razane yace ” Faty maiya faru , cikin kukan kissa momy tace ” nabaka haƙuri kaƙi saurarata kasan bana jurar ɓacin ranka , Janyota yayi jikinsa yafara shafa gashin kanta alamar tayi shiru , bakya girma , Dady yace ” yana murmishi , itama murmishin tayi tace ” to kaima ɗin haka ne , miƙewa dady yai yace ” zoki taimaka min inyi wanka idan na kintsa inason muyi magana dake , Miƙewa momy tayi daga kan cinyar dady ta riƙo masa hannu suka nufi toilet , Diyana da Afreeda ne a ɗaki kowacce na baƙin cikin dawowar Hajiya gidan , gaskiya dama Allah bai dawo dady yau ba da sunji daɗi , Diyana da abin duniya yataru yayi mata yawa tace ” kiji ɗazu wai laifin momy take cewa ?” Afreeda ce ta cire tagumin fuskarta tace ” ai wlh tadinga haɗa momy da dady faɗa kenan tunda bakinta bashida zip . Haka dai suka dinga jajantawa gashi sun rasa mafita da zasu ɓullowa lamarin. Yau Alhaji Safiyan ya sauka a Nigeria bai sanarwa kowa ya sauka ba sai drivern sa , kai tsaye daga airport unguwa uku aka wuce dashi wato gidansa , tun daga bakin get bodyguard keyi masa barka har yakai ga shiga cikin gidan , Hajiya Amina dake zaune a kujera wata dattijuwar mata tana mammatsa mata ƙafa ta miƙe , tana murmishi tare da cewa ” barka Alhaji dawowa babu sanarwa , Alhaji ne yace ” banda abinki Meena wanan karon nefa ban sanar miki ba to ayi haƙuri , sukasa dariya dukkansu , Tunda ma’aikatan gidan sukaga shigowar Alhaji kowacce tashe kitchen mai girki nayi mai haɗa lemo nayi mai farfesu kifi nayi mai farfesun kaji nayi abinci dai kala kala kowacce ta kama dama ƙa’idar gidan kenen , Amina ce tace ” Alhaji tashi muje kayi wanka sai kaci abinci , Babu musu ya miƙe amma a zahiri burinsa yaga Kamill , Bayan yayi wanka yai shigar alfarma ya fito shida Ameena suka nufi dining da masu aiki suka cikashi da kayan ciye ciye dakuma abinci masu lafiya , jollof ɗin shinkafa Ameena ta nunawa Alhaji tana dariya tana cewa ” alhaji ga abinda kakeso yaji kayan lambu , Alhaji dake daddana waya yace ” zubamin kisamin farfesun kifi a gefe, Bayan dady yaga cin abinci ya tambayi Kamill , yamutsa Fuska Ameena tayi tace ” rabona da insashi a ido 3 weeks kenan , Jinjina kai Alhaji yayi batare da yace ” komai ba ya miƙe ya fice direct ɗakinsa ya nufa ya kwaso wayoyinsa ,ya danna lambar Kamill , ring ɗaya ya ɗauka tare da sallama , Alhaji na amsawa yace ” kazo gida ina nemanka , Tom Abba harka iso ne ?” Eh Abban yace ” ya kashe waya . bubuga ƙafa Kamill yashiga yi kamar ƙaramin yaro yana cewa ” natsani zuwa gidannan wlh amma babu inda na iya dole na naje , wanka ya shiga ransa a ɓace ya fito ya zura jallabiya baƙa mai hula , ko shafa mai baiyi ba yafito riƙe da key a hanunsa ,bodyguard ɗinsa ne suka fara jero masa barka , Babu wanda ya kula driver ne ya fito da sauri yace ” Alhaji wacce motar za’a ɗauko , wani mugun kallo kamill ya watsawa driver , Babu shiri driver yayi ta kansa , ma’aikatan gidanne suka fara gulma akan yanayin da uban gidansu ya tashi Allah yasa lafiya , Jin faɗuwar gaba ta tsanta masa yasa shi ambato innalilahi a rayuwarsa yatsani Amina shiyasa ko gidan baya son zuwa , Allah yasa ba wani bom ɗin ta haɗa masa ba a gurin Abba , Shiga wata mota yayi fara kyakyawa ya harba titi , tafiya yakeyi yana tunani yarasa dalilin faɗuwar gabansa , wani mahaukacin horn yayi sanin ko waye yasa masu gadi da kowa na gidan saita nutsuwarsa , Mai gadi na buɗewa Kamill ya shiga , daga bakin get ɗin yayi parking ya nufi ciki , duk yawan mutanen da suke miƙo masa gaisuwa bai kula kowa ba, ko sallama baiyi ba ya shiga palon , Ameena na zaune tana kallo a tv ta ɗago kai ta kalesa ta mayar da hankali ga tv . Abba na ciki ?” Kamill yace ” kana ya kawar da kansa gefe yayi , Ganin bazai sami amsa ba ya wuce ta bai ko ƙara kallon inda take ba ,tofa maiya haɗa Ameena da ɗanta .. Yana shiga ya sami Abba zaune da laptop a hanunsa yana sanye da farin glass a fuskarsa , Cikin fara’a Abba ya ɗago kai yace ” oyoyo my son , Barka dai Abba Kamill yace ” yana neman gurin zama , Bayan sun gaisa da Abba shiru ya biyo baya na ƴan wasu mintuna , Kamill ne yafara dana sanin sanarwa da Abba , alƙawarin da yayi , Jin shiru yayi yawa Abba yace ” to Kamill Abbanka ya dawo cike da farincikin son jin albishir ɗin da zakayi masa , Wata mumunar faɗuwar gaba ce takuma ziyartar Kamill zufa na keto masa , Cikin ransa yace ” zan cuci kaina mai ya kaini gayawa Abba kuma inya faɗi magana baya sauyi , shafa sumar kansa yayi yace ” am Abba dama dama… Abba ne ya fahimci maganar tayiwa ɗan nasa nauyi ya murmusa yace”karka damu koma menene gayamin bakada matsala ko kaɗan , Kamill ne yace ” Abba yarinya nagani … Ragowar maganar ta maƙale masa a maƙoshi , masha Allah Abba yace ” yana faɗaɗa fara’arsa , Kamill ko sai yanzu yakeyin asalin dana sani sosai . Ƴar gidan waye ?” Abba ya tambayi Kamill , Ƴar gidan Alhaji Sani alherin Allah ce , Abba ne ya ƙara murmusawa yace ” haƙiƙa wanan rana nake jira naji daɗi sosai nayi farinciki , ai mutumuna ne shiɗin babu damuwa komai zai dai daita kaidai kaci gaba da nemanta insha Allah auranku zai zamo alkairi , Kan Kamill a sunkuye baice komai ba yanata nazarin maganar da ya yiwa Abba , nasiha Abba yashiga yimasa akan halin rayuwa , daga ƙarshe Abba yace” ka kiramin Amina , ɓata rai Kamill yayi yace ” tafice daga gidan zan shigo naga tahau mota driver ya jata, what..! Abba yace ” yaushe ta tambayeni dahar zata fita , oky jeka idan mukayi magana da uban yarinyar zan kiraka , tom Abba Kamill ya fice ranshi ta wani fannin fess wanan makirar zatasha faɗa , ya fice daga gidan , Yana shiga mota maganar da ya gayawa Abba dakuma farincikin da Abba yayi akan maganar auran ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba , Tabbas Diyana bata cikin jerin matan da yakeso , sbda ita ɗin batada kunya ga rashin sanin darajar mutane , ” Gaskiya nayiwa kaina da zuciyata rashin adalci Kamill yaketa nana tawa kamar bitar karatu , ikon Allah ne ya kaisa gidansa , yana zuwa yayi horn ba’a ɗauki lokaci ba mai gadi ya buɗe get ɗin da gudu tare da durƙusawa yana miƙa gaisuwa , ɗabi’ar Kamill ne in ana gaishesa ƙin daraja mai gaishesa , basajin daɗin abinda uban gidan nasu yake yimusu , amma babu inda suka iya shiyasa suke taka tsan tsan da duk wani abu dazai haɗasu dashi . [31/05, 12:47 am] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGA 15&16 bodyguard ɗinsa kuwa kowanne ya shiga tai tayinsa kasancewar oga baya wargi , Gashi yafita da ɓacin rai kuma ya dawo dashi . Fitowa palo Alhaji Safiyan yayi , ganin Ameena na zaune tana danna waya , yasashi neman guri ya zauna , kana yace ” meena yaushe zaki dena fita batare da izinina ba ?” waro ido Ameena tayi tace ” ina zanje Alhaji ?” Yanzu na aiko aka cemin kinfita a mota , buɗe baki tayi tasan babu mai yimata wannan sharin sai Kamill , Tarasa mai tayi masa ya ɗauki karan tsana ya ɗora mata , Hawaye ne suka fara zarya a fuskarta