GURBIN IDO

GURBIN IDO 51-56

Tana tafe a hanya tana surutai ita kadai tare da tuna cewa dazu da safe sanda take fitowa daga bandaki taga fitowarta wuff daga dakinta,saidai bata kawo komai ba,ta dauka sauri take ta dauki kununta ne zata kada dabbobin su fice.

*GWAMBE*

Suna idar da sallar la’asar cikin masallacin dake cikin katafariyar ma’aikatar tasa ya dawo third floor,inda anan makeken office dinsa yake,direct ya isa saman freezer ya dauki agogonsa ya daura,sannan ya dauki hularsa yana gyara karinta,a hankali yana tuna abubuwan da suka faru a yau din,dukka abubuwane masu tsayawa a rai,kai qararshi zuwa ga anni sai abunda yafi komai tsaya masa a rai ba tare da yasan dalilin hakan ba…..irin kallon da yaga khalid yana jifanta dashi,kallon titsiye kallon qurilla kuma kallon haramun,lips dinsa na qasa ya cije yana jin kamar yanzun abin yake wakana,ya daga hannunsa da niyyar sanya hularsa saman kansa Jabir ya turo qofa ya shigo office din,wanda a yau wannan shine shigowarsa karo na wajen hudu,abinda kusan ba al’adarsa bace.

Duk shigowarsa ta dazun yayine don yaji wani abu daga bakinsa,saboda yana da masaniya akan kiransa da anni tace zatayi,da goyon bayansa ma ta aikata hakan,saidai ko a fuskar gogan bai nuna masa ba,duk da cewa ya karanci akwai wani abu a qasan ransa,uwa uba kuma basa boyewa junansu komai

“Fita zakayi ne?” Jabir ya fada,saboda yasan lokacin tashinsa bai qarasa ba,saura kusan one hour,shanyayyun idanunsa ya daga ya kalleshi

“Eh,i have to go,ina da uzuri”

“Munyi maka,mu masu mace daya ma muke samun kanmu cikin irin wadan nan uzurorin balle kai me biyu?” Yayi maganar ta manufa biyu ne,da kuma salon jan zance tare da neman tsokana,ya sani sarai,amma sai ya shareshi,baiko daga kai ya kalleshi ba bare ya biye masa suyi,saima yaci gaba da gyara hularsa,sannan ya qarasa gaban dan madaidaicin madubin dake manne da bango cikin office din,zaka zaci ma wani abune a wajen idan baka sani ba saboda design din da aka masa,ya kafa hular da kyau a gaban goshi,sai gashi ya fito fes da wani irin kyau me daukar hankali tare da kwarjini

“Allah ya gyaraka,yasa ka koma ja’afar dinka na asal” Jabir ya fadi a fili,a wannan karon waiwayowa ja’afar yayi ya kalleshi

“Wait…..wai me yasa yau ka takura min ne?”

“Saboda yau kake ango” ya furta yana danne dariyar dake cinsa,maganar tasa ja’afar qarasa waiwayo gaba dayansa,ya zuba masa shanyayyun idanun nan nasa

“Daina kallona haka malam,ba maimunatu ko unaisa bane”

“Duk wani zagon qasa da akemin na fuskanci dakai ake shiryashi ko?”

“Dai dai kenan,munason ka zama mutum kamar kowa,ka ajjiye wannan son bayan rai din,ka fuskanci reality,ka kuma yima shaheeda soyayya ta gaskiya ta hanyar samarwa kanka farinciki ka kuma dawwama da yi mata addu’a,da kula da abinda ta bari” kashe bakinsa gaba daya jabir yayi,ba wanda yasan abinda yakeji sai Allah,yana tsintar kansa a matuqar damuwa da qunci duk sanda ya tuna yadda ya wofantar da kulawa da soyayyarta,bai tashi fargar jaji ba sai daya rasata,wannan yafi komai damunsa da hanashi dukkan wani sukuni da walwala,akwai ciwo ya zamana kayi rashin mutumin dake maka soyayyar gaskiya,baka tashi gane hakan ba sai daka rasashi,ya tafi,yayi maka nisa,nisan da babu dawowa,koda zaka salwantar da dukka abinda ka mallaka don ganin dawowar tasa.

      " Ga sauran agreement din nan,ka duba idan komai yayi ka sanya hannu,munata loosing opportunity dinmu,bansan a kwanakin nan me yasa ka kasa concentrating akan aiki ba,is there any problem?"

“Nop” ya amsa masa a taqaice,ya ciro wayarsa yana turawa driver dinsa tex kan ya fidda mota zai sauko

“Okay….i hope so” jabir din ya fada shima yana miqewa,ja’afar bai sake komai ba suka fito tare suna tattaunawa.

