HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

Kubiyo mom islam dan jin cigaban labarin akwai cakwakiya a gaba biya ɗarinki biyu ki karanta .
[31/05, 12:40 am] Mom Islam Ce????: ???????? ????????

*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 5&6

NA
*ZAINAB HABIB(MOM ISLAM)*

Wattpad momislam2020
Facbook mom islam mon islam
Email:
Zainabhabibu@gmail.com
Whtsapp: 08141799224

Dan Allah kuyi haƙuri kuji tausayin bil adama wata uwar dariya Diyana ta saki badan tasan tanada babbar murya haka ba, tsumar jikin da Hajiya takeyi ne ga ɓurma mmen baki gaskiya comedy.com taci dariya ita da bata dariya sosai ,
Girgiza kai Diyana ta fara yi da farin hijab ɗin da ya rufe mata fuska , itako Hajiya ta haɗe hannuwa biyu tana cewa kuyi haƙuri nidai bansan laifin danayi muku ba tunda kwana biyu ba higa jejin nakeyi ba bare kuce naje na yimuku wani abin ,
Wata uwar ƙara da Diyana ta saki ne yasa Hajiya zabura zatayi palo dosota Diyana tafarayi kana tace ” kwanta kuma da safe mukaji kinyi maganar mu sai mun juya miki baki gefe maza ki kwanta Allah sarki Hajiya an maidata kamar baby .
Ta koma ta kwanta tare da runtse ido Diyana ko yin alamun kamar mai fita tayi ta shigo a hankali ta kwanta .
Washe gari Hajiya a makare ta tashi lokacin ma anyi sallar asbha tunda ta tashi yau ko mita babu juyawa tayi taga inda Diyana ke kwance taje kusa da ita tace ” ke ƴar albarka tashi gari ya waye , tom kawai Diyana tace “jiki a sanyaye Hajiya taje ta haɗa wuta ta je yin alawalh kafin taje sallah wutar ta kama ta ɗora ruwan kunu ta je sallah tana idarwa ta koma uwar ɗaki ta riƙe baki tana mamakin abinda ya faru da ita jiya gashi ance karta gayawa kowa , girgiza kai tayi tana nazarin inhar Alhaji yazo yau to bazata zauna a garinnan ba sbda tunda aka fara yimata haka to gaba ranta za’a nema ta miƙe tayi waje ,
Diyana na lura da yanayin Hajiya jitayi kuma taɗan bata tausayi wata zuciyar tace ” ai da bakiyi mata haka ba da tana nan tana mitar da tasaba .
Tinene ce ta shigo tana kiran kaka ! kaka ! jin Hajiya taƙi kulata yasata ƙarasowa tace ” kaka lafiya kuwa ? Hajiya ta sako tuwo a kwano zatakai ɗaki tace ” ke ni kauce kibani gu , kaucewa Tinene tayi ganin yau babu masifa kuma babu alamun wasa .
ƙarfe goma na safe driver ya iso ƙauye lokacin Diyana ta shirya shi kawai take jira ai tanajin horn ɗin mota ta miƙe tana cewa to Hajiya a yafemu ,
Hajiya dake ɗaki tanayi walha sallamar ta kenan ko adu’a batayi ba ta taso tana mita ,
“Saikace ina cizonki ai kyabari in fito ke ga ganɗoki ko kokuma mun gundureki ne ?”.
Lumshe ido Diyana tayi batace komai ba , hakadai Hajiya tayi ta gama tayi shiru .
Driver ne ya fito daga mota ya shigo gidan Hajiya durƙusawa yayi har ƙasa ya gaisheta cikin fara’a ta amsa tana tambayarsa yasu Alhaji da Faɗimatu ?”.,
duk suna lpy suna gaidaki driver yace ” ya miƙe tare da kallon Diyana ya gaisheta a yangace ta amsa dama ɗabi’arta kenan,
Kana yace ” inkin shirya hajiya sai mu tafi ai kafin yakai ga ƙarasa magana Diyana tace ” nafa shirya dama kai nake jira Hajiya dai taga ikon Allah wata ƙatuwar leda tabawa driver ya bawa momy zasu fita kenan sai ga Talatu ta shigo ,
Ina kwana Diyana tace “da fara’a Talatu ta amsa da lpy yaune tafiyar ne ? eh Diyana tace suka ɗunguma sukayi waje ,
back side ta shiga suka kuma yin sallama Diyana ce ta kalli Hajiya kana ta ɗan yamutsa fuska tace ” ina wanan yarinyar ? washe baki Talatu takuma yi tace ” ai na aiketa hyagon Haliru 1k Diyana ta bawa Talatu ta ajiyewa Tinene aikuwa sun sanya mata albarka .