cikin she sheƙar kuka tace ” Alhaji sai yaushe ne zaka dena kama maganar wanan yaron , Ina nake zuwa ? Alhaji da ya ƙurawa fuskar Ameena ido yace ” naji ya wuce amma kisanj Kamill ba yaro bane yakai time ɗin da zandinga shawara dashi so kin fahimta?” Kawar da kanta gefe tayi dan intaci gaba da biye masa zasuyi babu daɗi ‘ Ita kuma batason musayar yawu da mijinta. Bayan dady ya fito daga wanka momy ta temaka masa ya shafa mai ya sanya kaya , janyota yayi kusada shi suka zauna akan kujera ya kalleta yace ” Faty mgnar da nakeson yi dake shine inason mahaifiyata ta zauna tare dani , Banison tayi nisa dani duk da akwai mai kula da ita a can ɗin ,nima inason samun nawa ladan , shafo kansa momy tayi kana tace ” Habiby nima inason zaman Hajiya a gidannan , Ita da kanta ta matsa wai saita koma ƙauye tace ” da aljanu a gidanan , nidai a iya sanina bansan dasu ba , amma bansan ko akwai ba . Gyra zama dady yayi yace ” ina tunanin harda rikicin tsufa . Daganan suka miƙe tare momy ta kashewa dady ido tare da cewa , ga shayinka fa na shigo dashi , okay dady yace ” ina zuwa yanzu zan dawo ya fice . ƙasa ya sauƙo yana tunanin tafiyar mahaifiyarshi , samunsu yayi a palo zaune suna kallo , Zama dady yayi kana yace ” barka da hutawa Hajiya , Ywwa barka Alhaji ya aikin naku ?” Lpy lou dady yace ” yana kallon Tinene da keta baza ido a tv ” ke baki iya gaisuwa bane ?” sosa kai ta shigayi tana washe haƙora tace ” hannu dai ina uni lpy dady yace ” yana murmishi , ring ɗin wayarsa ce ta katse masa maganar da yakeson yi . Ganin sunan mai kiran nasa yasa shi miƙewa da sauri ya haura steps zuwa ɗakinsa lokacin momy na toilet ɗinsa tana wankewa kasancewar bata yarda da ƴan aiki sudinga taɓa mata abinda ya shafi mijinta ba . Zama yayi a bakin gado tare da amsa kiran , Sadda kai ƙasa yayi da alama da wani babban yake waya , dady ne yace ” Allah ya temaki mai gida kuma Allah yaƙara maka lpy , daga can ɓangaren mutumin yace ” wata muhimmiyar magana ce ta taso amma dole sai mun haɗu . Cikin rawar jiki dady yace ” to ko inzo me kawai ace kamarka ka shigo layinnan , NO. mutumin yace ” karka damu dole nine zanzo buƙatar hakan ce ta taso karka damu. Cikin rawar jiki dady yace ” to da ƙarfe nawa zaka iso , mutuminne yace ” bayan sallahar isha’i yayi ko ?” dady da fara’arsa yace ” yayi Allah ya kawoka lpy , Sukayi sallama. bayan dady ya ajiye wayar ne yafara tunanin mai zai kawo Alhaji….gidannan kodai yayi laifi ne , wata zuciyar tace ” kazuba ido koma menene zaka gani Allah dai yasa alkairi ne . Har momy ta fito daga toilet dady bai sani ba yayi nisa a tunanin Alhaji…. kamo hanunsa momy tayi kana tace ” habiby ka zauna man amman dai lpy ko ?” Da ‘alamu na damuwa yace ” faty baƙo zanyi maza kisa ƴan aiki su haɗa abinci mai kyau kamar kala biyar haka , Ok momy tace ” kana ta fice , lokaci babu wuya jiyo kiran sallahar magrib yasa dady miƙewa ya yi alwalah ya nufi masallacin gidan , Bai dawo ba sai da akayi isha’i sanan ya shigo , babu kowa a palo ya haura step da sauri yana kiran momy , fitowa momy tayi daga ɗakinta , sai zuba ƙamshi takeyi tasa riga da skirt sun ɗameta amma tayi kyau , rungumota dady yai kana yace ” Faty na kullum kamar ana sake maidake baby , shafa fuskarshi momy tayi tana dariya tace ” to ya ka ganni nayi kyau ko ?” Yana shirin bata amsa kira ya shigo wayarsa. Sadda kansa ƙasa yayi tare da cewa ranka shi daɗe barka har kun iso ne ?” Eh Alhajin yace ” gani a mota anbuɗe min get na shigo , Dady na shirin ficewa da sauri momy ta taro shi , Maiya faru ne Faty ?” Haba habiby baka gayamin maike faruwa ba nadai ga kana rawar jiki , Cikin alamar yana sauri yace ” baƙo nayi kuma yanada muhimmanci a gurina, bugu da ƙari kuma kowane ma’aikaci nada burin ganin wanan bawan Allahn ya raɓesa sbda tsananin dukiyarsa dakuma goyon bayan manya daya samu , Riƙe baki momy tayi , Kana tace ” to Allah ya jishemu alkairi , Amma shida kansa yazo har gidanka ?” Ficewa dady yai batare da yabata amsa ba , Momy ta jimama zuwan wanan bawan Allahn daga ƙarshe dai tace ” Allah ya tabbatar da alkairi ko me ya kawosa oho , ta koma bedroom ɗinta. Dady na zuwa ya sami Alhaji ya fito daga mota yana zaune a wata farar kujera , Da sauri ya ƙarasa yana cemasa barka da zuwa , To tashi mu shiga daga ciki ranka shi daɗe , Miƙewa Alhaji yayi dady ya kaisa palonsa , palo ne daya ƙawatu da kayan alatu na zamani sai dai duk wanan ba komai bane a gurinsa kasancewar yatara gidajen da sukafi na Alhaji sani komai , Ƴan aikin ne suka fara shigo da abinci kala kala , ƴan aikin suna cikin shiga mai kyau drinks da abinci sunkai kala biyar . kunun aya Alhaji ya zuba a cup kasancewar baya baƙunta akan abinda yake so , Bayan ya ajiye cup ɗinne suka gaisa tare da tambayar iyalai dakuma aiyuka , Bayan sun gama gaisawa Alhaji ya gyara zama tare da kallon dady yace ” Alfarma nazo nema a gurinka , Cikin rawar jiki dady yace ” har saikazo daka kirani ai . Murmishi Alhaji yayi yace ” a gurguje dai inason gayamaka abinda ya kawoni . Dady da ya matsu yaji ko menene yace ” to ina jinka?. Masha Allah cewar Alhaji , yarona ne yaga ƴar gurinka yake sonta. Nisawa dady yai kana yace ” wacce daga ciki ?” Diyana Alhaji yace ” yana faɗaɗa fara’arsa. Dady sai da ya jinjina sunan Diyana a zuciyarsa yasan inhar bata son mutum to ko inuwarsa bata raɓa garama Afreeda . Alhaji ya lura da dady ya tafi dogon tunani , Baiyi masa magana ba saida suka dau tsawon mintuna kana dady yace ” karka damu insha Allah bazai gagara ba ranka shi daɗe , Washe baki Alhaji yayi yana ganin alamun nasara ta bayyana . Daganan Alhaji ya miƙe da niyar wucewa , rakashi har zuwa gurin motarsa dady yai Alhaji yace ” to nanda kwana uku zan kuma dawowa inhar Allah ya yarda dakuma yarinyar banason aɗau lokaci mai tsayi , insha Allah kawai dady yace ” dan bashida wata kalma dazai faɗa , Da haka dai sukayi sallama . Zuciyar dady babu daɗi kasancewar bayason yiwa yaransa auran dole . Bazai iya hana Alhaji Safiyan auran ƴarsa ba dan yayi masa abinda ba kowane zai iya yimasa ba. Har aka buɗewa Alhaji Safiyan get dady bai motsa ba , saida ya jima a tsaye sanan ya shige ciki . Momy nata tararradin dady ko lpy . suna zaune a palo dady ya shigo Hajiya da kecin tuwo tana suɗe hannu tace ” Alhaji ina ka shiga munjika shiru ga abincinka nan ko sai yayi sanyi zakaci ? Ganin yanayinsa yasa momy shan jinin jikinta , a zuciyarta tace ” akwai matsala , cigaba da magana hajiya tayi takuma cewa wai lafiya naganka haka ?” Lapy lau dady yace ” hajiya barin watsa ruwa ina zuwa , yana tafiya momy tabi bayansa . Mtsw Hajiya tayi tsaki tare da cewa kwaji da tsohuwar gulmarku ni har zan tambaye shi abu yaƙi gayamin , kwashewa da dariya Diyana da Afreeda sukayi dan lamarin yabasu nishaɗi sosai. Kunci gidanku wlh yarannan kun raina ni , Miƙewa sukayi kowacce bakinta a kunshe da alama dariya suke shirin yi akuwa suna isa kusada ɗakinsu suka saki