       A parking lot suka rabu,jabir din yayi motarsa,shima ja'afar ya shiga tasa,ajiyar zuciya ya sauke sanda suke fitowa a company din,idanunsa na bisa titi yana wani tunanin na daban.

      Maimunatu bata wani jima sosai ba a gidan su laila suka dawo,sai gidan ya rayu ya cika da hayaniya,don an jima ba'a hadu ba,rabonta da gidan tun kafin a koma makaranta,da aka dawo din nan kuma ta dawo da rashin lafiya,bata fito zuwa gidan ba sai yau.

       Harda anty maama suka dawo ita da yaranta,duka a falon anni suka yada zango,sai maimunatun ta dinga jinta sakayau,zaman kadaici sam baiyi ba,hirar tasu ta dinga debe mata kewa,duk da ba kasafai take sanya musu baki ba

“Kiri kiri manya yaqi kawomin ke,kusan shekara daya tunda hisham ya kawoki har yau baki sake dawomin ba,shi yasa nima nayi fushi naqi zuwa gidanku” anty maama tace da maimunatu wadda ke lallabewa ‘yar anty maama ta uku kanta da manyan kalba, yarinyar tana da suma,amma kuma batason kitso kwata kwata.

      Murmushi tayi

“Makaranta yasa bai kawoni ba,amma zanzo anty in sha Allah”

“Ina zuba ido” ta amsa mata tana bude wata leda me dauke da wani babban tambari da kuma suna,wasu kayayyaki ne a ciki,ya fiddosu ta ware wasu,sai ta dubi maimunatu

“Allah yasa kina amfani dasu,siya nayi daga baya kuma dana duba naga sunmin yawa,kada su lalace ban shanyesu ba,kwashe wadan nan kiyi amfani dasu” kunya ce sosai ya saukarwa maimunatu sanda ta kalli kayan,ko wanda baisan na meye ba idan ya duba jiki zai gane,magunguna ne irin na ma’aurata,da bayaninsu balo balo a jiki,a kunyace ta debe tana cewa

“Na gode anty”
“Ba komai,amma akwai wani a ciki miqo in gani,ki shanyeshi,don idan yakai gobe tace zai lalace” ba zata iya cewa da ita komai ba,saboda kunya da kuma nauyinta da takeji,hakanan ta karba takai bakinta a hankali ta fara kurba.

      Sosai abun yayi mata dadi a baki,tana sha gardinsa yana ratsa harshensa,shi ba gardin madara ba bana kwakwa ba,a hankali sai gashi ta gama dashi,dai dai sanda laila ke shigowa dauke da babban plate data shiga kitchen da kanta ta zubo musu abinci

“Me akasha ba’a rage mana ba,naga wani hadadden bottle haka a hannunki matar yaaya” tayi maganar tana ajjiye tray din tare da miqa wuya tana leqawa

“Matsa malama,ba irin naku bane,saiki jira sai anzo kanku”

“Don Allah a bani na dandana,da gani abun dadi ne wallahi anty maama kika sata a loko ita kadai kika bata” laila ta sake fada tana daga robar zata kai bakinta.

     Buge roban anty maama tayi tana harararta

“Baki da hankali ne laila?,baki gane me nake nufi ba kenan?,to kika sake kika sha wannan yau saidai abbi ya bada sadakar aurenki ko babu sadaki” ta qarashe fada tana sake zabga mata harara idanunta kamar zai fado.

     Dariya laila ta saki tana qunshe bakinta,ita har ga Allah tunaninta baikai can ba sai da tayi mata dalla dalla,nadiya dake chart ta sauke wayarta tana harararta itama

“Wannan inda abbi bai karba kudin aurenki ba,ina jin kanki da kanki zaki kai gidan auren,duk gidan nan banga mai jarabar son aure irinki ba” dariya sauran suka saka mata,saita bata fuska

“Nifa Allah ban gane na meye ba,shi yasa nace a bani nasha,naga yamin kama da milkshake ne”

“Ke kika sani dai fitsararriya” nadiya ta sake fada tana gyara zamanta

“Anty…..ki mata magana don Allah” laila ta fadi tana duban anty maama

“Ke nadiya…..kiyi ta kanki,banason shashancin banza,idan bataso aure ba boko zata so irin naku?,aini walle duk cikin jikokina ba wadda ta burgeni kamar laila?aure ai shine cikar mutunci da kamalar mace,ko wacece ita a duniya kuwa….ehe” Anni wadda shigowarta falon kenan ta kuma datsi maganar ba tare da tasan akan me suke tattaunawa ba tace laila,da wannan ta kashe bakin maganar,dole kowa yayi shuru,saboda sunsan halin anni,yanzu sai ta baro musu aiki.

