HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

???? HASKEN RAYUWATA

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIE’S WRITER’S ASSOCIATED

PAGE 0️⃣1️⃣➡️0️⃣2️⃣

        Zaune suke kowanne riƙeda Alƙur'ani megirma yana kalla ɓangaren mata daban na maza daban kowanne akan benci sekuma wani malami dake zaune yana musu ƙarin karatu wata kyakyawar yarinya ce ta shigo fara sol da ita daka ganinta kaga jinin fulani sanye da dogon hijab har ƙasa bakinta ɗaukeda sallama ta nufi gaban malamin nasu ta duƙa seda tabari yakai aya sannan tace"Malam yace ka ƙarasa inyaso gobe ya shigo a period ɗinka".

“toh Monitor jeki zauna kibuɗa”.
“toh”.
nanta miƙe cikeda nutsuwa ta ƙarasa wani benci wanda wasu ƴammata wanda zasu iyayin sa’anin juna ta zauna ɗagowa sukai suka sakarma juna murmushi sannan suka maida hankalinsu kan ƙarin da ake musu na suratul Ma’idah bayan Malamin yagama biyawa shikaɗai sannan yabiya suka biya sannan ya rife Alƙur’anin yace”kucigaba da muraji’ah ina zuwa Monitor kiyimusu ƙarin halil masa’il”.
“toh”.
nanya fice wannan kyakyawar budurwar ce ta miƙe tare da zama samn bencin da suke kai cikin muryarta me daɗin sauraro ta shiga ƙaramusu harseda ta tabbatar sun iya sannan ta zauna tana zama ɗaya daga cikin ƴammatan nan tace”Hafsat kiɗan daɗa maimaitamana dan gaskiya nidai se a hankali kefa Bilkisu kin iya”.
“kema dai Zulaihat da neman magana kike kinsan dai nima ban iyaba”.
murmushi wannan kyakyawar budurwar tayi tare da cewa”kundai kuncika gajan haƙuri kunsan dai dole zan maimaita muku”.
“eh dai gwara ki maimaita mana yanzu tinkafin mutane suyi yawa gwara ki fara dana jikinki dan kullum haushi kike bamu inkika farawa wa’incan yaran ko Billy”.
“sosaima kuwa mudai a fara yimana yanzu”.
“toh sarakan rashin haƙuri ku buɗo inba yimuku nayiba bazaku barni na hutaba”.
nan suka buɗa ta ƙara musu har seda ta tabbatar sun iya sannan ta cigaba da yiwa mutane .

Tana gama musu sannan itama tashi maimaita wanda Malaminsu yayimata da safe shigowa Malamin yayi tare da kallon ƴan ajin gabaki ɗaya yace”ku karantomin ƙarin da Hafsat tayomuku inji”.
caraf wata yarinya wadda zata girmi Hafsat da kaɗan tace”Malam Jalaludeen daka tafi cewa tayi bazata biyamana ba”.
“wlh Malam ƙarya take Hafsat ta biyamana kedai Habibah kinshiga uku da hassada me Hafsat ta taremiki ne a makarantar nan da bakya sonta ne”.
cikin ɓacin rai Malam Jalaludeen ya dakatar da Bilkisu tare da kallon Habibah dake hararsu Hafsat yace”kewai wacce irin yarinya ce kene Habibah banason shashanci inkika sake se ranki ya ɓacin sakarai kawai ku biya muyi mutashi”.
“toh malam”.
nansuka biya itako Habibah se cika take tana batsewa bayan sungama biyawa ne M.Jalalcudeen yace”jibi in Allah yakaimu zamuyi masabaƙa ta class kowa ya shirya”.
“toh Allah yakaimu”.
“amin”.
nan yayimusu addu’ah suka shafa ya fita Bilkisu cetace”yafa kamata mu koyawa waccan jakar hankali ace hassada tayiwa mutum yawa “.
“wlh kuwa itafa tunda taga da ita kemana first class zuwan Hafsat ta kwace shikenan ta ɗauki karan tsana ta ɗoramata”.
dafa kafaɗunsu Hafsat tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace”haba ƙawayena ku kyaleta dan Allah sekace yau kuka saba ganin halin Habibah ni yanzuma sauri nake ƙilama Bappana yadawo ina nan”.
“aiko dai bazamu haƙuraba wannan karon domin naga alama inba koyamata hankali mukaiba bazatayiba ke koda yaushe seki wani cemu barta anƙiɗin”.
marai raice musu tayi kamar zatai kuka tare da cewa”dan Allah Zully Billy ku kyaleta Innallaahaa ma’assabirin a sannu itama idan taga tayi tayi bama kulata zata dawo ta hankaltu domin in mutum yana abu yaga baka kulashi yafi jin zafin abin bare ita da tun abin yarinta amma taƙi ta dena”.
“toh shikenan mun kyaleta a tawomana da tsarabar Bappah gobe kice muna yimasa sannu da zuwa”.
“yauwa ƙawayena gari insha Allahu za’ah tawomuku da ita zeji”.
taƙarasa zancenta cikeda murna nan suka fita domin su kaɗai dama suka rage a class ɗin suna fita suka nufi gida itakuma ta nufi titi.

