GURBIN IDO

GURBIN IDO 9

“Allah ya saka da alkhairi,ya maida ninkinsu”

“Ameennn” anni ta fada cikin jin dadin addu’ar maimunatun.

Bata tsammanin ko sassan nasu su anni sun bari inna furera ta miqa mata hannu,ko batayi.magana ba tasan me take nufi,shi yasa gaba daya batayi nufin amsar kudin ba,saboda tasan cewa zata raba matar da kudinta ne,ita kuma da tayi niyyar bawa ba zata mori komai a cikinsu ba,duka ta dunqule kudin hannun nata ta miqawa inna fureran,sannan ta tsugunna ta debi kayan aikinta ta fara gyara wajen bata ko waiwayeta ba.

Babu kunya babu kuma tsoron Allah ko daya a tattare da ita ta hade dukka kudaden ta irge abunta cas ta soke su tayi gaba abinta tana rera waqa,yau itakam ranta fes,mutuwa batayi mata komai ba sai rana data yi mata,banda silar mutuwar ina ita wannan dukiyar?,ina ita ina mallakar wadan nan kudade?,kudi kam sunzo mata a dai dai,tanadin bikin gajenta zata farayi tun yanzu,saboda bikin gata takeso tayi mata.

“sannu anni…..an gama komai ko?” Yuuma ta fada sanda take shigowa rumfarta dauke da kwanon sha da ta cikashi da damammiyar fura da nono wadda babu surkin sugar ko kadan a cikinsa

“Mun gama komai ramatu..dabbobi lafiyayyu,har sunso sufi na labaran din ma”

“Ai sunfi ma anni,sun hadu da makiyayiya mai hazaqa da iya kiwo,irin kiwon da babu ha’inci a ciki” yuuma ta fadi tana zama sosai gaban anni tana murmushi

“Ai naga alama,ko ba wata yarinya maimunatu ba?”

“Itafa,baiwar Allah” yuuma ta fada fuskarta na dan canza yanayi

“Ai tunda na shigo Allah yake hadamu,naketa ganin abubuwan mamaki daga wajen yarinyar,na jima banga me kiwo irinta ba,sannan abinda zai sake baki mamaki da ita…..wajen cinikin nan,kowacce dabba da muka nuna manaso sai datayi mana bayanin lafiyarta da sauransu,babu ha’inci” cikin gamsuwa yuuma take gyada kai

“Bata tsinta a qasa ba ai,gado ne me kyau daga wajen mahaifiyarta,Allah ya jiqan ruma”

“Allah sarki,kice marainiya ce?” Anni ta fada tana jan kwanon furar gabanta tana qoqarin budewa

“Marainiya ce,wadda aka kasa yi mata riqo na tsakani da Allah…..kinsan mahaifiyarta anni,kin tuna matar da kikaga wata balama me juna biyu a wajenta kikai sha’awarta shekarun baya can da suka shude,ta qara miki da kyautar wata akuya,akuyar da kikace ta miki albarka fiye da kowacce dabba a kiwonki?”

“Af…..af ina zan manta da wannan baiwar Allar,dama itace mahaifiyarta?”

“Itace anni” yuuma ta amsa mata tana dauko wani kwanon da ta shaqewa anni shi da dambu me dumi tana aje mata

“Allahu akhbar…….” Maganar annin ta tsaya sakamakon shigowar laila tana qananun mita.

   Daga kai anni tayi ta dubeta,daure take da zani daurin qirji da kuma qaramin hijab fari,sai jakar kayan wankanta dake riqe a hannunta,daya hannun nata kuma wayarta ce

“Wanne irin sakarci ne haka zaki fadowa mutane ba sallama?,banason tsiyatakun banza da wofi fa?” Cuno bakinta tayi gaba tana sauke wayar daga fuskarta tana kallon anni

“Don girman Allah anni ki karba wayar da abbi ya baki ko zamu huta da ire iren takurar su ya jabir” gyara zamanta tayi tana kallonta sosai

“To…idan kuma naqi sai yaya kenan uwata?” Hannu laila ta yarfe,bataso annin ta hutsance mata,lallabata takeson yi ta karba a wuce wajen

“Anni…..yanzu fa wanka zan shiga,ashe muna hanya daxun ya kirani banga miscal dinsa ba sai yanzu,ina daga wayar ko tsayawa amsa sallamata baiyi ba ya hauni da balbalin masifa,Ni bansan sanda ya koma haka ba wall…..” Maganar tata ta katse saboda shigowar wani kiran,saita duba sannan tace

“Gashinan ma” gaba data tattar wayar harda earpiece din jiki ta miqawa anni ta juyawa tana shirin ficewa

“Wannan zaren na jiki da kika hadani dashi shi zan qaqabawa kunnena?,bada ni ba gada a maqabarta,zoki tsige abinki ki karbi naji da gayan wayar ma” dole ta dawo ta cire matan yadda ta buqata da sauri don kada kiran ya katse ta sake jazawa kanta wani sabon mita da qorafin.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button