HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

*GUGUWAR ZALUNCI*

PAGE 13&14

 

Hoton fuskar Diyana ne keyi masa yawo da wata shu’umar dariya yayi ya miƙe toilet ya nufa ya ɗauro alwala yafito domin zuwa masallaci.
Da wani buhu Tinene ta fito da alamu buhun kayansu ne , Nana tazo wucewa Hajiya ta kirata , durƙusawa tayi tace ” gani hajiya ,
Hajiya dake mamular goro tace ” ina abincin namu ?” da sauri Nana ta miƙe tanufi kitchen ta fito da shinkafa , da cokula guda biyu dakuma faranti ,
Bajeshi Hajiya tayi, suka fara ci jin abincin yayi daɗi Tinene ta turo baki tafara shura ƙafa tana cewa” gaskiya kaka inhar na yarda na biki to yasin nayi asara ,
Innalilahi bina hine asara?”
Ƙara kai lomar shinkafa Tinene tayi tana cewa wanan ai hine kaga samu kaga rahi any zan iya bin Kaka kuwa ,
11am momy da iyalanta sun hallara a dining yau kam sun gaishe da Hajiya , breakfast momy da Afreeda sukeyi banda Diyana da ruwan lifton takesha sai juya cokali takeyi a ciki alamar akwai abinda ke damunta, babu wanda ya kulata ,
Wayar momy ce tafara ring ganin sunan dady yasata ɗagawa tare da gaisuwa ,
Ganinan shigowa ma ina bakin get , masha Allah momy tace ” Allah ya shigo dakai lafiya ,
Hajiya da ɗan ƙullin buhunta da Tinene suna zaune ,
Sukaji sallamar Alhaji ,
Washe baki Hajiya tayi tace ” hannu dai Alhaji ,
ywwa Hajiya munsame ku lafiya ?
Lpy lou Hajiya tace ” tana daɗa gyara ɗaurin bakin buhunta ,
Hajiya mekuma muka samu ?”
Diyana da Afreeda ne suka karɓe zancen da cewa barka da dawowa dady , kafin ya amsa Hajiya tace ” gida zan wuce bazan ƙara kwana a gidanka ba kaji na gaya maka ,
Sunkuyar da kai momy tayi dan wanan al amarin yafi ƙarfinta da tana ganin abin kamar wasa yanzu ya wuce tunaninta , gara taja bakinta tayi shiru inyaso insun gama ta tofa nata ,
Gyara zama dady yayi yace ” Hajiya kina nufin wai ƙauye zaki koma ?” eh Hajiya tace ”
maiya faru da zaki ɗago tafiya haka yanzu da bayau zan dawo ba sai dai inji ta tafi kenan , Hajiya ce ta nuna momy tace” laifin matarka ni babu ruwana ehe tafiya zanyi gidanka duk aljanu hatta ɗakin da muke ma saida suka jamana kunne ,
Miƙewa tayi tare da janyo hanun Tinene tace ” tahi karmuyi dare, momy da sai yanzu tayi magana tace ” kayi haƙuri dan Allah ,
Da’ na ɗauka ba tafiyar zatayi ba , shiyasa ban gaya maka ba .
Hanyar fita Hajiya take shirin yi dady yasha gabanta tare da durƙusawa yace ” Hajiya dan girman Allah kiyi haƙuri ki zauna babu komai a gidannan ,
Zan kira ayiwa gidan sauka yau ɗinnan dan Allah karki tafi ,
Tausayi ɗa da uwa Hajiya ta juyo ta zauna kan kujera tana cewa ” to wlh tun wuri ka kira malamin dan jiya a rumfa muka kwana ,
Dady baiji daɗi ba sam amma baice komai ba ,
Sama ya haura zuciyarsa babu daɗi ,
Bin bayansa momy tayi tana jiran abinda zai biyi baya ,
Salama tayi ta samesa yana cire maɓallin rigarsa ,
Ciki ciki dady ya amsa bai ko kalleta ba ,
Zama momy tayi a gabansa tare da janyo hannayensa ta zaunar dashi ,
haba mijina mai nayi da zakayi fushi dani ?”
Inhar maganar Hajiya ne to kayi haƙuri naɗauki lefin dan girman Allah ,
duk da haka bai kulata ba saima shirin shiga toilet ɗin ɗakinsa daya fara yi ,
Da sauri momy taje ta tara masa ruwan wanka ta tsaya a toilet ɗin tana jiran shigowarsa , tasan mulki da isa irin tasa ,
Har ace gadon wa Diyana tayi hmm , momy taji shiru bai shigo ba ,
tana fitowa ta samesa a zaune yayi shiru yana bubuga ƙafa,
ɗumin hawayen da yaji ne yasa shi ɗago fuska a razane yace ” Faty maiya faru , cikin kukan kissa momy tace ” nabaka haƙuri kaƙi saurarata kasan bana jurar ɓacin ranka ,
Janyota yayi jikinsa yafara shafa gashin kanta alamar tayi shiru , bakya girma ,
Dady yace ” yana murmishi , itama murmishin tayi tace ” to kaima ɗin haka ne ,
miƙewa dady yai yace ” zoki taimaka min inyi wanka idan na kintsa inason muyi magana dake ,
Miƙewa momy tayi daga kan cinyar dady ta riƙo masa hannu suka nufi toilet ,
Diyana da Afreeda ne a ɗaki kowacce na baƙin cikin dawowar Hajiya gidan , gaskiya dama Allah bai dawo dady yau ba da sunji daɗi ,
Diyana da abin duniya yataru yayi mata yawa tace ” kiji ɗazu wai laifin momy take cewa ?” Afreeda ce ta cire tagumin fuskarta tace ” ai wlh tadinga haɗa momy da dady faɗa kenan tunda bakinta bashida zip .
Haka dai suka dinga jajantawa gashi sun rasa mafita da zasu ɓullowa lamarin.

