GURBIN IDONOVELS

GURBIN IDO CHAPTER 4

Ya daga labulen dakin ya samu barcinne kuwa ya dauketa,sai ya sauke ya wuce dakinsa,yayi abinda zaiyi a ciki sannan ya fito ya fara daura alwalar magriba,bai kammala ba innar ta fito tana daura dankwalinta

“denattoi ɗa himu(yaushe ka shigo himu?)” Ta fada tana dubansa,ita din duk da bafullatsna ce amma sam ba ruwanta da wannan kunyar da kaara tadan fari

“Ban jima ba,na leqo na samu kina bacci,ya jikin naki?”

“Alhamdlh,nasha ragowar maganin nan daka taba kawomin kwanaki kafin na kwanta,kaga kuwa har ya fara sakina”

“To alhmdlh,hammiyami jula miwarta(bari nayi sallah na dawo)” ya fada yana warware hannun rigarsa,a bakin kofar shigowa gidan sukayi kacibus da qannensa,yammata masu tasowa su biyu,yace maza su shige gida an fara kiran sallah,suka amsa masa amma suna binsa da.kallo,saboda labarin da suka samu a kansa tun a hanyarsu ta isowa gida.

Bayan sallar isha’i ya shigo gidan,babu kowa tsakar gidan sai yuuma dake zaune daga bakin kofar dakinta ita daya,gabanta fitilar aci balbal ce,sai qaramar redio da bata rabo da ita saboda jin labarai,sannu da gida yayi mata,ta amsa masa tare da shaida masa abincinsa na wajen innarsa,ya amsa mata yana wucewa kai tsaye zuwa dakin innar,bayajin dadin yadda wasu lokuta safiya da zubaida ke barin yuuma ita kadai,duk da lokaci lokaci zaka samesu wajenta,yana matuqar jin tausayinta,saboda rashin haihuwa abune mai ciwo da kuma sanya mutum cikin kewa da kadaici.

Da sallama ya shiga dakin,ya taras dasu sunata hira abinsu dukkansu,safiya zubida da sadam qaramin qaninsu,sannu da xuwa sukayi masa,ya samu waje yana zama

“Ra nyam kima,hokkumoki sadam(ga abincinka,sadam mika masa)” inna ta fada,sai sadam din ya mika masa,yaja kwanon ya bude ya fara ci bayan yayi bismillah,ba qaramin son tuwon yuuma yake ba,bama shi kadai ba,hatta da jama’ar gidan,saboda yadda ta iya girki,duk da innar tasa ma ba baya bace.

A hankali yake cin abincin yana kuma jefa baki a hirar tasu,saidai fiye da rabin hankalinsa nakan ta yadda zai gayawa inna maganar dake bakinsa,a qa’ida da yuuma zaiyi zancan,amma ya sani idan yayi hakan ransa ne xai baci wajen innar,saboda batason hakan,tafiso kowace magana suke da ita su sameta kai tsaye su shaida mata,itama yuuman tunda ta fuskanci haka,da sunzo sun gaya mata zata ce

“Kun gayawa innarku?” Idan sukace a’ah,takan ce

“Ku sameta ku fara shaida mata muji abinda xata ce”.

Sai da ya gama cin tuwon tas ya wanke hannu sanna ya gyara xamansa cikin jin nauyi da kunya yace

“iwodi haala kaginmi gaɗen Inna….(akwai maganar da nakeso muyi inna)”

“Shine tun daxu kaketa wani mutsu mutsu ka kasa gayamin?,tawi’aayanka,mojetta bi’owaka(idan baka gayamin ba wa zaka gayawa duk duniya?)” Ta qarashe da sigar tambaya tana kafeshi da idanu,yasan me take nufi,sai kawai yayi murmushi yana cewa

“Babu”

“iminamma(ina saurarenka)” dan jim yayi kadan sannan yace

“Inna…..na samu yarinyar da nakeso fa”.

Zuba masa idanu tayi saboda yadda maganar tazo mata a bazata,bata tsammaci jin maganar ba a wannan lokacin,saboda tuntuni tana da tsari da kuma muradi a kansa,amma duk da haka saita danne wannan a ranta,tace dashi

“Emi namma,immoi ‘onni?(ina jinka,wacece?)” Kansa yadan shafa kadan sannan yace

“Sunanta maimunatu”

“Maimunatu ta gidansu laulo” muryar zubaida ta ratsa hirar tasu,da hanzari inna ta juya tana duban zubaida saboda yadda maganar zubaidan ta dauki hankalinta,yayin da himu shima ya juya yana kallon zubaidan saboda baisan waye laulo din ba,saidai idan ita dince yaji dadin yin maganar da zubaidan tayi,saboda baisan ta yadda zai kwatantawa innar ita ba yadda zata fahimta

“Da gaske ita kake nufi himu?”

