GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

Gashi dai kayane da kowa na gurin yasan tsadarsa da kyansa kuma ba wata fayattaciyar makeup tayi ba amma hakan bai sa sundena kallonta ba ,
Cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da gurin zaman amarya,
Tun daga nesa Khairat tafara fara’a da dariya ɗauke a fuskarta , Diyana ma maida mata da dariyar takeyi tana tafiya ,
Batasan da mutum a gabanta ba ta bigeshi wayarta ta faɗi ƙasa ta watse gefe ,
A, zuciye ta ɗago kai ta waysawa wanda ta bige harara kana ta ƙara masa da mari ,
Baice komai ba sai shafa gurin da yayi kafin kace me hankalin kowa ya dawo gurinsu bodyguard ne guda uku suka yi kana da shirin duka ,
Matashin saurayin ya dakatar dasu yana huci .
Durƙusawa Diyana tayi ta cire sim ɗinta tabar wayar a gurin , ta ƙarasa gurinsu Khairat da taketa zubda hawaye tana kallon Diyana , zama Diyana tayi takai dubanta ga Khairat da idanunta sun fara ja tsabar kuka ,
“afuwan amaryar mu cewar Diyana , Kamill wato ango da yanzu ya dawo gurin zamansa , kasancewar yaje bawa babban amininsa haƙuri ya dubi Diyana ,
yace “amma Diyana kinyi ganganci maiya kaiki kula wanan bawan Allahan?”,
Lumshe ido Diyana tayi tace ” Kamill sanin kanka ne bana ɗaukar raini shiɗin waye waye babansa ? shiii!!!, Kamill yace ” karki ƙara magana ,
Ƴan matan dake gefe sai kallon Diyana sukeyi masu gulma nayi kowa yana ganin Diyana batada tarbiya wasu kuma daga can gefe , suna cewa ai gara da tayi masa haka ,
Maganin mutumin da bai ɗauki ɗan adan da daraja ba kenan ,
Shigowar Afreeda kenan taga anata nuna Diyana , kai dubanta tayi gurin da Diyana take zaune ,
ganin fuskarta babu walwalah yasata ƙarasawa da sauri ,
Ruƙo hanun Diyana tayi tace ” my sis maiya faru ?” kiyi haƙuri kinga na daɗe ko ?” munje duba wata abaya ne da za’ayi yayi wanan sallahar ,
lumshe ido Diyana tayi kana takuma buɗesu tace ” karki damu sis damuwata da ban kizo ki zauna ,
Khairat itama jikinta duk yayi sanyi , haka dai aka kira abokan ango da ƙawayen Amarya , farko sunan Diyana aka fara kira na biyu kuma babban aminin ango wato Kamill , sai da gaban Diyana ya faɗi , komawa gurin Kairat tayi ta raɗa mata a kunne cewar sis bazan iya rawa da wancan banzan ba…..!
[31/05, 12:43 am] Mom Islam Ce????: ???????? ????????
*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 9 & 10
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
Sa sauta murya Khairat tayi kana tace ” pls kiyi haƙuri kije na lokaci ɗaya nefa ,
Badan Diyana taso ba ta wuce ta nufi gurin da aka tanadar musu na rawa ,
Mc ne yasa mutanen gurin tafa musu , ya fara kwararo musu yabo , kaga matashin saurayi mai ji da kansa ƴan mata ma wawarka sukeyi , kai ku tafawa Alhaji Kamill ɗa ɗaya tilo a gurin mahaifinsa wato Alhaji Safiyan gidan kuɗi .