Yau Alhaji Safiyan ya sauka a Nigeria bai sanarwa kowa ya sauka ba sai drivern sa , kai tsaye daga airport unguwa uku aka wuce dashi wato gidansa ,
tun daga bakin get bodyguard keyi masa barka har yakai ga shiga cikin gidan ,
Hajiya Amina dake zaune a kujera wata dattijuwar mata tana mammatsa mata ƙafa ta miƙe , tana murmishi tare da cewa ” barka Alhaji dawowa babu sanarwa ,
Alhaji ne yace ” banda abinki Meena wanan karon nefa ban sanar miki ba to ayi haƙuri , sukasa dariya dukkansu ,
Tunda ma’aikatan gidan sukaga shigowar Alhaji kowacce tashe kitchen mai girki nayi mai haɗa lemo nayi mai farfesu kifi nayi mai farfesun kaji nayi abinci dai kala kala kowacce ta kama dama ƙa’idar gidan kenen ,
Amina ce tace ” Alhaji tashi muje kayi wanka sai kaci abinci ,
Babu musu ya miƙe amma a zahiri burinsa yaga Kamill ,
Bayan yayi wanka yai shigar alfarma ya fito shida Ameena suka nufi dining da masu aiki suka cikashi da kayan ciye ciye dakuma abinci masu lafiya ,
jollof ɗin shinkafa Ameena ta nunawa Alhaji tana dariya tana cewa ” alhaji ga abinda kakeso yaji kayan lambu ,
Alhaji dake daddana waya yace ” zubamin kisamin farfesun kifi a gefe,
Bayan dady yaga cin abinci ya tambayi Kamill ,
yamutsa Fuska Ameena tayi tace ” rabona da insashi a ido 3 weeks kenan ,
Jinjina kai Alhaji yayi batare da yace ” komai ba ya miƙe ya fice direct ɗakinsa ya nufa ya kwaso wayoyinsa ,ya danna lambar Kamill , ring ɗaya ya ɗauka tare da sallama , Alhaji na amsawa yace ” kazo gida ina nemanka ,
Tom Abba harka iso ne ?”
Eh Abban yace ” ya kashe waya .
bubuga ƙafa Kamill yashiga yi kamar ƙaramin yaro yana cewa ” natsani zuwa gidannan wlh amma babu inda na iya dole na naje ,
wanka ya shiga ransa a ɓace ya fito ya zura jallabiya baƙa mai hula ,
ko shafa mai baiyi ba yafito riƙe da key a hanunsa ,bodyguard ɗinsa ne suka fara jero masa barka ,
Babu wanda ya kula driver ne ya fito da sauri yace ” Alhaji wacce motar za’a ɗauko ,
wani mugun kallo kamill ya watsawa driver ,
Babu shiri driver yayi ta kansa , ma’aikatan gidanne suka fara gulma akan yanayin da uban gidansu ya tashi Allah yasa lafiya ,
Jin faɗuwar gaba ta tsanta masa yasa shi ambato innalilahi a rayuwarsa yatsani Amina shiyasa ko gidan baya son zuwa , Allah yasa ba wani bom ɗin ta haɗa masa ba a gurin Abba ,
Shiga wata mota yayi fara kyakyawa ya harba titi , tafiya yakeyi yana tunani yarasa dalilin faɗuwar gabansa ,
wani mahaukacin horn yayi sanin ko waye yasa masu gadi da kowa na gidan saita nutsuwarsa ,
Mai gadi na buɗewa Kamill ya shiga , daga bakin get ɗin yayi parking ya nufi ciki , duk yawan mutanen da suke miƙo masa gaisuwa bai kula kowa ba, ko sallama baiyi ba ya shiga palon , Ameena na zaune tana kallo a tv ta ɗago kai ta kalesa ta mayar da hankali ga tv .