“Gidansu na kusa da hanyar fegin maraba” mummunar faduwa gaban inna yayi,tabbas maimainunatun ya hango,take hankalinta yayi mummunan tashi,maimunatu ‘yar uwa ga gaje?,gaje dai ‘yar inna furaira

“Yuuma…..yuuma…..warnano wakka haala kawela(zo kiji wani mummunan labari)” ta fara qwalawa yuuma dake xaune qofar dakinta kiran,abinda ya sanya himu zubawa innar idanu cike da mamakin meye ya gigita innar tasa haka?,har take irin wannan kiran?.

“Ku tashi ku fita” innar ta fada tana waiwayawa gasu safiya dake zaune tun dazu suna kallon kallon a tsakaninsu,tsam suka miqe suna masu ficewa kowacce bakinga fal da magana,dai dai sanda yuuma ta shigo dakin a rude

“Lafiya kuwa?” Ta tambayi inna tana laluben wajen zama hankalinta a tashe,sai da inna taja wani dogon numfashi mai nauyi ta furzar da iska sannan tace

“Yaron nan ne yakeson dauko mana jaraba rana tsaka” sake tashi hankalin yuuma yayi tana duba inna tace

“Subhanallahi,jaraba wacce iri?” Kai inna ta gyada cike da jin xafi tace

“Wai yarinyar nan maimunatu ya gani yakeso?”

“Maimunatu?….maimunatu?” Yuuma ta maimaita sunan tana son tuna aka wace ake magana

“Diyam ta gidansu laulo” take yuuma ta fahimta,sunan kuma ya fado mata a rai,saboda ita daya keda sunan kaf rugar,hakanan kuma mahaifiyarta kadai ke kiranta da sunan,sai ta sauke ajiyar zuciya,alamun tashin hakalin da ya taso tun daga zuciya zuwa fuskarta ya fara zagwanyewa

“Hankalina ya tashi sosai innar sadam,na dauka wani abun tashin hankalinne”

“Yo akwai tashin hankalin da yafi wannan yuuma?””ai abinda yasa nace haka innar laulo…..kaf fadin rugarnan anyi ittifaqi babu yarinyar dake da nutsuwa da kuma kamun kai da tarbiyya irin maimunatu…..”

“Amma kinfi kowa sanin ainihin wacece ita ko?”

“Wannan duk camfi ne ko ince hasashe….duk cikin masu hasashen babu wanda yake da tabbas kan abinda yake fada koda kuwa a gaban Allah ne,dukka abinda al’umar rugar nan keyi ba komai bane illa jahilci zalla da kima gurguwar fahimta gami da mummunan zato,koda ba zato bane hakanne,babu wanda ya taba kama maimunatu da wani mummunan aibu da za’a qita,a karan kanta maimunatu bata da wata matsala ko illa…..” Idanu inna ta zubawa yuuma,a hankali a kuma sanyaye tace

“Yuuma…kodai don bake kika haifi himu ba kike qoqarin wanke maimunatu gami da kore kowanne aibu daga gareta?” Ba yuuma kawai ba,hatta da ibrahim sai da maganar ta tabashi,qas yayi da kanshi yana jin babu dadi a ransa,yayin da yuuma ta rintse idanu,maganar tana sauka saman zuciyarta da wani irin dafi mai zafi,dai dai maganar take da saukar mashi saman zuciyar tata,duk yadda take zaman kawaici da innar laulon….bata taba gwaba mata magana me zafi akan yaranta ba irin wannan

“Kaico!….kaico!” Yuuma ta fada tana girgiza kanta

“Inama ace Allah ya bani d’a na cikina wanda yakai shekarun ibrahim….kai koda ace bai qarasashi ba,matuqar ya isa a daura aurensa,da ba shakka na tabbatar miki da cewa magana nake Miki da zuciya daya…..Allah ya kyauta,kiyi haquri bisa shishshigin da nayi miki” yuuma ta fada bayan ta yunqura ta miqe,zuciyarta na wani irin tafasa,wanda tana fita qofar dakin hawaye ya silalo mata.

    Shuru ne ya ratsa dakin na wucin gadi,cikin ranta innar laulo tana jin kamar bata kyauta ba,wata zuciyar kuma na gaya mata daidai ne abinda tayin,zallar mugunta ce kawai tasa yuuman bada wannan shawarar a gaban himun,bayan tasan kowa gudu da qyamar yarinyar yakeyi,ko ita bata sake ganinta tana hulda da yarinyar ba

“Amma inna abinda kika yiwa…..”
“Kaga dakatamin” inna ta tsaida ibrahim dake Shirin nuna mata rashin dacewar abinda tayin

“Kada kace min komai,maganar maimunatu kada na sake jinta a bakinka,domin kuwa ba kai ba,koda wanda na isa na gaya masa yaji ne bazan bari ya aureta ba,bare kai dan cikina,bama maimunatu ba,banason ka sake kawomin maganar kowacce yarinya,na riga na zabar maka matar aure tun shekarun baya…..kaje gidansu maimunatun ka nemi gaje ku dai daita”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button