dariya mai sauti , Tinene dake kokawa da ƙashi tazaro ido kana tace ” wlh Kaka dariya suke yimiki , ƙwafa Hajiya tayi tana jiran shigowar dady. kwance dady yake a kan gado idanunsa a sama yana tunanin maganar Alhaji Safiyan , Momy tayi tambayar harta gaji daga ƙarshe ta miƙe idanunta sun kaɗa sunyi ja zata fice , Miƙewa dady yai tare da ruƙo hanunta yace ” matsalar nan ta shafemu duka , momy dake nazarin maganar dady tace ” kanata magana baka faɗi mafarinta ba . Dady ne yace ” yazo nemawa ɗansa auran Diyana ne , kuma kinga duk abinda Alhaji Safiyan ya nema a gurina dole in bashi koda banida shi dole in nemo masa bare jinina yake nemawa ɗansa . Jinjina zancen momy tayi ,wai hausawa sukace da kamar wuya gurguwa da auran nesa , To ai matsalar Diyanan ce akwai taurin kai ni kaina bata cika bin umarni na ba , Dama Afreeda ce to da sauƙi . Haka dai suka dinga saƙa da warwara suka yanke shawarar gobe insha Allah zasu yiwa Diyana magana dakuma Hajiya . Hajiya tagama zaman jiran fitowar dady shiru babu shi babu dalilinsa , Gashi Tinene nata rafka uban gyangyaɗi , Tashinta Hajiya tayi suka nufi ɗakinsu tanata mita harda cewa momy tsohuwar munafuka. 7:am Kamill ya tashi kasancewar yayi sallahar asbha shine ya koma ya kwanta , bathroom ya shiga yai wanka yana gama wanka yai brush tare da fesawa bakinsa mouth freshner ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani kuma rataye a kafaɗarsa , Gaban mirror ɗinsa ya nufa yana ƙarewa kansa kallo , tabbas a ƴan kwanakinnan ya rame , amma wanan yarinyar ta cucesa maiyasa zai sa tunaninta a ransa cox shi ba ƙara bibiyarta yayi ba , ƙwafa yai a fili yace ” da ƙafarki zaki tako har cikin gidana zakisha mamaki , Ɗauko mansa mai tsada yai kana ya shafe duk jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya gyara sumar kansa , Ya miƙe ya nufi drower gurin ajiyar kayansa , Riga da wando ya jiro na jeans rigar pink color wandon kuma blue , Bayan yasa boxer ya sanya wandon da riga yakuma feshe jikinsa da turare , ya fito palo kunna tv yayi tashar mbc action , Hankalinsa sam ba gurin tv n yake ba amma duk wanda ya kallesa zaice tv yake kallo time table na abincinsa ya duba , yau farfesun kifi da soyayyan dankalin turawa dakuma shayi mai kayan ƙamshi kana da kunun gyaɗa za’ayi masa , Kasancewar sai ƙare shabiyu na rana yake breakfast yasa babu wanda ya shigo masa da safe [03/06, 1:36 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 17 & 18 Yana tsaka da tunani wayarsa tafara ruri ,duba mai kiran yayi sai da yaɗan jinkirta dan kiran yakusa katsewa ya ɗaga tare da sallama ya langwaɓar da kai kamar yana kusa dashi ,, Abba daga can ɓangaren yace ” my lovely son ka tashi lpy ya hutawa , Kamill dake ɗan yamutsa fuska yace ” am fine Abba ya aiyuka , lafiya Abba yace “. Daganan Kamill yayi shiru , Abba ne yace ” jiya naje gidansu yarinyar nan munyi magana da mahaifinta yace ” insha Allah bazai gagara ba , Kamill da ko son jin sunan Diyana bayayi yace” tom Abba , Bakada lafiya ne ?” cewar Abba Cewa” Kamill yayi banajin daɗi ne , Subhanallah dady yace ” kayi ka fito kaje hospital , Kamill ne yace ” inada ragowar magani naji sauƙi , Alhaji bayason musu yayiwa Kamill sallama ya ajiye wayar . 10:am kowa ya hallara a dining domin karin kumallo inka cire Hajiya da Tinene dake ƙasa kan kafet a zaune suna nasu karin , Bayan sun kammala dady ya dubi Hajiya yace ” Hajiya ya kike ganin maganar da mukayi ɗazu dake , tunda yanzu ga sunan , daga Diyana har Afreeda babu wacce ta fahimci abinda dady yake nufi , gyara zama Hajiya tayi kana tace ” gaka gasunan ai kokuma ince gatanan ai , Komawa kan kujera dady yai Diyana na shirin barin gurin hanunta riƙe da waya dady ya tsayar da ita , Juyowa tayi batare da tace ” komai ba , sanin dama ba magana zatayi ba yasa momy buɗar baki tace “haba daughter ana yimiki magana kin tsaya kamar kurma?” tahowa tayi ta nemi guri nesa da kujerar dady ta zauna tare da cewa gani dady , Yatsina baki Hajiya tayi kana tace ” wlh bakida hali mahaifinki na yimiki magana kin wani tsaya kamar sa’anki , momy dai batada bakin magana ta rufe bakinta , Wata uwar harara Diyana ta dokawa Hajiya , cikin sauri Hajiya ta miƙe tare da saka kururuwa tana salati , Alhaji na gaya maka bazan zuna a gidanan ba ka matsa yanzu gashi wanan marar kunyar tana nema ta dokeni wlh kashiga tsakanina da ita tun wuri, dady kam yarasa ta cewa ga damuwar Hajiya ga damuwar shi , shida Diyana , Hajiya kiyi hauri dan Allah zanyi mata magana amma yanzu mu samu mu kashe wutar dake gabanmu , Shiru Hajiya tayi tana girgiza ƙafa kamar mai jiran a taɓota . Diyana ” dady ya kira sunanta a hankali . Na’am dady , Diyana tace ” ta maida hankalinta gareshi , Alfarma nake nema a gurinki da fatan bazaki watsamin ƙasa a ido ba ?” jimm Diyana tayi kana tace ” insha Allah dady bazan watsama ƙasa ba. good Dady yace ” nayi miki miji ……! Jin zancen tayi kamar saukan aradu ba ita kaɗai ba har Afreeda ma saida ta girgiza da jin wanan zance , Dady bai bari ya kaleta ba saboda kalonta zai iya sa zuciyarsa karaya , Yacigaba da cewa ” haƙiƙa ina alfahari daku dakuma tarbiyar da nabaku nidai banida burin yiwa ƴaƴana auran dole , yanzu dai inason jin ta bakinki Diyana sbda ba wani ne zaiyi miki zaman auran ba , kuma zaman aure ba abin wasa bane zamane na har abada . yanzu wace shawara kika yanke ?” Hawaye ne suka fara sintiri a kyakyawar fuskar Diyana babu sautin kuka sai zubar hawaye , tafa hannu Hajiya tashiga yi tana ni ƴasu sai kace ” wacce za’a fillewa kai toni lokacin da aka yimin aure bansan kakanku ba ,kuma ban taɓa ganinsa ba sai ranar da yashigo dakina bayan an ɗaura aure , Dariya ce taso kuɓucewa momy dake zaune a kujera ta zuba tagumi, toshe bakinta tayi bata bari kowa ya gane ba , Bayan Hajiya tayi shiru dady ya kuma tambayar Diyana a karo na biyu , kalmar da ta fito daga bakinta ne yayi matuƙar firgita mutane kowa yayi mamaki. Na ‘amince dady na amince ta miƙe tayi bedroom ɗinsu da gudu hawaye na zarya a fuskarta , momy ma hawayen take sharewa kasancewar tasan Diyana ba har cikin zuciyarta ta faɗi wanan kalmar ba, Liyafa dady yasa a shiryawa Alhaji Safiyan ta bangirma abinci kala2 . Bayan isha sai ga kiran Alhaji nan ya shigo , Dady na ganin kiran ya miƙe jiki na rawa ya fice , samun Alhajin yayi a jingine a jikin motarsa kamar inda yayi rannan da sauri dady yace ” haba Alhaji tashi mu shiga ciki dan Allah , Miƙewa Alhaji yayi tare da rufawa dady baya suka shiga palon dady , Bayan sun gaisa dady ya gabatar masa da abinci , kaɗan Alhaji ya taɓa kana yace ” ya ƙoshi kai tsaye suka fara maganar ƴa’ƴan nasu , dady ne yace ” na tuntuɓi ƴar gurina tace ” ta amince , Kafin dady ya kai ga ƙarasa magana Alhaji ya faɗaɗa fara’arsa yana yiwa Allah godiya , cikin zuciyarsa yana cewa haƙiƙa duk da bansan yarinyar ba nasan yarona yayi dace duba da halin mahaifinta na cika alƙawari , masha Allah kowanensu