GURBIN IDO

GURBIN IDO 51-56

52

Fuskar anni kadaran kadaham sanda yake gaidata,duk da ba wani kallonta yayi can can ba,amma kuma jiki da zuciyarsa sun gaya masa lallai akwai wata a qasa,maida idanunsa yayi ga haj munubiya,matar da tun da can ba wani yi masa tayi ba,dama babu wani jituwa sosai a tsakaninsu,duk da ba wani abu bane yake shiga tsakaninsu ba,amma jininsu bai hadu ba.

Tata gaisuwar mai guda daya ya miqa mata,ta amshe da sauri tana cewa

“Lafiya qalau manya,ya ayyuka ya iyali?”

“Alhamdulillah” ya amsa mata a taqaice idanunsa akan qafafun anni dmda aka shafawa magani,ta kuma miqesu,da alama ciwonsu ya motsa

“To Allah ya taimaka,ya kuma dafa mana” bai maida hankali kan amsa addu’arta ta qarshe ba,cikin muryarsa me taushi da wani lokaci kan fito da wani amo da nauyi yace

“Anni,har yanzun duka tarin magungunan da kike amfani dasu basa aiki?” Dan duban qafar tayi kafin ta maida dubanta gareshi

“Abunne kasan dacewa ne,anata yi dai,sai sanda Allah ya dauke”

“Bare ciwo,kasan idan ya hadu da girma sai haquri” haj munubiya ta tsoma musu baki,ba tare da yabi ta maganarta ba ya zaro wayarsa,ya budeta,yayi kiran waya sannan ya sanya ta a kunne.

    A hankali ya fara magana cikin yaren da maimunatu taji yana magana dazun,sai kuma yadan miqe a nutse yayi gaba dasu kadan can wajen dining din annin yana ci gaba da yin wayar,dai dai lokacin da khalid yayi sallama cikin falon.

   Kan maimunatu idanunsa suka fara sauka,zuciyarsa tadan motsa,ya dan kafeta da idanu yana qarasowa cikin falon,sanye da qananun kaya,ya cusa hannunsa guda daya a aljihun jeans dinsa,daya hannun kuma riqe da key din motarsa yana dan kadawa

“Har ka dawo?” Haj munubiya ta fada,don ba haka taso ba,bataso dawowarsa a yanxun ba,saboda tana son fara aiwatar da shirinta,maganarta tasa ya dauke dubansa ga maimunatun zuwa kanta

“Eh,naji kince sauri kike ko?”

“Eh…..bawai wani sosai ba,dama abinda yasa nace kayi saurin kazo mu wuce,hafsat tacemin zata shiga makaranta,to kuma yanzun naga tex dinta ta fasa fitar,kuma na dan kwana biyu ai banzo gidan ba,ya kamata nadan zauna kadan mu gaisa sosai,don ko wajen yaaya marwan din ban shiga mun gaisa ba” anni dake sauraronta baki ta tabe tana kauda kanta gefe,a dan zuwan da take jifa jifa bata taba ganinta ta shiga sashen marwanun haka siddan ba,saida dalili,saboda haka kawai ta dorawa aishatu amma tsangwamar da babu dalili,face zallar faccalanci,amma yau abun mamaki wai ita ke zancan bata shiga sun gaisa ba,kafada ya daga yana maida kallonsa kan maimunatu kamar da ita suke maganar

“Well…..shikenan,zan koma ni,driver ya maidake gida kenan?”

“Eh zan kirashi,ko zuwa azahar ne sai na koma”.

    "Ina kwana" maimunatun ta fada sanda ta fahimci sun gama maganar,fadada fuskarsa yayi da fara'a yana amsa mata tare da tambayarta gida da kuma karatu,sai tayi mamakin yadda akayi yasan tana makaranta,amma tadai amsa masa da

“Alhamdulillah” dai dai sanda ja’afar ke saukowa yana shigowa cikin falon,idanunsa duka akan khalid din,tunda ya shigo yana karance dashi,yana ganin kuma kome dake wakana cikin falon,wani dan zafi yake ji a qirjinsa da baisan dalili ba.

     Waiwayowa khalid din yayi sanda yaji muryarsa yana fadin

“I will call you back later” cikin wayar,sai ya tako a hankali yana miqa masa hannu cikin sakewar fuska,ja’afar na daya daga cikin mutanen da yake burin inama ace shine su,abubuwa da dama masa suna burgeshi,saidai girman kan da yake dashi yasa yake dannewa tare da hudubar haj munubiya dake nuna masa cewa gaba yake da ja’afar din a wajenta,kada ya sake ya nuna masa shine sama dashi.

