GURBIN IDO

GURBIN IDO 51-56

“Kalleni da kyau,kuma kayi ta kanka wallahi kafin nayi maka mai dungurungum,su yaran da aka kawo maka ka zubesu kana dirka musu abinci ce maka akayi auren yunwa sukayi?,ko babu abinci a gidajensu?,shi kadai aka kawo maka su ka basu?” Kamar ga maimunatu tayi tambayar,sai gata ta miqe cak tsaye,annin ta saurara tana kallonta

“Ina zaki?,zauna”

“Toilet zani,fitsari nakeji” jin abinda ta fada sai anni ta barta ta maida dubanta ga ja’afar,kamar wadda za’a kama haka maimunatu ta nufi sassan da zai sadata da toilets na sashen.

       Tana shiga ta maido qofar ta rufe,ilahirin jikinta rawa yakeyi,gaba daya maganar ta birkita mata kwanya,ga wata irin kunya da taji kamar qasa ta tsage ta shige,yanzu fisabilillahi banda abin anni me ya kawo wannan zancan ana zaman lafiya?,ina zasu kai ja'afar?,wannan abun me shegen wahalarwa annin ke kira musu?,bayan a drama din da take kallo,da karance karancen da afrah ta koya mata tana ganin yadda ake jin jiki,duk da wadanda take kallo da karantawa ba kai tsaye suke nunawa ko fadi ba,amma ai alamun qarfi yana ga me qiba.

      Minti kusan goma harda doriya ta kwashe kafin ta dage zaninta tayi fitsarin da ya cika mata mara tun sanda anni tayi mata tambayar farko,sai data daura alwala ko zataji dai dai,ta goge fuskarta ta kuma gyara daurinta sannan ta fito.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 51

   Shuru ne ya biyo baya cikin motar,tsakanin unaisa da maimunatu babu wanda ya cewa da dan uwansa uffan,sai ogan daketa amsa waya cikin wani yare da dukkansu basu gane wanne ba,daga bisani unaisa ta fahimci turkish language ne.

Girman kai da shegen son girma yasa unaisa taji zafin yadda maimunatu ta shareta,a ganinta maimunatun bata isa tayi mata haka ba,yarinyar gaba daya nawa take?,sa’annan kuma wace da ita?,banda martabar aure da ja’afar din daya hadasu qarqashin inuwa guda,bata jin maimunatu takai koda matsayin ‘yar aikinta ma bare zaman kishi,amma zata nuna mata ita din ba komai bace,sannu sannu bata hana zuwa ai,muddin ta samu ja’afar a hannunta sai ta gane shayi ruwa ne.

Itakam maimunatu gaba daya hankalinta na kan wayarta,chart suke da afrah tana bata labarin ahmad dinta,a zahiri gwasale afran take,amma a badini yadda salon soyayyar tasu take shine yake burgeta,abinda ya sanya murmushi kenan saman fuskarta lokaci lokaci,har bata maida hankali ga unaisa dake gefe tana ji da girmanta ba,bare ja’afar dake amsa waya cikin yaren da batasan wanne bane,saidai lokaci bayan lokaci idan yayi wata maganar lallausar muryarsa na ratsawa cikin hankalinta da yayi nisa a wajen jin labarin da afra ke bata.

Karamin tsaki unaisa taja,har cikin ruhi da zuciyarta tana sake jin zafin shariyar maimunatu,gefe guda kuma yadda yarinyar ta canza ya tsaye mata a rai,ta lura idan ta tsaya wasa sai wankin hula ya kaita dare,dole tayi amfani da dukka wayewarta da kuma iliminta da kuma gogewarta tayi abinda take ganin shi ya kamata.

Qaramar ajiyar zuciya ta sauke sanda motarsu ta tsaya a babbar mashigar gidan dr marwan,drivernsu ya saki horn me gadi ya taso ya bude musu,cikin girmamawa yaja da baya kana ya rusuna musu har xuwa sanda motar ta qarasa shigewa yaja gate din ya kulle.

Tun kafin motar ta tsaya suka hangi abbi shi da ammi,tana riqe da briefcase dinsa da alama rakiya tayo.masa zaya fita,wannan kusan dabi’ar dukka matan gidance,girma ko shekaru basu sanya sun canza ba,abbi din yana riqe da hannun amna,wadda tayi kyau cikin dinkin atamfa straight gown,kanta babu dankwali saidai a taje yake cikin band da aka matse mata yalwataccen gashinta dashi,ta noqe kanta a kafada,da alama rigima take tabawa.

Dukka hankalinsa nakan yarinyar tasa,don haka yayi sallama da wanda suke magana a wayar ya kashe yana sanya wayar cikin aljihun rigarsa,dai dai sanda motar ta tsaya ya bude yana fitowa kamar yadda suma su maimunatu suka fito,dukka suka dunguma zuwa inda abbi da ammi suke tsaye,wanda hankulansu yayi wajen motar tun tsaiwarsu.

