GURBIN IDO

GURBIN IDO 8

“Kayi haquri” bai amsa mata ba,sai ya miqawa maimunatu hannu ya karbi tabarmar,ya sani sarai anyi hakanne don a tozarta maimunatun,a sake kuma nuna masa ita din ba kowa bace,tunda daadansa bata boye masa komai ba,ta gaya masa duk irin matakin da suka dauka,tayi ne da nufin jan kunne,ta kuma gaya masa zaman lafiyar maimunatu shine ya rabu da ita,abinda basu sani ba shine,wannan abun da sukayin shi ya sake zubda darajar gajee harma da inna furera a ransa,ya kuma sake sanya masa tausayi da qaunar maimunatu.

Batasan cewa himu ya fara taka wani matsayi a zuciyarta,batasan cewa ya fara bude wata rufaffiyar qofar da bata tsammaci budewarta ba sai data koma daki,gaba daya ta gaza sukuni,ta kuma kasa kwanciya kamar yadda taso ta kwanta din,saboda yadda jikinta yake wani irin radadi da kuma zugi sakamakon aikin da tasha,ga kuma tabbai na duka wani wajen har ya fara rurucewa,abinda ya hade mata kenan,ya kuma saukar mata da zazzabin da ya tilasta mata kwanciyar da a daxu ta kasa yinta.

A hankali ta bude idanunta sakamakon muryar gaje data jiyo cikin muryar kuka

“Ke….mene….meye?” Inna furera data fito daga daki zaninta a hannu ta fada,hankali tashe tana duban gaje

“Inna,kai tsaye himu fa yake gayamin wai bani bace a zuciyarsa,zuciyarsa tuni wata ta karbeta,kuma wallahi nasan ba kowa yake nufi ba sai waccar mayyar,tunda na daka mata tsawa har ya tafi banga faraga a fuskarsa ba,ki taimakeni inna,wallahi inason himu” wani dogon tsaki innar ta saki tamkar zata tsige harshenta

“Ahaf…..aikin banza kenan,yo yayita fadi baya sonki.mana,qarewa ya samu amsa kuwwa ya daura,yayita bi rugage yana fadin hakan,ai yayi aikin banza,maganar nan babu me tashinsa,shi ya san wace uwarshi,tunda ta fada babu me tashin maganar,shi yasa ya biyo ta hakan don kice bakiyi,wadda kuma yake qulafucin haihata haihata shi da ita,qwalelen kare da hantar kura,yadda naci alwashi in sha maka Allahu….matuqar ina raye saikin aurin namijin da kaf rugar nan babu irinsa,ibrahimu ne,kuma shine naki,muje na karanta miki karatun zaman duniya” inna ta fada tana kama hannun gajee sukayi dakin innar.

Maida idanunta maimunatu tayi ta rufe,tana fitar da numfashi me azabar dumi saboda zafin zazzabin daya ratsa kowanne sashe na jikinta,kadaici gami da kewar mahaifiya ya cikata,koda zata mutu a saman wannan shimfidar babu lallai a ankara,koda za’a lura din wala’alla sai ta kumbura ta fara fidda wari,ko kuma sanda suka nufaci tashinta don ta biya musu buqatunsu

“Innalillahi wa inna ilahi raji’un” ta samu kanta da fada tana rushewa da kuka mara sauti,addu’a ce da take yawan jin mahaifiyarta tana yi,rashin uwa wani babban gibi ne a cikin rayuwa,wanda babu wani abu da ya isa ya cike maka wannan gurbin.

Duk yadda take jin jikinta bayan ta idar da sallar asuba amma hakan baisa ta koma barci ba,tasan koda ta koma din ma wani tashin hankali da kuma firgici zata kirawa kanta,don haka taci gaba da zama,har zuwa lokacin daya dace ta fara aiki yayi,ta miqe a hankali ta yaye labulen zanin atamfa dake qofar dakin nasu tayo waje.

Duk da yadda suke da sammako da kuma tashin wuri amma wajen tsit yake,kowa yana ta sashensa,babu komai sai kukan dabbobi dake turke a muhallensu.

Sannu sannu tana aikin gari na dada yin haske,mutane na sake fitowa daga muhallansu kowa na kama sabgar gabansa.

Inna furera ce ta fara fitowa daga nasu gefan,ta saki wanke wanken da takeyi ta qarasa inda take tsaye tana gaidata,bata bi takan gaisuwar tata ba tace

“Ki saki wanke wanken,kije ki gyara wajen dabbobin can,nasan masu sayen suna hanya,tunda da wuri zasu zo,sannan inaso ki nutsu da kyau,na tabbatar sai an kiraki lokacin cinikin,saboda ke kike kiwonsu,kinfi kowa sanin wadanda sukafi kowanne lafiya da nada nono da kyau,to bance ki tsaya nune nune ba,ki barsu su zaba da kansu,ki kula….bazan lamunci ki jawomin asara ba” kanta a qasa take amsawa innar,bata miqe ba sai data bata umarni,ta taka zuwa inda take adana kayan sharar wajen ta debesu da qyar ta zagaya zuwa makwantar dabbobin.

Sanda suka ganta sai da dukkaninsu suka motsa,ta saki murmushi itama tana isa gabansu,kwanaki biyun da bata gansu ba sai takejin tayi kewarsu ba kadan ba,suma kuma tasan hakanne,don dai kawai basu da baki bare su bata labari.

Duk da jikinta babu qwari,cikin boyeyyen ciwo dake cin naman jikinta take amma cikin qawa zuci take aikin,tana yi yana musu magana kai kace da dan adam take,sai data bi kowacce dabba data saba dubawa ta dubata sannan ta fara aikin.

A hankali suke takowa da qafa,tun daga gidan bappa labaran din,anni da kanta ta zabi su tako da qafan

“Ku barni da qarfen nasaran nan,gwara mu taka da qafa tunda ba nisa ke da gidan ba” tace da daada,wadda da kanta tayi mata rakiya ita da safiya da kuma laila.

Tahowar da sukayi din ya bawa lailan dama daada damar kallon rugar sosai,bambancin rayuwa qarara na zahiri da suke gani,wanda yayi dai dai da karin maganar nan ta bahaushe da hake cewa Allah daya gari banban,suna tafe laila na tambayar sadam wasu abubuwan,tafiyar ta zama wani mabudi na ilimi a gareta.

“Maraba,lale,sannunku da zuwa” shine abinda inna furera ke faman fadi,tana kai kawo tare da qoqarin shimfida musu tabarma gaban dakinta,yayin da gajee ke zaune abinta saman kujerar tsuguno.

Don samun ci gaban sabbin galla gallan pages,ziyarci page dina a AREWABOOKS da sunan HUGUMA

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button