GURBIN IDO 51-56

“Allah ya kyauta” sannan ta maida kallonta ga ja’afar
“Ya kamata ku dinga daurewa kuna zuwa koda ba zama zakuyi ba,ba zai yiwu ace ko da yaushe saidai matan suje ba,nima banda yau na tashi banajin dadin jikina ai babu abinda zai hanani zuwa”
“Me ya sameki amma?” Ja’afar din ya fada da sauri cikin nuna tsantsar kulawa,tafin hannunta ta murza kadan
“Ba wani abu serious bane,kawai nauyi naji jikina yayimin” motsawa yayi yana miqewa
“Noo,bai kamata ace kin zauna ba bakiyi checking me yake faruwa ba,dauko mayafi amma muje a dubaki” qaramin murmushi ta sauke,ta jima da sanin irin soyayya da kulawa da ja’afar ke mata ta dabance ko cikin yaranta,shi yasa komai nasa itama ya fita daban cikin zuciyarta,duk da tana qoqarin dannewa
“Ba komai fa,jiki ne da jini,dama ba za’a yita zama haka ba ba’a taba lafiyarka ba,yanzu ba gani a zaune ba muna magana” duk yadda yaso suje amma tace masa aah,dole ya haqura ya zauna,saidai dukka hankalinsa yana kanta
“Ina fatan kuna lafiya” amma ta fada,tambaya ce guda daya,amma tana dauke da ma’anoni,kara ya hanata buda tambayar,kai maimunatu ta gyada kanta a qasa cike da kunya da kuma surukuta,yadan saci kallonta,yadda takeyi din kamar yadda shaheeda kema amman,can qasan ransa yaja tsaki,me yasa yake yawan kwatanta da shaheeda bayan ba ita bace?,sai ya miqe yana fadin
“Zan shiga wajen anni”
“To ba laifi,ki shiga ku gaisa maimunatu” ta fadi don tasan yawanci direct nan suke fara yowa sai sun gaisa suke wucewa sassan annin.
A hankali suke takawa zuwa sassan annin,yana gaba tana biye dashi a baya,tamkar wata maras gaskiya,jifa jifa take satar kallonshi,yadda yake takawa majestically,cikin aji da izza,ba zato taga ya ja birki ya kuma waiwayo,ta daga idanunta a hankali tana duban inda yake tsaye ba tare data iya kallon qwayar idanunsa kai tsaye ba,nuni yayi mata da hannu kan ta wuce gaba,sai ta tako a hankali tazo ta giftashi,ta wuce kamar yadda ya buqata,lumshe idanunsa yayi sanda iska ta kwaso masa qamshinta,wannan qamshin dake maqale a wani bangare na kwanyarsa tun a wancan lokacin,sai ya rufa mata baya,suna ci gaba da takawa daya bayan daya.
Yaso yima idanunsa shamaki amma hakan bai samu ba,qwayar idanunsa na biye da duk wani taku nata,ance ido guba ne,kuma dafi gareshi,koda bata waiwaya ba tasan kallonta ake,cikin jikinta takejin idanuwansa bisa kanta,abinda ya sanyata daburcewa gaba daya,ta kuma ji tana hardewa a tafiyar tata,saboda laushi da qafafuwanta sukayi,wannan ya taimaka wajen yin baya zata fadi lokacin da taci karo da wani dan qaramin dutse.
Baisan ya isa gareta har ya tallafota ba saida ta samu masauki a jikinsa,qamshinta ya cika masa hanci,fuskarta na kallon sama ne,yayin dashi kuma ya zame mata kamar rumfa,wannan ya sanya idanuwansu sukayi saurin haduwa wajen guda,sai ya zareta daga jikinsa da sauri yana hade ransa tsaf,kamar bai taba dariya ba,ya miqe da dukka tsahonsa ya tsaya sosai yana sake zuba mata arwa,sai ta rasa abinda zatayi,don haka ta bige da gyara zaman hijabinta tana bashi baya,kamar zaice mata wani abu kuma sai ya fasa,ya zarce da yin gyaran murya saboda yadda yaji muryarsa ta maqale,duk wani furuci da zaiyi ya kakare masa a maqoshi
“Thank you” ta fada tana daga qafarta zuwa next step,saidai wannan karon ta sanya idanuwanta ne a qasa,gudun maimaituwar faruwar abinda ya farun yanzun,tana shaqar iska me tsaho zuwa hunhunta wai ko zata rage kaifin qamshinsa daya cika mata hanci,wani irin scent dake haifar da wani yanayi me dadi a zuciya da gangar jiki,koda mutum baiso ba,ya kuma canzawa zuciya tsarin tunani,sai taci gaba da zuqar iskar tana fesarwa a hankali,qamshin yana sake yi mata yawo a hanci,yana kuma haduwa da iskar safiyar dake kadawa da wani irin yanayi dake nuna da gabatowar zafi.
Muryarsa cikin sautin sallama ita ta maye gurbin tata siririyar muryar,mutum biyu ne suka amsa sallamar,anni da hajiya munubiya(mahaifiyar hafsat),ta ukunsu unaisa ce,wadda a maimakon amsa sallamar tasu,sai ta bisu da idanu sanda suke shigowan.