Tana isa ta tarar da wata hayis saura maleji nanta hau suka nufi getso suna zuwa ta sauka a kwanar Ɗan Nafada taba memota nera talatin ɗinda Ummita tabata ta tsallaka titi cikeda nutsuwa take tafiya a labin nasu harta isa rugarsu wato Rumada tana isa ta taddasu Hanne zaune a dakalin gidansu suna ganinta suka tintsire da dariya haɗe da tafa hannu suka haɗa baki gurin cewa”ai dolema mutum ya rasa mashinshini ba tunda yasa karuwanci a gaba da sunan karatu ai mutum yana nan zaune zamuyi aurenmu shiko ko kare bama ze kalleshi da sunan soba bare harya aureshi andaiji kunya kaf rugar nan tamu babu me shekarun daya kai naka ko kunya bakƴaji”.
“kuma dai da wani zance kuke kaf rugar nan wakuke tinanin ze kwasarwa kansa alaƙaƙai da hankalinsa da komai bakujima wani zancen dake yawo bane ina jikan Malle dayazo daka birni ya nuna yanasonta beson dawan garinba yana zuwa gida ya faɗawa Malle itako cikin murna ta ɗauka wata yagani tacemasa ƴar waye nanyayi mata kwatance aiko tana gane kyalkyal banza yake nufi tace be isaba koya rasa mata duk duniya baze auromata alaƙaƙaiba aiko ta aika birni iyayensa sukazo tace kota mutu bata yafewa Babanshiba indai ya bari aka auromata ƴar bariki ai wannanfa batada wanda zezo ya aureta sede ta ƙare a ganta falfalarta ta mutu a haka”.
“wlh kuwa furera kinyi gaskiya sede a ƙare da yawon banzan da aka saba da gaskiyar Malle wlh bamuga laifintaba”.
suka ƙarashe zancensu da tattakewa da dariyar izgili Hafsat ko dama inda sabo tasaba da abubuwan da mutanen rugarsu ke mata dana gidansu jiki a sanyaye ta shige gidansu .

