HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

*GUGUWAR ZALUNCI*

PAGA 15&16

bodyguard ɗinsa kuwa kowanne ya shiga tai tayinsa kasancewar oga baya wargi ,
Gashi yafita da ɓacin rai kuma ya dawo dashi .
Fitowa palo Alhaji Safiyan yayi , ganin Ameena na zaune tana danna waya , yasashi neman guri ya zauna , kana yace ” meena yaushe zaki dena fita batare da izinina ba ?” waro ido Ameena tayi tace ” ina zanje Alhaji ?”
Yanzu na aiko aka cemin kinfita a mota , buɗe baki tayi tasan babu mai yimata wannan sharin sai Kamill ,
Tarasa mai tayi masa ya ɗauki karan tsana ya ɗora mata ,
Hawaye ne suka fara zarya a fuskarta cikin she sheƙar kuka tace ” Alhaji sai yaushe ne zaka dena kama maganar wanan yaron ,
Ina nake zuwa ?
Alhaji da ya ƙurawa fuskar Ameena ido yace ” naji ya wuce amma kisanj Kamill ba yaro bane yakai time ɗin da zandinga shawara dashi so kin fahimta?”
Kawar da kanta gefe tayi dan intaci gaba da biye masa zasuyi babu daɗi ‘
Ita kuma batason musayar yawu da mijinta.
Bayan dady ya fito daga wanka momy ta temaka masa ya shafa mai ya sanya kaya , janyota yayi kusada shi suka zauna akan kujera ya kalleta yace ” Faty mgnar da nakeson yi dake shine inason mahaifiyata ta zauna tare dani ,
Banison tayi nisa dani duk da akwai mai kula da ita a can ɗin ,nima inason samun nawa ladan , shafo kansa momy tayi kana tace ” Habiby nima inason zaman Hajiya a gidannan ,
Ita da kanta ta matsa wai saita koma ƙauye tace ” da aljanu a gidanan , nidai a iya sanina bansan dasu ba , amma bansan ko akwai ba .
Gyra zama dady yayi yace ” ina tunanin harda rikicin tsufa .
Daganan suka miƙe tare momy ta kashewa dady ido tare da cewa , ga shayinka fa na shigo dashi , okay dady yace ” ina zuwa yanzu zan dawo ya fice .
ƙasa ya sauƙo yana tunanin tafiyar mahaifiyarshi , samunsu yayi a palo zaune suna kallo ,
Zama dady yayi kana yace ” barka da hutawa Hajiya ,
Ywwa barka Alhaji ya aikin naku ?”
Lpy lou dady yace ” yana kallon Tinene da keta baza ido a tv ” ke baki iya gaisuwa bane ?” sosa kai ta shigayi tana washe haƙora tace ” hannu dai ina uni lpy dady yace ” yana murmishi , ring ɗin wayarsa ce ta katse masa maganar da yakeson yi .
Ganin sunan mai kiran nasa yasa shi miƙewa da sauri ya haura steps zuwa ɗakinsa lokacin momy na toilet ɗinsa tana wankewa kasancewar bata yarda da ƴan aiki sudinga taɓa mata abinda ya shafi mijinta ba .
Zama yayi a bakin gado tare da amsa kiran ,
Sadda kai ƙasa yayi da alama da wani babban yake waya ,
dady ne yace ” Allah ya temaki mai gida kuma Allah yaƙara maka lpy , daga can ɓangaren mutumin yace ” wata muhimmiyar magana ce ta taso amma dole sai mun haɗu .
Cikin rawar jiki dady yace ” to ko inzo me kawai ace kamarka ka shigo layinnan ,
NO. mutumin yace ” karka damu dole nine zanzo buƙatar hakan ce ta taso karka damu.
Cikin rawar jiki dady yace ” to da ƙarfe nawa zaka iso , mutuminne yace ” bayan sallahar isha’i yayi ko ?” dady da fara’arsa yace ” yayi Allah ya kawoka lpy ,
Sukayi sallama.
bayan dady ya ajiye wayar ne yafara tunanin mai zai kawo Alhaji….gidannan kodai yayi laifi ne , wata zuciyar tace ” kazuba ido koma menene zaka gani Allah dai yasa alkairi ne .
Har momy ta fito daga toilet dady bai sani ba yayi nisa a tunanin Alhaji…. kamo hanunsa momy tayi kana tace ” habiby ka zauna man amman dai lpy ko ?”
