GWAURO COMPLETE HAUSA NOVEL

GWAURO COMPLETE HAUSA NOVEL

To Ni duk ba wanann yike mun ciwo ba ,bata bani dan madaran nan insha tea sai tace madara da sugar dinta na masu diabetics ne (masu ciwon siga) bazan shaba ,kullum inta jika gero inashan kunu da mazarkwaila ,da rana a hadani da katta kafura Ita kuwa kaga yaushe rabonmu da sallar layya? Ba wata shida ba,to naman layyanta nanan tayi masa suya ƙau ƙau kamar gawayi wai saboda kar ya lalace ,kuma a haka fa ɓoyeshi tayi saboda kar inci saidai kullum ta watsa a saman abincin da zataci ta hada da coslow mai daɗi yaji salad cream haka zataci Ni Ko ohooo ,wallahi na gaji gidan mu zan koma nasani sarai malamin mu yace mu masu ƙuruciya mukafi bukatar abinci mai gina jiki ba itaba gawa taƙi rami …..”

“To naji yanzu duk mai ya kawo maganar nan?”

“Fruit ne su baba Ado suka kawo ta shaƙe fridge dashi ta kulle da kwado tayi pillow da ɗan mukullin kuma inason sha ta hanani”

“Barci take?” Daga mata kai tayi alamar Eh

Kunnenta ya kama ya rada mata magana kawai sai ta zaro ido “Aah halim “

“Ke dai kawai sa ido”

Shiga ɗakin yayi saɗaf saɗaf ba tsoro ya kama kanta ya ɗage sama a hankali ,ya mata sigina da ido aikuwa tazo ta saka hannu ta zare mukullin ta falla da gudu ,juyi hajiya tayi jin an aje mata kai gwaraff

Wangale ido tayi a furgice ganin inuwar mutun a take bakinta ya kama rawa duk zatonta mala’ikan zare rai ne

“To bana sa’i yayi? Ash_hadu an laaa ha’ila ha ilalahu…” Kawai sai ta fashe da kuka tana rokonsa ya zare ranta a hankali” dariya halim ya bushe dashi

“Hajjaju makkatun nine fa”

Daɗa gwagwale idon ta ringayi da tsakiyar baƙin idon ya danyi haske kamar na hakiya “Kaine wa ,ciwo da tsufa ya cinya idon”

Dariyar en China Hadiza ta bushe dashi “Hajiya halim ne” juyi tayi ta miƙe zaune “Ai Halim??? Kaci gidanku halim Bello ka razana bani ba”

Dariya suka fashe dashi ko a jikinsu basu damu da masifarta ba “Hajiya an shaƙo ƙamshin lahira ta ganka da jallabiya ta zata azara’ilu ne????”

Miƙa hannu tayi zata dauko dorinar da take ajiyewa na dukan jikokin ,suka kuwa fita da gudu suka bar mata gidan gabaɗaya suna dariya

Saida sukayi nisa da gida sannan suka tsaya a gefen wani shagon aski suna dariya “Kinga yanzu mukulli na hannunki duk nema karki fito dashi ,ki bari sai ta zagaya ban daki ko tana wannan dogayen sallan nata ki sadada ko debi rabonki haka har su ƙare…” Miƙa masa hannu tayi suka tafa

“Kai halim abokin arziki Inshaalh innayi kudi kai zan fara kaiwa Makka”

“Kinji gaɓuwa nida nike namiji bance zanyi kudi In kaiki makka bane sai ke zakiyi wani magana dallah rufe mana baki…” Buɗe baki tayi za tayi mai da masa martani wayarta ya fara neman agaji

Dasauri ta kwakuloshi cikin zani ,sai kuma ta fashe da dariya tana nuna ma halin ɗin

“Halim jibi wani ɗan wahala kullum kira nace masa wrong number Amma yaki ji Ni nama daina ɗauka “

“Ɗauka muji” shiru tayi kamar bazata daukaba kafin kuma ta danna koren madannin

“Hello waikai ɗan damfara ne ko ɗan yankan kai ? Eye kayi shiru ko kidnapping dina kake son yi? To wallahi gwara ka nema wata don ko kun kamani gajiya da ciyar dani zakuyi ku sakeni ba mai karɓoni…” Shiru nuru yayi yina sauraron Muryar daya ta cikin wayarsa daya ta wajen shagon askin da yake

Da sauri ya fito don ya tabbatar da zarginsa ,aikuwa Hadiza ya gani tana bubbuda ƙafa kamar mai shirin dambe tana ihu ma wayar kunnenta

A tsorace yace “Hello”

“Kaji ɗan ƙusar uwa da bakajina ne??” Da sauri Nuru ya karasa gabanta bata ankare ba sai dai ya warce wayar a hannunta ,ya duba Number tabbas numbersa ne

Da sauri ya nemi wani ɗan dutse ya zaune dafe da kai ya rasa tunanin me ma zaiyi

“Ha’ahhh malaminsu ɗan bani wayata ko?” A sanyaye ya kashe wayarsa ya yafitota da hannu “zo ki karɓar” turo baki tayi

“Iyeeh dama kana ƙumina wato inzo ka zalunceni naƙi wayon bare ma naga ka soma zama ɗan gaye cikin kwanakin nan” Murmushine ya ƙwace masa abinda bai taba shiga tsakaninsu ba

“Ba dukanki zan ba kawai dai nine nike kiran wayarki kina cemun dan kidnapper ,shine na tabbatar da zargina ke dince zo amshi wayarki”

Jikinta dan sanyi yayi “To wa ya baka Number na ko kawai ka ganshi a wayarka ne?”