Abba na ciki ?” Kamill yace ” kana ya kawar da kansa gefe yayi ,
Ganin bazai sami amsa ba ya wuce ta bai ko ƙara kallon inda take ba ,tofa maiya haɗa Ameena da ɗanta ..
Yana shiga ya sami Abba zaune da laptop a hanunsa yana sanye da farin glass a fuskarsa ,
Cikin fara’a Abba ya ɗago kai yace ” oyoyo my son ,
Barka dai Abba Kamill yace ” yana neman gurin zama ,
Bayan sun gaisa da Abba shiru ya biyo baya na ƴan wasu mintuna , Kamill ne yafara dana sanin sanarwa da Abba , alƙawarin da yayi ,
Jin shiru yayi yawa Abba yace ” to Kamill Abbanka ya dawo cike da farincikin son jin albishir ɗin da zakayi masa ,
Wata mumunar faɗuwar gaba ce takuma ziyartar Kamill zufa na keto masa ,
Cikin ransa yace ” zan cuci kaina mai ya kaini gayawa Abba kuma inya faɗi magana baya sauyi , shafa sumar kansa yayi yace ” am Abba dama dama…
Abba ne ya fahimci maganar tayiwa ɗan nasa nauyi ya murmusa yace”karka damu koma menene gayamin bakada matsala ko kaɗan ,
Kamill ne yace ” Abba yarinya nagani …
Ragowar maganar ta maƙale masa a maƙoshi , masha Allah Abba yace ” yana faɗaɗa fara’arsa , Kamill ko sai yanzu yakeyin asalin dana sani sosai .
Ƴar gidan waye ?” Abba ya tambayi Kamill ,
Ƴar gidan Alhaji Sani alherin Allah ce , Abba ne ya ƙara murmusawa yace ” haƙiƙa wanan rana nake jira naji daɗi sosai nayi farinciki , ai mutumuna ne shiɗin babu damuwa komai zai dai daita kaidai kaci gaba da nemanta insha Allah auranku zai zamo alkairi ,
Kan Kamill a sunkuye baice komai ba yanata nazarin maganar da ya yiwa Abba , nasiha Abba yashiga yimasa akan halin rayuwa , daga ƙarshe Abba yace” ka kiramin Amina ,
ɓata rai Kamill yayi yace ” tafice daga gidan zan shigo naga tahau mota driver ya jata, what..! Abba yace ” yaushe ta tambayeni dahar zata fita , oky jeka idan mukayi magana da uban yarinyar zan kiraka , tom Abba Kamill ya fice ranshi ta wani fannin fess wanan makirar zatasha faɗa , ya fice daga gidan ,
Yana shiga mota maganar da ya gayawa Abba dakuma farincikin da Abba yayi akan maganar auran ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba ,
Tabbas Diyana bata cikin jerin matan da yakeso , sbda ita ɗin batada kunya ga rashin sanin darajar mutane ,
” Gaskiya nayiwa kaina da zuciyata rashin adalci Kamill yaketa nana tawa kamar bitar karatu ,
ikon Allah ne ya kaisa gidansa , yana zuwa yayi horn ba’a ɗauki lokaci ba mai gadi ya buɗe get ɗin da gudu tare da durƙusawa yana miƙa gaisuwa , ɗabi’ar Kamill ne in ana gaishesa ƙin daraja mai gaishesa , basajin daɗin abinda uban gidan nasu yake yimusu , amma babu inda suka iya shiyasa suke taka tsan tsan da duk wani abu dazai haɗasu dashi .
[31/05, 12:47 am] Mom Islam Ce????: ???????? ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button