Da ‘alamu na damuwa yace ” faty baƙo zanyi maza kisa ƴan aiki su haɗa abinci mai kyau kamar kala biyar haka ,
Ok momy tace ” kana ta fice , lokaci babu wuya jiyo kiran sallahar magrib yasa dady miƙewa ya yi alwalah ya nufi masallacin gidan ,
Bai dawo ba sai da akayi isha’i sanan ya shigo , babu kowa a palo ya haura step da sauri yana kiran momy , fitowa momy tayi daga ɗakinta , sai zuba ƙamshi takeyi tasa riga da skirt sun ɗameta amma tayi kyau , rungumota dady yai kana yace ” Faty na kullum kamar ana sake maidake baby , shafa fuskarshi momy tayi tana dariya tace ” to ya ka ganni nayi kyau ko ?”
Yana shirin bata amsa kira ya shigo wayarsa.
Sadda kansa ƙasa yayi tare da cewa ranka shi daɗe barka har kun iso ne ?”
Eh Alhajin yace ” gani a mota anbuɗe min get na shigo ,
Dady na shirin ficewa da sauri momy ta taro shi ,
Maiya faru ne Faty ?”
Haba habiby baka gayamin maike faruwa ba nadai ga kana rawar jiki ,
Cikin alamar yana sauri yace ” baƙo nayi kuma yanada muhimmanci a gurina, bugu da ƙari kuma kowane ma’aikaci nada burin ganin wanan bawan Allahn ya raɓesa sbda tsananin dukiyarsa dakuma goyon bayan manya daya samu ,
Riƙe baki momy tayi ,
Kana tace ” to Allah ya jishemu alkairi ,
Amma shida kansa yazo har gidanka ?”
Ficewa dady yai batare da yabata amsa ba ,
Momy ta jimama zuwan wanan bawan Allahn daga ƙarshe dai tace ” Allah ya tabbatar da alkairi ko me ya kawosa oho , ta koma bedroom ɗinta.
Dady na zuwa ya sami Alhaji ya fito daga mota yana zaune a wata farar kujera ,
Da sauri ya ƙarasa yana cemasa barka da zuwa ,
To tashi mu shiga daga ciki ranka shi daɗe ,
Miƙewa Alhaji yayi dady ya kaisa palonsa , palo ne daya ƙawatu da kayan alatu na zamani sai dai duk wanan ba komai bane a gurinsa kasancewar yatara gidajen da sukafi na Alhaji sani komai ,
Ƴan aikin ne suka fara shigo da abinci kala kala , ƴan aikin suna cikin shiga mai kyau drinks da abinci sunkai kala biyar .
kunun aya Alhaji ya zuba a cup kasancewar baya baƙunta akan abinda yake so ,
Bayan ya ajiye cup ɗinne suka gaisa tare da tambayar iyalai dakuma aiyuka ,
Bayan sun gama gaisawa Alhaji ya gyara zama tare da kallon dady yace ” Alfarma nazo nema a gurinka ,
Cikin rawar jiki dady yace ” har saikazo daka kirani ai .
Murmishi Alhaji yayi yace ” a gurguje dai inason gayamaka abinda ya kawoni .
Dady da ya matsu yaji ko menene yace ” to ina jinka?.
Masha Allah cewar Alhaji , yarona ne yaga ƴar gurinka yake sonta.
Nisawa dady yai kana yace ” wacce daga ciki ?”
Diyana Alhaji yace ” yana faɗaɗa fara’arsa.
Dady sai da ya jinjina sunan Diyana a zuciyarsa yasan inhar bata son mutum to ko inuwarsa bata raɓa garama Afreeda .
Alhaji ya lura da dady ya tafi dogon tunani ,
Baiyi masa magana ba saida suka dau tsawon mintuna kana dady yace ” karka damu insha Allah bazai gagara ba ranka shi daɗe ,
Washe baki Alhaji yayi yana ganin alamun nasara ta bayyana .
Daganan Alhaji ya miƙe da niyar wucewa , rakashi har zuwa gurin motarsa dady yai Alhaji yace ” to nanda kwana uku zan kuma dawowa inhar Allah ya yarda dakuma yarinyar banason aɗau lokaci mai tsayi , insha Allah kawai dady yace ” dan bashida wata kalma dazai faɗa ,
Da haka dai sukayi sallama .
Zuciyar dady babu daɗi kasancewar bayason yiwa yaransa auran dole .
