GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

*GUGUWAR ZALUNCI*
11&12
Afreeda ta sanya farin hijab wanda ya rufe mata fuska ko ina kasancewarsa kamar mai niƙaf , ta ɗauki teddy ta rungume .
Sanya fuskar Diyana tayi ta kalli kanta a mirorr ta kwashe da dariya tana cewa yau zamu birkito musu kabej lol.
Fita daga ɗakin nasu sukayi suka nufi ɗakin da aka bawa Hajiya ,
A buɗe ƙofar take hakan yasa basu sha wuya ba suka kutsa kai ciki ,
Hajiya na kwance ansami katifa mai laushi sai gwarti take kwasa,
Tinene na gefenta itama bacci takeyi yau na gangarowa ,
Afreeda ce ta shafa fuskar Hajiya tana cewa munzo ne muji dalili ,
Buɗe idon da Hajiya zatayi ai taga kammanni kamar na aljanu ta tashi ta zauna dama ɗakin ba wani hasken kirki sbda tunda suka shigo Diyana ta rage Hasken ,
mai kuma yau nayi muku bayin Allah ?”
Maƙale murya sukayi dukkansu sukace , wayace kizo birni ?” bakisan mun maida ɗakin ki na ƙauye turakar babanmu ba ?” a razane Hajiya ta runtse ido tana shirin kurma ihu ,
rufe mata baki sukayi da hanunsu dake sanye da hand globe , kikayi ihu zakisha mamaki zamu tafi da jikarki , Tinene da tun ɗazu ta tashi taƙi ɗago kai dan itama Allah ya zuba mata tsoro, Hajiya duk jikinta rawa yakeyi kasancewarta matsoraciya ba ta wasa ba , haɗe fuskarsu Diyana tayi tanata zaro ido cikin fuskar nan jin fitsari yana ɗiga ta gefe yasa Diyana cewa , shine aka jiƙa mana ƴaƴanmu to tun wuri ki kwashe shi kokuma yanzu mu tafi dake ƙasarmu , Hajiya na kuka tana tsane fitsari da zaninta sbda akwai sikel ɗin ciki a jikinta , tagumi ta zuba tana magana , duk inda naje sai kun biyoni?” a ‘garin namu ma baku barni ba ,haka anan ma bazaku barni ba ?” .
Hajiya tasa kuka tace ” wlh kakanmu ya cucemu da yabar mana gadon aljanu wayoo mun higa uku , nanfa Diyana da Afreeda suka fara kwasar rawa suna takawa kai kace aljanun gaske ,
Jiyo tari sukayi ta gefen Tinene , Afreeda ce ta ƙarasa gurin tace ” idan baki tashi ba saimun maidaki akuya , ai da gudu ta miƙe jiki na rawa kan kace me ji kake ɓirrr tana shirin sake musu kashi ,
Waro ido Diyana tayi tace ” kifito kizo yanzu birnin mu zamu kaiku ,
Cikin azama Hajiya ta sakko ta durƙusa gaban Afreeda kasancewar tafijin tsoron teddyn hanunta , tace ” kuyi haƙuri yarinya ce batasan komai ba kuyi mata aikin gafara dan Allah , nasanku kunfimu haƙuri to ku ƙara , Afreeda ce ta kece da dariya marar sauti sosai ta dubi Hajiya da ta jiƙe da zufa dakuma hawaye , jitayi tausayinta ya shigeta ta dubi Diyana tafara yimata wani irin yare , gani nayi Diyana ta girgiza kai alamar a’a .
Matsowa Diyana tayi tace ” nan ɗakin na uban ubanmu ne yatafi misira kuma yabamu ajiyarsa to kufice kokuwa musa a ɗagaku sama ,
Tinene da taƙi fitowa daga bayi , Afreeda ta ƙwanƙwasa ƙofar tace ” kigama muna jiranki, ku bakwa ganin mutane a gefenku a kwance zaku shigo mana ɗaki koku bar wanan ɗakin ko gidan gaba ɗaya kokuma mu ɓatar daku daga duniyar …..! kafin su ƙarasa magana Hajiya ta buɗe bayi ta janyo Tinene dake tsaye babu ko wando kasancewar in zatayi kashi saita cire wando , suka nufi palo babu ko magana,
Tafawa sukayi Afreeda tace ” zamu gudu , raɓawa sukayi ta gefe suka wuce batare da kowa ya gansu ba , dama momy na can sama sukuma suna ƙasa ,
Suna shiga bedroom ɗinsu suka fara tsalle sunata dariya ,
Duba wayarta Diyana tayi lokacin ƙarfe biyu da rabi na dare, kowacce ta nemi gurin kwanciya asuba ta gari.