“Baki santa ba wata Bee ne ta bani a matsayin numberta ” dafe gefen goshi tayi alamar tunani

“Bee!…bee…!! Ohooo na tuna badai Anty bee ba?”

“Kin san wata Anty bee ce?”
“Eh wata er gayuce har ma tana da mota ,ina zuwa mata aiki da saƙo tana biyana….” Da sauri kuma ta rufe bakinta da hannu tana kallon halim da Nuru a tare

“Don Allah karka fadawa Hajiya wallahi batasan ina zuwa ba”

Cikin zumudi ya tashi yamatsa gabanta jikinsa har rawa yike “Ya kamanninta yike? Wallahi ba wanda zan fada mawa i promise “

“To malami ɗan jirga baya mana kana shige mun kamar wani dan iska” matsawa yayi kaɗan ba tareda ya damu da zagin cusa haushin da ta masa ba

Nan ta fara zayyana masa kamanninta . Murmushi yayi gamida mata thumb up “wallahi itace kuwa amma me yasa ta bani numberki?”

“Ohon muku kai me ya kaika tataro wacce tafi ƙarfin ka ai gashinan ka wulaƙanta”

Kallon Halim Yayi da tundazu bai saka masu baki ba ,sannan ya danyi jimmmmm kafin yace “Hadiza kike ko?” Jinjina masa kai tayi “Eh Hadizan Hajiya sai dubu ta taru”

“Yawwa Plz zamu hada colliding dake waccan Anty bee ɗin taki sonta nike amma ga alama bata sona,zamuyi wani abu don ta gani ko Allah zaisa hankalinta ya dawo kaina ,karki damu akwai biya!!! Zan baki kudin fiye da wanda take baki”

“Uhum uhum nuru ku fa gayune ba ko sisi”

“Eh naji zan biya dai wai ba ni nace ba ko tamabayata kikayi?”

“To yanzu yanzu zaka bani ka yarda?” Gyada mata kai yayi a take ya zaro miƙaƙun en 1k guda biyar a Aljihun bayan wandon jeans ɗin sa ya miƙa mata

Kasa karba tayi tana jin tantama a kansa

“Kai nuru nidai inajin tsoron karɓar kudinka karka iskan ta ni ,fara fada me zan maka tukun”

Murmushi yayi ɓaro ɓaro ɗin ta yina bashi mamaki

To … To shknn inaso mu fara soyayya Ni dake ina Nufin soyayyar ƙarya ……….✍????
[10/8, 7:35 PM] baby na: ????GWAURO…????

              *007...*

Kamar yanda na faɗa bazan daɗe ina free page ba ,a ko yaushe na kyauta zai iya ƙarewa….masu biya suna ta biya purchase via 7782217014, Mohammad hassana, fcmb shaidar biya ta nan 09065990265

Zaro duk idonta tayi waje “So me? Ban gane ba ,Au Nuru iskancin naka bana ta kaina ya biyo ƙwaila na dani” ba Nuru ba harta Halim saida ya fashe da dariya ina kurin dijen yake ? Gabaɗaya ta furgice kamar ance ta zo su shiga halaka

“Haba come on! ba wani abu bane ai ke din babbar yarinya ce da kin sama kula kawai dai goyon kaka ne da tashi a gaban tsoffi yasa kike ganin ke ƙwailace “

“To shikenan duk abunda za’a ce ace amma wannan abun yafi karfin Hadiza” ta wuce fuuuu ta bar halim da Nuru a tsaye…..

Kallon juna sukayi Nuru cikin kissa ya langaɓar da kai sak kalar tausayi Halim da baisan wanene Nuru ba a take yaji tausayinsa ya tsirgan masa

“Kayi hakuri bro zan tayaka shawo kanta” miƙa masa hannu yayi kamar wani sa’an shi suka gaisa

“Dako ka kyauta kai Nagode ” suka yi sallama Halim yina yabon kyawun halitta da saukin halin Nuru shi kuma Nuru yina tunanin hanyar da zaibi ya shawo kan Bee ta hanyar amfani da Hadiza


Nasmah Daga gida kamar yanda sukayi da ummanta zataje lunch tlda ƙawayenta ba haka abin yake ba
Wani shahararren Hotel taje inda suka shirya zasu haɗu da wani mawaki da ya mata alkawarin koya mata waka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button