Idanu amna ta fiddo sanda ta hangi daddynta ta kuma hangi anty maimoon,da sauri ta zame hannunta ta manta da rigimar ma da take wa abbi ta nufesu da matuqar sauri,saidai tana isa dab dasu ta yanke ta nufi maimunatu wadda ta bude mata dukkan hannayenta fuskarta fadade da wata lallausar fara’a da murnar ganin yarinyar,ta dauketa cak suna dariya su duka

“To alhamdulillahi,shikenan rigima ta qare,an fansheni” abbi ya fada sanda suke sake qarasowa wajensa,ammi da maimunatu suka saki murmushi,banda ja’afar da ya dauke kansa daga kansu,karon farko da amna ta taba ganinsa ta wuceshi,koda waye ta gani kuwa shine mutum na farko da take fara zuwa wajensa kafin kowa,sai kuma unaisa da wani haushi ya saukar mata,wanda ya bayyana har saman fuskarta,ta kuma kasa danneshi.

Maimunatun ce ta fara isa gabansu,ta zube tana gaidasu,cikin nuna kulawa suka amsa,tadan miqe dauke da amna a hankali sanda ja’afar ya iso shima ya sunkuya yana gaidasu,bata tsaya jiransu ba tayi gaba abinta da amnan zuwa sashen amma,amna nata zuba mata zance yadda ta saba,ita kuma tana biye mata suna dariya,har suka isa sassan amma.

A falo suka gaisa da masu aikin amma cikin mutuntawa,suka shaida mata tana wanka,amma dab take da fitowa,sai ta zauna saman carfet tana dakon fitowarta.

Sallamar da akayi cikin falon ta sanyata daga kanta,hisham ne ya shigo,sanye da jallabiya, da alama yau din bashi da niyyar fita kenan,duk da ranar ranar aiki ce bawai weekend ba

“Matar babban yaaya” ya fada cikin dan zolaya yana wucewa gaban freezer din amma dake falon ya bude yana duba abinda ya shigo dauka din

“Barka da safiya” ta gaidashi cikin mutuntawa da kuma jin nauyi

“Barka kadai yayarmu…..jiki yayi sauqi kenan?”

“Alhmdlh ya hisham na warware”

“Allah ya qara afuwa……rigima’u,yau kuma me aka tashi dashi?,wa kike juyewa rigimar safiyar alhamis din?” Yayi maganar yana duban amna dake zaune gefan maimunatu,saidai ta kanainayeta gaba daya,duka gwiwoyinta na kan cinyarta,kamar jira take ta miqe ta isa gareshi,da niyyar fita ya shigo,amma dole amnan ta tsaidashi ya samu waje ya zauna a nan,ya ballowa kansa ruwa kenan.

Maimunatu na daga gefe tana murmushin jin yadda rigima ta barke tsakanin hisham din da amna,sauqin kansa da yadda ya iya tafi da rigimammun yara yana burgeta,gaba daya ya maida kansa shima kamar amnan,dai dai lokacin da ja’afar ya sako kansa zuwa falon.

Akan fuskarta idanuwansa suka fara sauka,fuskar dake cike da fara’a,jerarrun fararen haqoranta da suka bayyana,da wata lobawa ta musamman dake tsakiyar habarta,hasken fatarta ya sake fitowa sosai ta tsakiyar fuskar hijabinta,tana gab da dago idanunta don amsa sallamarsa ya kauda kansa,ya maida dubansa ga amna,wannan karon sauri tayi ta sabule daga gefan hisham da take zaune,ta nufoshi da sauri tana wara hannuwanta

“Dadddyy” tana isowa ya dauketa cak a hannunsa yana kallon fuskarta dake matuqar kamanceceniya da tasa,yasa yatsuntsa guda biyu yaja kumatunta,cikin low sound wanda ita daya zata jishi yace

“Naqi wayon,babu wani daddy,tun dazu ba’ayi welcoming daddy ba sai yanxu?” Wuta ta langabe masa fuskarta a narke

“Sorry….sorry dad” ba tare da ya shirya ba murmushin gefan baki ya kubce masa,yadda tayin sai ya tuna masa da maimunatu dake zaune a gefe,kamar ita,koda yaushe aka kamata ko ake tuhumarta da laifi ko aka ritsata haka fuskarta yake komawa,yayi kaman zai kalleta sanda yaji hisham na magana da ita amma sai ya dauke kansa,saidai kunnensa na sauraren hirarsu,yana mamakin yadda take dan sakin jiki haka da hisham din.

Yana qoqarin zama amma ta fito,maimunatu ta dubeta cikin girmamawa tana mata sannu da fitowa,fes ds ita cikin atamfa super exclusive,kai baka ce itace ta haifa kamar ja’afar ba saboda tsabar gayu da gyara.

Waje ta samu ta zauna lokacin hisham ya kama hanyan ficewa

“Me yasa ne baka tafi ba hisham?” Amma ta jefa masa tambayar tana zama,fuska yadan yatsina yana satar kallon ja’afar,suka hada idanu kuwa,ja’afar din ya watsa masa harara,sai yadan saki dariya hisham din,kafin ma yace komai amma tace

“Kada ka daka ta tashi,dama ka sani ba zuwa yake ba,tun can baya ma sai na matsa sosai yake zuwa,yanzun ma ya daina gaba daya” gyara tsaiwarsa yayi

“Taron family dinne anni….. sometimes kawai gulma ne da kuma daukan bangaranci,ga yarinyar can fawwaza…..ta cika naci wlh,idan ma naje ba barina zatayi na sake ba” ya qarasa maganar yana sanya kansa wajen,dauke dubanta amma tayi daga kansa tana cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button