Washe gari da safe kowa na gidan na bacci kasancewar weekend ne sai shaɗaya 11am suke breakfast,
Tun shida Hajiya ta tashi taje ɗakin Nana mai aiki ta tasota ,
Sata ɗora ruwa tayi da abinci , babu shiri tafara kiciniyar abinda Hajiya ta sakata ,
Da farko dai ruwan wanka aka miƙowa Hajiya cikin sauri ta karɓa tana sakawa Nana albarka , tashin Tinene tayi tazo tayi wanka yau a garinsu zasu kwana , Tinene dake bacci mai daɗi cikin bacci , tace “Kaka ni kibarni nayi bacci kina ganin jiya gudawa tasani gaba , tsabar haushi da ya cika Hajiya tace ” uban gudawa , dan uwaki ni zaki gayawa kinyi gudawa to tun wuri kitashi muje kiyi wanka , dan yau sai Shafa ƙauyenmu , a zabure Tinene ta miƙe ta riƙe ƙugu tace ” wlh babu inda zani ,
Kaji kaka dai da wani zance , muna hyan hyayi da burodi kice mutafi to yasin ko dafani akeyi nan naga gurin zaman dan haka kima canza tunani ,
Riƙe baki Hajiya tayi tana tunanin kodai Tinene ta mance halin da suka shiga jiya take batun zama, to bara inje inyi wankan in fito wlh saikin bini bazakisa ubanki ya tambayeni ina kikaje ba ,
Wucewa Hajiya tayi ta nufi ɗakinsu da ya zame mata abin tsoro tashiga da adu’a tana cewa ” wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir rahim, tashige ta surka ruwan ,
Bayan tayi wanka ta fito ta , tattara kayanta a buhu ta shafa manta da farin kwali ta sanya kaya ta fito palo.
Baccin kuwa ta koma hankali kwance da mamaki inna ta hamɓareta tace ” wlh kitahi kokuwa insa masu gadi su ɗaukeki , da sauri ta tashi tayi ɗakinsu , tana shiga aljanun jiya suka faɗo mata ihu tafara kurmawa tana ƙarawa , a na biyun ne ya tashi mutanen gidan dukansu da sauri momy ta fito tana tambayar lpy kuwa? Hajiya da yanzu take shirin shiga ɗakin dan tsoro ya hanata tace ” leƙa kigani faɗimatu ko aljanu ne , aljanu kuma ? momy ta mai maita ,
Eh leƙata , Hajiya ta kasa taɓuka komai sai cewa leƙata, shiga momy tayi ta leƙa bedroom ɗin ganin tinene na wanka tana tsala ihu yasa momy shiga tafara tambayar anya lpy kuwa Tinene ? , nan ma hankalin Hajiya yakuma tashi taƙara tattaro kaya tana cewa wlh aljanu sun samu a gaba a gidannan , inna zuwa ƙauyenmu bazan sauka ko ina ba sai gidan malam fari ,dan wlh dole ya yimin istahara akan aljanun gidan Alhaji ,
Duk da nima na gidana basu barni ba dole naɗau mataki , momy dai jin hajiya takeyi dan ba abokiyar yinta bane ,
Amma su da basu taɓa jin hayaniyar komai ba amma ace wai gidansu da aljanu , kodai rikicin tsufanne ya motsa , to Allah ya daɗa karewa momy tace ” ta fice , Diyan da Afreeda suna zaune a palo kowacce ranta fess Hajiya zatabar gida , amma basu nuna a fuskarsu ba ,
Ganinsu a palo yasa momy cewa ” ku bakusan abinda ke faruwa bane ?” yamutsa fuska Diyana tayi tace ” good morning momy , bata amsa ba sai ƙara jero musu tambayar taƙarayi ,
langwaɓar da kai Afreeda tayi kana tace ” momy munji ihu ne mafa ya tashemu wlh “mai ya faru ne , kuje ku tambayi Hajiya , daganan momy tayi gaba ,
suna ganin momy ta wuce suka tafa suka miƙe kowacce ta koma gado ,
Ɓangaren Hajiya tagama shiri tsaf Tinene take jira , itama Tinenen tunda Hajiya tace mata inhar bata zo sun tafi ba to babu ruwanta ,
Ko ta mance da takarar da aljanun jiya sukayi na cewa zasu ɓatar damu , aikwa babu shiri Tinene jiki na tsuma tace ” zan biki yasin bazan zauna ba ,
Amma fa zamuyi kewar ruwan hyayi mai madara ,
Ke dalla can marar tunani lafiyar mu tafi hyayi dan haka mutafi kawai , basa bibiyar ƴan gidan sai baƙi to dole na nemowa Alhaji magani wataran mutan gidan zasu nema ,
Nafito ina zaure kisameni a can , Tinene dake ɗaura zani tace ” ganinan .
