HAUSA NOVEL

GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

*GUGUWAR ZALUNCI*

PAGE 17 & 18

Yana tsaka da tunani wayarsa tafara ruri ,duba mai kiran yayi sai da yaɗan jinkirta dan kiran yakusa katsewa ya ɗaga tare da sallama ya langwaɓar da kai kamar yana kusa dashi ,,
Abba daga can ɓangaren yace ” my lovely son ka tashi lpy ya hutawa , Kamill dake ɗan yamutsa fuska yace ” am fine Abba ya aiyuka , lafiya Abba yace “.
Daganan Kamill yayi shiru , Abba ne yace ” jiya naje gidansu yarinyar nan munyi magana da mahaifinta yace ” insha Allah bazai gagara ba ,
Kamill da ko son jin sunan Diyana bayayi yace” tom Abba ,
Bakada lafiya ne ?” cewar Abba Cewa” Kamill yayi banajin daɗi ne ,
Subhanallah dady yace ” kayi ka fito kaje hospital ,
Kamill ne yace ” inada ragowar magani naji sauƙi ,
Alhaji bayason musu yayiwa Kamill sallama ya ajiye wayar .
10:am kowa ya hallara a dining domin karin kumallo inka cire Hajiya da Tinene dake ƙasa kan kafet a zaune suna nasu karin ,
Bayan sun kammala dady ya dubi Hajiya yace ” Hajiya ya kike ganin maganar da mukayi ɗazu dake , tunda yanzu ga sunan ,
daga Diyana har Afreeda babu wacce ta fahimci abinda dady yake nufi ,
gyara zama Hajiya tayi kana tace ” gaka gasunan ai kokuma ince gatanan ai ,
Komawa kan kujera dady yai Diyana na shirin barin gurin hanunta riƙe da waya dady ya tsayar da ita ,
Juyowa tayi batare da tace ” komai ba , sanin dama ba magana zatayi ba yasa momy buɗar baki tace “haba daughter ana yimiki magana kin tsaya kamar kurma?” tahowa tayi ta nemi guri nesa da kujerar dady ta zauna tare da cewa gani dady ,
Yatsina baki Hajiya tayi kana tace ” wlh bakida hali mahaifinki na yimiki magana kin wani tsaya kamar sa’anki ,
momy dai batada bakin magana ta rufe bakinta ,
Wata uwar harara Diyana ta dokawa Hajiya , cikin sauri Hajiya ta miƙe tare da saka kururuwa tana salati ,
Alhaji na gaya maka bazan zuna a gidanan ba ka matsa yanzu gashi wanan marar kunyar tana nema ta dokeni wlh kashiga tsakanina da ita tun wuri,
dady kam yarasa ta cewa ga damuwar Hajiya ga damuwar shi , shida Diyana ,
Hajiya kiyi hauri dan Allah zanyi mata magana amma yanzu mu samu mu kashe wutar dake gabanmu ,
Shiru Hajiya tayi tana girgiza ƙafa kamar mai jiran a taɓota .
Diyana ” dady ya kira sunanta a hankali .
Na’am dady , Diyana tace ” ta maida hankalinta gareshi ,
Alfarma nake nema a gurinki da fatan bazaki watsamin ƙasa a ido ba ?” jimm Diyana tayi kana tace ” insha Allah dady bazan watsama ƙasa ba.
good Dady yace ” nayi miki miji ……! Jin zancen tayi kamar saukan aradu ba ita kaɗai ba har Afreeda ma saida ta girgiza da jin wanan zance ,
Dady bai bari ya kaleta ba saboda kalonta zai iya sa zuciyarsa karaya ,
Yacigaba da cewa ” haƙiƙa ina alfahari daku dakuma tarbiyar da nabaku nidai banida burin yiwa ƴaƴana auran dole ,
yanzu dai inason jin ta bakinki Diyana sbda ba wani ne zaiyi miki zaman auran ba , kuma zaman aure ba abin wasa bane zamane na har abada .
yanzu wace shawara kika yanke ?” Hawaye ne suka fara sintiri a kyakyawar fuskar Diyana babu sautin kuka sai zubar hawaye , tafa hannu Hajiya tashiga yi tana ni ƴasu sai kace ” wacce za’a fillewa kai toni lokacin da aka yimin aure bansan kakanku ba ,kuma ban taɓa ganinsa ba sai ranar da yashigo dakina bayan an ɗaura aure ,
Dariya ce taso kuɓucewa momy dake zaune a kujera ta zuba tagumi, toshe bakinta tayi bata bari kowa ya gane ba ,
Bayan Hajiya tayi shiru dady ya kuma tambayar Diyana a karo na biyu ,
kalmar da ta fito daga bakinta ne yayi matuƙar firgita mutane kowa yayi mamaki.
