HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

Alhaji nayima magana a inaka samo wanan yarinyar mai kamada aljana kayimin kunen uwar shegu ko ? dady ne yace “Hajiya Diyana ce fa ko kin manta ta yayar Afreeda ,kaji ai kusawa yara sunan mutunci bazaku sa ba sai wani suna mai kamada na biririka ,dariya ce taso kuɓucewa Diyana amma ta make , miƙawa dady haɗin furar tayi kana ta miƙawa driver dake zaune can gefe a tabarma takuma ajiyewa Diyana a gabanta yatsina fuska Diyana tayi kana tace “I dont like this thing dady ta miƙe tana tari , la haula wala ƙuwata illabillah Hjiya take ta mai maitawa tana tafa hannu ta dubi Alhaji tace ” mudai bamu ɗauko wanan mugun halin ba gaskiya ɗayar ƴar uwarta tafi daɗin sha’ani ,
Nikam yaushe zamu jitu da wanan mai kamada zabiyoyin chaɓɗijan ,
Diyana dai na zaune dan hankalinta na kan wayarta maganar da taji dady nayi ne yasa ta juyo a tsorace ” zaku jitu ita da zata yimiki sati ,
Washe baki Hajiya tayi tace “aiko dana sami ƴa suka haɗa ido da Hajiya Diyana ta sakar mata harara ,
Dady ne ya kalli Diyana yace ” wai kin mance gurin wacce nace miki zanzo ne ?” wanan fa da kike gani mahaifiyata ce walh zan saɓa miki , Diyana dai kanta na ƙasa ba ma’abociyar surutu bace , wata yarinya ce ta shigo da gudu tana cewa kaka yau bazakije itacen bane ? Hajiya dake shan rahowar furar da dady ya rage tace ” nayi baƙi jeki cewa mamanki Alhaji yazo to yarinyar tace ” kana ta fice da gudu .
Da isarta gidan nasu dake zagaye da dangar kara tafara ƙwalawa mahaifiyar tata kira tana cewa ” Talatu ki fito wanan yayan naki na bini yazo wlh harda baturiya kiyi sauri ,
Talatu dake ɗaki tana fere rogo ta leƙo tare da cewa da gaske kike yi tinene eh ? yasin kizo zaki ganhi harda baturiya ,
Yafo gyale talatu tayi jiki na rawa ta saka takalmin ta ‘ ta fice ta kwashi sauri dan tasan yau ta warke .
Kasancewar basuda nisa sosai dan danan sai gata a ƙofar gidan ganin sabuwar mota ne yasata tabatarwa ,tinene ce ta biyota da gudu tana cewa ” Talatu kinga zahiri ko ga motarhi nan , ƙarasawa sukayi tayi sallama Hajiya ce ta amsa gimbiya Diyana na sallah a sallayar da ta ɗauko a mota ,
Harkin iso Hajiya tace tana washe baki yayanki ne yazo kuma yau ze wuce shine nace “tinene ta kirawo ki , Talatu na fama da susar kai tace ” ai ganinan Inna ina yaje ne ? Hajiya ce tace?yaje sallah ai ba jimawa zaiyi ba yanzu zai dawo,
Talatu ce ta cire mayafin kanta tare da cire ɗankwali tasa hanu biyu tana sosa kanta ,
Hajiya ce ta dubeta tace ” wai talatu har yanzu baki sawa ƙwarƙwatar magani bane ?dagudu Diyana ta miƙe ta daka tsalle sai gata a waje , shigowar dady ne yasata sunkuyar da kai tace “sannu da dawowa dady ywwa daughter lafiya na ganki a nan ?” kafin tayi magana Hajiya tace ” uwarta Talatu take gudu dady ne yace ” to maiya faru ? Diyana idanunta cike da hawaye tace ” Dady ka tafi dani wlh bazan iya zama a nan garin ba ,