yace ” Alhaji ya dubi dady yace ” a yanke dukiyar aure atemaka mana banason auran ya wuce wata ɗaya . Dubu ɗari ma yayi Allah yasa ma dukiyar da auran albarka , Dariya Alhaji yasa kana yace ” a haba zanbada 1 million ƴarka ƴata ce . Nasani dady yace ” karka manta Alhaji bawai naƙi bane amma mafi ƙanƙantar sadaki yafi daraja dakuma ƙarawa aure ƙarko , daganan sukayi sallama Akan gobe zai turo magabata , dady na komawa bai zarce ko ina ba sai ɗakin mahaifiyarsa , ya bata labarin abinda ke wakana cewa Hajiya tayi ” karka damu ka tura direba ya taho da ɗan uwanka hudu sai ya tsaya akan komai , dady yai farinciki yayiwa Hajiya sai da safe . Duk wanan abin da akeyi Diyana batasan waye mijin ba ita dai ta amsa . Washe gari abinka da masu shi ƙarfe biyar har ƴan uwan dady sunzo su biyu , Bayan sallahar isha’i baƙin dady sun hallara , aka bada dukiyar aure dubu ɗari biyar dady yaƙi karɓa amma sun turje sai da sukasa ƴan uwan dady karɓar kuɗin. Suka sanyawa dukiyar Albarka tare da auran in an ɗaura , daganan aka saka rana wata ɗaya , Dady bai dawo cikin gida ba sai wajen ƙare 11pm na dare direct ɗakin momy ya nufa , tana sanye da sleeping drees wanda ya fito da ilahirin kyanta , Dady da yazo bata labarin abinda sukayi ai yama mance ya shiga toile ya yi brush kana ya watsa ruwa ya sanya jallabiya yabi bayan momy , niko nace asbha ta gari dady lol. Washe gari dady ya dawo daga masallaci da asbha , ya sami momy da zaune kan sallaya tana karatun alqur’ani , saida ya jira ta idar kana ta gaishesa , Bayan sun gaisa dady yace ” Faty jiya fa ankawo kuɗin auran Diyana wani uban faɗuwar gaba taji amma tarasa dalilin hakan , murmishin yaƙe tayi tare da cewa Allah ya sanya alkairi , Suka shiga wata hirar daban , momy ce ta katse musu hirar ta hanyar cewa ” niko sunama waya da saurayin kuwa ?” dady dake nazarin maganar momy yace ” to wayasani ko zatayi ai ba sani zakiyi ba , shiru momy tayi daganan kowa ya kama gabansa , Dady yayi ɗakin Hajiya dan ya gaisheta momy kuma ta shiga wanka , Zaune take itada Afreeda suna tattauna abinda ya faru jiya , Afreeada ce ta dubi Diyana tace ” sis yanzu kin yarda da auran dole kenan bakima san mijin ba ?” karki damu my sis su dady nayiwa biyayya ina tausayin momy yanzu da ban yarda ba sai kiga Hajiya da dady sunkama jin haushinta , nasani itama bataji daɗin hakan ba , amma a yau ɗinan danaji ance wai ankawo dukiyar aurena , nayi danasanin cewa na yarda , ta fashe da kuka , Lil sis ban taɓa soyayya ba bansan ya ake yinta ba to yazanyi da mijin takuma fashewa da kuka mai sauti a karo na biyu , Rungumeta Afreeda tayi suka cigaba da kuka . kira ne ya shigo wayar momy lokacin tana zaune a dining zasu fara breakfast , kasancewar ta shiga ta kira su Diyana , Allah ya temaka lokacin sungama kukan har sunyi wanka amma mai lura yaga idanunsu zai gane sun zubarda hawaye , Ɗaga kiran momy tayi tana dariya tace ” haba mom Khady zan aiko su Afreeda anjima suzo su karɓa min , jinayi momy ta ce sai anjima tare da ajiye wayar , dady ne ya kalli momy yace ” dawa kike waya?” murmishi momy tayi kana tace ” da matar abokinka man Mom Khady ok dady yace ” Hajiya dake ƙasa ana cin farfesun kaza ta taɓe baki tana zabgawa momy harara , lol ko meye damuwarki ƴar tsohuwa oho . Suna gama breakfast sukayi bedroom ɗinsu , Shigowa momy tayi riƙe da wata bag a hanunta ta miƙawa Diyana , amsa Diyana tayi tare da cewa meye wanan momy , momy ce tai murmushi tace ” kwalabe ne zakiji komai idan kukaje amma karfa ku daɗe dan Allah , to sukace kowacce ta canza kaya , iri ɗaya sukasa riga da skirt na atamfa mai ratsin green and wite ba ƙaramin kyau sukayi ba musamman ma Diyana da kamar dan ita akayi atamfar ko ince ɗinkin , takalminsu kala ɗaya kai komai ma wayace kowa da kalar tashi suka fito tare da bag ɗin da momy ta basu suka nufi gurin driver , sbda babu wanda zasu aika ƴar aikinsu ta tafi garinsu gaida mahaifiyarta ba lpy , samun drivern sukayi a tsaye yana jiransu , motar da ya fito da ita Diyana ta kalla tare da yamutsa fuska ta lumshe ido , ta buɗesu kamar mai jin bacci tace ” bazamu shiga wanan ba ka fito da sharon nafijin daɗin hawanta , Jikin driver na rawa ya fito da motar suka shige , mai gadi ya buɗe suka ɗauki hanya , suna cikin tafiya go slow ya haɗu , mutane kowa na tofa albarkacin bakinsa , Wata mota mai ɗan karan kyau ce ta fito daga wani titi da yayi hanyar gaban wato titin da su Diyana zasu bi , Ran Diyana ya ɓaci a masifa tafara tana shirin buɗe murfin mota tana cewa ” wanan ai rainin wayo ne yaushene za’a tare mutane akan wanan banzar motar shi waye mai motar ? ta ƙarasa fitowa tana bam bamin masifa , wani bawan Allah dake kan mashin kana ganinsa zaka gane ya haifi Diyana dan a ƙalla yayi sa’an mahaifinta , yawu Diyana ta tofar tana ƙaƙarin amai , kai kuma waye da zaka zo ina magana kana magana , Allah ya baki haƙuri mutumin yace ” tare da jan mashin ɗinsa gefe , sbda kar ya janyowa kansa sanin ƴaƴan masu kuɗi basu ganin mutane da daraja, Leƙa cikin motar tayi tana yiwa drivern su masifa , tana cemasa maza ka tada mota mu tafi inga uban da ya tsayawa wanda suke jira ya wuce , dan rainin wayo ma tafiyar kamar motar bazata wuce ba sukeyi , ta shige mota , Afreeda na tsoron magana karta haɗu da nata kason yasata yin shiru , tafiya Drivern yakeyi cikin fargaba dan yana tsoron mutanen gabansa da suketa wucewa motar ogan nasu na gefe. [14/06, 5:47 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* PAGE 19 & 20 Zune yake a cikin mota fuskarsa rufe da farin gilashi ba ƙaramin kyau yayi ba, Wace mota ce ta shiga gabanmu ?” tambayar da ya watsawa securities ɗinsa kenan drivern sa ne yace ” wata yarinya ne a cikin motar inaga batasan ko waye a cikin motar bane yasa basu kauce ba , Kamill da ransa ya fara ɓaci yace ” maxa sha gabansu mu wuce waye ubanta , Da gudu drivern Kamill ya wuce su Diyana Masifar da take yiwa drivern su ne yasa shi gogar motar Kamill batare da ya lura ba , wani wawan birki drivern Kamill ya doka yana salati , Ba shiri Kamil ya buɗe mota ya fito ya nufi gurin motar su Diyana , Kai waye dahar zanzo wucewa kasha gabana . Cikin tsiwa Diyana ta zuge glass ɗin mota zatayi magana taga Kamill ,saida gabanta ya faɗi tayi ƙarfin halin cewa ” kai ɗin waye dazaka tarewa mutane hanya , Yana shirin buɗe motar tasu ya figota wani mutum yazo yana cewa ” haba babban yaro ba girmanka bane ka ƙyaleta pls , juyawa Kamill yayi ransa a ɓace tareda ƙwafa , saida ya wuce su Diyana suka wuce lol. suna isa ƙofar gidan da momy ta aikosu ta fice daga motar babu wanda ta kula , bubuga get ɗin tayi ba’a ɗau lokaci ba sai ga mai gadi ya buɗe , cikin sauri ta shige gidan tana sallama kamar ansata dole sai tayi, mom Khady da yanzu ta fito ta iske Diyana zaune a kan kujera tana kuka , Shigowar Afreeda ne yasata maida kallonta ga Afrredan tace ” ƴata mai ya sami kyakyawa ne naga tana kuka ? dariyar yaƙe