A zabure Diyana ta ɗago kai takai dubanta ga Kamill da shi hankalinsa ma ba a gurinta yake ba ta kawar da kai ,
innalilahi ragowar ta maƙale mata ma maƙoshi , tasani ubansa ba sa’an ubanta bane yafi ubanta dukiya hatta mahaifinta yana girmama Alhaji Safiyan kuma yafi mahaifinta suna kasancewar sunansa ya zaga ƙasashe da dama harda na ƙetare ,
Duk da shima ubanta sunanshi ya shahara amma ko kwatan na uban Kamill bai yi ba ,
Jiyo maganar Mc tayi yana cewa ” an gaisheki babbar ƙawa aminiya kyakyawa kuma kuma fasihiya a fanin iya kwaliya kai kubata tafi , kowa yakama raf raf hankalin mutanen duk ya dawo gurinsu ,
mc ne ya bada umarni aka sanya waƙar da akayi ta biki , Kamill rawa yakeyi tsakaninsa da Allah matsowa kusa da Diyana yayi yace ” ƴan mata ki taka man karki bada manyan mata har video akeyi fa , wanan sunkuyowar da Kamill yayi yana yiwa Diyana magana wasu abokan Kamill suka fara ɗaukarsu hoto aikuwa sun bada kala ,
Ɗan takawa tafara a hankali jikinta a sanyaye amma tanajin inhar Kamill ya kuma ɓata mata rai babu abinda zai hanata ci masa mutunci koda komai zai faru ,
tsayar da kiɗan akayi mc yace suje su huta , ran Diyana ya ɓacci sosai musamman da zasu sauko Kamill yakuma sunkuyawa yayi mata magana .
Khairat ce ta janyo Diyana tace ” nagode sis nasaki abinda bakiso ko am sorry , rufe mata baki Diyana tayi da cewa ” a’a sis karki damu wancan banzan ne ya ɓatamin rai badan haka ba da komai zai tafi normal,
ƙarfe 8pm an tashi anyi su yanka cake da hotuna, Afreeda ce ta kamo hanun Diyana tana cewa sis momy na kira wai mudawo gida okay Diyana tace “.
Bayan sun bawa ƙanwar Khairat abinda zasu bata sukayi sallama , kasancewar Afreeda ta kira driver yazo ya ɗaukesu , suna fitowa sukaci karo da Kamill yana waya yana murmishi , tsaki Diyana taja kana ta janyo Afreeda sukayi mota , wani killer smile Kamill yayi ya zura hannayensa cikin aljihun shaddarsa , ganin motarsu na shirin tashi ya koma gefe ya tsaya tare da ciro wayarsa , numbar bodyguard naga ya dannawa kira ko 3 mins ba ‘ayi ba sai gasu nan sun taho sun tsa tsaya a gabansa tare da sunkuyar da kai ,
sukace barka prince yawancin abokansa da sunan suke kiransa amma ba kowa yasan da wanan sunan ba ,saboda wasu dalilai , haɗe rai yayi yace ” kunga waccan motar maza kubita karku bari su gane okay sukace , cikin hanzari suka shige mota ,
Sukabi motar da yanzu ta fice daga harabar gurin.
Tafiya drivern nasu yakeyi cikin ƙwarewa ba kowa zai san yanabin wata mota ba kasancewar ko kwana motarsu Diyana batayi ba .
Tunda Diyana ta shiga mota tafara tuno abinda ya haɗasu da kamill a zahiri itama tanada laifi amma sam batason raini hakan yasata yimasa rashin mutunci ,sai huro hanci takeyi .
Afreeda ta lura da yanayin sis ɗin nata amma bata kulata ba kasancewar tasan halinta inta fiya shiga harkarta a time ɗin da take cikin baƙin ciki sukan iya ɓatawa su kuwana ma basu shirya ba ,
A haka suka isa gida babu mai cewa komai ,
Bata jira driver yazo ya buɗe motar ba ta fice zuciyarta nayi mata ƙuna ,
ko sallama batayi ba ta shiga palon ganin Hajiya da Tinene a palo yasata yamutsa fuska ta wuce bedroom ɗinta ,
Hajiya dake zaune ta riƙe haɓa tana jinjina lamari irin na Diyana ,
A fili tace ” nikam wanan wace irin yarinya ce batasan darajar mutane ba , Tinene dake zaune gefen Hajiya tace Hajiya sufa ƴan binni basu damu da sallama ba ,
Hajiya ce ta ranƙwasheta kana tace ” badai duka ba ita wanan mai zuciya kamar faɗa wuta bansan gadon wa tayo ba,
Sallamar Afreeda ce ta katse musu zance suka amsa tace ” sannu Hajiya ,
Washe baki Hajiya tayi kana tace ” ywwa ƴar albarka kun dawo lafiya ?” lafiya Afreeda tace” ta wuce ciki .