Kinci gidanku dady ya cewa Diyana , ya shige ɗakin Hajiya washe haƙora Talatu tayi tace ” yaya hannu da zuwa kunsha hanya , wlh kuwa ya yara ? lafiyansu lau Alhaji ya hidimomi mungode fa , babu komai Alhaji yace ” yana kallon tinene wanan ƴar gurin waye ?, Hajiya ce tace ” ɗiyar Talatu ce fa gatanan kamar ka kifeta da kwando ga guru gurun idanuwa kamar na waccan ta wajen ,

Kwashewa da dariya sukayi Alhaji ya miƙe yace “toni zan tafi Diyana kiramin driver kokuma kice ya kwaso kaya a mota oky tace ” ta fice tare suka shigo da drivern hanunsa ɗauke da buhunnan shinkafa da katan ɗin taliya da jarkar man gyaɗa da maggi da gishiri , dubu arba’in dady ya miƙawa Hajiya ita kuma Talatu ya bata dubu ashirin ai kamar an jefata a aljanna tahau zuba godiya tana ƙarawa ,
Dady ne yace “hajiya nanda wata ɗaya zaki dawo ABUJA dan wlh kina kusa abin zai fi ,zaro ido Diyana tayi tana nazarin irin zaman da zasuyi da wanan tsohuwar mai bala’in sa ido amma babu komai da ƙafarta zata nemi ta dawo ƙauyensu , hajiya na kuka tana sanyawa dady albarka tare da duk abinda yasa gaba ,
Shigewa cikin palon Diyana tayi tare da ɗauko jakarta ta dubi dady zan bika bazan iya zama a nan garin ba cikin ɓacin rai dady yace ” anan na girma komai nawa anan yake kaf cikin ƴaƴana kece mai tsananin ƙyamar jinina ,to dole ki zauna har sati ya zagayo saboda zumunci abu ne mai ƙarfi , kuka Diyana takeyi kamar ranta zai fita da ajinta da komai ta zauna a wanan banzan gidan wanda ko ɗakin zuba shararsu bai kai ba wajen kyau , niko nace wanan gida da kike rainawa shine ƙurewa gurin kyau a wanan ƙauyen ,
20k dady ya bata yace ” to mu mun tafi Hajiya najin duk dramar da sukeyi taƙi kulasu Talatu ko tsabar murna har yanzu murmishin fuskarta bai ɗauke ba, dady 20k is to shot tana bubuga ƙafa 5k ya ciro ya daɗa mata yana bata haƙuri akan zai turo driver ya zo ya ɗauketa , Hajiya ce ta matso tana cewa maganar sai kace ta munafurci da wani yare kukeyi dan kar ajiku ko , wlh Alhaji ka sakalta ƴaƴanka da kashe kuɗi , dariya dady yasa dan inya biyewa Hajiya bazai tafi yanzu ba , shigewa mota yayi yana ɗaga musu hannu ,
Tinene dake gefe tana ƙarewa Diyana kallo gaskiya kaf cikin ƙauyenan bata taɓa ganin mai kyau irinta ba gaskiya ƴan binni sunji daɗi ko kaushi basuyi bare faso, Hajiya ce tace ” baiwar Allah taso mu higa gida yamma tayi Talatu ce tace ” Hajiya nikam nayi gida yau zamu hyarɓi jar miya yasin yaya Sani ya jiƙani da nera ai wlh ko Ado bazan nunawa ba dan yana ƙyala ido to zai rabani dasu ,
Hajiya ce tace ” harkin gama abincin ne ? a’a wlh ina cikin gyaran rogo he ga tinens tazo kirana wai Alhaji yazo inafa zan gama tinene ce ta kwashe da dariya kana tace ” wayaga kaka a binni yasin sai sun koroki ,

Hajiya da haushi ya ɗebeta tace ” cin uwaki niɗin bzan iya zama a can ɗin bane to kikasa wasa ma dake zani , Diyana ce takuma cika a zuciye ta shige tabarsu anan sunata surkulllen maganarsu….!

Kubiyo ni dan jin cigaban labarin ya rayuwar Diyana zata ƙare a ƙauye biya 200 ki karance shi cikin kwanciyar hankali .
[31/05, 12:39 am] Mom Islam Ce????: ???????? ????????
