GURBIN IDONOVELS

GURBIN IDO CHAPTER 1

GURBIN IDO
Ba ido bane

Mallakar
Safiyya Abdullahi huguma
Arewabooks username
HUGUMA

©️®️ ZAFAFABIYAR

ƊANƊANO
Page 01

Faffada kuma yalwataccen daji ne iya ganinka,wanda ya wadatu da korayen tsirrai da kuma shukoki nau’i daban daban,masu tsaho da kuma gajeru,ciyawa tafasa da sauran tsirrai da ubangiji ya huwace musu su wanzu a wajen,wanda wasu ma dan adam bai san meye ba,wasunsu kuma magani ne da garkuwa ga jikkunan dan adam.

Yadda sararin yayi kore shar da nau’in tsirran da kuma yawaitarsu kadai xai bayyana maka cewa muna lokacine na yawaitar saukar ruwan sama wato lokaci na damina,duk da da cewa gurin waje ne mai cike da ni’ima da kuma albarka,albarka data sanya mawuyacine ka samu wajen a bushe ko kuma a qafe…..wannan dalili ya kawo wanzuwar fulani wajen a muhallin,suka kafa bukkokinsu suka kuma tashi gagarumar ruga a wajen….saboda waje ne daya dace da muradinsu da kuma buqatar dabbobinsu,wanda buqatar dabbobin nasu sama take da tasu buqatar.

Yammaci ne lis,wanda daqiqu kadanne ne zasu ratsa magariba ta shiga,lokacine da kowanne makiyayi yake qoqarin kada kan dabbobinsu zuwa gida inda zai turkesu saboda gabatowar dare,daga cikin wannan dajin mabanbantan tawagar shanu wani lokaci harda raguna da akuyoyi ke kutsowa cikin ainihin wajen da suke kira da gari a wajensu,kowanne tawaga na tafe ne da masu kula da ita,mutum biyu uku hudu har zuwa biyar idan sunyi yawa,yawancinsu maza ne,matan dake ciki daidaiku ne.

Da sannu sannu wadan nan dabbobi ke wucewa zuwa guraben da muhallinsu yake,kamar sun gama wucewa…..saiga wani garken na daban na bullowa a hankali.

Kyawawan shanu ne tunkiyoyi raguna da kuma awaki masu tarin yawa da daukar hankali,ba komaine ya kawo haka ba sai yanayin qoshi da kuma tsaft da garken keda yashi,kusan duk dabbar dake ciki fara ce…..sai wasu daga ciki dake da ratsin ruwan qasa……duka ba wannan ne abun mamakin ba,abu mafi daukar hankali shine Kyakkyawar matashiyar dake kara kaina daga hagu tsakiya xuwa daman dabbobin tana saita su,da fari zaka zaci ba ita daya ke wannan aikin ba,amma idan ka tsawaita dubanka a kanta zaka fahimci ita kadai dince,dauke da sanda guda daya tak.

Kyakkyawa kyau na musamman kuma na asali koda cikin fulanin,irin kyan da zaka tsammaci half case ce,maimunatu nada wani irin kyau na daban wanda ke sanya duk wanda yake baqon gani a gareta ke bata lokacinsa wajen binta da kallo,saidai kuma…..duk da wannan kyau nata babu mutum daya daya aboceta wajen tahowa gida,kusan kowa ya kado dabbobinsa ya barta,babu koda mutum daya ma cikin wadanda sukayi gaba dake waiwayota ko duba halin da take ciki bare yayi niyyar tayata ta samu ta iso gida da wuri.

Kusan itama hakan bai dameta ba,duk da tanashan wahala,amma ya zamar mata jiki,ta kuma saba da yanayin……sanye take da baqin saqi maimakon farin saqi da akasan mafi akasarin fulani na tu’ammali dashi,zaka iya hangen yadda kayan suka dangale mata sosai fiye da dangalewa ta al’ada da aka saba gani tattare da fulanin,don kuwa koda rigar maimunatu tayi dagewar da banda baqar rigar yadi data saka daga ciki,babu abinda zai hana mutum ya hango albarkatun qirjinta da suka fara tasawa,sai kuma yalolon baqin mayafin data sake rufe qirjin nata dashi,duk kuwa da cewa ba wani kauri ne dashi ba,bashi da maraba da abun tace koko,hakanan bashi da tsaho,don ko mazaunanta baikai ba,tun abun yana da girma da kuma kaurinsa take amfani dashi,amma har kwanan gobe ta kasa rabuwa dashi,saboda dumbin tarihin da mayanin yake dashi a gareta da kuma rayuwarta gaba daya.

