GURBIN IDONOVELS

GURBIN IDO CHAPTER 4

GURBIN IDO
Arewabooks::HUGUMA

Free page 04

Sallamarsa ta yanke mata dan qaramin bacci mai dadi data fara yi,ta daga kanta tana amsa masa,da murmushi ya bita,hannunsa dauke da baqar leda qananu guda biyu,inda ya tashi dazun ya koma ya zauna,sannan ya bude ledan yana cewa

“Ga magani kisha” idanunta ta lumshe gami da budesu lokaci guda cike da.mamaki,yau ita ake cewa ga magani?,anya kuwa ita dince……maimunatu?,bata sauka daga wannan mamakin ba ta sake jin muryarsa yana sake miko mata wata ledar

“Amma ki fara cin wani abun tukunna,na sani idan baku da lafiya bason cin abinci kuke ba,haka innata ke fama dasu zubaida idan basu da lafiya” ya qarashe maganar yana miqewa

“Bari na baki waje,amma idan bakisha maganin ba zan dawo” saiya juya yayi nesa da ita,yayin da ta rakashi da kallo har sai data daina hangoshi,sannan ta janye manyan idanunta ta mayar kan ledojin,ta sanya hannu ta jawosu tana budewa.

Ledar farko magunguna ne,qwayoyi tablet sosai,sai leda fa biyu dake dauke da gurasa mai kyau,wani yawu ta hadiya,duk da yanayi na lalurar rashin lafiya da take amma sai da tsohuwar yunwa ta taso mata,batayi qasa a gwiwa ba ta dauka ta fara ci,tana ci tana lumshe idanunta tsananin azabar yunwar data tarawa cikinta,dama don bata da lafiya ne,amma duk sanda inna ta gwada mata irin wannan rashin imanin……a nan gurin kiwo take samun daya daga cikin naggen ta tatsi nono mai dumi tasha,duk da ta sani,yawanci da safe shine lokacin tatsar,amma dole tasa wasu lokutan take hakan,idan kuma ta samu ta faki idon innar sanda take tatsar da sassafen ta ɗaɗɗaki wani,shine zata wuni nata damu ba,yunwa kuma bata addabeta ba kamar yanzun,har shan nonon ya zame mata jiki,ya koma kamar shine abincin nata,abinda yasa ko kadan bata da wani jiki kwata kwata,duk sirantaka irin ta bafullace tata ramar ta fita daban.

Bawai don ta qoshi ba ta janye hannunta,a’a,tayi hakanne saboda kunya kara da alkunya,kada yazo ya taras ta tashi da ita,ta bude ledar maganin wanda ya sanya ledar ruwan pure water guda daya,ta daga pure water din ta jujjuya shi a hannunta,ba zata iya tuna sanda tasha ruwan leda ba a rayuwarta,saita koma kan magungunan,ta balli kowanne kamar yadda taga anja sandunan layi ajiki ta kora da ruwan.

Idanunta ta mayar tana sake lumshesu,tana jin yadda numfashinta yadan fara daidaita albarkacin gurasar data ci tun kafin magani ya soma mata aiki,a hankali take zuqan iskan wajen tana kuma sauraren koke koken dabbobi dake kai kaw a wajen,jikinta yana mutuwa murus kamar wadda aka yiwa dukan tsiya.

Tun daga nesa ya kafeta da ido,idanunta dake lumshe sai suka sake qarawa fuskarta kyau,yana ganin baqonnin yanayi tattare da ita,yana son sanin wace ita sani na haqiqa,da kuma dalilin da yasa take kebance kanta take nesa da jama’a haka.

Sallamarsa ta sanyata bude idanunta

“A henyi?(Kin gama?)” Kai ta gyada masa tana kallon qasa,kunya tana cikata,tanajin yadda tayi abun kunya,na yadda zata zauna taci abinda ya futo daga hannun saurayi

“hokkoyon dunni sauro(miko min sandar can)” ya fada yana nuna sandarta dae gefe,sai data kalli sandar sannan ta maida dubanta kanshi,ya fahimci me take nufi,don haka murmushi kawai ya sakar mata,ya taka da kansa zuwa gefanta ya dauki sandar,ga bishi da kallo mamaki fal zuciyarta
“waye shi?” Tambayar da taketa nanatawa kanta kenan.

Daga nan inda take tana iya hangen yadda yake tattare mata kan dabbobin nata cike da hikima da kuma qwarewa wadda ta lunka tata,da alamu shima din gwanine wajen iya kiwo,bai dauki wasu lokuta masu dama ba ya dawo gareta,yana sabe da sandar kan kafadarsa

“indillo(Muje ko?)” Yace da ita,dubansa tayi sanna ta janye idanunta gefe daya,sam maganar batayi mata ba,ta yaya zata jera dashi har cikin gari?,akwai idanun mutane masu yawa a kanta,sannan tana da kunyar da ba zata iya aikata hakan ba

“ummadillen(Tashi mu tafi),ko ba zaki iya tashi ba?”ya sake maimaitawa a tausashe,a hankali ta girgiza masa kai

“Kaje kawai,na gode,zan qarasa kaisu gida da kaina,na gode qwarai” idanu yadan zuba mata kadan,sai ya sauke ajiyar zuciya yana sauke sandar daga kafadarsa,ya fahimci me take nufi,tabbas ga cika bafulatanar gaske.