Na ‘amince dady na amince ta miƙe tayi bedroom ɗinsu da gudu hawaye na zarya a fuskarta , momy ma hawayen take sharewa kasancewar tasan Diyana ba har cikin zuciyarta ta faɗi wanan kalmar ba,
Liyafa dady yasa a shiryawa Alhaji Safiyan ta bangirma abinci kala2 .
Bayan isha sai ga kiran Alhaji nan ya shigo ,
Dady na ganin kiran ya miƙe jiki na rawa ya fice , samun Alhajin yayi a jingine a jikin motarsa kamar inda yayi rannan da sauri dady yace ” haba Alhaji tashi mu shiga ciki dan Allah ,
Miƙewa Alhaji yayi tare da rufawa dady baya suka shiga palon dady ,
Bayan sun gaisa dady ya gabatar masa da abinci , kaɗan Alhaji ya taɓa kana yace ” ya ƙoshi kai tsaye suka fara maganar ƴa’ƴan nasu , dady ne yace ” na tuntuɓi ƴar gurina tace ” ta amince ,
Kafin dady ya kai ga ƙarasa magana Alhaji ya faɗaɗa fara’arsa yana yiwa Allah godiya , cikin zuciyarsa yana cewa haƙiƙa duk da bansan yarinyar ba nasan yarona yayi dace duba da halin mahaifinta na cika alƙawari , masha Allah kowanensu yace ” Alhaji ya dubi dady yace ” a yanke dukiyar aure atemaka mana banason auran ya wuce wata ɗaya .
Dubu ɗari ma yayi Allah yasa ma dukiyar da auran albarka ,
Dariya Alhaji yasa kana yace ” a haba zanbada 1 million ƴarka ƴata ce .
Nasani dady yace ” karka manta Alhaji bawai naƙi bane amma mafi ƙanƙantar sadaki yafi daraja dakuma ƙarawa aure ƙarko , daganan sukayi sallama
Akan gobe zai turo magabata ,
dady na komawa bai zarce ko ina ba sai ɗakin mahaifiyarsa , ya bata labarin abinda ke wakana cewa Hajiya tayi ” karka damu ka tura direba ya taho da ɗan uwanka hudu sai ya tsaya akan komai , dady yai farinciki yayiwa Hajiya sai da safe .
Duk wanan abin da akeyi Diyana batasan waye mijin ba ita dai ta amsa .
Washe gari abinka da masu shi ƙarfe biyar har ƴan uwan dady sunzo su biyu ,
Bayan sallahar isha’i baƙin dady sun hallara , aka bada dukiyar aure dubu ɗari biyar dady yaƙi karɓa amma sun turje sai da sukasa ƴan uwan dady karɓar kuɗin.
Suka sanyawa dukiyar Albarka tare da auran in an ɗaura , daganan aka saka rana wata ɗaya ,
Dady bai dawo cikin gida ba sai wajen ƙare 11pm na dare direct ɗakin momy ya nufa , tana sanye da sleeping drees wanda ya fito da ilahirin kyanta ,
Dady da yazo bata labarin abinda sukayi ai yama mance ya shiga toile ya yi brush kana ya watsa ruwa ya sanya jallabiya yabi bayan momy , niko nace asbha ta gari dady lol.
Washe gari dady ya dawo daga masallaci da asbha , ya sami momy da zaune kan sallaya tana karatun alqur’ani , saida ya jira ta idar kana ta gaishesa ,
Bayan sun gaisa dady yace ” Faty jiya fa ankawo kuɗin auran Diyana wani uban faɗuwar gaba taji amma tarasa dalilin hakan , murmishin yaƙe tayi tare da cewa Allah ya sanya alkairi ,
Suka shiga wata hirar daban , momy ce ta katse musu hirar ta hanyar cewa ” niko sunama waya da saurayin kuwa ?” dady dake nazarin maganar momy yace ” to wayasani ko zatayi ai ba sani zakiyi ba , shiru momy tayi daganan kowa ya kama gabansa ,
Dady yayi ɗakin Hajiya dan ya gaisheta momy kuma ta shiga wanka ,
Zaune take itada Afreeda suna tattauna abinda ya faru jiya , Afreeada ce ta dubi Diyana tace ” sis yanzu kin yarda da auran dole kenan bakima san mijin ba ?” karki damu my sis su dady nayiwa biyayya ina tausayin momy yanzu da ban yarda ba sai kiga Hajiya da dady sunkama jin haushinta , nasani itama bataji daɗin hakan ba , amma a yau ɗinan danaji ance wai ankawo dukiyar aurena , nayi danasanin cewa na yarda , ta fashe da kuka ,
Lil sis ban taɓa soyayya ba bansan ya ake yinta ba to yazanyi da mijin takuma fashewa da kuka mai sauti a karo na biyu ,
Rungumeta Afreeda tayi suka cigaba da kuka .
