GWAURO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Awwwwn???? I will….. byeeeee” ta fice cikin tsantsan farinciki ba abu ɗaya da yike damunta a rayuwa
Nasreen tana shiga ɗaki sauya kayan jikinta tayi zuwa doguwar Abaya da yaki na farko yalwa ,mai masifar tsada daɓa² da kwalliyar stone ,ta cire ɗan kunnen gold ɗin da ke kunnenta ta ajiye akan Dressing mirror taje ta wanko fuskarta ta ɗauko haramain irin wanda maza suke rawani dashi ta ɗan yi rolling ta fesa turare ta saka plate cover shoe ,ta dauki car key ɗinta ƙirar KIA latest modern ta kullo ƙofarta ta nufi hanyar dakin mamansu
“Assalamu alaiki ya ummy ana zahibun ilal mustashfa”
“Assalamu alaikum mamana ,Inaso zanje asibiti”
Waigawa tayi ta kalleta a take taji tausayin yarinyar ya tsirga mata ina gayun Nasreen yake itace yau zata fita ba dan kunne kamar mai takaba!? Wani ƙwalla ne taji yina neman cika mata ido da sauri tai dodging tana nodding off
“Ma’assalama Ya habibty la taqnaɗiy lillah” (ok bye my love ,plz don’t give up) shikenan sai kin dawo masoyiyata karki karaya kinji”
Jinjina mata kai kawai tayi tana ƙoƙarin shanye kukan da yazo mata “Shikenan ya ummy” (Nagode mamata) ta juya ta fice da sauri, tana tunanin yanda tattaunawarsu zai kasance da likitar da aka bata labari mai bada shawara akan matsalar auratayya na matan aure da suke fama da matsala a gidajensu da wanda suka rasa mazajensu (zawrawa) da en mata da suka rasa samarinsu suna neman su dawo da soyayyar su………………..✍????
LITTAFIN KUƊINE , 500₦ REGULAR GROUP ,MASU SON VIP GROUP 1000₦ ,MASU SON SPECIAL 2000₦
ZAKI BIYA TA BANK ƊINA 7782217014 , MOHAMMED HASSANA,FCMB, SHAIDAR BIYA TA 09065990265
KO KATIN MTN TA 09065990265
ƳAN NIGER KATIN ARTEL ,KUMA REGULAR 500F ,VIP 1000F ,SPECIAL 2000F
Oum Aphnan
[10/8, 7:34 PM] baby na: ????GWAURO…????
*003*
Immaculate
Cikin slow motion farar venzan ta shiga ma’adanan ajiyar motocin wajen, en matane en makaranta su biyu a cikin motar kyawawan gaske wanda kyau ya gauraya da Hutu da naira ya sasu zama classic babes.
Tunda sukayi parking Bee ke Kallon Hanna dake shafa iphone 13 ɗin ta tana ɗan murmushi basai an gaya maka chatting take mai dadi ba.
“Hanna shiga ki mana order kawai ina jiranki a nan”
Kyakkyawa Black beautyn da aka kira da Hanna ce ta ɗan kalli na gefen tata sannan ta ɗan cuno baki
“Haba ƙawata mu shiga tare mana ,Ni wallahi kunyar shiga Ni kaɗai nike”
Hassala tayi ta daki sitiyarin motar ta hayayyaƙo mata da fitina “To saboda mene ke sai kiyi tayin abu kamar wata er ƙauye ,a haka kuma wai kike karantan civil law wacce wataran zata fita gaban kotu ta wakilci client ɗin ta gaskiya ki koma Home management kawai….to waima dakata mai kika mai dani in driving ɗinki kina huce in kawoki eatry kuma inje in maki order naxama er aikinki kenan”
Ajiye wayar tayi akan laps ɗin ta sannan ta saki murmushi wanda yasa dimple dinta loɓawa a hankali
“Ƙawata Calm down ,me yayi zafi shi ba wuta ba…” Buɗe baki tayi zatayi magana kawai sai ta ɗauke wuta saboda hango Nurain saye da T_shirt ɗin ma’aikatan gurin an rubuta sunan gurin cin abincin da logo a daga gaba .
Dafe kai Bee tayi kamar xata fashe da kuka itakuma a ɗayan gefen fara’ar Hanna ƙaruwa yayi ,ta ɗan zungureta da wayar hannunta “Ƙawata kinga gayen da nike baki labari nan ,sam bai kama da en Nigeria ba”
Tsaki taja daidai sanda yazo gefen bee ya tsaya “Hey damsel ” wani ɗauke kai bee tayi tanajin idonta na kawo ruwa don takaici ta rasa me yasa wannan faƙirin talakan ke nace mata
“Queen bee ,yau kune a eatry ɗin mu…Ina tsakiya da tunanin inda zan sake arba da kyakyawar fuskarki ma’abociyar kyau da tsari kawai sai na hango plate number ɗinki an rubuta queen bee ,nace wow amazing sunan ya dace da mamallakiyar motar kwatsaham ashe kece a eatry ɗin namu….” Katsesa tayi da hargowa ” hey kaga dakata eatry ɗinku ? Are You not a common Waiter here?”