Motar na shirin tashi Hajiya tace “to ƴar albarka sai Allah yayi zuwanmu killer small Diyana tayi kana tace ” saikin zo driver yafara tafiya .
Shunyi tafiya mai nisan gaske kana suka ɗauki hanyar Abuja Diyana takan tuna rayuwarta ta ƙauye jifa jifa tayita murmushi musamman farin hijab ɗunnan data sawa Hajiya yana matuƙar sata nishaɗi ,
Jin horn da driver yakeyi ne yasata ɗago kai Alhmdulilh tace cikin ranta ,mai gadi na wangale get ta
Hango momy da Afreeda suna tahowa da murmishi a fuskar su hawaye ne suka zubo mata tarasa na miye ,
Mai gadi ne ya buɗe mata murfin mota ta fito da gudu ta faɗa jikin momy ta saki kuka ,
Afreeda ganin kukan sistan ta yasata fara kuka ,
Momy ce ta hausu da faɗa tana cewa ” meye kuma na kuka bayan Allah ya dawo dake lafiya ,
Diyana batayi magana ba suka ɗunguma zuwa palo zama sukayi a kujera momy sai kallon ɗiyar tata takeyi ga wata muguwar ramar da tayi kuma jikinta ta gefen fuskarta ga cizon sauro nan, jinina kai momy tayi batare da tace komai ba ,
Tunani ta fara batada ikon hana Alhaji tafiya da Diyana ƙauye .
Jin hirarsu ce ta dawo da ita daga duniyar tunani Diyana tace ” momy mai kuka dafa ne ? Afreeda ce tace ” tuwon shinkafa miyar shuwaka ,
Yamutsa fuska tayi kana ta ƙara da shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace ” acan ma mutum baiji daɗi ba , anan ma bazanji ba ?” momy dai batace komai ba sbda rigimar Diyana tafi ta ɗan yaye wani time ɗin ,
Diyana ce ta miƙe tana fushi ta nufi fridge hango fanta tayi mai sanyi hakan ya sata ɗaukowa ta ciro ragowar cake ɗinta a hanbag tafara ci kamar an aikota ,
Niko nace su Diyana an daɗe ba’a haɗu ba .
Saida ta shanye babbar kwalba kana tayi gyatsa ta maida kanta ga kujera ta jingina ,
Momy da Afreeda banda kallonta babu abinda sukeyi ,
Afreeda ce ta ƙunshe dariya tace ” sis yaushe rabon da kisha fanta ?”.
Shigowar dady ne ya hana Diyana bawa Afreeda amsa .
Momy ce ta miƙe tayi masa barka da dawowa tare da karɓo wata takarda dake riƙe a hanunsa ,
Diyana da Afreeda ma sannu da dawowa sukayi masa ,
Cikin farinciki ya amsa yace ” daughter ansha ƙauye ina kika baro Hajiya ?” Diyana ce tace ” ai tana gaishe ka wai sai tazo ,
Madallah dady yace ” ai takusa zuwa ma nanda two weeks insha Allah ,
sunkuyar da kai momy tayi dan batada ta cewa a wanan gaɓar haka dai suka dinga hira da dady .
Afreeda ce suka haɗa ido da Diyana tayi mata alamun ta, taso akwai labari da sauri sukayi ciki suka bar momy da dady a palo suma tashin sukayi kowa ya watse akabar palon shi kaɗai .
bayan sunyi sallahr magrib Afreeda ta gyara zama ta dawo kusa da Diyana tace ” my sis kinsan me ? nayi sabon saurayi a bikin Hindu da naje shekaran jiya ,
Diyana ce ta dubi Afreeda kana tace ” sis karfa ace soyayya zaki fara a ƙarancin shekarunki yanzu fa kina 18 years ne amma kike maganar soyayya .