*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 3&4

NA
*ZAINAB HABIB (MOM ISLAM)*

Wattpad momislam2020
Facbook mom islam mon islam
Email:
Zainabhabibu@gmail.com
Whtsapp: 08141799224

Mangariba ta sako kai Talatu ta wuce gida itama kamar ba mai son mutane ba dan kamar batasan Diyana yarinyar Alhaji bace kodan yangar da taga tanayi ne oho ,
Tinene da bata wuce gida ba ta dawo gidan Hajiya ta zauna a bakin kofa ,
Hajiya ce tace ” tahi karki janyo mana fitina kina sane almuru tayi ,tinene ce ta harari Hajiya kana tace ” wlh sa ido yayi yawa ƴar birninnan da wuya ta iya zama dake wataran sai tayi kamar zata gudu ga ki da gani babu ƙyalewa ,
Tafa hannu Hajiya tashiga yi tana salati tare da cewa” au ni zakiyiwa cin mutunci wlh Ado kika yiwa ba niba hyahya hya kawai wanan kalmar tabawa Diyana dariya dan duk ɓacin randa take ciki sai da ta dara ,
Tinene ce ta miƙe tare da karkaɗe zani tace ” ha muzo muyi daka tsami dan yasin bazanyi wanka ba ko kallonta Hajiya batayi ba da alamu anyi faɗa kenan .
Wayar Diyana ce tafara ring cikin farinciki ta duba number dan tun ɗazu take ta neman network babu ,
Da sauri ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta tace ” hello Afreeda yakike ?”
daga can ɓangaren Afreeda tace “sis kina jina kuwa ? alamu dai na rashin network babu ya ɗauke ,
Diyana rasa me zatayi kawai tahau kuka tana kiran ta shiga uku harda shure shure gata ƙatuwa ,
Da gudu Hajiya tayo ɗakin har tana shirin faɗuwa ta sameta a zaune kan jakar kayanta tana shure shuren ƙafafunta ,
Nidai naga ta kaina yanzu waccan mai kamada bulaliyar ta gama gayamin magana yanzu kuma ga wanan mai kamada yan ruwan aljanunta sun motsa Hajiya harda ƴar kwallarta wai ta tausayawa Diyana hhh,
Batasan ciwon rashin network bane ya motsa ,ƙwalawa tinene kira ta farayi tinene dake goge kaushi da dutsen goge ƙafa taƙi kulata , can kuma tace “ashedai mutum yanada rana eh naji koma mai zakice zoki kirayo min malam fari ya duba yarinyar nan ,
Diyana ji takeyi kamar ta ɓarar da Hajiya saboda tun farko jininsu bai haɗu ba rasa inda zatayi ta hukunta hajiya tayi can wata dabara ta faɗo mata aikuwa ta tuntsire da dariya ,
wanan karon saura kaɗan Hajiya tasa ihu ,
tinene ce tace ” toshi malam farin me zaiyi miki wlh kincika fitina ,
Hajiya ce tace ” kice inada mara lafiya a gidannan ni dare ma nake tsoro wlh,
Ficewa tinene tayi tana tafiya tana mita da isarta gidan ta ganshi zaune akan wani dutse yana alwala ina wuni tace ” lafiya lau ƴar budurwa , tinene ce tace ” wai kazo inji Hajiya tanada mara lafiya a ɗakinta ,
Subhanllahi wacece ?” malam fari ya tambaya,
Wata baturiya ce wlh kazo zaka ganta,
washe baki malam fari yayi kana yace ” bari a fito sallaj kice mata ganinan zuwa yanzu ,
To tinene tace ” ta koma gidan ta samu Hajiya na sallah ta koma waje ta kwaso kwandan soso ta shige cikin uwar ɗakin Hajiya da murmishi a fuskarta , Hajiya na idarwa ta zabura tayo uwar ɗakin tana cewa ubanme zakiyimin wlh ban yarda dake ba kitafi gidan ubanki ni banison shishigi yanzu ma badan dare yayi ba wlh dana watso miki kayanki kin wuce tunda ni yanzu kin rainani ,
Hajiya nata banbamin faɗa itako Tinene na shafa mai ko a jikinta dan inda sabo ta saba baya damunta ,
Ko uffan batace wa Hajiya ba sai ma waƙa data kamayi .
Sallamar malam fari ce tasa Hajiya fitowa tana washe baki suka gaisa yake tabyarta ya mai jiki da sauƙi Hajiya tace ” amma fa bata dena kukan ba ,
Malam ne ya matso kusada Diyana yana tambayarta maiya sameta ,
Wani azababben tsami dataji yana tashi ta gefensa yasata ficewa da gudu tana kuka , Hajiya ma fitowar tayi ta riƙota Diyana na ƙwacewa dan kaf mutanen gurinnan ɗaukar ƙazamai take yimusu har Hajiyan ma ,
Samun kujera Diyana tayi ƴar tsuguno ta zauna amma fa a dole tacigaba da kuka , takalmi malam yasa kana ya sami kujera shima ya zauna dan bai fahimci mai yasa ta gudu ba ya ɗauka aljanunne tunda basa tsoron adu’a ko kaɗan.
