HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

NA

Wattpad momislam2020
Facbook mom islam mon islam
Email:
Zainabhabibu@gmail.com
Whtsapp: 08141799224

To Inna Allah ya saukeku lafiya cewar Talatu , Hajiya ma dauriya takeyi haka dai akasa abubuwan da takeso suka shiga mota ,
Tinene ta ƙwalawa Talatu kira , tana matsowa tace ” Talatu dan Allah ki gayawa Bashiru nayi tafiya , maketa Talatu tayi kana tace ” bakida kunya ne kifa kintsu Tinene rayuwar binni ba irin tamu bace ki nitsu ina gaya miki , sallama suka kuma yi motarsu ta tashi zuwa garin shugaban ƙasa wato Abuja ,
Basuyi wata tafiya mai nisa ba dan basu fita a kano ba Hajiya ta tsayar da driver tana cewa” kai baka tsayawa mutane suyi fitsari ne ? ko kuma so kakeyi yarinya tayi a wando ,
Ayi haƙuri Hajiya driver yace yana parking ɗin motarsa a gefen titi fita sukayi tare da wani galan da suka ɗuro ruwa a cikinsa,
Hajiya ma fitsarin tayi suka dawo mota .
Fitarsu Kano keda wuya Tinene ta hango mai gasa masara shirin kuka tahau yi tana cewa Hajiya itafa yunwa takeji ,
Shidai driver badan uwar mai gidanshi ya ɗauko ba babu abinda zai hana baiyi musu magana ba ,
Hajiya ce tace ” kai tsaya a siya mata wani abun tasa a bakin salati ,
Driver ne yace ” Hajiya nan basu siyar da komai fa , Tinene ce ta karɓe da cewa ga mai masara can wlh ko ita nasamu ai ƴaƴan cikina sa barni na huta ,
Hajiya ce ta ciro nera ɗari tace ” driver ya siyo musu ƴan uku hamsin ,
driver yasan babu hakan yasa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa mai masara dan yasan inhar yakoma bai siyo ba Hajiya zata iya tsigaleshi , yana miƙa musu ,ya tada mota .
Sunyi tafiya mai nisa sbda sun wuce garuruwa da dama , jin motar tayi shiru yasa shi leƙa wa ta mudubi , hamdallah driver yayi ganin mai damun mutane tayi bacci , cikin ikon Allah sai gasu a Abuja har sunkusa layin su , Hajiya ba taɓa zuwa tayi ba shiyasa tayi gum da bakinta ,
Horn ya shiga yi , mai gadi ne ya wangale get ɗin yana ɗaga musu hannu ,
Hajiya ƙarewa gidan kallo takeyi badan ta ɗan yarda da drivern nan ba da zata iya cewa gidan ƴan yankan kai ya kawota amma bari ta zuba masa ido tagani ,
Yana parking ya fito tare da buɗewa su Hajiya ,
Tinene tayi bacci Hajiya ce ta ɗaka mata duka a razane ta tashi takalli Hajiya sanan ta kalli ina suke , mutsuke ido tayi tace ” alkur’ani da gaske ne nayi mafarkin gani a wata sabuwar duniyar Hajiya ce ta sharara mata mari kana tace ” zaki fito ko zaki zauna ni gaba zanyi dan inama tunanin kamar ba gidan Alhajin ya kawomu ba sbda babu ko wulƙawar mutane sai tsintsaye , Tinene ce ta fito tana shafa kumatunta ,
Ta nufi gurin mai gadi , gaishe sa tayi kana tace ” muna neman masu gidannan , mai gadi ne yace “ciki zaku shiga bazasu jiku daga nan ba amma kuzo muje ,
Sai da ya kaisu har bakin wata ƙofa mai glass kana ya ƙwanƙwasa ,
Da sauri ta fito jikinta sanye da kayan bacci da alamu bugun ƙofar ne ya tasheta ,
Tsawa ta dakawa mai gadi kana tace ” waye ya baka izinin shigowa nan ?” durƙusawa yayi har ƙasa yana bawa Diyana haƙuri saboda kaf cikin ma’aikatan gidan tsoronta sukeji sosai ,
Kasancewarta mace mai wani irin hali wato ƙasai ta bugu da ƙari kwarjini , Hjiya ce tayi saurin leƙowa tana cewa ” waye yake mgna Diyana da bata gane ko wacece ke magana ba kasancewar Hajiya na can baya mai gadi kuma yana kusa da ƙofar ,Tinenuwa kumatanacan gurin tsintsaye tana kallonsu ,
Diyana tace ” nice nan Diyana ,
Ai da sauri Hajiya ta matso tana cewa kauce kibani guri iyayi yayi muku yawa ,in mutum zai shigo har sai an tambaya ,
tunda Diyana ta tabbatar Hajiya ce ta iso tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta Allah ne kaɗai yasan irin abinda zuciyarta ke shirya mata,
Kutsawa Hajiya tayi tana tana sana’ar tata wato mita , shikam mai gadi ya wuce tuni .