Lanƙwashe kai yayi kamar zai kuka sannan yayi magana relunctantly “Yes I am”
“Then kaga nayi kalar type ɗin ka da zaka ringa nace mun ? Gaskiya ka cuce Ni wallahi ban yafe ba” kawai sai ta fara alamar kuka
Gabaɗaya birkicewa yayi “plx ki saurareni Bee ba laifina bane sonki ne ” tsawa ta daka masa, ta fara aniyar Takeshi da motar da dama bata kashe ba, da sauri ya ja da baya ,itakuma ta ja muguwar tsaki “wowowowo ba laifina bane sonki ne(ta kwaikwayi maganarsa) mtsewww foolish banza mai kama da pig in ma don farar fatan shine ni sam bai burgeni ba ƙunatacce maye aita wulaƙantaka kana nace”
Hanna ji tayi kamar ta shaƙe queen bee SABODA wulakancin da tayiwa crush dinta da take mugun so ashe wai shi aminiyarta ma yike yayi
Abincin da basuci ba kenan suka wuce gida
Upk ne mai kyau baban Bee ya kama mata akwai komai a ciki na more rayuwa tamkar gidan wata matar auren ,tana kiran Hadiza tana mata gyaran gida duk bayan kwana biyu ,tana biyanta,amma fa ba tare da sanin Hajiya ba Hadiza take zuwa wannan aikin
Yauma haka ta kasance tana maƙale cikin uwarɗaki tana tunanin hanyar da zataje ta roƙi Nurain ya yafe mata sai taji wayarta rakani toilet na tsukku cikin silin saman ɗakin Hajiya .
Sosai vibration ɗin wayar ke daɗa tayar mata da hankali gashi an ƙi daina kira ,tana tsoron kar Hajiya ta farga tana da waya ,da sauri ta miƙe ta taka gadon Hajiya mai rumfa ta haye saman ,ta sa hannu ta ciro huji ɗaya na silin ɗin da dama ta ciroshi tanan take ɓoye wayar in ta saka ta rufe .
A hankali ta zaro ,wani siririn tsaki taja ganin Number Anty bee ne ,sakkowa tayi a hankali ta suri buta ta wuce toilet da gudu daidai nan ta sake kira
“Hello Anty bilki”
“Mtseww useless bee …. bee …stop calling me bilki ok?”
“To Anty bee????”
Hadiza ta faɗa cikin ladabi kamar Mutuniyar ƙwarai
“Kinajina gidana yayi datti kuma munason sakon kasuwa kizo yanzu”
Rau rau rau idonta ya kawo ruwa gabanta ya fadi ,a ƙasa² tace “Na shiga uku ,Anty nayi ma wani laifi wallahi ana ƙumi na ,ina fita zane ni za’ayi”
Cikin hargowa tace “And so? bazaki zo bane in nema wata?” Bakinta na rawa tace “zanzo zanzo”
Tsaki ta kuma ja “na baki 30minutes” ta kashe wayar ,a hankali Hadiza tabi wayan da kallo gashidai tana neman kudi gashi kuma tayi tsokanar fada yaya kenan?
“Ke Hadiza zama bata ganki ba,tashi kije gurin salame basakkwata kice ta roki danta ya yi hakuri ya kyaleki ba’a sanyin jiki da neman kuɗi” tana kaiwa nan a tunaninta ta ,soka wayarta cikin zani ta fito tana wanke ƙafa
Wani yamutsatsen hijabinta ta zaro cikin akwatin ƙarfenta da ta dawo dashi daga boarding ,leƙawa shirayi tayi taga Hajiya na kwance shirim a katifa tana barci aikuwa sanɗa ta fara yi zata fice ,ba zato ta ce “ke! ke!! Kinci gidanku ina zaki”
Zuwa tayi ɗan nesa kaɗan daga ita ta lanƙwashe ƙafa “Hajiya bakida saƙo ne?” Salati Hajiya ta rafka yanda kasan anyi mutuwa ,sai kuma ta gimtse fuska ,tana wulla mata harara “to ban dashi”
“Taf aikuwa hajiya wallahi sai kin yi shi Ni na gaji da zama a gida sai kace ƙonanniya ,ai al’umma rahama ne…”
Banza ta mata ta juya ta gyara kwanciya
“Hajiya nifa in bakida saƙon nan zan fita ba nisa zanba iyakata gidan basakkwata gwara in je da kaina innemi yafiya kafin ya nakasa banza don na lura ke abun dadi ma ya Maki” shiru Hajiya tayi mata aikuwa ta mike ta kwashe takalminta a hannu ta danna da gudu ,karan gudun ya ankarar da Hajiya ,buɗe maƙoshi tayi tana kwarara mata kira Amma inaaa ta samfe.