Bazai iya hana Alhaji Safiyan auran ƴarsa ba dan yayi masa abinda ba kowane zai iya yimasa ba.
Har aka buɗewa Alhaji Safiyan get dady bai motsa ba , saida ya jima a tsaye sanan ya shige ciki .
Momy nata tararradin dady ko lpy .
suna zaune a palo dady ya shigo Hajiya da kecin tuwo tana suɗe hannu tace ” Alhaji ina ka shiga munjika shiru ga abincinka nan ko sai yayi sanyi zakaci ?
Ganin yanayinsa yasa momy shan jinin jikinta , a zuciyarta tace ” akwai matsala , cigaba da magana hajiya tayi takuma cewa wai lafiya naganka haka ?”
Lapy lau dady yace ” hajiya barin watsa ruwa ina zuwa ,
yana tafiya momy tabi bayansa .
Mtsw Hajiya tayi tsaki tare da cewa kwaji da tsohuwar gulmarku ni har zan tambaye shi abu yaƙi gayamin ,
kwashewa da dariya Diyana da Afreeda sukayi dan lamarin yabasu nishaɗi sosai.
Kunci gidanku wlh yarannan kun raina ni ,
Miƙewa sukayi kowacce bakinta a kunshe da alama dariya suke shirin yi akuwa suna isa kusada ɗakinsu suka saki dariya mai sauti ,
Tinene dake kokawa da ƙashi tazaro ido kana tace ” wlh Kaka dariya suke yimiki , ƙwafa Hajiya tayi tana jiran shigowar dady.
kwance dady yake a kan gado idanunsa a sama yana tunanin maganar Alhaji Safiyan ,
Momy tayi tambayar harta gaji daga ƙarshe ta miƙe idanunta sun kaɗa sunyi ja zata fice ,
Miƙewa dady yai tare da ruƙo hanunta yace ” matsalar nan ta shafemu duka ,
momy dake nazarin maganar dady tace ” kanata magana baka faɗi mafarinta ba .
Dady ne yace ” yazo nemawa ɗansa auran Diyana ne , kuma kinga duk abinda Alhaji Safiyan ya nema a gurina dole in bashi koda banida shi dole in nemo masa bare jinina yake nemawa ɗansa .
Jinjina zancen momy tayi ,wai hausawa sukace da kamar wuya gurguwa da auran nesa ,
To ai matsalar Diyanan ce akwai taurin kai ni kaina bata cika bin umarni na ba ,
Dama Afreeda ce to da sauƙi .
Haka dai suka dinga saƙa da warwara suka yanke shawarar gobe insha Allah zasu yiwa Diyana magana dakuma Hajiya .
Hajiya tagama zaman jiran fitowar dady shiru babu shi babu dalilinsa ,
Gashi Tinene nata rafka uban gyangyaɗi ,
Tashinta Hajiya tayi suka nufi ɗakinsu tanata mita harda cewa momy tsohuwar munafuka.
7:am Kamill ya tashi kasancewar yayi sallahar asbha shine ya koma ya kwanta , bathroom ya shiga yai wanka yana gama wanka yai brush tare da fesawa bakinsa mouth freshner ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani kuma rataye a kafaɗarsa ,
Gaban mirror ɗinsa ya nufa yana ƙarewa kansa kallo ,
tabbas a ƴan kwanakinnan ya rame , amma wanan yarinyar ta cucesa maiyasa zai sa tunaninta a ransa cox shi ba ƙara bibiyarta yayi ba , ƙwafa yai a fili yace ” da ƙafarki zaki tako har cikin gidana zakisha mamaki ,
Ɗauko mansa mai tsada yai kana ya shafe duk jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya gyara sumar kansa ,
Ya miƙe ya nufi drower gurin ajiyar kayansa ,
Riga da wando ya jiro na jeans rigar pink color wandon kuma blue ,
Bayan yasa boxer ya sanya wandon da riga yakuma feshe jikinsa da turare , ya fito palo kunna tv yayi tashar mbc action ,
Hankalinsa sam ba gurin tv n yake ba amma duk wanda ya kallesa zaice tv yake kallo time table na abincinsa ya duba , yau farfesun kifi da soyayyan dankalin turawa dakuma shayi mai kayan ƙamshi kana da kunun gyaɗa za’ayi masa ,
Kasancewar sai ƙare shabiyu na rana yake breakfast yasa babu wanda ya shigo masa da safe
[03/06, 1:36 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button