Ɓata rai Afreeda tayi tace ” haba sis mai yasa aduk lokacin da na kawo miki shawara sai kin nemi hanani yin abu ,
Afreeda tafara kuka. gyara zama Diyana tayi ta rungumo Afreeda tace ” my little sis ina sonki banison ta sanadiyar soyayya karatunki da brain ɗinki su shiga wani hali , so yanzu dai kibari zuwa tomorrow zamuyi magana karki damu .
Haka dai suka bar zancen sai zuwa gobe amma ran Afreeda ya ɓaci bata bari sistern ta ‘ ta fahimta ba kasancewarta mace mai fushi sosai.
Kawar da ɓacin ran tayi ta hanyar cewa ” sis ya kikayi da zaman village ? naga kin rame sosai kuma kinyi baƙi .
Hmm kedai bari wlh nasha wuya ko a mafarki bana burin sake zuwa wanan ƙauyen sbda wlh ni nasan halin da na shiga ga tsohuwar nan masifa tayi mata yawa , Diyana ce ta kwashe labarin bidirin da tayiwa Hajiya aikuwa suka dinga dariya .
Afreeda ce ta riƙe haɓa tace ” sis ashe wanan tsohuwar zata dawo gidannan ? gaskiya tana dawowa mun shiga uku .
“hmm ai bakisan wani abu ba wlh inhar tadawo saita gwammace dan wlh momy zata dinga sawa ido , muma dai ba barinmu zatayi ba aikuwa zata gwammace kiɗa da karatu dan wlh duk dare sai na horata dariya suka sa kana ko wacce taje toilet tayi wanka Afreeda saida ta fita sbda cikinta baya jurar yunwa ,tasami abinda zatasa a bakin ta suna ƙarasa salolinsu kowa ya kwanta .
9am kow yayi sallahr asbha ya koma bacci kasancewar yau weekend sai 11:am suke breakfast ,
Ƴar aikin su na kitchen tana ta haɗa musu abinci ,
Afreeda ce ta fara motsawa brush ta shiga toilet tayi kana ta nufi kitchen dan cikinta baya yimata uzuri ,
Diyana kam anata sharar bacci anji katifa mai laushi lol,
Ƙarfe sha ɗaya kowa ya hallara a palo kan dining momy dady Diyana dakuma Afreeda kowa yai wnka da shiga ta alfarma a jikinsa , bayan sun gaisa ne kowa ya maida hankali ga cin bincinsa saɓanin Diyana da takecin soyayyen dankali da shayi ,
Dady ne ya kalli momy yace ” Hajiya fa gobe zata zo Fatima , momy ce tace “Allah yasa muga goben lfiya Alhaji amen dady yace ” Diyana da Afreeda suka haɗa ido kowacce ta buɗe baki basu bari dady ya gansu ba kowacce ta maida hankali ga plet ɗin gabanta , suna gamawa dady ya miƙe ya shige ciki binsa momy tayi kasancewar tun jiya ya gaya mata sunada meeting a office .
Diyana ce tace ” wlh dady yasa wanan tsohuwar a rai bai san inhar ya kawota aiki zata basa ba hmm , haka dai suka dinga hira wacce duk ta Hajiya ce dakuma abubuwan da zau shirya mata .
gari na wayewa dady ya fara ƙwalawa driver kira da azama ya ƙaraso ya durƙusa gaban dady,
Dady ne yace “inason ka ɗauko Hajiya ne amma karka bari ta kwaso komai iya kayanta kawai,
Angama Alhaji driver yace ” kana ya miƙe .
Lokacin da ya ɗauki hanya ƙarfe tara na safe sai dai muyi masa fatan isa lafiya ,
Da isarsa yai sallama Hajiya na girka daddawa gidan ya gurme da wari ya durƙusa ya gaisheta amsawa tayi tana cewa” lalle lale da ƴan binni barka da zuwa ,yawwa driver ya amsa Hajiya .
Wanke hannu tayi tace ” to shiga ɗakin man, da shigarshi Hajiya ta miƙo masa kwanon fura da nono aikuwa driver yayi murna sosai dama yana abota da fura da nono ita kuma Hajiya bata rabo dashi , sai da ya cika cikinsa dam sanan ya dubi Hajiya dake zaune hankalinta na kan kalwarta yace ” Alhaji ne yace ” inzo in taho dake , hajiya ce tace ” har satin ya zagayo ne dahar zai turoka , driver ne yace ” to yadai ce inzo in tafi dake , jinjina kai Hajiya tayi tace ” leƙa ƙwar gida ka kiramin yaro
to driver yace ” ya miƙe yana fita yayi sa’ar ganin wata yayarinya tana doso gidan ,
ina wuni tace masa ‘amsawa dtiver yayi da lafiya lao ,
Nan gidan zaki shiga?