        Abincinsu suka ci gaba daci,ana kuma tattauna yadda bikinsu zai kasance, kasancewar watanni shida kacal aka sanya,kafin lokacin duk sun gama exams nasu,laila ma ta gama nata,zata shiga 300ll level ne,a wannan hutun aka tsara za'ayi komai a gama.

       Gida yakeson komawa ya kwanta ko zai samu hutu daga gajiyar da ya rasa musabbabinta,har sun dauki titin da zai sadashi da gida ya dan yima drivern gyaran murya,a ladabce ya waiwayo

“sulaiman kumo road zamu shiga”

“Okay sir” ya fadi a ladabce yana sanya signal,yayi yanke ta wani titi dake gabansu kadan,wanda zai kaisu inda yace din.

       Baisan me yake daukan hankalinsa zuwa gidan ba,ya tabbatar dai zuwa yanzu tana gidan,da wuya ace ta koma,zuciyarsa ta kasa nutsuwa akan ya tafi ya barta a gidan,sai yakejin kamar khalid xai iya dawowa gidan,tunda yaji haj munubiya tana fadin ba yanzu zata koma gida ba.

    Wani sashen na zuciyarsa na tuhumarsa....shin meye damuwarsa ne a kai?,yayin da wani sashen ke fadin

“Ko babu komai akwai igiyarka har guda uku a kanta,sannan sadakinka daka fidda daga aljihunka zaka barshi ya tozarta?,ko auren wasa ne a tsakaninku yafi qarfin a wulaqantashi” sai yaji zuciyarsa na aminta da hanzarin da wani sashen na zuciyar tasa ya bashi.

        Tuni ta gama gama cin nata abincin,amna ce kawai zaune a cinyarta tana bata nata a baki,lokaci lokaci kunnuwanta na sauraren hirarkinsu da suke sanyata dariya can qasan ranta,saidai a saman fuskarta murmushi kawai takeyi,hirarrakinsu shigen nasu afra ne,ko da yaushe idan aka zauna maganar aure ce dai,itakam bata taba tsintar kanta da jin wannan cikin zuciyarta ba,ko don bata rayu da mutane irin rayuwar da kowacce mace budurwa ke yi ba shi yasa batasan wannan ba?.

       A nutse yayi sallama falon anni wanda a yanzun ita da anty maama ne kawai a zaune,don sun sauya mazauni zuwa daya falon saboda sufi cin karensu babu babbaka,da mamaki anni ke amsa sallamar tashi,tasan dai daxun da safe yazo gidan,wanda zuwa daya yake ba kasafai yake zuwa biyu ba,idanma zaiyi zuwa biyun to dab da magarib yake sake zuwa,ko bayan sallar magariba da kadan.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 53

   A tsaye ta taddashi,da alama anni ta gama tartsatsin nata,bata iya duban fuskarsa ba kamar yadda takejin ba zata iya hada idanu da kowa cikin falon ba

“A nan zaka barsu?” Annin ta jefa masa tambayar

“Driver zai maidasu gida, office zan wuce,akwai wadanda na basu lokaci zamu hadu qarfe daya”

“Ni gida zan wuce,ka saukeni mana” unaisa ta fada tana rangwada kai,zuciyarta fes,tana jin lokaci yayi da za’a kirata amarya da gaske,farincikin da take ciki yasa takeson komawa gida ta baje kolinta,sa’an nan ta fara shirin shiga turakarsa.

       Ko kallon gefan da take baiyi ba ya soma yin gaba,don bayajin zai iya daukarta cikin motarsa,dukkansu sunzo masa iya wuya,daga yadda anni ke maganar nan ya tabbatar qararsa aka kawo mata,to amma wace a cikinsu?.

       Maimunatu da bata son tafiya yanzu sai tabi bayansu tana son gaya masa a barta sai zuwa anjima,bata tsaya ga unaisa dake sallama da anni tana mata godiya ba tabi bayansa,saidai ta kasa bude murya ta tsaidashi.

     Cak ya tsaya jin ana bin bayansa

“Don Allah……zan zauna zuwa anjima” ta fada da sassanyar muryarta dake cike da wani sauti na tsoro,idanunsa ya dan rufe kadan ya bude,har yanzu yana jin wannan zafin na tun dazu cikin ransa,kamar ya juyo ya rufeta da fada,sai kuma yaga fadan me zaiyi mata?,wanne laifi taqamaimai tayi?,yana da tabbacin wanda yakai qararsa ga anni cikin su biyun?,ko kuma itace ta kira khalid da har xai fusata a kanta har haka?,wannan dalilin ya sanya ya gyada mata kai kawai ya fara takawa zuwa parking lot na gidan,yana jin jiyo motsin komawarta ciki cikin murna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button