“Shikenan,zan kora miki su,tumudilli tokkirawaya gaɗa taajan banna wala kyettaiɗo ingwandi(idan na tafi ki biyo bayana,karki damu,ba wanda zai gane tare muke)” duk da hakan yayi mata,amma kuma batason dora masa wani nauyin kuma ko dawainiyarta,saidai kafin ta sake cewa komai yayi gaba,dole ta miqe,ta dauki malfajenta ta mayar saman kanta,ta dauki jakarta ta daura tabi bayansa.

Bata sani ba ko shima ya kula,sharewa kawai yayi,ko kuma bai kula din ba…..da gaske ita daya ta lura,yadda mutane keta binsa da kallo a sanda aka ganshi yana kora shanun da ita ke da hakkin kula dasu,yayin da ita kums ke biye dasu a baya,kasan samun nutsuwa tayi kwata kwata,jinta take a daure,har sai da suka isa gida,ya miqa mata sandanta idanuwansa akanta,fuskarsa dauke da murmushi

“Sai jaaango?” Ya fada yana sake nazartar kyakkyawan fuskarta

“Miyatti” ta amsa masa a gajarce,sai ya jinjina kansa

“Alla ɗaudane jamu(Allah ya qara lafiya)kisha magungunanki da kyau”

“to Allah jaɓe” ta fada tana jin nauyin mixanin kyautatawarsa a gareta.

Ko sanda himu yake nufar gida tunaninta ne fal cikin ransa,kamar yadda murmushi yaqi barin fuska da bakinsa su huta,sosai yake ji cewa yayi gamo da Matar aure,ta kuma zo dai dai lokacin da ya kamata ace tazo din,bayajin zaiyi nauyin baki ko jinkirin shaidawa innarsa,duk da cewa babansu baya nan,amma dai yana da kyau innar ta sani,ta kuma shaidawa baban da zarar ya dawo.

Da sallama ya shiga faffadan tsakar gidan nasu,kishiyar mahaifiyarsu wadda asalin sunanta shine rahama….amma sauran dangi da ‘yan rigarsu na kiranta da ramatu,su kuma yaran gidan suna kiranta da yuuma,tana duqe gaban murhu,ta kammala kwashe tuwon dare tana wanke muciyar cikin tukunyar tuwon himu ya shigo.

Fuskarta dauke da fara’a take amsa sallamar tasa,macace mai matuqar kirki haquri hagen nesa da kuma sanin ya kamata,duk da kasancewarta wadda Allah bai azurtata da haihuwar yaro ko daya ba,amma sam bata kasance mai baqin hali gabyaran mikin nata ba,mutum ce mai sauqin kai,wadda take kallonsu ibrahim tamkar ita ta haifesu,tana kulawa da kowanne daya daga cikinsu,duk da zamantowar safara’u mahaifiyar ibrahim mace mara haquri da biyema zuciyarta a wadansu lokuta,amma yuuma ta danne,suna zaman lafiyar daya sanya jama’a da dama cikin karkarar ke sha’awar zaman nasu,ba tare da sunsan cewa fiye da kashi tamanin cikin dari na zaman nasu haqurin yuuma ne ya qawatashi.

Barka da gida yayi mata ta amsa tana masa sannu da zuwa

“Inna walaɗon(inna bata nan ne?)”

“o’o immoder,one ɓayi e’ummakiɗo(A’ah tana ciki,don bata jima da tashi daga nan ba),kila barci ne ya saceta,don tacemin bata danjin dadin jikinta sosai” kai ya gyada sannan ya sake tambaya

“Yaran nan fa?,su safiya?”

“inna’onliliɓe,amma ɓeɓadake wartuki(Innar ce ta aikesu,amma suna gab da dawowa)” har ya taka zaiyi gaba sai ya sake tambayarta

“Yaushe baaba yace zai dawo ne?” Murmushi ta sake

“Yau kuma ‘yan tambayar ne a kusa himu?,rana wata yau in sha Allah” kai ya gyada yana murmushi,yaji dadin jin cewa bazai jima ba zai dawo gidan,ya tafi ikko ne da wasu shanunsa zai saidasu,wanda dama.yawanci can yake kaisu,shi kansa ibarahim din yafi zama a can,mafi yawan rayuwarsa ta can ce wajen wani dan uwan baaban nasa,yanzu ma gajiya yayi da zaman can din ya dawo gida yadan huta sannan ya koma,uwa uba kuma sun samu hutun semester,don acan din bai zauna ba yana karatunsa.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button