GURBIN IDO

GURBIN IDO 8

08

    Fitar jauro daga gidan sai dukkan bala'i da masifar suka dawo kan maimunatun,inna nayi gajee nayi

“Tunda ya daure miki gindi ko?,to wallahi baki isa ki kwanta kiyimin saqe saqe kamar gawar sababi ba,bayan jiya ya shirga miki abinci kin cinye,to kin ciyoma kanki,kinci abincinki na jiya dana yau,waryo wan en jungul!,(zoki dora mana abinci)” ta fada a tsawace,har maimunatun tana jin kanta kamar zai cire.

Tuwo ne na masara miyar danyar kubewa,gaba daya kayan aikin innar ta tura mata,ta baza tabarma tayi zamanta qasan bishiyar dake basu iska.

Zata iya cewa batasan ta yadda akayi take aikin ba,don komai tana yinsa ne a wahalce,cikinsu kuma babu wanda ya taimaka mata koda da firfita wuta ne,yadda bata da lafiya haka aikin yaja lokaci yaqiyin sauri,saboda rashin kazar kazar da kuma qwarin jiki,abinda ya qara iza wutar masifa da bala’in inna,ya kuma sanya maimunatun taji inama ace kiwon ta tafi a haka,tabbas ya fiye mata wannan wahalar girkin.

Tana zaune tana niqan kayan miyan da zata dora miya saman dutsen markade taji sallama,ta daga kanta a wahalce tana amsawa,matashiyar da aqalla zatayi sa’a da ita ce(zubaida),sai kuma yaron dake gefanta(sadam),kasa dauke idonta maimunatu tayi daga kan fuskar yaron,saboda kamarsa muraran da ibrahimunta.

Shima yaron ita yake kalla,kafin daga bisani ya dauke kansa,abinda ya bata mamaki hararan da zubaidan ta wurga mata kafin su miqa zuwa inda inna ke zaune tana kada nono,maimunatun kuma ta maida kanta ga aikin da takeyi cikin mamaki,iyaka saninta da zubaida saidai kallo daga nesa,ba abinda ya taba hadata dasu,koda gaisuwa kuwa,takan jima bata gansu ba,kamar yadda suma suke jimawa basu ganta ba,domin su din zuwansu kiwo na lokaci bayan lokaci ne bawai koda yaushe ba,koda ma koda yaushe ne,tana daukar watanni kafin magana ta hadata da wani a wajen kowo har taje ta dawo,saidai idan baqin makiyaya da ba ‘yan asalin rigarsu ba sun ratso ta dajin da suke kiwo.

“Maraba da zubaida da saddam” innar laulo ta fada cikin wani irin kirki da kuma fara’a,wanda ya sanya har sai da maimunatu ta tasa kanta dake mugun sarawa ta saci kallonta.

Daga gefan tabarmar da take kai suka zauna,gaisheta yaron ya farayi sannan zubaidan

“Dama daada ce ta ailo na gaya miki,akwai baqi da sukazo daga gombe,naggen bappa suka saba siya,to wannan karon babu,bappan ya fita dasu gaba daya,shine tace nazo na gaya miki,tasan cikin naki akwai irin wadanda sukeso,gobe zasu zo da safe kafin a fita dasu su gani” madaukakin farinciki ya kama inna furera,cikin ranta ta sake jin duk duniya bata da masoyi sama da daada din,dama ta jima tana shawarin saida wasu daga ciki,ko don ta saku ta sake badda dukka wata alama da zata iya zama shaidar rashin zamowarta mallakin dabbobin,to amma kuma batason saidawa anan kusa,tafison waje me nisa inda zasu siya da daraja

“Miyatti Allah,miyatti daada,amma naji dadi wallahi,Allah ya kawosu”

“Ameen,sannan tace na gaya miki,anjima yaaya himu zaizo wajen gaaje,su sake ganin juna” kamar inna furera zafa taka rawa haka tayi,takai ta kawo ta rasa wanne tukuci zata bawa zubaida,qarshe dai har suka bae gidan bakinta yaqi rufawa.

      Saukar zancan a kunnuwan maimunatu sai ta kasa tantance cikin wanne yanayi take ciki

“Ibrahimu zaizo yaga gaaje” wannan shine dalilin da yasa ta daina ganinsa kenan?,me hakan yake nufi?. Tunanin ya sanya aikin nata ya sake yin slow fiye da dazu,tun inna na mita da baki har sai data fara kai mata duka da hannu

“Me shegen baqin halin tsiya,bakyason aikinne,a haka kuma zakiyi shi”.

Takanas innar ta taso gaje,ta hada mata madarar shanu da lalle ta murje mata jikinta,zaka tsammaci kamu za’ayi mata irin na amare,duka a wannan lokacin ta sanyata ta tsefe kanta mai yalwar gashi,wanda datti ya dakushe tsahonsa ta wanke mata shi fes,ta raba mata gida biyu ta zubo mata da jelarsa hagu da dama.

