GWAURO COMPLETE HAUSA NOVEL

GWAURO COMPLETE HAUSA NOVEL

……Daga zauren gidan taja ta tsaya ganin zulai mai shinkafa tana dukan ɗakin Nuru cikin rashin mutunci,sosai aljanun son jin gulmarta suka motso sam tama manta yina nemanta ruwa a jallo ,da sauri ta zo bayan zulai ta tsaya “Baba zulai mai kike nema akuyanki ne ta ɓata?” Banza tayi mata ta cigaba da dukan ƙofa “Nuru gwara ka buɗen ƙofa in tasa ƴata tun muna tantance juna kafin in Kira maka en sanda “

Daga cikin ɗakin ya buɗe murya “ba kowa fa”
“To buɗe in gani wallahi abokanka sunce tsawon sati guda sun ganku tare kuma a ɗakinka take kwana na sani” tuni mutane sun fara taruwa ana dirga² saida yaji mutane na yawa ya ba aina’u bargo ta lulluɓa ya taso a hankali ya cire bidan ƙofar ,angaje shi tayi ta shige ɗakin

Kunyane ta lulluɓesa ganin taje ta jawo hannun erta aikuwa tana zuwa ta dage ta rangaɗa masa sandar hannunta “wannan uwar kace ko?”

Dafe wajen yayi cikin jin azaba “Lalala me na maki ?da zaki dakeni”

“Kaji tantiri na daka ko zaka rama ne?shegu masu ƙwaƙule yaran layi allah zai mana maganinku” Ɗaga hannu yayi kuwa ya tsinke uwar da mari ,nan mata suka harraƙo da hayagaga ,hakan ya taso salame daga wajen hadin alalan ta

“Kaikai meke faruwa?”
“Ɗanki aka kama ya kulle masu er mutane sati guda” riƙe ƙugu tayi ta kalli nuru

“Daka kulleta a ɗakin mai ka mata ?” Shiru yayi ya ɗan sunkuyar dakai

“Nuru sa idonka cikin idona!…daka kulle ta tsawon sati kana ciyar da ita ,Nuru ka cita?” Kowa kama baki yayi cikin mamaki ya diddilo ido waje

Jinjina mata kai yayi alaman eh ya ƙwaƙule masu er mutane

“To MashaAllah ,tunda kai ɗin lafiyayyene Allah mun gode maka ……Nuru ji Ni da kyau ,ko gobe duk yarinyar da tabiyoka ɗakinka kaci shegiya kaji nuru……….”

Ɓarkewa da salati akayi shikuma ya ɗan ringa murmusawa ,daga baya Hadiza ta zallaƙo kai “Mama salame to ai ya gaurawa mai shinkafa mari takan ta kwaɗa masa sanda da ta ciro aina’u a ɗakinsa”

Zabura tayi ta dafe ƙirji “ta kwaɗa maka sanda ?! ” Shaƙo wuyar nuru tayi “ka mare ta daidai dukanka?”

“Eh mama nafa rama “

Cikashi tayi “To Allah yayi maka Albarka ,banni da ita” ta ƙare maganar tana shan ɗan mara da mayafinta……….✍????

Oum Aphnan
09065990265
[10/8, 7:34 PM] baby na: ????GWAURO…????

              *004*

Ihu mutanen wajen suka ɗauka don abune mai saukin gaske salame tayi dambe da mata ta haye ruwan cikinta taita sukuwa ,tsakiyan mai shinkafa da salame mutanen suka shiga suna bata haƙuri kamar itace akayi ma laifi ba itane da danta sukayi aika²n ba .

Saida akaci fada aka cinye akan idon Hadiza sannan Hadiza ta sulale ta wuce gidan Antynta bee


2 months later

Bayan wata biyu da faruwar abun ,Wani ɗan natsuwa na ba gaira ba daliline haka sddan ya shiga Nuru tun hadiza, in ta gansa tana tserewa a tunaninta zai biyota ne ya daka banza ya mata lamfa,har ta zo tana wucesa shiru baya tamkata ,sosai ita da kanta abun yike Bata mamaki gashi an rabu da fada a gidan salame takan nuru to wai me ya sauya sa ne ?


Bee tafe take da hanna zasu isa parking lot ɗin farfajiyar makarantar ,hannunta rungume da littafanta ta gaji sosai saboda an dade sosai lectures ɗin yau, don haka ba abunda ta ƙosa irin ta ganta a gida