Kamill ne zaune a wata ƙayatacciyar kujera ita kanta kujerar abin kallo ce bare wanda ya zauna akan kujerar , dogo ne fari ,
yanada manyan idanu inka ganshi kamar balarabe ,
Gashin kannan nasa luf luf kamar wanda ake shafashi ga baƙin sajen da ya ɗan kewaye bakinsa yana ɗauke da pink lips ,
Yanayin jikinsa kaɗai ya ishi mai kallonsa yasan cewar kuɗi yazauna bai taɓa neman abu ya rasa ba ,
idan kuɗi yakasa samar masa yakan sa basira ,
Idan basira ma bata samo masa ba yakansa ƙarfinsa domin ya mallaki abinda zuciyarsa takeso ,
iyayensa suna zaune a kano unguwa uku , gidansu ya fita daban da shauran gine gine amma shi ba mazauni bane, haka mahaifinsa Alhaji Safiyan gidan kuɗi baya rayuwa a Nigeria , kasancewar sa hamshaƙi , bare uban gayya wato Kamill .
Ɗai ɗai garin da bai mallaki gida ba saboda hutawa aure baya gabansa hakan yasa iyayensa zuba masa ido yakeyin abinda ranshi yakeso,
Juyi yayi a kujerar ya kalli bodyguard ɗin dake zagaye dashi yace ” kun gano min gidan su wanan yarinyar ?” yes oga mun ganshi mahaifinta shine Alhaji Sani alherin Allah , buga ƙasa Kamill yayi tare da furzar da isa daga bakinsa ya katse mai maganar da cewa ” wato ubanta bama kowa bane amma ta takani , to wlh bazan barta ba saina tozarta ta dole tayi hankali koda a gaba akace ta yiwa wani haka bazatayi ba ,
Miƙewa yayi ya nufi ciki daga bakin ƙofar flowers ne suketa haska ko ina , shiga yayi yana takunsa na ƙasaita ya zauna a kan wata fitinanniyar kujera ,wanan ɗaki na Kamill faɗar kyansa bazai rubutu ba,
Kasancewar ya tsaru shi kansa palon kai kace ɗakin mai mata ne , ga wani ƙamshi dake tasowa ta jikin wasu flawoyi dake manne a bango, ɗaukar apple ya ɗauka yakai bakinsa , kaɗan ya gutsura ya ajiye tare da cewa , natsaneki!!!!.
Ya riƙe kansa dake yimasa wani irin ciwo kasancewar sa inhar yasa damuwa a ransa to sai yayi zazzaɓi ,
wanan karon ma hakan ce zata faru ,
tashi ɗaya jikinsa yai zafi , babu inda ya iya bare ya kira bodyguard ɗin nasa su temaka masa sbda ya hanasu shiga part ɗinsa muddin ba shine ya turosu ba ,
Baccin wahala ne ya ɗaukesa sai wajen ƙarfe uku na rana ya farka ,
Jikin yayi masa sauƙi sosai miƙewa yayi ya zauna kan bed tare da janyo bed side ya ciro maganinsa ya ɗauki ruwa a fridge yasha ,
Jin wayarsa na ring ya dawo kan kujera ya ɗauki wayar , cikin muryar tasa da duk wanda yasansa yasan babu lafiya , yace ” Aslamu Alaikum Abba .
Wa’alaikumussalam ɗan albarka ya kake , Kamill ne yace ” lpy lou Abba yaushe zaka dawo ?” gobe insha Allah mai kakeso ?” dariya Kamill yasa kana yace ” Abba akwai kyakyawan albishir wlh Allah dai ya dawo dakai lafiya , kodai mafarkina na ne zai tabbata zan sami suruka , dariya kamill yayi yace ” saidai kazo ɗin sukayi sallama.Ce ????????