GURBIN IDO

GURBIN IDO 51-56

Hankalin inna furera ya tashi qwarai,ta tashi haiqan don rabasu amma a banza,da sun fita kiwo suke jonewa,kuma gashi ta gaza hanata fita kiwon,saboda bata dame fidda mata dabbobin,daga qarshe ta yanke shawarar bari kawai ta samu daadar himu da maganar aurensu,gwara ayi a daura,duk tsiya idan tasan da igiyar wani a kanta kome zai yanke,shima harunan bazai bita ba.

Sai data gama maganarta tsaf sannan daadar himu ta watsa mata wani kallon banza

“An gaya miki shashasha nike?,ko ba’a cikin garin nan nake ba ai nasan kome ke faruwa,da farko kinso kai diyarki birni ki hana dana,saboda kina ganin acanne zata samu me arziqi,da hakan bai yiwu ba sai kika haqura,yanzun kuma diyarki ta gama lalacewa….ta gama bidar maza shine kikeso ki joganawa dana?,bazai yiwu ba,nima na fasa hadin,dana fita zaiyi duniya ya nemi arziqi kamar kowanne namiji,ko nima zan kere sa’a cikin rugar nan” sosai ran innafurera ya baci,ta dinga zage zage tana cewa daadar himu ta yiwa diyarta sharri,daga abun arziqi sai ya zama na tsiya?,idan himu bazai auri gaje ba ai basai ta hada da sharri ba.

      To itama daadar ba baya bace,sai ta tasowa inna furera,suka fito har tsakar gida suna yi,yuuma na jinsu bata ce musu ta tafas ku sauke ba,sosai daadar himu ta tasar mata,har ta fara bankada sirrin inna fureran,da roqarta da tayi kan ta rufa mata asiri,shine silar alqawarin da ta yiwa daadar himu na bawa himu gaje don su samu suci dukiyar a tare asiri a rufe 

“Barni yuuma,rabu dani na nunawa matar nan nima ba kanwar lasa bace” daada tace da yuuma sanda ta taso tana shirin kashe rigimar,saboda yadda suka fara tonawa junansu asiri,da qyar ta samu ta raba,bayan mutane ‘yan gulma sun fara marmatsowa,kowa yana son jin abinda ya shiga tsakanin tsaffin aminan,tun daga sannan sukayi baram baram,aka rabu dutse a hannun riga(dama duka tarayyar da babu Allah a ciki,to tabbas qarshenta kenan koma fiye da wannan).

Ajiyar zuciya inna furera ta saki,sai ta miqe tana zura takalmanta,ta kuma nufi turken dabbobin,tsaiwa tayi tana qare musu kallo,baqinciki na sake sudarta,wai me yasa komai yake shirin tabarbare mata ne?,watsewar wadan nan dabbobin dai dai yake da watsewar dukka farincikinta da kuma kima da daraja data samu a baya cikin qauyen ta dalilinsu,kuma hanya ce da zata bawa maqiyanta kamar su daadar himu damar yi mata dariya gami da zundenta,kai ta girgiza da sauri,ba zata taba barin hakan ta faru ba,ko ta yaya sai ta dawo da garkenta kamar yadda yake ada,amma kuma ta yaya?,ina taga kudin da zata sake siyan wasu dabbobin ta cakuda da nata?.

“Maimunatu” shine sunan daya fado mata,tabbas!,wannan itace amsa,tun daga kan kayan lefe sadaki da irin mutanen da suka je daurin auren yarinyar ta tabbatar ta taka wani babban shinge,kuma koda bata gani ba,jikan tsohuwa anni ai ba wasa bane,tunda tasan anni,sani na daga ni sai ke ba sanin shanu ba,ko daga motocin dake shigowa da ita garin da irin rabon da take zakasan ba qananun mutane bane.

Murmushin samun mafita ne ya subuce mata,ta saki ajiyar zuciya,hankalinta kuma taji ya kwanta sosai,dole ta nemo gidan maimunatu,tana da tabbacin zata samu dukkan kudaden data yanka mata,ai dai komai lalacewarta ita taci gaba da riqonta bayan bacewar ubanta da kuma gushewar uwarta daga doron duniya,idan ta kama ma sai ayi lissafin din abincin data dinga ci da ita har zuwa sanda aka aurar da ita,da wannan tunanin ta juya zuwa cikin gida,saidai abu daya da take ganin zai kawo mata tarnaqi shine,ina zata samu kwatancen gidan maimunatu,daga nan har garin gombe?.

“Yuuma mana” tsukakkiyar kwanyarta ta bata amsa,take kuma ta gamsu,don haka ta dage katifar ciyawa dake dakinta tana laluben sauran kudaden data adana,ta lissafa taga nawa suka rage mata?,tunda tun bayan auren maimunatun anni tace yuuma ta shaida mata,kudin aikatau an gama biyansu,tunda a yanzu tana gidabta tana zaman aure bautar Allah bata mutum ba,a ranta take qiyasta adadin kudin zasu kaita gwambe?,don bata tunanin kudin dawowa,tasan ko a jirgi tace tanaso a dawo da ita za’a kawo ta.

