GWAURO COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana leƙensa har ya dauko mata botikin yazo ya bata ,cikin murya ƙasa² tace “kaga wani da akuya” yamutsa fuska yayi cikin rashin fahimta “Ni banga kowa ba”
Gyaɗa masa kai tayi ya wuce ta wuce dab da zata isa gida ta hango ƙawarta Ramatu a ƙofar wani kanti tana siyan maggi “Au Ramatu Ba magana?”
“Wayyo ban gankiba ne ƙawata zo mana in siyayya mu jera hanya” hira ne kamar abun arziki ya sarƙe har akaxo hiran Nuru da mamansa salame basakkwata
“Ke ƙawata bakiji ba yaudai mutuminki ta ƙare masa ,kinsan dama ance da salame basakkwata da ɗan arzikin ta su nuru suka dunga mata sata suna zuwa suna aro iyayen karya in sunga budurwa tai masu sai akai kudin aure in ya lalata masu yarinya ya gudu ko?….”
“Eh haka kuwa naji labari amma ance sharri akai masu”
“Injiwa to gaskiya ne don Ni ganau ne ba jiyau ba. yau ba mace ba jar akuya ya matse a lungu sai ihu take ,na ɗebo ruwa na ganshi “
“Ke don Allah “
“Wallahi kuwa kuma akuyar tasalla ne kuma na zuba ido indai ta haihu saina hana kowa ya siya akuyan nan don ɗan ɗan nuru ne ba akuya bane,kinga kuwa bashi yuwuwa mutum yaci ɗan uwansa mutum”
“Kinada gaskiyar ki ,kice kwanan nan zamuga akuya mai fuskar mutum”
“Wallahi ƙawata” suka haɗa hannu suka tafa ,suna dariyar shaƙiyanci . Duk mutanen da suka cika shagon tsuru tsuru sukayi da ido sunajin wagga almara
Aikuwa suna bada baya abokin nuru, Abdullahi da duk ya gama jinsu ya ciro waya ya shaidawa nuru labarin da yaji a bakin hadiza……….Tashin hankali wanda ba’a saka maki rana ,Nuru da dama yina kwancene akan er keson katifarsa ,cikinsa sai ƙugi yike yina burgima ƴan hanjayensa na disko saboda yunwa dake cin ƙaniyarsa ga zafi da ake zubawa ya dage singileti sai fifita yike da mahucin kaba………
Ai yinajin wannan labarin yayi zubur ya miƙe zaune ,ya saka jallabiya ya ciro bulalarsa dake rataye a ƙusa yayi hanyar gidan su Hadiza
Hadiza na tsugune gefen Hajiya da take rigar shinkafa sukaji ana kwarara sallama a zaure ,haba ai ko cikin dubu tasan Muryar Nuru ,tsam ta miƙe tayi bayan kofa da gudu
“Hajiya na watsa masa ruwa ya biyoni ya zane ni don Allah kar kice masa ina nan”
Jin ba’a da niyyar amsa masa sallamar yasashi ufowa cikin gidan
“Maraba marhabin nurun kaine a gidan” karkaɗa bulalar hannunsa yayi sannan yace “Ina Hadiza”
“Bata nan lafiya”
“Lafiya ba lau ba,amma Hajiya ki sani na rantse da Allah na zuba bulalai a kaf kwalbatin unguwar nan ,duk inda naga Hadiza sai dai in faɗa kwata mafi kusa in ciro bulalana wallahi sai na zubar mata da jini daga kaina zata daina munafurci…”
Yana dasa aya anan ,kawai ya juya ya hankaɗe botikin ruwan da Hadiza ta ɗebo ma Hajiya na ƙofar ɗaki yayi waje yina zage² “Shegiya Mummuna fuska kamar babbakakkiyar ƙuli zan gamu dake saina watsar maki da wa’innan haƙoran masu kama da kacaaa”
Hajiya buɗe murya tayi tana “Yaka nuru…nuru!” Ai ko sauraranta bai yi ba ,nan ta shiga tafa hannu tana salati “Wohoho Ni jikan mutum huɗu,kaga mun majanunin yaro ,anya kan yaron nan ɗaya ne kuwa?!” tana ɗage labule Hadiza ta fito daga bayan ƙyaure ta ɗaura hannu aka ta fashe da ihu
“Wayyo Allah Hajiya ki mun rai,daga nace yina kai mata ɗakin sa ai bance yina masu komai ba……(kawai saiga hawaye sharrr ya biyo kuncinta) tsaki Hajiya tayi ta wuce ɗaki ba tare da ta tamkata ba
Buɗe murya tayi “Ai Hajiya yama kasheni ba damuwarki bane ko ?,kina ganin shi kamar zuriyar samudawa! To wallahi in bakije kin bashi hakuri ba na daina fita maki saƙo”
Bahrain
(Al_Undulus)
Tun daga bakin ƙofar Dam door ɗin kikejin wani irin kwantaccen kuka mai tada tsikar jiki,wanda komin ƙin Allahn ka sai ma’abocin wannan kukan ta baka tausayi ….Pure balarabiya ce kyau ko a cikin larabawan sai an tona zaune cikin ɗaya daga cikin lumtsuma²n fararen kujerun falon ,ta takure cikin baƙar jallabiya gashin kanta ya barbazu saboda tsabagen rashin gyara da kwanciyar hankali