Zanin jikinta shima a dage yake sasai,kanta na sanye da Hular kaba irin wadda fulani ke yawaita amfani da ita da suke kira da(malafare)sakamakon yawaitar zafin rana ko kuma tunanin saukar ruwan sama,wadda ta baiwa doguwar jelar gashin tsohon kitson dake kanta bayyana sosai,kitson DOKA inji hausawa,su kuma suce dashi(BIƊEJI)(mai tudu daga tsakiya)shine a kanta,don haka jelar ga sauko dama da hagu na fuskarta da kuma bayanta,abinda ya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau da kuma bayyana asalin yarenta.

Kunnenta babu dan kunne,saboda bata dashi,bata ma ta’ammali dashi,amma hannayenta cike suke cankas da duwatsu kalar kore shar da kuma ja,irin shirin duwatsun da akasan fulani dashi,hagu da damanta gaba daya,masu yawan gaske,wasu daga ciki ma sun girme mata,amma dai wasu abubuwane da bata iya rabo dasu,tana jinsu ne tamkar fitar numfashinta.

Daga qugunta salkar ruwa ce ta duma da aka fafe daure tam,abu guda daya da take da damar tafiya dashi zuwa wajen kiwo,qafafunta kuwa wasu takalman roba ne rufaffu wanda baka rasa bafulatani dashi saboda yanayin shiga daji qayoyi da sauransu,shi kadaine fari a jikinta,duk da tsufar da yayi amma fes yake,da alama ya samu kulawa.

Cikin matuqar juriya da kuma jajircewa take wulga sandar tata tana maida dabbobin hanya,duk kuwa da cewa numfashinta baya sauka zuwa cikin cikinta saboda uwar yunwar dake sakadar hanjinta kamar zata tsinka mata su,cikin matuqar kulawa take kada sandar,saboda ko kadan batasan ta samu kowacce dabba a cikinsu,wannan kusan al’adarta ne,bata dukansu,saidai duk umarnin da zata basu suna ji suna kuma biye da ita,hakan ya haifar da shaquwa mai ban mamaki tsakaninsu,idan tana magana dasu wani lokaci,kai kace tana magana ne da mutane ‘ya uwanta.

Har mantawa take cewa ba bil’adama bane kamarta,sau tari takanji sunfi mata mutanen dake kewaye da ita take kuma rayuwa a cikinsu,idan tana tare dasu,tana jin kamar bata da wata sauran damuwa,tana daukansu ne kamar wasu ‘yan uwanta.

Sannu a hankali take ci gaba da kadasu cikin juriya da qarfin hali zuwa hayar da zata sadasu da gida.

Tafiya me matsakaicin nisa suka bayyana a rugar ummaru,faffadan riga mai dauke da bukkoki masu yawa,ga wadanda suka zaunu kuma sun fara gini na jar qasa da kara wanda suka tasheshi a matsayin katanga.

Ta bayan dakunan da suke mallakin wasu suka keta,jimawa kadan sai gasu a haggo(wajen daure dabbobi),ta waiwaya a hankali tana duban sararin gidan,babu matar daya zame mata wajibi duk sanda fa dawo ta shaida mata dawowarta,wannan qa’ida ce,wadda tsallaketa ko saba mata dai dai yake da saima kanta tashin hankali da rashin nutsuwa tsahon wasu kwanaki,idan ma batayi sa’a ba,cikin duka kwanakin da zasu biyo…..za’a yita kiranta da sunan da duk duniya babu sunan data tsana sama dashi

“Miwarti inna!” Ta bude dukka kaifi muryar da Allah ya bata tana qwalawa innar kira tare da shaida mata ta dawo,saidai yanayin zaqin da muryarta ke dashi,sam bata da amsa amo ko kuwwar da kiran xai isa inda takeso

“Inna miwarti!” Ta sake fadi,saidai da alama ko kusa da inda innar take basu jita ba.

Waiwaya tayi gefe guda,yarone dan kimanin shekara takwas,zaune yana wasa abinsa,yayi fututu,kai zaka ce daga sansanin gudun hijira aka tsamoshi,kai ta jinjina,tanason tace dashi wani abu amma tana tsoro kada cibi ya zama qari,bata da zabi illa ta aikeshi ya kira innar

“Laulo,yanoddanan inna” daga kai yayi ya dubeta yana yamutse fuskarsa dake harmutse da qasa

“Owalad’o(bata nan)” ya amsa mata a tsiwace yana maida kansa ga wasansa.

“Maimunatu!”ta qwala mata kira bayan taja birki tana hangota tsakiyar dabbobin cikin dan ragowar hasken da duhun hadari dana dare ya fara hadiyeshi

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button