GURBIN IDO

GURBIN IDO 51-56

A hankali ya zame idanuwansa daga cikin nata,ya maida qwayar idanun nasa ga jikinta yana kallonta har zuwa saman tafin qafarta,sai yaja baya ganin yadda jikinta ke dan rawa,mamaki na darsuwa a ransa,baiga wata magana da yayi da zata sanyata shiga wannan mood din ba,amma sai ya sassauta kafin fushinsa wanda baisan me yake sake hasalashi ba

“Ki dauko mayafinki ki sakemi a mota” yayi maganar yana bata hanya,tuni ta tsallake,ko takan wayar tata bata bi ba ta wuce da sauri sauri,ya bita da kallo,sai data bace ya maido dubansa ga wayar,sai ya duqa a hankali ya daukota,ya dannan gurin power ta kawo haske.

Face dinta dake cike da cuteness ce ta cuka screen na wayar,cikin uniform dinta na makaranta,lafiyayyen murmushi ne kwance akan fuskar tata daya qara mata wani kyau na musamman,duk da screen din wayar ya fashe amma hakan bai hana bayyanuwar kyan hoton ba,samun kanshi yayi da kallon hoton na wasu sakanni,sannan ya kashe hasken wayar,ya sanyata a aljihunsa yana miqewa,a kasalance yabi ta qofar baya ba tare da ya koma ta cikin gidan ba ya fice parking lot na gidan.

Toilet ta fara shigewa ta maida qofan ta rufe,numfashi take ajewa gami da cure hannayenta waje daya,tanason ta gama tantance abinda ke damunta tukunna,tsahon minti biyu kafin bugun zuciyarta ya dai daita,hawayenta kuma suka tsaya,saidai abinda takeji cikin jikinta bai sauya ba,famfo ta kunna,ta tara hannayenta ta wanke fuskarta da kyau ta gyarata sannan ta fito,tana takawa a hankali cikin sake daidaita nutsuwarta don kada yanayinta ya nuna wani abu.

Ranta fal haushinsa,me tayi haka da zai sanyata a kwana yana mata irin wannan tambayar?,ya kuma rutsata da idanuwansan nan data tsani ya kalleta dasu,tana cewa dukkansu a haka suke zaune kamar ita?,meye tayi wanda ba dai dai ba?,ko wani tafi a cikinsu?,don kawai tana da aurensa?.

Laila fa’iza rahama da sahla ‘yar anty maama ne sukayo mata rakiya,sai amna dake riqe da hannun maimunatu wadda ta kafe kai da fata yau fa a wajen anty moon zata kwana.

Daga dan baya kadan dukka suka tsaya,saboda kowannensu shakkarsa yake,ta qarasa ta sanya hannu ta bude qofar,tana addu’ar Allah yasa ba’a bayan yake ba,gaba daya batason haduwar sabgarta da tashi sam,saidai yana zaune a owners corner,hannunsa dauke da ragowar ruwan daya dauko a hanyan kitchen kafin ya fito.

Tana shiga amna ta shigo tana fadin

“Daddy…..tare zamu tafiko?” Ta wuce kai tsaye kusa dashi,duban maimunatu yayi,bata yarda sun hada ido ba,sai kuma ya maida kallonsa ga amnan

“Ban miki bayani ba?,ba yau zamu tafi ba,I have prepared something for you soon” kafada ta maqale,idanunta na hada ruwan hawaye

“Nooo daddy….,nafison na bika yanzu” yadda ta narke din sai ta bashi tausayi matuqa,tana yawan son ta bishi,amma kuma sai yake ganin kamar ba zata samu kulawa irin tasu amma ba.

“Let’s go”
“Yeeyy….. that’s my dad” dolensa tasa murmushi kubce masa,sai yasa hannu ya lakaci kumatunta

“That’s my baby” shima ya mayar mata.murmushin da bata shirya ba mai dan sauti ya kubce mata,fitar sautin sa ya sanyashi waiwayowa ya dubeta,sai kuma ta maze,kamar ba ita ba,ta maida idanunta da hankalinta sosai ga titi.

Bata sake tabbatar da surutu da kuma wayon amna ba sai da suka dauki hanya,hakanan ya daure ya dinga biye mata a wasu maganganun nata,itakam farinciki ya cikata,yau zata kwana a wajen daddynta.

Shuru maimunatu tayi tana saurarensu,a hankali taji kewa sosai na cikata,kewa ta mahaifi,tana iya tuna wasu abubuwa da suka faru tsakaninta dashi,gata da soyayyar da yake gwada mata a wancan lokacin,bata manta wasu ba duk da shekaru sun fara nisa,gefe guda kuma tana bin yadda jikinta keta motsawa, mood dinta yana dan canzawa kadan kadan,wanda ita kanta batasan dalili ba,wannan yasa motsinta ya dauke kwata kwata daga cikin motar,har sai da amna tace

“Anty moon,zaki dafamin pepper chicken?” Murmushi ta sauke tana duban fuskarta,har cikin ranta take jin tausayin yarinyar data rasa yar uwarta dama mahaifiyarta tun batasan rayuwa da dadinta ba

“Komai ma kikeso amna….zaki samu” juyi tayi.najin dadi

“Bazan sanwa khadim ba,saboda ya cinyemin wanda amma tasa raliya tayimin jiya,nayita kuka”

“Zan sake miki wani” Allah ya taimaketa hirar ta sake komawa tsakaninta da daddyn nata.

     A hankali motarsu ta sanya kai cikin gidan,a lokacin yammaci sosai ya qara yi,qeme me amna taqi takawa da kanta,ta noqe kafada

“Daddy ka daukeni” sai ya sunkuya a hankali ya azata saman kafadarsa,cikin jin dadi kuwa ta saki dariya tana kwantar da kanta saman kafadarsa tana ci gaba da dariya.

     Ta rigasu yin gaba,ta buda sashen nata ta shige,kafin ta maida qofar sai gashi sun iso shi da ita,ya duqa a qasa a hankali yana fadin

“Get down” tsalle tayo ta sauka tana dariya ya juya yana fita gami da cewa

“Am tired amnee,let me rest for a while,i will get back to you”

“Okay dad,rest well,am waiting for” qaramin murmushi ya kuma saki na gefan baki,daga tahowarsu tare zuwa yanzu tana ta debe masa kewa tare da rage masa tamper dake ransa,ya yadda ya kuma sake tabbatarwa nisanta da tayi a rayuwarsa bau qareshi da komai ba sai qarin qunci da takura,sai ya samu kansa da tunanin yadda zai dawo da ita kusa dashi kamar haka,ko babu komai he will get some one who will take away his loneliness.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button