Daga annin har haj munubiyan suma sai da duka bisu da kallo,saidai kowanne da irin kallon da yake musu,ta fannin anni wani farinciki ne ya tsarga mata,zallar dacewa ta hango mai yawa tsakaninsa da maimunatu,ganinsu tare kuma ya ninka kwadayinta nason daidaituwar al’amura a tsakaninsu,ya kuma sake saka mata kwadayin son dorewar alaqarsu,sannan kuma ta hangi wani haske a tattare dasu da take fatan tabbatarsa da kuma dorewarsa.
Haj munubiya kuwa wani abu ne yayi mata tsaye a rai mai kama da kishi qyashi da hassada,tun shigowar unaisan ita kadai ta fara jin hakan,a yanzun kuma ya sake qaruwa da shigowar maimunatu da ja’afar din,yadda taga ya sake fresh ya kuma qara haske ya tabbatar msta da gaskiyan labaran da suke ji a kansa na yadda yaketa samun budi,arziqinsa kuma ke dada ninkuwa,wannan shine dai dai lokacin da ya kamata ace diyarta ta kasance daya daga cikin jerin matansa,saidai sam bata mata sha’awar zama mace ta uku kwata kwata,inda da hali so takeyi ta zama mace qwalli daua tilo ga ja’afar din,to amma hausawa sukance da babu gwanda babu dadi,ya kamata tayi wani abu akai,ta kuma gwada sa’arta,koda basu zama du uku ba ya kasance su biyu ne,wannan tunanin yasa ta sake fuskarta sosai tana gyara zamanta gami da dubansu maimunatu tare da sanya baki wajen musu marhaba,tana kuma qara kaifin hankalinta da hasashenta akan fuskar unaisa,take ta fara shinshino al’amura,ta kuma fara kuma tunanin daga inda zata dasa harsashinta.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 54
Kudin da iya su kenan cikin abinda ta mallaka?,sai ragowar dabbobin da suketa sulalewa suna qarewa daya bayan daya,sauran kuma suna bushewa kamar ana lasarsu?.
Sallamar jauro yayi dai dai da tunanin daya darsu a ranta na cewa tabbas shine ya debe mata kudin,domin kuwa taga yana ta gyaran bangare daya na cikin gidan,idan bashi ba bataga wanda zai debar mata kudi ba,tunda dai saman katifar suke kwana,kwana biyu ne ma yayi qaura yabar dakin saboda fushin da yake da ita kan abinda ke faruwa game da gajee.
Zumbur tayi ta miqe ta fito,tayi tsaye a bakin qofar dakin nata,hannuwanta a qugu tana kallonsa,sai ta zare hannuwan nata ta miqa masa tana dubansa da idanuwanta dake cike taf da rashin kunya da diban albarka,bin hannuwan nata yayi da kallo cikin mamaki,don baisan me take nufi ba
“Meye hakan ke kuma?”
“Ai kafi kowa sani,kudi na….kudi na nake so ka tafen ka bani,kuma wallahi sisi idan yayi ciwon kai sai ka fiddoshi” kallon mara cikakken hankali yake mata,don shi gaba daya kwana biyun nan kamar a zare kuma a firgice yake ganinta
“Kanki daya kuwa?” Ya soma da tambayarta,saboda yasan ta inda zai kamo maganganun dake bakinsa
“Ras nake jauro,kuma babu abinda zaka layancemin,kudina kawai nake da buqata,zaa cuceni a ha’inceni,har an tada gini ban sani ba” qare mata kallo tas yayi,yadda take girgije girgije ya tabbatar masa da gaske take maganarta,shikam a yanzun bashi da magana da ita,burinsa kawai ya gama gininsa lafiya Lau a daura masa aure da bazawararsa sadiya,ya tabbatar zatayi dai dai da furera da kuma dukka iskancin dake kanta
“Allah ya baki lafiya furera,na fuskanci tunda dabbobin marainiya suka fara kama gabansu aka soma taba naki tunanin,Allah ya kawo manzan sauqi,amma ki sani,koda zanyi sata bazan saci dukiyar haram dukiyar marayu irin taki ba,na dirkawa cikina wutar sa’ira,zan shiga dakina,kada kuma ki kuskura ki biyoni ballantana kice zakimin hauka,kije can ki nema inda dukiyarki ta salwanta” ya dire maganar tasa cikin tsananin kaushi da tsaurara harshe,sannan yayi gaba abinsa dauke da jakar buhun da ya dawo da ita daga cin kasuwar cikin wani qauye dake gaban nasu.
Binsa tayi da kallo,tafi kowa sanin jauro,kuma yadda yayi maganar ya sagar mata da gwiwa,tare da debe tunanin shi ya dauka kudin,sai ta koma bakin karan gadon ta zauna gwiwa a sanyaye tana zurfafa tunaninta kan inda kudinta suka shiga.
Zumbur ta sake miqewa tana kama sunan gaje,sai a sannan ma ta tuna yarinyar bata shigo gida ba har yanxu,mayafinta taja sannan tayo waje ba tare da neman izini ko ta tsaya gayawa jauron zata fita ba.