       Barazanar daukewa numfashinta yake daga qirjinta sanda ta daga wajen ta kuma kakkabe katifar taga wayam

“Hukumullahu min zalika” ta fadi kalmar da ita kanta batasan cikakkiyar ma’anarta ba,yadai fadane kurum,gumi ne ya fara tsargo mata,ina kudadenta suka shiga?,cikin lokaci qalilan tayi gumi kashirban,ta koma bakin itacen gadon ta zauna tana sauke numfashi kuka kamar zai qwace mata,ta xurfafa tunaninta kan waye yabi dare yabi rana ya dauke mata kudinta?.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 55

 Yana daga tsaye ya dauki yaron anty maama yana dan jan kumatunsa suna gaisawa da ita,tana dan dubansa yadda yake sake zama fresh cikar hankali zati da kuma kamala na sake bayyanar masa,wanda sau da yawa cewa akeyi captain J yayanta ne,itama ba musawa take ba,cewa takeyi eh,don ba kowane zai yarda kan qaninta bane

       "Sun wuce gida ne?" Ya aza shanyyun idanunsa dake nuna zallar gajiya kan fuskar anni yana tura mata tambayar

“Maimunatu?….tana ciki” baba tabawa dake fitowa dauke da plate data yayyanka fruit ta amsa masa saboda tayi tsammanin da ita yake.

       "Da kin barshi ai tabawa,dan kusun uwa,mutum sai shegen izza?,sunan iyalinka ba xaka iya fada ba,so nayi naga qarshen iya shege" anni ta bishi da mita sanda yake takawa da kansa zuwa cikin gidan,baiso ma ya tsaya bata lokaci wajen,don yasan yau a ciki suke da juna shi da anni

“Haba anni,kaara dai yake miki,sunan ne na zamani dai,ba’a fadi dai a gabanki ba” anty maama dake dariya a ciki ciki ta fada qasa qasa yadda bazai jiyota ba

“Shidai ya sani,wallahi gwara yayi ta kansa tun wuri bai qure masa ba” annin ta fada taba miqe qafarta sosai yadda zata fi jin dadin zama sosai, anty maama dai nata tsokanarta,don batasan me ake ciki ba game da gidan ja’afar din ba,daga annin har baba tabawa sun sirranta abin,suna fatan komai zai dai daita a kurkusa.

Ba zato ba tsammani sukaga an dauke labulen falon,kamar saukar ruwa da daukewarsa kowa yayi tsit,idanunsu suka sarqafe guri daya lokacij data daga kai don ganin wanda ya shigo din,da qyar ta qwaci kallonta daga kansa,ya jingina da bakin qofar hannayensa shoke a aljihunsa yana ci gaba da kallonta.

Dan kwalinta ya zame ya koma rabin kanta saboda santsi,hakanan babu lafayar jikinta ta cireta ganin cewa su kadai ne,santala santalan fararen qafafunta sun fito sosai har qaurinta saboda miqe qafar datayi ta dora amna akai,sai ya lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa nadan bugawa kamar alamu na fara jin bacin ransa, imagining yake a ransa khalid ko hisham…..wani a cikinsu ya shigo ya sameta a haka?,tunanin da yasa ya gaza bude idanunsa,yana jin sautin muryar qannensa dake wucewa ta gefansa sumi sumi daya bayan daya suna gaidashi,ba wadda ya amsawa,haka suka wuce don idan da sabo sun saba,idan ta motsa masa hakan yake musu.

Sautin muryar amna data taho da sauri tana kiran

“Welcome dad” ya sanyashi bude idanun nasa,kana ya bude mata hannayensa gaba daya ta taho da sauri,tashin amna daga saman qafafunta ya bata damar miqewa itama,haushi yadan kamata na yadda duka suka sulale suka barta ita kadai,sai ta gyara dankwalinta sosai,tayi masa sannu da zuwa,sannu da zuwan da yayi kaman bai jita ba,ta duqa a hankali ta dauki wayarta,sannan itama tayi hanyar fita.

        Yana sane da ita,amma ya basar kamar baiga tahowarta ba,sai data ratso ta shiga tsakiya,sannan ya juyo,da wani irin zafi da zafin nama yana fuskantarta,fuskokinsu suka hadu waje guda,sai ta tsorata da yanayin da taga fuskarsa,duqawa yayi a hankali ya sauke amna qasa

“Jeki cema maama ta goge miki baki da tissue,am coming”

“Zan bika dad?” Ba tare da ya gama tantance me ta fada ba ya daga mata kai,sai ta cilla tayi gida cikin tsananin murna.

Tazarar dake tsakaninsu ya sake ragewa,abinda ya sabbaba musu fara musayar numfashi,ya kafeta da dukka idanunsa yana kallon matsoraciyar fuskarta,wadda har ta runtse idanunta,zuciyarta na wani irin bugawa fiye da kima,a hankali kuma tsigar jikinta ta fara tashi,jikinta ya fara saukar mata da wani feeling saboda dumin numfashinsa dake gauraye da lallausan qamshinsa wanda ke sauka saman fuskarta,yar yar jikinta ya fara yi tako ina,wani baqon yanayi da tunda take bata taba jinsa a tattare da ita ba.

“Me yasa kika zauna haka?,kin manta ke matar aure ce?” Maganar da sam ba ita yaso yi ba ta subuce ta fita daga bakinsa da husky voice dinsa wadda ta cika kunnuwan maimunatu.

Jikinta ne gaba daya ya dauki rawa,wayar hannunta ta sulale a take ta fadi a qasa,qarar faduwar tata ya sanya idanuwansu shida ita kaiwa kan wayar,suka kuma dauke a tare suna kallon juna,sai ya tsaya kawai yana kallon kyawawan idanuwanta da suka sakeyin kyau kamar kullum a lokaci irinn wannan,idanuwan da suka dan sauya launi,suka kuma cika da qwalla,ya sanya hankalinsa sosai ga qwayar idanun nata yanason karantarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button