Tinene tunda taji anfara artabu da Diyana ta daka tsalle tana dariya kujera ta taka ta janyo wani ƙaton kwanon silba mai cike da soyayyen nama da cincin tasan koda yaushe Hajiya bata rabo dashi wanan zuwan na dady ma sai da ya kawo mata wani na yau kam ta cika baƙar leda tam dan ledar ma daga mararta take .
Hajiya ta mance Tinene na ɗaki saboda ta ruɗe malamin ne yace ” baiwar Allah maiya sameki ?”da kamar Diyana bazatayi magana ba can kuma tace “nifa lafiyata ƙalau rashin network ne yasani kuka ,
Hajiya ce ta mai maita newak ? no am say network shima dai malamin ba fahimta yayi ba amma yafi bada ƙarkin abin cine kokuma abin sha miƙewa yayi jiki babu ƙwari garin kallon Diyana ya bige da bango ,
Fitowar Tinene daga ɗakin Hajiya ta dubeta tace ” kakalliya nayi kyau kuwa ? yaufa haladu zai zo kinga ya kamata na tsara kwaliya tana fari da ido ,
Diyana ce ta ɗago kai ta kalli Tinene fuskar nan tasha jar hoda ga farin janbaki ƙamshim man ma da ta shafa bai yiwa Diyana daɗi ba dariya Diyana tasa kana ta miƙe tabar Hajiya a gurin,
Hajiya na tsaye kamar gunki har yanzu bata yarda Diyana batada aljanu ba .
Tinene dataga Hajiya taƙi kulata tayi hanyar waje zuciyarta farinciki dama a gidansu daga sallah sai cika ciki suke cin nama ,
Diyana ce ta ciro hijab a cikin kayanta ta fito batare da ta kula Hajiya dake tsaye tun ɗazu ba itako Hajiya wanan abun yafara yimata ciwo amma tabari duk lokacin da Alhaji yakuma zuwa zasuje gurin wani malami mai aganin Aljanu.
Fita tayi batasan ina zata nufa ba tafara tafiya tana dube dube wani yaro ne yazo wucewa da alamu aikansa akayi , Diyana ce tace ” kai dan Allah innane ake siyarda Swan water tsayawa yaron yayi yana kallon ta tunowa tayi da maganar sis tanta , tace ” am sorry to ko kasan shagon da ake siyarda ruwan gora ko ruwan leda ? eh yaron yace ” wancan hyagon ne can zani ok to nagode ,
Yana gaba tana binsa a baya cikin salo da iya taku har suka iso shagon ,
Jitayi yaron yace “Idi abani ƙarago da garin kwaki zaro ido tayi badai shine zai ci ba ? a zuciyarta take maganar ,
Yaron yazo wucewa ta kira shi ta miƙa masa ɗari biyar kallonta yayi yace ” me za’a sawo miki ?”Diyana sai da taɗan lumshe ido dan ɗabi’arta ce hakan tace “nabaka ne , cikin murna ya hau yimata godiya Idi ne yace ” wlh kazo mu raba dan idona yagani abinka da basusan zasu samu ba suka raba ɗari biyu da hamsin kowannen su ,
mai shago kabani ruwan leda bag ɗaya dakuma Faro in akwai ,
Idi ne ya dubi Diyana da sai yamutsa fuskarta takeyi yace ” Hajiya akwai ruwan leda amma banida jakar saka miki ,Diyana taso yin dariya amma ta fizge tace ” duka ledar cikin rawar jiki ya ɗauko ya bata , kana yace ” ammafa babu ruwan gora ,okay Diyana tace ” bani canji yaron da tabawa kuɗi ne yace” kawo in kai miki , badan kayan sunyi mata nauyi ba da bazata bashi ruƙon ɗaukar leda ba kasancewar duk ƴan ƙauyen ƙyamarsu takeyi, haka dai ta barshi ya ɗauka bayan ta karɓi chanjin ta suka wuce gida .