kira ne ya shigo wayar momy lokacin tana zaune a dining zasu fara breakfast , kasancewar ta shiga ta kira su Diyana ,
Allah ya temaka lokacin sungama kukan har sunyi wanka amma mai lura yaga idanunsu zai gane sun zubarda hawaye ,
Ɗaga kiran momy tayi tana dariya tace ” haba mom Khady zan aiko su Afreeda anjima suzo su karɓa min , jinayi momy ta ce sai anjima tare da ajiye wayar , dady ne ya kalli momy yace ” dawa kike waya?” murmishi momy tayi kana tace ” da matar abokinka man Mom Khady ok dady yace ”
Hajiya dake ƙasa ana cin farfesun kaza ta taɓe baki tana zabgawa momy harara , lol ko meye damuwarki ƴar tsohuwa oho .
Suna gama breakfast sukayi bedroom ɗinsu ,
Shigowa momy tayi riƙe da wata bag a hanunta ta miƙawa Diyana , amsa Diyana tayi tare da cewa meye wanan momy , momy ce tai murmushi tace ” kwalabe ne zakiji komai idan kukaje amma karfa ku daɗe dan Allah ,
to sukace kowacce ta canza kaya , iri ɗaya sukasa riga da skirt na atamfa mai ratsin green and wite ba ƙaramin kyau sukayi ba musamman ma Diyana da kamar dan ita akayi atamfar ko ince ɗinkin ,
takalminsu kala ɗaya kai komai ma wayace kowa da kalar tashi suka fito tare da bag ɗin da momy ta basu suka nufi gurin driver , sbda babu wanda zasu aika ƴar aikinsu ta tafi garinsu gaida mahaifiyarta ba lpy , samun drivern sukayi a tsaye yana jiransu , motar da ya fito da ita Diyana ta kalla tare da yamutsa fuska ta lumshe ido , ta buɗesu kamar mai jin bacci tace ” bazamu shiga wanan ba ka fito da sharon nafijin daɗin hawanta ,
Jikin driver na rawa ya fito da motar suka shige , mai gadi ya buɗe suka ɗauki hanya ,
suna cikin tafiya go slow ya haɗu , mutane kowa na tofa albarkacin bakinsa ,
Wata mota mai ɗan karan kyau ce ta fito daga wani titi da yayi hanyar gaban wato titin da su Diyana zasu bi ,
Ran Diyana ya ɓaci a masifa tafara tana shirin buɗe murfin mota tana cewa ” wanan ai rainin wayo ne yaushene za’a tare mutane akan wanan banzar motar shi waye mai motar ? ta ƙarasa fitowa tana bam bamin masifa , wani bawan Allah dake kan mashin kana ganinsa zaka gane ya haifi Diyana dan a ƙalla yayi sa’an mahaifinta , yawu Diyana ta tofar tana ƙaƙarin amai , kai kuma waye da zaka zo ina magana kana magana , Allah ya baki haƙuri mutumin yace ” tare da jan mashin ɗinsa gefe , sbda kar ya janyowa kansa sanin ƴaƴan masu kuɗi basu ganin mutane da daraja,
Leƙa cikin motar tayi tana yiwa drivern su masifa , tana cemasa maza ka tada mota mu tafi inga uban da ya tsayawa wanda suke jira ya wuce , dan rainin wayo ma tafiyar kamar motar bazata wuce ba sukeyi , ta shige mota , Afreeda na tsoron magana karta haɗu da nata kason yasata yin shiru ,
tafiya Drivern yakeyi cikin fargaba dan yana tsoron mutanen gabansa da suketa wucewa motar ogan nasu na gefe.
[14/06, 5:47 pm] Mom Islam Ce????: ???????? ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button