Tun yammaci aketa shiri gamida da gwada yadda zata tarbi ibrahim din,duk don saboda ta burgeshi,mudukaje(kayan saqin fulani) na can qasan kayanta ta ciro ta ajjiye,dukka abin nan da ake na maimunatu idanu ne,saidai gefe daya zuciyarta ta gaza hutawa da tunanin abinda zaije yazo.

Dai dai sanda maimunatun ke saman dan mayafin da take shimfidawa tayi sallah….dai dai sannan gaje keta faman fecewa fuskarta kwalliya,ta kalli madubi yafi sau shurin masaki,ta juya ta sake juyawa har sau babu adadi,burinta shine taga komai yayi,sannan ta burge ibarahim matuqa,maimunatu tana zaune a wajen,bata motsa ba bare ta waiwaya taga abinda gajen keyi,saidai kuma kunnuwanta na samun aiken saqonnin waqe waqen da gajen keyi cikin harshen fullanci,tana yi tana juyi,abinda zai nuna maka cikin zallar farinciki take a yau din.

Laulo ne ya shigo dakin,yaron da za’a iya cewa yafi gaje hankali,don wasu abubuwan da shi din yakeyi yana yinsu ne da yarinyata,da kuma rashin samun isashshiyar tarbiyya da kyau

“Himu yazo,inna tace akai masa taburma” sai yaron ya juya ya fita yana tsalle tsalle abinsa.

Juya idanunta gajee tayi cikin farinciki,ta jima tana qaunar himu tun ba yanzu ba,tun daga sanda inna ta gaya mata cewa shine mijin da suka zaba mata ta riqe hakan a ranta,bata taba mancewa ba,hakanan bata yarda ta kula kowa ba saboda ibrahim,duk da tarin masoyan da take dasu a rugar,don dai dai gwargwado tana da irin nata kyan.

“Ki dauko tabarma ki kawomin zagaye” ta bawa maimunatu umarni kai tsaye tana ajjiye madubin hannunta,har takai bakin qofa ta tsaya ta juyo tana duban maimunatun jin bata ce komai ba

“Ko ba zaki kawo bane?”
“Yanzu zan tashi” ta amsa mata murya a raunace,qwafa gajee taja sannan ta sanya kai ta fice.

Babu yadda zata kaucewa umarnin gajen,ya zame mata dole,hakanan ta miqe dauke da tabarmar ta nufi inda gaje ta umarceta.

Salon tafiya na daban ta canza kamar yadda suka wuni suna gwadawa ita da inna furera,ibrahim din na tsaye,jingine da wani kutturen ice,qafarsa harde da juna yana duban gajen sanda take tahowa,cikin salo na nuna jin kunya ta dan sunne kai sanda ta fuskanci kallonta yake,farinciki ya cika zuciyarta,tana hangen ba wani faɗi tashi me yawa zatayi ba zata samu kan ibrahim din.

Wani tattauran yawu me daci ibrahim din ya hadiye,ya rufe idanunsa yana sake tursasawa kansa da zuciyarsa daurewa da kuma bin umarnin daada,yana jin kamar zuciyarsa zata fashe saboda takaici,meye ne daada ta hango masa tattare da gaje,me yasa idanunta suka rufe ta kasa gano abubuwa masu tarin yawa da yake gani tattare da maimunatu?.

Yana bude idanunsa ya hangi maimunatun biye da gaje,gaba daya sai ta wafce kallonsa,ya tattaru gaba daya a kanta,hasken wutar kara da mazauna wajen suka kunna daga can gurin zuwa can ya haske wajen sosai da har yake samun damar ganin kowacce a cikinsu

“Sannu da zuwa” gajee ta fada tana dan russunawa hadi da rausayar da idanu

“Sannunki” ya amsa mata murya a ciki,yana dauke dubansa daga maimunatu wadda ta qaraso wajen riqe da tabarmar

“Ki shimfida masa mana kin bar mutane a tsaye,sai wani abu kike kamar mara laka a jiki…..mayya….” Hannu ibrahim ya daga mata da sauri,saboda zafi da zuciyarsa ta fara yi masa,bazai iya daukan hakan ba,a nutse ya dubi gaje

“Wannan din ba bil’adama bace kamarki?,bakisan Allah ya karrama dan adam ya kuma mutuntashi ba?,matuqar wannan itace dabi’arki,to kin dauko hanyar da ba zaki sake ganina a nan ba” sosai maganar ta bata mata rai,ta kuma sake saka mata kishin maimunatu a ranta me yawa,amma a yanzun nema take,dole ta jure,don haka ta sadda kai

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button