Kai tsaye bedroom ɗin momy ta wuce , da sallama ta shiga ta gaida momy , kun dawo sai yanzu ko ? momy ta jerowa Afreeda tambayoyi , am sorry mom wlh matsala aka samu amma yanzu komai yai normal ,
Momy dake kallon fuskar Afreeda tana nazrin ta tace ” ina Diyana ?” tana bedroom ,
Kiramin ita,
Tom Afreeda tace ” Afreeda na fita momy tashiga tunani tasan duk lokacin da ran Diyana ya ɓaci bata wai wayar kowa har ita ma to yau kuma maiya faru ?” batada mai bata amsa yasata zama gefen gado tana jiran shigowar Diyana ,
A’ ɗakin Diyana Hajiya ce tsaye a bakin ƙofa tana balbale Diyana da masifa akan rashin ladabi , kuka Diyana tasa mai sauti dan a halin yanzu babu abinda zatayi zuciyarta tayi mata daɗi sama da kuka ,
Tafa hannu Hajiya tafara tana salati tace ” to sharri zakiyimin ? shigowar Afreeda ne yasa Hajiya yin shiru ta juya bata ƙara magana ba .
Dafata Afreeda tayi kana tace ” my sis momy na kira pls ki share hawayennan karki ɗaga mata hankali ,
To kona share hawaye mezan ce mata banison tasan irin target ɗin da na shiryawa wancan jakin dan wlh tunda yasani zubar da hawaye nima sai na wulaƙantashi , Afreeda ce tace ” sis wai kina nufin Kamill ?” eh Diyana tace tana girgiza kai alamar tabatarwa ,
Wani marayan nunfashi Afreeda ta sauke kana tace ” sis ki janye wanan maganar bazaki iya da Kamill ba mahaifinsa yafi dady komai hasali ma dady zai iya zama ɗan aikensa…..! wani mahaukacin mari Diyana ta sakarwa Afreeda tare da nuna mata hanyar waje,
why zaki ƙara ɓatamin rai kinada hankali kuwa ?” Afreeda ficewa tayi tana kuka a ranta kuwa cewa ” tayi da badan tunda suka taso bata taɓa yiwa Diyana rashin kunya ba ,
Da yau sai sunyi dambe ,
ficewarta shine mafita,
Fitowa tayi daga sashin ta rufo door ɗin , mai gadi na hangota yafara miƙo gaisuwa dan jininsu ya haɗu da Afreeda kasancewarta batada wulaƙanci ,
Yanata gaisheta amma ko saurarar shi batayi ba , bai damu ba yasan hakan tana faruwa in tana cikin fushi bata cika magana ba ,
Gurin furannin gidan ta nufa tanata tsinkarsu tana jefarwa , miƙewa tayi ta dawo cikin gida ,
Samun momy da ƴar aiki tayi sunaya jera abinci a dining saita nutsuwarta tayi , kana tace ” sannu da aiki momy, murmishi momy tayi kana tace ” to ayi magrib azo aci abinci food is ready ,
sunkuyar da kai Afreed tayi tace ” okay momy ta shige ciki , jinjina kai momy tayi dan taji faɗansu na ɗazu amma ba komai nasu take shiga ba tunda daga sunyi faɗan suke shiryawa kamar ba suba ,
Kai tsaye Bedroom ɗinsu Afreeda ta wuce ,
Samun Diyana tana sallah yasata shiga toilet tayi alwalar itama ta ɗauki sallaya tafara sallah , bayan sun idar dukansu,
Diyana ta rungume Afreeda tace ” am sorry my sis kiyimin afuwa karkiyi fushi da sistanki tana buƙatar taimakonki ,
Sauke ajiyar zuciya Afreeda tayi tace ” karki damu komai ya wuce momy na kiranmun,
Afreeda tayi hanyar waje zata fita Diyana ta riƙo mata hannu , haɗe hanuwanta Diyana tayialamun neman alfarma tace ” my sis pls karki sanarwa momy abinda ke fariwa kinsanta da saka abu a ranta,oky dont worry i promise bazan faɗa ba zomuje kici abinci yau abinda kikeso ne akayi,
Menene shi?” Diyana ta tambayi Afreeda, plantain and egg Afreeda tabata amsa da sauri suka nufi dining kowacce fuskrta a sake,
Sannu momy ,
Ywwa daughters harkun fito ?”.