Hajiya na tsaye a bakin ƙofa tayi zugum tana jiran shigowar Diyana tsoronta ɗaya kar ƴar mutane tabi wani ƙauyen ,
Jin sallamarta yasa Hajiya washe baki tace ” ina kika higa ne ƴar albarka ?” Diyana ce ta taɓe baki kana tace ” naje siyo ruwa ne ,yaron yana ajiyewa ya fita .
Salati Hajiya tahau rafkawa tare da cewa”au yanzu duk tsaftatacen ruwan dake tuluncan be i’heki ba saikin siyo ruwan bature ? dont worry Diyana tacewa Hajiya ,
A’ lallai kuwa wlh Alhaji ya ɗauko hanya marar ɓulewa amma zai kuma dawowa wlh bazata saɓu ba ,
Ita dai Diyana tama wuce abinta ta ɗauki ruwan alwalah tana idarwa ta tada sallah janyo jakarta tayi ta ɗauki cake ɗin da momy tayi mata tafara ci da nutrimilk , ƙara duba wayarta tayi chaji saura 20% gashi tunda tazo bata sami lambar momynta ba sunfara waya da Afreeda network ya ɗauke , dafe kanta tayi tana tunanin anya zamanta zai yi a ƙauyen nan,
Bayan sallahar isha’i Hajiya ta zubowa Diyana tuwo miyar kuka da man shanu tunda Hajiya ta shigoda tuwon tafara jin tashin zuciya da sauri ta kawar da kwanon tana toshe hanci , wata uwar harara Hajiya ta wurga wa Diyana dan yau ta ƙureta ,
Hajiya ce ta kama ƙugu tace ” ke ƴarnan banison kinibibi wlh inbaki fita idona ba zan dakaki ,
dariya ma tabawa Diyana aikuwa tahau ƙyaƙyatawa dukda ita ɗin ba mai son yawan dariya bace , aikuwa Hajiya ta ƙara ƙuluwa ta kuma girgiza ƙugu niko nace kamar muciya lol Diyana kam zanyo blanket ɗinta tayi ta shimfiɗa a palo ta yi filo da jakar kayanta , tsabar bakinciki da ya isheta ma waƙa ta kunna ta toshe kunenta ,
mita Hajiya taci gaba dayi kamar zata ari baki oh ni Hafsu naga ta kaina indai birni ne wlh Allah wadai nikam tayi uwar ɗaki tana kakaɓe zaninta ,
tana zama tayi bakin gado tana lilo da ƙafarta ,kasancewar gado mai rumfa ,
juyawar da zatayi taji cizo innalilahi to mai ya sameni ?” hango cinnaka tayi yana tafiya ta gefenta sai yanzu ma tafara jin cizon , abinka da jikin tsohuwa yaji jiki tafara susa lalubar ƙarƙashin filo tayi koda zataga man zafi gurin harya kwaile tsabar susa tana ganin man tahau sharɓawa aikuwa tasha zafi ƙaramin hauka ne batayi ba, Diyana tana jiyo surutunta tayi shiru tana bin waƙar Hamisu breaker mai taken Jarumar mata anan gurin ma Hajiya tana jiyo saurin muryarta dan taƙi jinin tayi magana ayi kunnen uwar shegu da ita ,tofa da alamu dai Hajiya bazasu jitu da Diyana ba ..
Diyana kuwa cikin ranta cewa takeyi ai tunda kince sa ido ne aikinki to wlh nafiki bari dare yayi sosai zaki gane .
Bayan wasu mintuna bacci ya ɗauki Diyana bata samu tayiwa Hajiya hukunci ba .
Washe gari da asbha Hajiya ce tafara tashi sai da ta idar da nafil filinta tazo ta tashi Diyana ganin taƙi tashi yasa Hajiya fara sana’ar tata wato mita komawa tayi ta kwanta tunda ta tasheta taƙi tashi ,
Saida gari yayi haske misalin ƙarfe bakwai Diyana ta motsa lokacin Hajiya ta kuma tashi tana gaban murhu ɗumama tuwo ,
Sannu Diyana tacewa Hajiya kanta a ƙasa ,
Yawwa ƴar albarka Hajiya tace ” shigewa banɗakin da ya zame mata dole tayi bayan ta fito ne ta sunkuya zatayi alwalah taji Hajiya na masifa Diyana ce tace ” shidai mutum kullum cikin masifa yake ,
ashe Hajiya ta ji, aikuwa takuma ɗorawa tana cewa yanzu ban isa nayi ajiya ba sai anyimin sata ankwahe nama ankwahe abinnan da akeyi da fulawa to yau zanci uwar ɓarawon nan bari Tinene ta shigo ƴar kan uba datanada gaskiya da asubar fari zaka jiyo sallaɓarta tazo cin ɗumamen tuwo .