   A daqile ya bashi hannun sukayi musabaha,haka kawai yakejin zafin har yanzun a cikin ransa,idanuwansa kuma ya kasa kaudasu tsakanin maimunatu dake zaune properly waje guda,bata ma san meke faruwa ba,don dukka idanunta ta tattarasu kan wayarta ne

“Ba zaki sake amfani da kowanne irin magani ba,nayi magana da wani qwararren asibiti a turkey,zan qoqarin nema miki visa in sha Allah” ya fada muryarsa na dauke da wani irin amo kamar wanda yake fushi.

    Sak hajiya munubiya tayi,cikin ranta tana debowa ja'afar tsinuwa,dan rawar ganin da yaronta yakeyi take taqama dashi,iyayensa maza ke yabonsa yana kula da mahaifiyarsu shine wannan shegen yaron me kafirin izza da jin kai zai soke?

“Amma…….naga a nan akwai likitan da nake turata abuja tana gani” khalid ya fada yana jin ba dadi cikin ranshi,kai tsaye ya kalla khalid din

“I know…….”ya bashi amsa,gyara tsaiwa khalid din yayi,yana jin shima namiji ne kamar ja’afar din,kuma yana da say akan annin kamar yadda shima yake ganin hakan

“To inaga a barta zuwa wani lokaci mana”

“Ciwon yaci gaba da cin jikinta har sai ta daina tafiya?,banga wani ci gaba ba” ya fada hakan bayan yaja dan qaramin tsaki.

    Idanu anni ta zuba masa tana karantarsa tare da son lalubo dalilin wannan fushin da kuma inda ya deboshi bayan ba haka ya shigo ba,dole ta tsoma baki,don kada ja'afar din ya sake fadin wani abu da bazaiwa munubiya dake zaune tana kallonsu dadi ba,batason kuma wani sabani ya dinga giftawa tsakanin jikokinta,bata jina da kashe case din khalid din da hisham ba,kada kuma wata sabuwa ta danno kai

“Shi ciwo fitarsa aisai a hankali,kuma shima likitan inajin dadin maganinsa sosai,kwana biyu ne da naqi komawa lokacin da yace abun ya dawomin” bai sake cewa kowannensu komai ba,sabida ya riga daya qudurce a ransa abinda yayi niyya,bazai kuma fasa ba.

     Sallama khalid din yayi musu,sai haj munubiya ta miqe tabi bayansa,don tana son tace wani abu dashi,tanason kuma kafin taje ta dawo su gama abinda zasuyi itama ta dora nata

“Bari na shiga mu gaisa”

“To” anni ta bita dashi,don dama wajen takeson ta fita ta basu.

    Falon ya dauki saiti shuru ba wanda yace komi,cikin zuciyar unaisa fal haushi,ita ba wannan ya fiddota gida ba,so take kawai a fara maganar da data tarasun.

     Duban unaisa anni tayi,tana sane tace

“Shiga kitchen unaisa ki hadowa mijinku abinci” don ta sani sarai bai karya ba,don ba sanin jiya ko yau ta yiwa ja’afar din ba,kai ya girgiza

“Coffee kawai is okay” ya fadi a hankali yana rage kaifin idanunsa,har yanzun yana jin ransa yana suya.

Haushi ya sake qume unaisa,itakam meye hadin zuwansu nan da shiga kitchen ne?,ita tsakaninta da coffee ai saidai tasha,batasan takan yadda zata hadashi ba,to amma ba yadda zatayi,sai ta ajjiye maqallaliyar jakarta ta miqe ta nufi inda anni ke nuna mata.

“Bakwa bawa mijinku abinci ne maimunatu?” Anni ta jefa mata tambayar kai tsaye,sai maimunatun tadan rude, saboda bata tsammaci zuwan tambayar a sannan ba,ta daga kai ta kalli anni,sai kuma ta mayar ta sunkuyar ba tare da tace mata komai ba,ta yaya zata amsa mata?,tace mata batasan lokacin tashinsa da fitarsa ba?,ko kuwa tace batasan dawowarsa da lokacin buqatar abincinsa ba,ajiyar zuciya annin ta sake ta share maganar itama bata sake cewa komai ba.

Bata jima ba ta dawo dauke da mug a hannunta,ta ajje masa a gabansa tana sauke numfashi,sannan ta koma inda ta tashi ta zauna tana baza kunne.