Eh momy .
Hajiya dake gefe a zaune a kan kafet itada Tinene tace ” to sabon salo uwar waye bazaku cewa hannu ba , yara sai kinibi bin tsiya to ba mutuwa zanyi ba , Tinene dake gyara zani tace ” kaka wanan abin yayi daɗi aɗan ƙaramin asamin kabejin da yawa , momy ce ta ƙwalawa Nana ƴar aikinsu kira tace ” ta daɗowa Tinene kabej kasancewar Hajiya ce tace ” dole ayi mata kwaɗon kabeji da ƙuli kuli ,
Aikuwa basuci abincin kirki ba sai kabeji ,
Afreeda ce ta ƙunshe dariya yanda taga Hajiya na kwasar kabeji to Allah ya kyauta .
Suna gama ci momy tace ” in akayi isha’i tanason ganinsu , Hajiya ta miƙe tana dogara ƙafa ta nufi ɗakinsu ,
Sanda Tinene tayi fam da kabeji sanan itama tabi bayan Hajiya ,dan bataga alamar gidan suna wasa da yara ba shiyasa takejin tsoronsu ,
Bayan isha’i Diyana da Afreeda suka shigo ɗakin momy kowacce na jiran taji metayi ,
dubansu momy tayi kana tace ” gaskiya kuna shirin bani kunya ,
Kunga tsohuwar nan duk ranat da ta haɗaku da dadynku wlh zakuji babu daɗi tunda yana amfani da duk abinda ta gaya masa to wlh ku kiyaye ,
Kuma batun gaisuwa kowacce daga cikinku tadinga zuwa da safe tana gaisheta Afreeda banida matsala dake amma Diyana yakamata ki rage abubuwan da kikeyi ke mace ce fa gidan wani zaki,
Haƙuri suka shiga bawa momy da alƙawarin bazasu sake ba lol nidai nasan gimbiya da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa ,
Allah yayi muku albarka kuje saida safe , miƙewa sukayi kowacce da abinda take saƙawa a ranta .
Tunda suka shiga ɗaki , Diyana taketa ƙwafa tana tsaki zama tayi a gaban dress mirror kan wata ƙujera mai kyau ta dubi Afreeda tace ” wanan tsohuwar tafara kaini maƙura, cikin sauri Afreeda ta ƙarɓi zance tare da cewa wlh kamar kin shiga zuciyata dan dazarar dady ya dawo zata iya haddasa mana fitina,
Diyana ce tace ” zokiji , banji mai sukace ba naga sunyi dariya harda tafawa ,
Dare yayi sosai kowa na gidan yayi bacci bakajin ƙarar komai sai na AC da fridge , Diyana ce ta farka dan har bacci ya ɗaukesu tashin Afreeda tayi suka farashirin abinda yakamata suyi , wani jan ƙyale Diyana ta ɗauko kana tace ” Afreeda ta ɗauko mata teddy , tana ɗaukowa suka fara kiciniyar sanyawa teddy janbaki da jan ƙyale , kana suka ɗauko wata hoton fuska , wace suke sawa in zasuyi wasa a school lokacin suna secondary ,
Nice zansa wanan kekuma ki ɗauki farin hijab ɗinnan kisa ki riƙe teddy ki tabbatar da kin rufe fuskarki…….!.
[31/05, 12:44 am] Mom Islam Ce????: ???????? ????????