Wata tamfatsetsiyar land cruiser baƙa wuluk sai kashe ma rana ido take,, ita ta gani ya ɗan kakare mata hanya don haka baza ta iya zakalo motarta ba ,shiru tayi na en sekonni sai kuma ta karasa gaban motar ta ɗan ƙwonƙosa , ta bayanta ya taho ,sam bataji takunsa ba saidai taki ance “Ƴan mata adon gari” waigawa tayi da sauri don tabbas taso sanin mai Muryar nan ,wani kallon sheƙeƙe ta bisa dashi tana mamakin mai wanki da gugan da ya iya ara ma wannan fatararren kayan mutane ,ya fito a wani hamshaƙin Matashi mai ji da Naira da kyau ,ji tayi gabaɗaya ya bata mata kwalliya a take duk ta ɗarari kanta a ranta tana cewa “wannan inda mai kudine waikkk an bani ga kyau ga gayu” don haka,sakin baki tayi galala tana ta kallonsa ita ko sani ma batayi ba

Yatsunsa yakai kusa da idon ta da sauri ta kifta Ido ,tare da sauke sassanyar ajiyar zuciyar da batasan zai ƙwace ba

“Kallon ya ɗan isa” yayi mata magana cikeda tsokana
Ba kunya ta wani basar saima ta tsaresa da tambayar rainin wayo

“Aina kayi aron kayan nan? Subhanallh na tausaya ma budurwan da ka toaster ta zaci ajebo ne batasan ajekwali bane “
Murmushi yayi “don ke nazo ai ba wata ba so in zan iya toaster wata kece,haƙana ya cimma ruwa?”

Tsaki taja ,ta ɗanyi banza dashi tana waige²

Hanna dake mota fitowa tayi ta gaishesa a mutunce “Suna na Hanna kawar bilkis kaifa?”

Kallo ɗaya ya mata ya kauda kai don sam batayi masa ba ,kazalika rawar kanta bai samu wajen zama ba,a gintse ya amsa mata da “Nurain”

“Wow nice one ,ko zaka shigo Mu rage maka hanya?” Ta wano washe baki kamar wawiya

“Oh thanks ga mota na nan ” ya nuna wannan kafcecen motar da tun ɗazu take walƙiya tana hararansu

Ba bee ba harta Hanna saida abun ya basu dariya don haka kuwa suka tuntsure da dariya irin na ka samu taɓin hankalin nan

“Oh really,to ka toshe mun hanya zan fita da mota a bani space plx”

“To kyakyawa zanyi hakan amma ina rokon a bani Number waya don Allah,wlh in kika bani numberki bazan sake tareki a hanya ba” ƙanƙance ido tayi “Kai wai kayi hauka ne?? Bakaji kunya ba jika jiya jiyan nan kana faƙirin ka yau ka aro kaya da mota kazo wai in baka numberta “

“Dare ɗaya Allah kanyi Bature” caɓe baki tayi zata cigaba da tsigalesa
Hanna tai saurin katseta

“Haba bee Number dai? ki basa mana ai soyayya ba’a dole” ƙure shi da ido tayi na en mintoci

“Inna Baka zaka rabu dani?” Gyada mata kai yayi da sauri

“Eh wallahi i promise”

Ciro wayarta tayi gamida scrolling ta Nemo number hadiza ta karanta masa ,cikin zumudi ya kwafe Number yina murna ya fara dialing Saidai har ta tsinke baa daga ba ,kallonta yayi alamar tambaya da sauri ta daga masa gira “Yes ,ƙaramar wayace….buɗen hanya kana exhausting energy ɗina”

Jinjina kai yayi ya buɗe motar da sauri ya mata key ya fitar a hanyar

Saida suka hau kan hanya sosai sannan hanna ta waiga ta kalli bee “wata number kika bashi naji kince yina karamar waya”

“Number me zuwa yin mana aiki mana…wannan burgi birgin Hadizan ai da ita suka dace ɗan ghetto da bagidajiya”

Dafe kai hanna tayi “Haba me yasa zakiyi haka?”

“Ke kin isheni mana wai ina ruwan ki……………..


Hadiza da wakarta ta shigo gidan ƙafa butu butu anci dambe wajen roron diddigan itace da suke samowa in sunje siyan itace
Watsa itacen da ta rungume cikin hijabi tayi a kicin ta wuce ɗaki tana ƙunƙunai tana zare sartsen da itacen sukayi mata a hannu

Tana shiga uwardakin su taji waya na ringing haba batasan sanda ta saki ƙara ba “Ohhhhh na shiga uku ,yaushe nabar wayar nan ba a silent ba?” Kama gado tayi da sauri ta zura hannunta ta ciro wayar ,ta natse jar madannin tayi hanyar ƙofar gida da sauri ta ɗauka “Hello wanene”

Muryane yaji gazar gazar ba dadi,ba irin na bee ba classic

Hura iskar bakinta tayi a jikin gurun speaker wai ko itane bataji ,saboda taji ba ayi magana na

“Wai waye”

“Ammm ɗan ba mai wayar”

“Jar uban nan to waye mai wayar bayan Ni ? Malam ka ɓata Number ” ɗissss! Ta kashe wayar

Cigaba da kira yayi amma ta soke a zani batamasan yina kira ba

0um Aphnan
09065990265
(Wxp only ????????)
[10/8, 7:34 PM] baby na: ????GWAURO…????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button