Gidan tsit yake bakajin ƙarar komai sai TV da ta kamo tasoshin ƙasashen turawa sai kuma ƙarar Ac
Nasmah fitowa tayi cikin shirin tafiya party saye dawata yaloluwar ya riga da wando ta gyare gashin kanta ta ɗan yane da karamin veil
Gaban Nasreen da ke raira kuka taxo ta fara makama cinyarta duka kamar mara galibin l da za’a tasa daga barci “Hey ma’am ātini bi sa’atiy ya mu’allimah…oya oya bissur ‘a” (ke Madam ɗan bani agogona ko Malama….Oya Oya tashi ki bani da sauri)
Ta shiga mata magana cikin kyara da hantara
Nasreen zuru ta mata da ido kawai sai ta girgiza kai ta kuma kife kanta a hannun kujera
“Am I not talking to you? What kind of nonsense is this…you steal my wrist watch and I can’t pardon….mtew arrogant” (wai ba dake nake magana ba wannan wani irin rashin hankaline,kin sace mun agogona kuma ba iya yafewa zan ba) taja tsaki ta dogare a gabanta riƙe da ƙugu tana wani karkaɗa jiki irin na fitsararrun ƙanne masu yiwa yayunsu rashin kunya
Miƙewa Nasreen tayi zata wuce ba tareda ta tamka ta ba kuma daidai nan mamansu ta fito da kofin gahwa (tea) a hannu
Nasmah ganin zata wuce yasa ta finciko ta ta dawo da ita baya “Dallah Malama bamu agogonmu wannan ai baƙin cikine kinga kin zama divorcy (bazawara) kina bakin ciki kar in sama fine guy in aure in barki”
Wani abu mai ɗacine yazo ya tokare a maƙoshin Nasreen da sauri ta dafe ƙirjinta wani irin kakkauran hawaye ya gangaro mata a ido ,kallon direction ɗin da mamansu take tayi ,amma itama ko a jikinta sai ma sipping coffee (kurɓan coffee) ɗin ta da take
Cikin takaici ta ƙwalla ma maman kira ,irin kira na mamaki ɗin nan
“Ummyyy…..” ɗagowa tayi ta kallesu kawai ta kauda kai ,ta wuce gaban Tv ta kashe kayan kallon
Girgiza kai Nasreen tayi ta daɗa raɓawa zata wuce Nasma ba tareda tace komai ba ,still sake cukuikuyeta Nasma tayi sannan cikin fitsara tace “Momy kice mata ta bani agogona”
Cikin gajiyawa uwar tace “Bata agogonta” wani kuka mai dafa zuciya ne ya daɗa turnuƙe Nasreen kawai ta fixge kanta da sauri tayi hanyar stairs da gudun gaske tana kuka mai gunji kamar wanda ta rasa iyayenta
Binta Nasmah zatayi da sauri uwar ta dakatar da ita “La! Nasma ta’ali huna” (No! Nasma come here) Zo nan”
“Momy gold watch ɗin nan ne fa da na samu a birthday gift haba !”
“Meye to a ciki ki ƙyaleta taji da depression ɗin da take ciki ,kin tabbatar ita ta ɗauka ? Na sanki da tsinannan ƙwuiya bincikawa ne baza kiyi ba”
Magana tayi surprisingly “wow good! Momy kin tare mata kenan? Kin tarewa erki ta fari kin wulakanta autarki…yarinyar da ta jawo maki abun kunya cikin maƙoftanki ta aura bare gashi an saketa ,amma ita kike tare mawa?”
“No ban tare mata ba ,fada ne banaso kuna yi ,You know she age you , atleast she needs some certain respect from you ,beside why the quarrel? But you’re quarreling over a watch this is not fair my dear” (kinsan dai tagirme ki atleast tana bukatar girmamawa a wajenki ,to meye abun fada ? Kun zauna kuna fada akan abinda bai taka kara ya karya ba wannan abun kunya ne…..”
Tura baki tayi tana diddirke ƙafa “Ni dai uhmmmm shikenan na tafi lunch da ƙawayena “
“Ok bye”
Zuwa tayi da sauri ta turo mata ƙirji ta rungumo uwar ta manna mata kiss a gefen kunci “Momy I love You”
Hannu tasa ta goge wajen da Nasman ta mata kiss gamida ɗanyin murmushi ganin birgi birgin er tata har takai ƙofa ,sai kuma ta juyo rike da ƙofar “Momy nace ina sonki” miƙewa tayi gamida kama hanyar ɗaki sannan ta ɗan ɗaga murya “You know your momy loves you more! So take care of your self please”
(Kinsan mamanki tana ringa sonki da yawa ,to ki kula da kanki don Allah)