Afreeda tayi dan ita duk budurin da Diyana keyi a titi dariyama ya bata , momy ƙila batada lpy ne , Afreeda tace ” tana shirin zama akan kujera , Driver ne ya shigo da bag a hanunsa ya gaida momy ya miƙawa Afreeda , Miƙawa momy Afreeda tayi tare da cewa inji momy tace abaki , oky mom Khady tace tare da karɓa , Tayimin bayanin komai . Diyana ce ta miƙe tare da cewa mom muntafi , haryanzu idanunta basu dena fidda hawaye ba , Janta momyn Khady tayi suka nufi bedroom ɗinta , zaunar da ita momyn Khady tayi a bakin bed ɗinta, itama ta zauna , fuskantar Diyana tayi kana tace ” daughter na nasan problem ɗinki momynki tayimin bayanin komai so insha Allah zamuyi iya bakin ƙoƙarinmu gurin ganin kin sami farinciki , A gidan auranki , share hawayenki . Share hawayenta tayi tace ” momy na gode , Yanzu saura 29 days bikin zaki dawo gidannan nanda 1 week zan fara haɗa miki magani , kinji ?” Tom Diyana tace ” ta miƙe batare da momy tace ” jeki ba , Da kallon tausayi momy ta bita tana girgiza kai . Bayan Diyana ta dawo palo ta sami Afreeda da Khady a zaune sunata hira cikin farinci , Zama Diyana tayi nesa dasu , Khady ce ta miƙe ta nufi gurin Diyana , kasancewar sa’ar Diyana ce amma da yake su ba ƙawance sukeyi ba ƴan uwantaka suke , Khady ce tayiwa Diyana magana a kunne bansan mai tace mata ba naga Diyana na dariya . Afreeda ce tace ” sis zomu tafi okay Diyana tace ” ta miƙe Khady tace ” barin kira momy , Bayan momy ta fito sukayi sallama tace ” zata kira momy suyi magana. Suna fita suka shige mota driver ya kaisu gida kasancewar titin babu yawan motoci , Alhaji Safiyan ne zaune shida Amena yana waya , bayan ya ajiye wayar ne Amena ta dubeshi tace ” Alhaji maganar kayan auran Kamill lokaci ya ƙarato , gyara zama Alhaji yayi kana yace ” aikuwa wlh inason ayi kamar akwatuna dozin biyu , riƙe baki tayi tana jinjina kai , a ranta tana cewa sai kace zai auri ƴar shugaban ƙasa , Alhaji ne yace ” menna naji kinyi shiru , Dariyar yaƙe ta ƙaƙalo kana tace ” to yaushe za’a fara siyayyar ? gobe insha Allah Alhaji yace ” yana washe haƙora , Zansa ayau ɗinnan a tanadi komai gobe kawai sai mu wuce london a jirgi , farinciki fall zuciyar Amina sbda koba komai itama zata yagi rabonta . after 2 weeks Diyana ta koma gidan mom Khady acan ake yimata gyara kama daga tsumi na gargajiya haɗin turaruka da shayin amare tare da kaji ga dilka da halawa da ake yiwa Diyana , abinka da farar mace sai ta koma kamar baturiya . Wata ranar juma’a suna zaune ita da Khady , Khady na bata labarin wani novels da take karantawa a wattpad suna dariya , taji kira ya shigo wayarta, batasan mai kiran ba hakan yasata ɓata rai ,ta ajiye wayar gefe, Khady da ta tsaya da karatun ta ɗaga wayar lokacin anyi kira na biyu , ta danna receive ta karawa Diyana a kunne , Mai kiran baiyi magana ba haka itama batace komai ba , jin Diyana tayi shiru yasa Khady ƙara volume ɗin wayar , Saida aka ɗauki mintuna mai kiran yace ” barka dai amarya bakya lefi zaro ido tayi tanason tuno mai muryar ta kasa tayi iya tunaninta amma takasa tunowa , Waye kai??” Diyana tace ” cikin sanyin muryarta . Mijinki ne . A ina ka sami number ta karka ƙara kiran wanan layin dan wanan baiyi kamada mijin da zan aura ba ta katse wayar. Iya ƙolokuwar ɓacin rai Kamill yayi wani uban ƙara yasa wanda yaja hankalin masu tsaronsa dakuma masu yimasa hidima , suka shigo da saur, lpy oga ? suka tambaya a tsorace , idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ya kallesu kana yace ” karku damu kowa ya koma gurin aikin sa zan nemeku anjima, Haka suka fice jiki babu ƙwari dan kwana biyunnan basajin daɗin ganin shugaban nasu haka . Yanzu burinsa kawai yaga ankawo masa Diyana a matsayin mata Allah ne kaɗai yasan hukuncin da zaiyi mata , Ya miƙe tare da zagaye ko ina na ɗakin ranshi a ɓace . Biki ya ƙarato shiri akeyi na musamman fanin momy da dady dakuma fanin iyayen ango , satin Diyana ɗaya a gidan momyn Khady yau ta dawo gida , kowa ya ganta sai yai sha’awarta . Momy ce ta jata zuwa ɗaki , Diyana . momy ta kira sunanta Na ‘am Diyana tace ” momy ce tace ” shi mijin naki ya taɓa kiranki kuwa ?” a’a momy . Diyana tace ” kanta a sunkuye , momy tace ” bare har akai ga maganar kuɗin anko taɓɓ , Diyana dai batace komai ba taci gaba da wasa da gezar rigarta , fashewa da kuka momy tayi tana salati , wanan aure shine ake kira da auran dole. shigowar dady ne yasa momy saurin share hawayenta ta ƙaƙalo murmishin ɗole , tace ” barka da dawowa Alhaji , ywwa dady yace ” ya nemi guri ya zauna , Kalon diyana yayi tare da cewa kibamu guri daughter. Dama abinda takeson ji kenan dan zaman ɗakin ya isheta kasancewarta ba mai son yawan surutu ba , Tana shiga bedroom ɗinsu taga Afreeda a zaune tanata kuka ƙara tashi hankalinta yayi , Da sauri ta iso kusada ƙa nwar tata tayi ta rungumeta , meya faru ne my sis ? wani kukan Afreeda takuma saki tana cewa ” sis yanzu kin yarda ki auri wanan mutumin sis tafiya zakiyi ki barni , hawaye masu zafi ne suka zubo daga fuskar Diyana , Takuma rungume Afreeda sunata kuka . BAYAN KWANA BIYAR. Zaune yake kan ƴayataccen bed ɗinsa da yaji tsadden zanin gado , idan nayiwa yarinyar nan haka banyi mata adalci ba koda yake ta wula ƙanta ni , amma duk da haka kamata yayi nayi ruwa biyu , sai tashigo in tada mata da GUGUWAR ZALUNCI na shi kaɗai yaketa zancen zuci , yaci gaba da cewa” iyayenta zasu fahimci wani abun fa… janyo wayarsa yayi ya danna lambarta da yai seven da no. ring ɗaya ta ɗauka cikin sanyin murya , kwanciya yayi tare da cewa ” barka da wanan lokacin ƴan mata , ywwa dawa nake magana , ƙara duba number tayi tanajin kamar ta gane mai muryar amma tarasa inda tasanshi , fatan masoyinki ne mijin da zaki aura , zatayi magana ya katseta da cewa ” ayimin haƙuri nasan nayi laifi dahar saida lokacin bikinmu ya ƙarato nafara kira , Diyana da taji wani sanyi ya mamaye zuciyarta tace ” babu komai karka damu ta lunshe ido kamar yana ganinta , janyo fillo Kamill yayi tare da rungumewa ya daɗa kashe murya , yace ” ya shirye shiryen bikinmu ni yanzu burina inganki kusa dani saboda in nuna miki zallar soyayya dakuma farinciki , Diyana da tayi nisa cikin love ta gyara kwanciyarta dama a kujerar palo take kwance , batasan Hajiya na gefe a tsaye ba tun ɗazu . Gaskiya nayi sa’a nima ina fatan hakan amma meye na zumuɗi , dole nayi sbda muryarki nasani bansan kyawunki ba koda yake inada tabbacin kyanki shima ƙarshe ne, dariya tasa marar sauti sosai tace ” kaima hakan ai , to yanzu dai nawa kikeda buƙata sbda a halin yanzu zanbar ƙasar sai ana gobe ɗaurin aure zan dawo , cewar Kamill . Lumshe ido Diyana tayi kana tace “duk abinda ka bada yayi . Kamill ne yace ” 3 hundred thousand yayi ? eh tace ” cikin farin ciki . sallama sukayi kana ta miƙe waigowar da zatayi sukayi ido biyu da Hajiya , ko kallon inda Hajiya take Diyana batayi ba , jiyo maganar Hajiya tayi tana cewa ” gulma da ance ba’aso yanzu