juyawar da Tinene zatayi taga babu Hajiya ai da gudu ta ƙara taje ta tura ƙofar ta shige ,
Samun su Hajiya da momy da Diyana da Afreeda tayi suna zaune a kujera anata gaisawa , samun guri tayi itama ta zauna tare da cewa ” ina wuninku , lpy momy da Afreeda sukace banda Diyana daketa yamutsa fuska , Hajiya kam anbaje akan kujera anata zubawa momy labari , Tinene ce ta kalli Diyana ta nunata da yatsa tace ” kaka wanan ce tazo gidanmu hekaran jiya ko ?” eh Hajiya tace ” ai wanan da kike gani bansan gadon waye tayo ba , sam batason mutane .
Momy ce tayi dariya kana tace ” ai wlh Hajiya nima ina tunanin hali irinna Diyana amma inaga halitta ce kawai ,
Hajiya ce ta gyara zama tace” inason Alhaji yazo muje gurin wani babban malami ƙila tanada matsalar aljanu dan naga kamar ba ita kaɗai bace ,
Tuntsirewa da dariya Afreeda tayi tana kallon bakin Hajiya sai kai lomar shinkafa takeyi ita da Tinene ,
Kuma kai wata lomar Hajiya tayi tace ” tun lokacin da tazo gurina naga take taken hakan , momy ce tac” to Allah yabasu haƙuri , amen suka amsa banda Diyana da haushi ya cikata ,
Cikin ranta tace wato wanan tsohuwar tun yanzu zata fara ɓatamin rai ko ?” to wlh mu zuba zata gane batada wayo ta miƙe tayi bedroom ɗinsu, da yamma bayan la’asar kowa ya shige ɗaki Hajiya da Alhaji ne a zaune sai Tinene dake ƙasa a gefe tana kallo a tv hango wani mutum tayi yana kuka da alamu wani abinne ya sameshi a shirin film ɗin ai itama tahau share hawaye tana cewa” Allah sarki hankalinsu Hajiya bai kai gurinba sai da taji anja mata ƙafa tayi ƙasa ,wani wawan ihu Hajiya tasa tana riƙe da gurin ,Tinene da tayi abun hankalin na gurin tv tana kuma kaiwa Alhaji shirin naushi ,
Kaucewa Alhaji yayi yana tunanin anya wanan yarinyar mai lafiya ce kuwa ?.
Sannu Hajiya dady yace ” yana kallon ƙafarta ,
Fitowar momy da Diyana da Afreeda ne yasa dady cewa zoki ɗaga Hajiya da azama momy ta ƙaraso tana cewa mai ya sami Hajiya ? abinda ya faru dady ya gayawa momy , ji sukayi an kwashe da dariya ,juyawa sukayi dukkansu harda mai kallo , ba kowa bace sai Diyana da ta riƙe ciki tana dariya , dady ne ya ɓata rai kana yace ” ke Diyana kinci gidanku dan bakida kunya Hajiyar ce abin yiwa dariya kina gani tana fama da ƙafa wanan sakaran takuma jibga mata naushi ,
Da gudu Diyana tayi ɗaki saboda wata sabuwar dariyar ce takuma kawo mata ziyara,
riƙe haɓa Hajiya tayi tace “Faɗimatu kingani ko kinga abin da nake gaya miki ko ?” to Alhaji tun wuri kayiwa tufka hanci tun kafin suyi mata illa ,
dady da bai fahimci abinda Hajiya take cewa ba yafara tambayar mai ya faru ,mayar masa Hajiya tayi kana ta ƙara da cewa ” a gaggauta wlh .
Itadai momy batada bakin magana sai eh da eh , dady ne yafara yiwa Tinene faɗa yake gaya mata mutanen tv ba fitowa sukeyi ba kuma basujin mutane , shiru tayi kai kace ba ita ta aikata ba ,
Miƙewa Afreeda tayi ta nufi bedroom ɗinsu tinda comedy ya ƙare , da dare yayi bayan isha’i mai aiki ta jera musu abinci a dining , Hajiya tunda taga anan za’aci abinci tace ” bata yarda ba a kawo mata nata ƙasa , babu mai yimata musu kaf ɗinsu momy ta sauko mata dashi akan faranti ,
Diyana bata fito cin abinci ba sai Afreeda da ta zuba farfesun kifi tana ci ,
ina daughter ?”dady ya tambayi Afreeda ,
Afreeda ce tace ” tana bedroom tunda tayi sallah ta kwanta ,
Buɗar bakin Hajiya tace ” ba dole kaga mutum kamar muciya ba babu auki saboda baici abincin gidansu ya ƙohi ba,
Kai lomar tuwon shinkafa tayi tana mita ,
Tinene dake zaune da shinkafa da miyar kifi a gabanta tace ” Allah sarki Talatu ko taci hinkafar da kika barmata oho ,
Hajiya ce ta dubi Tinene tace ” maza kiyi kici kije ki kwanta , Faɗimatu ki nuna mata ɗaki karta cika mutane da surutu ,
Miƙewa dady yayi ya yiwa su Hajiya sallama ya shige ciki .