Tana shiga ta tadda matan gidansu zaune jikin bishiya ƙarasawa tayi har inda suke zazzaune tace”sannunku da hutawa Innah”.
“wannan yarinya da gulmarki tayi yawa tashi ki ɓacemana da gani kullum cikin hijabi waya sanima ƙila ankwasowa su Lantana abinda ake shukawa a birnin”.
“amma gaskiya Hali bakida mutunci kice ankwasowa su Mero da Iro jikadai amma ba niba “.
jiki a saluɓe ta nufi ɓangarensu tana shiga ta tadda Ummita na kunna turaren wuta ganin yanayin Hafsat kawai tayi tasan wani abu ya faru tsira turaren wutar tayi tare da faɗaɗa murmushinta tace”sannu da zuwa ɗiyar kirki waya taɓamun Autata”.
murmushin itama ta mayar mata tare da ƙarasawa ta rungumeta zama sukai a gefan katifa datasha gyara ta tuɓe hijab ɗinta tare da cewa”Ummita narasa menayiwa mutanen rugar nan da suka tsaneni kaf rugar nan daga ke se Bappina dasu Inna wuro ne kawai kukesona “.
taƙarasa zancenta tare da fashewa da matsanancin kuka rungumota Ummita tayi jikinta tashiga bubuga bayanta har tayi shiru kama hannuwanta Ummita tayi tare da cewa”haba Auta keda naketa farinciki yarinyata saura izuh biyu ta haɗe shine zaki tsaya har wani surutan wa’innan marasa ilimin yayi tasiri akanki baki cika burin mahaifiyarki dana mahaifinkiba na karatu dukda mu bamu saukeba ku muka tsaya tsayin daka dankuyi inda sabo ai yaci ace kunsaba da halin ƴan garinnan dan Allah Hafsa kamar yadda kike ƙoƙarin cire abu in anmiki kicigaba da daurewa bakya ganin Yayanki yadda ya toshe kunnenshi kike koyamasa kema kicire komai a ranki in Allah ya yarda sekinyi sanadiyyar yayewar duhun dake rayuwar mutanen rugar nan Auta kinji kedai kicigaba da ƙoƙari mukuma zamu cigaba da tayaku da addu’ah Allah yabada sa’ah kije ki amso abincinki kici mujira Bappinki”.
murmushin farinciki ta sakarwa Ummati tare da cewa”insha Allahu zancigaba da ƙoƙari kodan nacika muku burinku sukuma Allah ya shiryesu yasa su gane Ilimi shine HASKEN RAYUWA a kullum ina godema Allah daya bani iyayen da kowanne ɗa yake fatan yasamu kamarsu Allah yajada kwananku ina alfahari daku Ummita na”.
taƙarasa zancenta tare da rungume Ummita ƙara rungumeta Ummita tayi tace”muma muna alfahari daku Auta Allah yayimuku albarka tashi kiyi maza ki amso abincinki kici”.
“toh”.
nanta miƙe cikeda jindaɗi ta ninke hijab ɗinta ta saka a cikin adaka ta ɗauki wani iya guiwa ta zura ta nufi ɗakin Innah Lantana samun Isah tayi yana cin abinci daka bakin ƙofa ta tsaya cikeda ladabi tace”salamu alaikum”.
fitowa Lantana tayi daga ita se braziya da ɗaurin zane a dama batare data amsa sallamar da Hafsat tayiba tace”meyene kiketa dokamun sallama kamar nayi sata”.
“yah haƙuri Innah Lantana abincina nazo amsa”.
tsaki Innah Lantana tayi tare da yatsuna fuska tace”yau ban girka dakeba acan yawon dandin naki yau ba’ah bakiba kenan”.
kallon Hafsat yayi dake shirin juyawa yace”Innah zan ƙara abincin indashi”.
washe jajayen haƙoranta tayi da suka dafe tace”jeka ɗan albarka ka ƙaro abinka akwai”.
dariyar shaƙiyanci yayi yace”toh bara inƙaro”.
ba tare data damuba ta nufi ɗakin Ummita samunsu tayi zaune itada Yayanta Aminu kallonta Ummita tayi ganin ba kwano yasa tagane bata bataba tace”ɗauki hamsin a cikin kwaryar can kisiyo brodi gurin Haladu in ebarmiki miyar dana yiwa Bappinki ki dangwala”.
“ga hamsin inada ita kisiyo ƴar ƙanwata kici ki koyamun karatu kafin Bappi ya iso”.
“toh Yayah Aminu”.
taƙarasa tare da amsa ta tafi.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button