Kurba daya yayi masa daci ya gauraye masa baki,sai ya maida ruwan coffee din cikin cup din yana duban unaisa da batasan ma me ake ba,saidai duka anni tana ankare dashi,ransa yaji ya quntata,ya dire cup din yana cewa

“Baaba tabawa fa?”

“Taje a lallabe mata kanta” bai wani san lallabewa ba,sai kawai ya lumshe idanunsa ba tare da yace komai ba

“Ko a canza maka wani?” Ta tambayeshi,kai kawai ya kada idanuwansa na a lumshen,tunda unaisan ta kasa hada coffee yayi dadi ina ga maimunatun haihuwar shekaran jiya?,qilan ma har gwara na unaisa akan nata.

    "Ku bani hankulanku nan" anni ta fada tana saka seriousness cikin muryarta,dukka suka maida hankalinsun nasu a kanta,jaafar din shima ya bude nasa idanun ya zubesu akan annin

“Maimunatu” ta kirayeta kai tsaye,gaban maimunatu ya fadi,ta amsa mata cikin sanyi

“Akwai cutarwa a zamanki da ja’afar?,ko akwai wani abun qi da yake miki?” Tirqashi,girman tambayar da taji a tsakiyar kanta ya wuce yadda zata misalta,wannan shi ake kira da ‘yar tinqe,me anni take son tace?,me takeson ji daga gareta?

“Uhmmm,ina jinki” anni ta fada tana kafeta da idanu,kamar yadda ja’afar shima ya kafeta da nasa,mamaki da kuma son gano manufa ko kuma ma’anar tambayar na masa yawo a kwanyarsa.

    A hankali ta girgiza kanta,don itakam bata data cewa,to me take buqata daga gareshi?,bata taba rasa ci sha suttura ko magani ba,meye ya rage mata

“Kin tabbatar?,banda ci sha da suttura komai ma kina samu?” Anni tayi tambayar cikin fillanci ba tare data bayyana komai ba,sai ta sake gyada kanta tana tabbatarwa anni.

   Dauke idanunta anni tayi daga kanta tana sake jin girma martaba da darajar maimunatu na ninkuwa a idanu da zuciyarta,ba zata iya fitowa kai tsaye ta fadi laifi ko aibun jikanta ba gaban idanunta,kunya kara da yakana suna tattare da jininta,tasan yadda komai ke wakana tun dawowar baba tabawa data matsa sai taji,tun kafin ma unaisa ta daga waya ta kawo mata qararsa

“Kefa unaisa?”

“Bani da matsalan wannan duka,saidai……” Shuru tayi tana dan jin nauyi ita kanta na fadin abinda ke ranta yake kuma damunta

“Uhnnnn……fadi matsalarki,ai dama dalilin zaman namu kenan”

“Ban taba kwana a dakinsa ba,shima kuma bai taba kwana a nawa ba” ta qarashe maganar tana baiwa kanta qwarin gwiwa da taimakon qarfafa mata gwiwa da anty talatu tayi kan ta fadi maganarta kanta tsaue,saboda indai aka dace aka shawo kansa to wannan abun shine hanya guda daya tilo da zata mallakeshi,kuma hanya mafi sauqi da zata ja masa zarenta yadda take so.

    Wani abu mai nauyi ne ya sauka saman kansa,sai ya rufe idanunsa,zallar mamaki da takaici suna cin zuciyarsa,kan unaisan daya kuwa?,da zata furta wannan maganar wa anni,bayan kowanne mai hankali kai tsaye zai fahimci abinda take nufi.

    Waiwayawa anni tayi ga maimunatu

“Karya kikamin kenan?” A rude maimunatun ke girgiza kai,don gaba daya ta rude,mamaki da al’ajabin unaisa ya cikata,kunya kamar zata kasheta

“Ba gashi abinds ‘yar uwarki ta fada ba?,kuma ni nasan hali,sanin hali kuma yafi sanin kama,sannan nasan abinda yaci doma bazai bar awai ba” saita maida dubanta ga ja’afar,ta kuma kira sunansa da kakkausar murya,a nutse ya bude idanunsa yana kallonta,kallon da anni ta tsani ya mata shi,saboda zaka haqiqance ne kana fada,amma sai kaga fuskarsa na nuna hankalinsa kwance yake,ya zuba maka ido yana kallonka kamar wani kurma har kayi ka gama

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button