Washe gari takama laraba Diyana da Afreeda zasuje bikin wata classmate ɗinsu ko wacce burinta tayi kwaliya ta kece raini kasancewar yarinyar wani babban ma’aikaci ne amma bai kai dadynsu Diyana kuɗi ba,
Kar mai karatu ya ɗauka shima mahaifin amaryar talaka ne , no yanada kuɗi sosai kuma babu wanda bashida labarin mahaifin amaryar harnyanzu ana damawa dashi ,
Sai dai shi mahaifinsu Diyana wani attajiri ne wanda ko shi bai san iya adadin dukiyarsa ba , kasancewar sa mai kuɗish sosai ,
Kayane anko suka ɗinka kala uku uku kowane ɗaya zaiyi 50k ɗinki kuwa anyi masa na 5k atamfa da less da material babu na kushewa a cikinsu ,
Yau akeyi ɗaurin aure , in suka tafi yau sai gobe zasu dawo .
Diyana ce ta kalli Afreeda tace ” sis yanzu mai zamu kaiwa amarya a matsayin tamu gudun mawar kinsan dai in muka bata kuɗi ba karɓa zatayi ba ,
Afreeda na saka skirt da ƙyar tace ” sis yanzu dai gurin momy zamu dan wlh nima kaina yayi zafi burina inganni a gurin bikinnan ,
ƙarfe huɗu duk sun gama shiri Maltina Diyana ta ɗauko a fridge kaɗan tasha ta riƙe ragowar a hanunta suka nufi bedroom ɗin momy .
Samunta sukayi tana sa kaya ,zama Diyana tayi a bakin gado ita kuma Afreeda ta zauna a kan stool dake gaban mirror ,
Kallonsu momy tayi da fara’a tace ” harkun shirya ne ?” eh suka ce Diyana ce ta shagwaɓe fuska tace ” mom munrasa abinda zamu kaiwa Khairat a matsayin namu kyautar , riƙe baki momy tayi kana tace “karku damu ga wani haɗin humra da turaren wuta da nasa aka yimin haɗinsa tun daga maiduguri so ku tafi dashi kawai duka inyaso zanyiwa Hajiya Falmata magana ta ajiye min in tanada ragowa , rungume momy sukayi suna godiya ,
Afreeda ce tace ” momy bakice munyi kyau ba , dariya momy tasa tace ” ai wanan kwaliyar taku ko maƙiyi ,
sukasa dariya dukkansu lokacin da suka kammala shiri ƙarfe biyar na yamma , sunyi kyau kamar ka sacesu ka gudu Diyana ce ta ɗora baƙin glass ɗinta a ido kasancewar ta ma’abociyar son sakashi amma Afreeda bata damu da sanyawa ba,
ƴar aiki suka aika kiran driver , sai gasu sun dawo a tare Diyana ce tace ” driver sabuwar mota zaka fito da ita , kafin ta ƙarasa magana driver yace ” to Hajiya angama insha Allah , fitowar momy taci karo dasu sai ga Hajiya nan ta ɓullo tana ɗingishi , wayar Diyana ce ta fara ring ko kallon Hajiya bata yi ba ta ɗaga wayar , Khairat ce take magana kamar zatayi kuka ,
Haba sis kufa ake jira a gurin reception ɗinnan pls kuyi sauri , Hajiya ce ta gyara tsayuwarta tace “yau naga duniya yara su koma kamar zabiyoyi jibeku ko kyau bakuyi ba ,
Afreeda da hankalinta yayi gurin shagali tace ” bye momy Hajiya bye tana ɗaga musu hannu , ganin cikinsu babu wacce ta kulata yasata cewa ” ke zabiya zoki tafi da Auta itama taga gari ,
Ai da gudu suka fice,
Suka shige mota sai gurin biki , sunyi tafiya mai nisa kana suka iso ƙawataccen gurin da idan ka ganshi sai ka rantse a ƙasar waje ne , iya tsaruwa gurin yayi, suna sauka a mota na hango wata budurwa batada jiki tana sanye da doguwar riga fara ta yafa mayafin rigar a kanta ,
da gudu tayo gutinsu Diyana tana faɗin barkan ku sists wato munce bamuson let sai da kukayi ko ? ga anty Khairat can taƙi sakin jiki wai dan babu anty Diyana , lumshe ido Diyana tayi kana tace “am sorry amaryar mu tayi haƙuri ganinan na ƙaraso ,
Afreeda ce taja budurwar mai suna Siyama sukayi gefe ita kuma Diyana ta shige ciki ,
Da shigarta kallo ya dawo kanta kowane saurayi mai ji da kansa ita yake kallo hatt MC ma ita yake kallo ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button