Eh yarinyar tace ” okay suka shiga a tare , tun daga tsakar gida Tinene tafara wankawa Hajiya kira ,kaka kizo Talatu ta aikoni wai ki hammata gihiri ,
Hajiya na mita ta fito tana cewa Tinene kiyi maza ki hirya yau binni zamu kwana ki gayawa Talatu ta haɗo miki kayanki ,
Driver dai komawa mota yayi yabarsu a gurin.
Wani uban tsalle Tinene ta doka harda taka rawa tace “hikenan zamu zamo ƴan binni tafara tafiya tana yarfe hannu tasa dariya , takuma canza tafiya wai zatayi kalar tafiyar Diyana .
Hajiya dai tashige gurin shirya kayanta ,
Kamar wacce aka zabura tayi waje da gudu driver dake mota ya hangota dariya yasa yace ” ƴan matan ƙauye hhh.
Tinene na isa gida tafara wankawa Talatu kira fitowa tayi tafara yimata faɗa akan wanan kiraye kirayen da takeyi tun daga ƙofar gida , to albishir zan yimiki yau kaka zata binni ,
Da sauri Talatu ta ajiye ledar gyaɗar da take ɓarewa tace ” kai dan Allah ?” wlh kuwa to zomu tafi gidan Tinene ce tace ” a’a nidai kayana zan tsaya shiryawa Talatu bata jira ta saurari Tinene ba tayi waje , a ƙofar gida ta ƙarasa sa mayafin.
Tana shiga tasami Hajiya a tsakar gida ta fito da buhu , cikin azama ta ƙarasa tace ” inna wai yau zaku tafi binni ? gashi kuma kina gani , ina tace tana ciciɓar buhun ,
Talatu ce tace inna yanzu tafiya zakiyi ki barni ?” kuka Hajiya tasa tana cewa ” zan dinga zuwa karki damu nima ba ason raina zanyi tafiyar nan yau ba ,ina Tinene tazo ta kawo buhun nata in haɗa da nawa Talatu ce ta share hawayen da suka kwaranyo mata tace “inna inkika tafi wazai dinga bani wani abin idan na nema , Hajiya ce ta kunce ɗaurin zaninta kana ta ciro kuɗi a lalitarta, sunkai dubu goma ta miƙawa Talatu da keta share idanunta da mayafi ,
Cikin farinciki ta karɓa tana godiya .
Hajiya tasan wuyar da Talatu kesha a gidan mijinta wata rana baya bada kuɗin cefane kokuma yace” ta auni masara ta kai niƙa babu kuɗin girkawa hakan yasa Hajiya take matuƙar tausaya mata amma bata cika nuna mata a fili ba sbda gudun wata rana ,
Hasali ma shine yasa takeson ɗaukar Tinene duk da ta zamo budurwa dan a ƙalla zatayi shekara goma sha huɗu ,
Hajiya nada tabbacin kakar baɗi ubanta zai ce aure zaiyi mata kuma gidansu haɗin zumunci sukeyi .
Hajiya ce ta ƙara kai kallonta ga Talatu tace ” inada buhun masara a ɗaki dana wake kuma ga shinkafa nan rabin buhu akwai mangyaɗa , duk ranar da bakida kayan awo ga mukulli nan kizo ki buɗe ,
Wani sabon kukan Talatu ta ƙara fashewa dashi tana tunanin kowa ya rasa mahaifiya yayi kuka tabbasmahaifiya itace abin alfahari ga kowane ɗa kuma itace take sanin ɗanta yaci ko bai ciba dazarar taga bai ciba zata fasa cin nata ta miƙa masa ,
haka dai sukayi sallama jikinsu duk a mace Tinene kam murna ta cika zuciyarta burinta taje birni ta waye tadinga kalar tafiyar Diyana dan komai na Diyana birgeta yakeyi .
Hajiya na kulle ƙofar ta miƙawa Talatu mukulli takuma ce mata akwai dambun nama a kwallah ki ɗauka mukan mun fito.
[31/05, 12:42 am] Mom Islam Ce????: ???????? ????????
*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 7 & 8

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button