kuma anzo ana kwarkwasa , wucewa Diyana tayi zuwa bedroom ɗinsu batare da ta kula Hajiya ba jin son lovely ɗinta takeyi kamar zai fasa zuciyarta , shigowar Afreeda yasa Diyana faɗaɗa fara’a tace ” sis yanzu my husband ya kiranj , murmishi Afreeda tayi cikin zuciyarta tace ” hmm ƴar uwata har yanzu bakisan wa zaki aura ba ina tausaya miki dakinsan Kamill zaki aura nasan da kina nan kina rusa ihu inma ba’a kaiki asibiti ba da sauƙi , sis sis me kike tunani a firgice Afreeda ta waigo idanunta cike da hawaye tace ” banason rabuwar mu my sis , Diyana dariya tasa tana cewa inajin kamar nafi kowa sa’a a duniya sbda mijin da Allah yai min zaɓi, hmm Afreeda tace ” tare da kwanciya a gefen Diyana . Kamill ya turo wa Diyana kuɗi , bayan ta ciro a p o s kasancewar yanzu bata cika zuwa bank ba , dama sunsi komai karɓar kuɗin momy tayi tabata 50k ta riƙe a hanunta , ƙanwar momy data zo daga kano ta tsarawa Diyana haɗaɗen lalle baƙi da ja , ga gyaran gashi da sukaje jiya , ɗinkuna akalla tayi sunkai kala ashirin kuma duba babu marar tsada . a ƴan kwanakin nan tayi ƙiba saboda kulawar da take samu daga gurin Kamill , suna tsaka da waya yace ” amma baxa’ayi wani event ba ko dan har yanzu ban dawo nigeria ba , my lovely babu abinda za’ayi karka damu cewar Diyana killer smile Kamill yayi yasan yafara sata a layi kafin ya goce ta . *RANAR ƊAURIN AURE* Da safe misalin ƙarfe bakwai ƴan uwan momy suka sata gaba wai gashi biki na ƴar fari amma babu wani wasa da akayi , momy da ta jiyosu tace ” ku ƙyaleta karku damu Allah dai yabasu zaman haƙuri kowa ya amsa da amen . Zuwa ƙarfe goma angama tsarawa Diyana kwaliya ta haɗe cikin material less mai tsada anyi mata ɗinkin riga da sikel ba ƙaramin kyau tayi ba , wasu magunguna aka dinga ɗura mata da turaruka momy da momyn Khady suka faɗa mata inda zatayi dasu , Zuwa sha ɗaya Kamill ya kirata ya sauka a garin kano , wani irin farinciki takeji na daban , iskar ma da take kaɗata ta ranar ta daban ce , [15/06, 6:43 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* Page 21 & 22 A yau dubban mutane suka sheda ɗaurin auran Kamill Safiyan da amaryarsa Diyana Sani , ɗaurin auran da yasami halartar manyan mutane ta kowane ɓangare musamman ma ɓangaren mahaifin Kamill , kowa ya sanyawa auran Albarka , Kamill kam bai sanarwa yawancin abokansa ba a cewarsa wanan auren nasa auran hukunci ne sbda yanason tada GUGUWAR ZALUNCIN sa bayan amarya tazo , mahaifinsa duk bai fahimci hakan ba , kayan lefen da aka kawo gidansu Diyana ya girgiza mutane tabbas nera tayi kuka duk cikin kayan babu na 50k momy ma tasha mamaki amma ba’a mamaki da ikon Allah yasata jan bakinta tayi shiru . Hajiya da tinene sunsha ɗinkin atamfa riga da zani suma ba ƙaramin kyau sukayi ba amma Tinene na gefen Hajiya bata bari tayi nisa da ita . Bayan sallahar magrib Diyana da Afreeda na hango manne da juna sunata kuka kowacce idanunta fal da hawaye , momy da ta shigo kiran Diyana ta gansu a haka , itama kawar da kanta gefe tayi tana share hawayen daya zubo mata daughter kizo dadynku na nemanki , daga haka momy ta fice , sakin juna sukayi Diyana ta tafi kiran dady . Da sallama ta shiga palon dady kanta a sunkuye , kallon tausayi dady yayi mata yasan tayi masa biyayya kuma shima yana son ya kwatanta kyautata mata , Dady gani , ywwa daughter abinda nakeso kisani aure ibada ne yinayi bari na bari karki maida gidan auranki gurin cin kasuwa kokuma filin faɗa da miji karkiga dan bai baki kulawa kina waje kice inkin shiga ciki bazaki bashi kulawa ba , kizamo mai tausasa murya ga mijinki kizamo mai tausayinsa kizamo mai faranta masa kamar inda kika yimin biyayya Allah yabaki ƴaƴa masu albarka masu biyayya , cikin muryar kuka Diyana tace ” dady ka yafe min. Dagani kasan ƙarfin halin magana yakeyi yace ” na yafe miki Diyana . yayi mata umarni da ta tafi , tana tafiya tana kuka wata yayar momy ta jata zuwa part ɗin momy , nan ma nasiha suka yimata mai ratsa zuciya kowa tausayinta yakeji kasancewar labarin auran da akayi mata , 9:pm motar ɗaukar amarya ta ƙaraso tayi wanka ankuma shiryata jikinnan kamar anyi ɓarin turare , duk inda ta zauna ƙamshi ke tashi sai ta barmusu tsaraba , rabuwa da momy ba ƙaramin kuka tayi ba sbda sabo turken wawa , Afreeda gata ga amarya suna riƙe da hanun juna , Hajiya cewa tayi bazataje ba sai daga baya zataje taga gida a nutse , sunyi tafiya mai nisa sosai sanan suka shigo anguwar da dadyn Kamill ya siya masa gida , tun daga nesa suka hango gidan shi kaɗai , gashi ba wani ƙato sosai ba amma nera tayi kuka , horn drivern nasu yayi aka buɗe masa get ya shige dasu , yana parking wata ƙanwar momy tace ” fito da ƙafar dama kiyi bismillah , tana fitowa itama ganin tsaruwa da kyan gidan yasata sunkuyar da kai gefen zuciyarta tanajin tayi sa’ar miji , mai kula da ita , rungumeta sukayi kai tsaye suka kutsa cikin gidan gaskiya inhar nace zan tsaya misalta kyan gidannan bansan irin misalin da zanyi muku ba ku ƙaddara gidannan kamar irin ginin turai bedrom aka shige da ita aka zaunar da ita akan gado , cigaba sukayi dayi mata nasiha sanan suka sata tayi wanka ta sauya kaya , suka feshe mata jiki da turare sukabi ko ina na ɗakin da turare mai sanyin ƙamshi , Sallama sukayi mata , a lokacin ta gane lallai aure ya wuce tunanin mai tunani , Afreeda da ta kwanta jikinta taba kowa tausayi janta sukayi tare da cewa ” yanzu ba’a kwanan gidan amarya kiyi haƙuri kizo muje kiyimata adu’ar zaman lafiya kawai , haka aka janye Afreeda tana kuka suka fice daga ɗakin , kasancewar batada wasu ƙawaye . Bata gama tsorata ba sai dataga mutane sun watse ita kaɗaice a gidan hankalinta ya fara tashi , miƙewa tayi ta murɗa handle ɗin ƙofar toilet , alwala ta ɗauro sbda batayi magriba da isha ba , tana fitowa ta shimfiɗa dar duma ta tada sallah , bayan ta idar ta kwararo adu’oi ta shafa , lumshe idonta tayi tana mai godiya ga Allah ta ninke dardumar ta koma kan gado ta kwanta kamar wata baby , jin shiru har ƙarfe 10: yasata janyo wayarta ta lalubo lamar Kamill da tayi seven da my blood danna kira tayi , jin tana ring ba’a ɗaga ba tafara tunanin ko lafiya tunda bai saba yimata haka ba . Ƙara danna kira tayi a karo na biyu nanma shiru ba’a ɗaga ba , ajiye wayar tayi tare da fashewa da kuka dama idanunta sun kuɓbura daƙyar take buɗesu , shiru shiru har ƙarfe sha biyu na dare , lokacin ma bacci mai nauyi yayi gaba da ita sbda gajiyar biki. Zaune yake a guest hause ɗinsa dake kano , tofa masu karatu ango baya Abuja yana ma kano . bacinsa yake shara hankalinsa a kwance kamar ba ango ba bashi ya farka ba sai wajen asbha lokacin anata kiraye kirayen sallah daga ma ban bantan masallatai , kasancewar akwai masallaci a gidan yasashi nufar masallacin . Har akayi sallahar asbah Diyana na bacci ba ita ta tashi ba sai ƙarfe bakwai na safe , a firgice ta sako daga gado tare da nufar toilet tayi brush ta ɗauro alwalah tafara sallah tana idarwa