Diyana dai bata sake magana ba tana gamawa taje ta fara sallah tana idarwa tayi adu’oin ta, ɗibi ruwa a randa badan ranta yaso ba ta koma ɗakin ta ɗauki soso da sabulu tashiga wanka , ta daɗe tana wanka kasancewar jiya bata samu tayi wankan dare ba ,
Tsaye Hajiya take tana jiran shigowar Tinene ganin ta shafe mintuna bata shigo ba yasa Hajiya komawa ɗaki tafara cin tuwonta ,
sai da rana tayi sosai har anyi azhar Tinene ta kwaɗo sallama , gyan gyaɗi Hajiya takeyi a kan kujera amma dake tasa abin a ranta a zabure ta miƙe tanajin Tinene ta shigo ta cakumo ta tare da cewa yanzu kin kyauta kenan? ” Tinene ce tahau borin ƙarya tana cewa wlh kaka kidena ƙalamin sata nice kaɗai a ɗakin ? Hajiya ce takai dubanta ga Diyana dake tsara kwaliya tana shirin sa kaya tace ” to wazan ƙalawa inba keba waccan mai kamada zabiyoyin ba komai takeci ba bare nace ita to wlh zan haɗaki da Talatu dan bazan yarda ba, haka dai Tinene tasamu ta zulle dama ba yau suka fara ba .
Kwanci tashi asarar mai rai yau kwanan Diyana shida a ƙauyen SHAFA babu abinda ya sauya na daga ɗabi’unta sai dai takanci abinci intaga yayi mata .
Diyana ta gyara kayanta sbda basuyi datti ba ta ninkesu ta saka a jaka a ƴan kwanakinnan suna ɗan magana da Hajiya ,
Gobe takesa ran driver zai zo ɗaukarta wayoyinta babu caji duka sbda garin babu gurin caji tun tana baƙincikin hakan har tazo ta haƙura ,
A daren yau ne Diyana ta shirya yiwa Hajiya mugunta .
7:pm na dare bayan Talatu tazo sunɗan taɓa hira da Hajiya har Diyana ta gaishe ta ,ta jima a gidan sanan ta tafi yau dai tunda Tinene ta tafi gida bata shigo ba gashi dare yayi sosai lokacin ƙarfe tara da rabi , Diyana ce ta ɗauko bredin da Hajiya ta bada aka siyo mata da madara kasancewar yanzu dai ƙyan ƙyamin ba kamar da ba amma fa akwai ,
yanzu damuwarta ɗaya Allah yasa kar ace za’a tafi da Hajiya dan tanada yaƙinin zata dinga haɗasu faɗa da dadynsu amma daga yau zata fara tsorara ta ta ,
Hajiya tagama gyan gyaɗin da tasaba akan kujera ta miƙe tacewa “Diyana ƴar albarka sai da safe, Allah ya tashemu lpy Diyana tace ” yaukam bacci babushi a idanunta duk akan za’ayiwa Hajiya hukunci .
Ƙarfe goma da rabi kamar an tsikari Diyana ta miƙe ta juya ta ciro wani farin hijab nata mai niƙab dogo har ƙasa da ‘ alama na sallah ne ,
Shiga cikin uwar ɗakin tayi tana ƙarewa jeren ɗakin kallo taɓ wasu ɗakuna ma sai ƙauye wai yazuma anan gidan a dol gidan masu kuɗi kenen ko uhm ,
Tunowa tayi da abinda ya kawota , tsinken tsintsiya tasamu tafara shafo fuskar Hajiya dashi kana ta ɗauko kujera ta zauna tanata bin fuskar da tsinken tsintsiya , jin anyo ta wajen kunnen Hajiya yasata farkawa a zabure tana cewa yauma shazumamun ne suka kuma shigowa bayan na rannan dana kwashe ,
Bata lura da Diyana dake gefe ba sauya murya Diyana tayi tace ” nazo tayaki kwana ne nice yarinyar Aljani ɗan kutub wata uwar durowa Hajiya tayi ganin farin abu, babu fuska kamar likafani…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button