ta koma ta kwanta inka ganta abin tausayi . Kogin tunani ta shiga to ina my blood tamayar da take yiwa zuciyarta kenan , babu mai bata amsa yasata janyo filo ta rungume tare da share ƴar kwallar data zubo mata. Wayar ta ce tafara ruri cikin sauri ta janyo wayar ta ɗauka Kamill ne mai kiran hakan yasata gyaran murya , tana duba fuskar wayar taga my sis cikin ƙarfin hali ta kara a kunne tare da cewa” ƴar uwata yakike ? ya momy da dady , Afreeda dake dariya tace ” kowa lafiya dafatan dai amarya na cikin ƙoshin lafiya , normal sis ina lafiya yaushe zaki zo ? zaro ido Afreeda tayi kana tace ” kema kinsan ba barina fita za’ayi ba amma karki damu inanan zanzo cikin satinnan , daga haka sukayi sallama . tashi tayi tafara zagaya ko ina na palon babu laifi nera tayi kuka kuma ko ina ƙamshi ke tashi ga kayan kallo nagani na faɗa , haurawa step tayi tana mai ƙarewa fentin kallo kai kace ƴar ƙauye , ɗakuna uku ne a saman, Na farkon tafara buɗewa wani fitinannen ƙamshi ne ya daki hancin ta batasan lokacin data kutsa kai ciki ba , Hoton da tagani ne yasata faɗi jugub cikin firgici da tashin hankali tafara nuna hoton da yatsanta tana cewa ” kardai shine , wayo nashiga uku na lalace badai shine mijina ba dady bakuyimin adalci ba inhar shine baku sanar dani ba , kuka takeyi tana matse kanta lokaci ɗaya ciwon kai yayi mata sallama , amma har yanzu bata dena kallon hoton Kamill ba . ƙara nuna hoton tayi a karo na biyu tare da cewa ” natsaneka na tsaneka bana sonka bana ƙaunarka takuma fashewa da kuka mai ban tausayi , jan ƙafafunta tayi da suke neman ƙin ɗaukarta ta nufi ƙasa nata riƙe da kai , bata sami damar ganin sauran ɗakunan ba tayi gamo da ɓacin rai, gado ta faɗa zuciyarta fal baƙinciki inta tuno maƙiyinta shine mijinta lallai akwai aiki tasan auran hukunci yayi bawai na tsakani da Allah ba , tabbas shine mai kirana a waya tabbas shine , magana takeyi kamar zararriya tana riƙe da kanta har yanzu . Bayan tagama juye juyenta bacci mai nauyi yai nasarar ɗaukarta , baccinta takeyi cike da mafarkai iri iri duk na Kamill dakuma yanayin zamansu . sai ƙarfe ɗaya ta farka tana tashi yunwa tayi mata sallama , kitchen ta nufa cikin sanyi jiki ta buɗe handle ɗin ƙofar ,komai akwai a kitchen ɗin babu abinda babu , in baku manta ba dama ba gwanar cin abinci bace , fridge ta buɗe shima cike yake da lemu kala kala , nutrimilk ta ɗauka mai sanyi ta koma kitchen ta ɗauko cake ta ɗora kan plet ta dawo palo tafara ci , bawani daɗi yake yimata ba amma saboda yunwar data addabeta yasata maida hankali ga ci . Zaune momy suke a dining kowa da sakwara a gabansa da miyar egusi da naman kaza gefen kowanen su shayi ne mai kauri gakuma bredi da wainar ƙwai . Hajiya dake kan kafet a zaune ita da Tinene ta dubi dady tace ” Alhaji gobe in Allah ya yarda zanje gidan wanan zabiyar in dubota , to Hajiya dady yace ” yaƙara da cewa ” Allah ya tsare hanya driver zai kaiki , dady nima zani cewar Afreeda Allah ya tsare dady yace ” musu momy kam tunda ta tashi takejin jikinta babu daɗi tanajin kamar akwai abinda ke faruwa da Diyana kasancewar ta mai zurfin ciki yasata yin shiru batare da ta gayawa dady ba . Haka dai suka gama breakfast ɗinsu kowa ya watse . yau kwanansu biyu da aure ko leƙowa bai yi ba ,a iya kwana biyu Diyana ta rame sosai fuskarta babu wani farinciki kana ganinta zaka gane . Sallamar su Hajiya ne yasata amsawa cikin fara’a niko nace aure mai gyara hmm . Guri Hajiya da Tinene da Afreeda suka nema tare da kallon Diyana dake zaune da remote a hanunta , bayan sun gaisa Hajiya tace ” ƴarnan mai yaja miki rama haka ? kinfara nuna masa halinki na ragwanta da raki ko ?” sunkuyar da kai Diyana tayi dan bazata iya sanar da wanan tsohuwar damuwarta ba , miƙewa Afreeda tayi ta koma kusa da ita suka rungume juna , tashi ki kawo musu wani abin akwai drinks a fridge ɗauko musu kiduba kitchen akwai cin cin. Riƙe baki Hajiya tayi tare da cewa kinci gidanku ta watsawa Diyana daƙuwa , waye yace “miki yanajin yunwa kokuma kawo ko bazanci ba sai naci ehe ,Diyana ba surutun Hajiya ne a gabanta ba hakan yasa ta gyara kwanciya a doguwar kujerar da take zaune tayi matashi da cinyar Afreeda . Riƙe baki Hajiya tayi bata ƙara cewa komai ba , ta miƙe tare da juye abinda Afreeda ta ɗebo a gaban hijab ɗin Tinene ,to kitaso mu tafi inkuma kinzo zaman ɗaki ne sai muji , Hajiya tace tana shirin ficewa , miƙewa Afreeda tayi idanunta sun ciko da hawaye tace ” my sis sai munyi waya . Kasa magana Diyana tayi saboda kukan da ya ƙwace mata , tanaji tana gani suka tafi suka barta a gidan da shida kurkuku duk ɗaya. Yau kwaanta uku a gidan bayan tayi sallahar Azhar ta jingina kanta da gado tun tana wani tunani daban har bacci yai nasarar ɗaukarta , jin an watsa mata ruwa mai kamada na ƙanƙara yasata saurin buɗe ido ta miƙe cikin tsoro , Kamill ne tsaye yana sanye da shadda fara tasha aiki kannan yasha hula sajens luf luf ba ƙaramin kyau yayi ba , wayabaki lokacin bacci a gidana ? cikin tsiwa Diyana ta taɓe baki kana tace ” inbanyi bacci ba mai kakeso nayi ? ke karki kuskura kiyimin rashin kunya dan ni da kike ganina ina hukunta marasa kunya so ki kiyaye kisan ko da wa kike magana , taɓe baki takuma yi a karo na biyu tace ” mtsw har ya ɗaga hannu zai kai mata mari ko mai ya tuna oho sai ya fasa ya fice daga ɗakin [22/06, 3:30 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ???????? *GUGUWAR ZALUNCI* Page 23 & 24 Part ɗinsa ya wuce ya watsa ruwa kana ya fito ya shafa mayukansa masu ƙamshi ya nufi drower ya ciro gajeren wando da farar singlet ya sanya , ɗaukar wayoyinsa yayi kana ya sauka ƙasa , yana sauka yaji wani ƙamshi mai daɗu ya bugi hancin sa , leƙe ya shiga yi ta ina ne jin ko ta ko ina ƙamshin ke fitowa yasa shi nufar ɗakin Diyana cikin ƙasaita , samunta yayi a kwance kan gado hawaye sun bushe a fuskarta keee…! tashi ki dafamin indomie Diyana da takejin maganar kamar a mafarki ta kuma juyawa tana gyara kwanciya , fincikota yayi tare da cewa ” gidanku babu manya ne ? karki manta yazu daga ni sai ke a gidannan so kuma kinsan matsayina a gurinki ko kin mance my blood ɗinne yau ? kuka Diyana ta fara mai sauti tana cewa “wlh ka cuceni Allah sai ya sakamin danasan kai ne zaɓin da iyayena sukayi min wlh bazan amince ba , zama gefe gado yayi tare da janyota yana riƙe da bakin maganar yace ” sai kuma gashi kin yarda kuma inyi abinda nakeso dake , runtse ido tayi tana tuno irin tsanar da tayi masa tabbas bazata taɓa son sa ba koda nan gaba. Ƙara matsowa yayi kusa da ita suna jin nunfashin juna yace ” baby tashi ki dafamin indomie kuma wlh nabaki 3mins zaro ido Diyana tayi dan wanan lokacin yayi kaɗan , tunowa tayi to inma bata dafa ba uban me ya isa yayi mata , yana ficewa ta koma ta kwanta,kamar daga sama taji saukar bulala mai tsafi , innalilahi ta ambata cikin muryar kuka . Mai nayi maka ? jaka aka kawo maka? to wlh ka kuma dukana ka gani, duk wanan maganar da Diyana takeyi idanunta a rufe , janyota Kamil yayi haɗi da cigaba da janta har hanyar kitchen , haka tadinga jin zafin janta da yayi a step ga kurjewa da tayi bugu da ƙari ƙarfinsu ma ba ɗaya ba , tayi iya yinta gurin ganin ta ƙwace amma abin ya citura , babu tausayi ko imani ya wurgata kitchen yana mayarda nunfashi tare da gurnani kamar zaki , oya ki wuce ki dafamin ko inyi miki abinda yafi haka , babu shiri Diyana ta miƙe bakinta da guwai war hanunta duk ya ƙuje ta kuna gas kana ta ɗora ruwa yana tafasa tasa komai tare da mangyaɗa da sauransu , sai da ta juye a plet ganin baya kallonta ta zabga gishiri a ciki ta miƙa masa , banza kalmar da ta fito daga bakinsa kenan , sai da Diyana ta ruga da gudu tace ” ai ba’a banza ɗaya sai dai biyu ta shige bedroom tana cigaba da kuka tare da murɗa key ɗin ƙofar. Ƙwafa yayi dan yasan bakinta ba mutuwa zai yi ba , dining ya nufa ya zauna tare da ɗaukar cokali ya fara juya indomien lomar farko yaji ɗan karen gishiri kamar iya shine a abincin , Diyana ….bazaki fito ba wlh yau sai kin gane bakida wayo uban wa yace miki haka ake girki ? shiru batare da ta amsa ba ya sashi ƙara tunzura yana huci ya haura up step , kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya faɗa gado zuciyarsa nayi masa saƙe saƙe , ring ɗin wayarsa ne yasa shi ɗago kai ya nuba mai kiran nasa Abba ne , Kamill yace ” tare da ɗaukar kiran ya kara a kunne , Aslamu alaikum Abba barka , cikin farinciki Abba yace ” dafatan kuna lafiya ya ɗiyata ? tana lafiya Kamill yace ” to masha Allah ka nutsu my son yanzu kayi aure fa . To insha Allah Kamill yace ” daga nan sukayi sallama . Kwanciya yayi kansa na kallon sama yana tuno kalar muguntar da zai sake yiwa Diyana a karo na biyu , daga haka bacci mai nauyi yayi nasarar saceshi , jinshi shiru yasa ta buɗe ƙofa ta fito saɗaf saɗaf tayi kitchen flaks ɗin ruwan zafi ta ɗauka kasancewar tunda masu kawota suka cikashi da tafasashen ruwa batayi amfani dashi ba , ɗibo kayan haɗa tea tayi da duk wani abinda zata buƙata harda ragowar cake ɗinta da butter duk ta kawosu ɗakinta ta jeresu kan bedsite ɗinta kana takuma dannawa ƙofar key , haɗa shayinta tayi mai kauri tanasha tana gutsirar cake , da haka har ta ƙoshi sosai , ajiye cup ɗin tayi tare da gyatsa ta lumshe idanunta , tunowa tayi rabonta da waya da momyn ta tun safe dan haka ta ɗauki wayarta ta danna number my mom , ring ɗaya momy ta ɗauka cikin farinciki tace ” my daughter dafatan kina nan lafiya ? eh ina lafiya momy ya Afreeda dakuma wanan tsohuwar ? dariya momy tayi tace ” duk suna nan lafiya amma babu wata matsala ko ? naji muryarki babu daɗi ? uhm babu komai Diyana tace ” akwai fa naji muryarki ta sauya ni mahaifiyarki bazaki sanar dani ba ko to wa zaki gayawa ? kuka Diyana ta fashe dashi dan zuciyarta ta tsinke da kalamin momy. Bankaɗo ƙofar da taji anyi ne ya hanata gayawa momy halin da take ciki , bata ankara ba taji an fizge wayar daga hanunta , Aslamu alaikum momy ya gida ya aiki yakuma lil sis , dagajin muryar tasan mijin Diyana ne , washe baki momy tayi tace ” lafiya lao ya ƙoƙari Allah yayi muku albarka Allah ya albarkaci rayuwarku , amen Kamill yace ” tare da cewa mun gode momy muna nan zuwa gobe insha Allah, momy ta mance da maganar su da Diyana cikin farinciki sukayi sallama da Kamill . wurgo mata wayar yayi Allah ya temaka bata faɗi ƙasa ba , tare da cewa ” wlh duk ranar da naji kin gayawa wani yanayin zaman mu sai na illata ki , lumshe ido tayi batare da ta kalli inda yake ba , sai da ya gama surutansa sanan ya fice . Washe gari bayan sallahar ashba garin ya tashi da sanyi mai shiga jiki kwance Diyana take a bed ta ƙudun dune da blanket sai kwasar baccinta takeyi . Tunda Kamill ya dawo daga masallaci yake jinsa cikin wani yanayi , ɗakinsa ya wuce yana rawar sanyi , idanunsa sun kaɗa sunyi jawur dama a dai dai wanan time ɗin yakeda buƙatar mace ” a duk lokacin da gari yai sanyi to baya cikin kwanciyar hankali ,ga gararsa kwanciyar tayi ya dawo palo ya kwanta yana rawar sanyi , haƙoransa babu inda baya rawa ga wani wahalalen nunfashi dayake sauƙarwa . Kamar an tsikari Diyana ta miƙe tare da buɗe ƙofa ta fito palo ko me take nema oho , jiyo sautin sauƙar wahalalen nunfashi ya sata ƙarasawa da gudu domin taga waye , Kamill ne kwance jikinsa nata ɓari , abinka da mace mai tausayi sai ta tallafo kansa ta gyara masa kwanciya tare da miƙewa ta nufi ɗakinta ta haɗo masa shayi mai zafi ta kawo masa , tashi kasha , jiki na rawa Kamill ya fara shan shayin cikin ikon Allah zufa ta fara keto masa ta ko ina yadena jin sanyin , tunda Diyana ta tabbatar ya dawo hayyacin sa ta janyeshi tare da cewa ” kaci darajar tausayin da Allah yasa min amma badan haka ba babu dalilin da zai sa in temakeka taja tsaki. Kamill dai jiki babu ƙwari dan haka bai kulata ba ya maida kansa ya kwanta , Zuwa ƙarfe goma da rabi yaji sauƙi sai ciwon mara dake ɗan damunsa , haka dai ya haura zuwa ɗakinsa yai wanka ya sauya kaya sai ƙamshi yake zubawa dole duk macen da ta gansa sai ta yi sha’awar ya kasance mijinta , fararen kayane a jikinsa ta baƙar hula mai adon farin zare ga tsadaden agogon sa da takalminsa fari , sakowa yakeyi a hankali kamar ba shine mai rashin lafiya ba , direct ɗakin Diyana ya dosa ya murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa’a ta buɗe , zaune ya sameta tana makeup itama fa tayi kyau sosai ta haɗe cikin baƙin leshi mai adon jan flawoyi tagama shafa powder tana shafa pink ɗin janbaki ɗakin ya game da ƙamshi , tsayawa Kamill yayi yana ƙare mata kallo cikin zuciyarsa yana cewa ” gaskiya da auran soyayya mukayi da na more wanan mai zan so a jikinta mtsw ya kauda tunanin da ɓacin rai , Baiyi magana ba ya fice itako tun shigowar sa tana kallonsa ta mirorr bata kulasa ba , ɗage kafaɗa tayi irin ko a jikina ɗinnan . Ba’a jima ba taji ƙarar tsayawar motarsa tasan shine ya dawo , kuloli ne masu kyau a hanunsa guda biyu ya nufi dining dasu ya jere su tare da ɗauko su fanta da 5alive da sauransu ya ajiye , kuma komawa ɗakin Diyana yayi wanan karon harda sallama , amsawa tayi cikin siririyar muryarta , zama yai a gefen bed tare da cewa am sorry mata ta kiyi haƙuri da dukkan laifukan da nayi miki nasan ban kyauta ba , nan danan zuciyar Diyana ta karaya kasancewar ta mai saurin fushi dakuma tausayi uwa uba ga son a risina mata, bakice komai ba my Diya? sharesa tayi tana ƙoƙarin miƙewa , janyota yayi ta faɗa jikinsa suna jin ninfashin juna ya kai fuskarsa kan tata tare da cewa nayi miki magana tare da bada haƙuri kinƙi kulani ko kinason Allah yayi fushi dake ? tuno nasihar su momy da dady tayi cikin karayar zuciya tace ” na haƙura wata irin runguma ya kai mata tare da manna mata kiss a kumatunta , munada baƙi fa , waro ido Diyana tayi tare da cewa ” mai za’a dafa musu ? no nasiyo kawai inason ki zama cikin shiri , oky Diyana ta faɗa da murmishi ɗauke a fuskarta. Post navigation [ad_2]