Uncategorized

HALIN GIRMA 1-5


HALIN GIRMA Hausa Novel

(1)

 

09134848107

 

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽

#team zafafa biyar

 

 

(1)

 

***Komai na rayuwa na tafiya ne bisa tsari da kudurar ubangiji,
komai ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin kaddarar sa, Wala kaddara
mai kyau ko kuma akasin ta. Yarda da Kaddara me kyau ko mara kyau na cikin
Imani!

 

   A tsaye take gaban sink din cikin toilet din tana
wanke kananan kayan da ya kasance mallakin Maama da Zeenat, lokaci zuwa lokaci
tana cire hannun ta tana yarfe shi saboda sanyin da ake zugawa kasancewar
karshen December ne a lokacin da ake zuga sanyi. Dauraye kayan tayi ta yi
saurin fitowa ganin haske ya hudo ta window din toilet din. Karfe shida da rabi
agogon falon ya nuna, tayi saurin karasawa kitchen din domin dora abin karin
kumallo kafin ahalin gidan su tashi.

  Tun kafin asubah take fara ayyukan gidan wani lokacin
har karfe tara na safe bata kamalla wa, duk kuwa da tana iyakar kokarin ganin
bata wuce taran ba saboda karatun ta na islamiya da take zuwa duk weekend, tana
ganin shine kadai gatan da zata yi wa rayuwar ta a halin da take ciki a gidan
mahaifin ta. Bata fatan wani ya shiga irin rayuwar da take ta kunci da tsantsar
makirci, babu wanda ya san halin da take ciki balle ya kawo mata dauki, bata
isa ta bud’e baki ba saboda kowa ganin kirki da karamcin Maman yake, mace ce me
masifar kirki, me haba haba da saka duk wani abu nata gaba da na duk sauran
yayanta a idon ahalin gidan,a badini kuwa bata da maraba da bola.

   Kowa kallon mara dadin zama yake mata ko kuma
mara godiyar Allah saboda rashin walwalar da take fama da har ya shafi kaso
mafi rinjaye na rayuwar ta, zaka dauka bata dariya ko doguwar magana sai dai
bata da sukunin yin kamar sauran yan matan gidan nasu.

  Kowa kallon wadda tayi sa’ar uwar riko yake mata, ayi ta
sakawa Maman albarka da yabo a gabanta tana amshewa amma a bayan idon mutane!
Bakar wahalar da take sha ba zata misaltu ba.

   Da tunanin ta kammala aikin ta dauraye hannayen
ta sannan ta fito ta jera musu a saman dining ta dauko nata a dan plate ta wuce
zuwa dakin su.

 

   Bude kofar da tayi ya farkar da Zeenat, a zafafe
ta dago ta watsa mata kallon banza gami da jan d’an karamin tsaki tana sake
rufe kanta da katon duvet din da take kanannade a cikin sa. Cikin nutsuwarta ta
karasa shigowa d’akin tana dora plate din saman d’an madaidaicin mudubin dake
cike da kayan shafe-shafe ta soma gyara wajen data tashi. Katifar ta fara
daukewa ta kaita chan store sannan ta dawo ta share dakin a hankali gudun
magana taci abincin a tsaitsaye ganin lokaci na neman kurewa tayi saurin watsa
ruwa a gaggauce ta fito.

  Dogon hijabin ta ash colour daya kasance a matsayin
uniform din islamiyar tasu ta saka bayan ta gama shiryawa ta dau yar
madaidaiciyar jakarta me dauke da Al-kurani me girma da sauran littafan addini
ta fito.

   Habib na zaune saman dining da alamun zaman sa
kenan ta gaishe shi a nutse sannan tayi masa sallama ta wuce islamiyyar dake
chan kasan layin su inda take zuwa duk asabar da lahadi da safe sai sauran
ranakun da yamma amma banda juma’ah.

  

  

 

   *Babban gida ne irin wanda zaka kirashi da Family
house, bangarori ne da dama a ciki wanda yake dauke da gidaje guda shida dake
kunshe da mutane cikin su suna rayuwa irin wadda suka zaba ma kansu. Duk da
kowanne bangare na da tsarin da yake tafiyar da rayuwar sa akai amma kuma suna
tafiya ne da ra’ayoyin juna, daya baya taba zartar da hukunci be sanar da daya
ba, sannan duk abinda suka zartar din dole ne ya samu amincewar mahaifiyar su
Hajiya Fatima wadda suke kira da Gaji.

   Gidan ta ne a tsakiya in da sauran gidajen ke
kewaye da ita, galibin yan matan family din suna tattare ne a shashen nata da
ya zama tamkar matattarar su, yanayin haihuwa a family din na tafiya ne kusa da
kusa, inda zaka samu yawanci sa’oin juna a kowanne gida.

  Duk da basu da tarin dukiya irin me yawan nan amma suna
da rufin asiri daidai gwargwado, sannan ana damawa dasu a duk bangarorin ilimi
na Islama dana bokon hakan ma bangaren kasuwanci da siyasa duk babu wanda basa
tabawa.

   Zamu iya cewa kowanne a cikin yayan Gajin yayi
sa’ar abokiyar zama ta kwarai dan babu wanda yake kuka da abokiyar zaman sa,
daidai gwargwado suna zaman su lafiya suna kuma mutunta juna suna girmana Gaji
da duk wata bukatar ta.

   Muguwar mace me kinibibi da kissa zai yi wuya ka
gane alkiblar ta farat daya, komai su kayi daidai ne suna kuma da kokarin
kyautatawa kowa, suna kokarin boye aibun su suyi amfani da hakan wajen
muzgunawa wanda basu so, idan yayi korafi a bashi rashin gaskiya saboda kirkin
su.

   Alhaji Muktar shine Babban dan Hajiya Gaji bayan
Babbar Yayar su mace da suke kira da Hajiya Babba dake zaune a Sheffield dake
birnin London tare da family dinta , sai me bi masa Dr Ibrahim, sai Abba Usman
sai Abba Musa sai dan auta Abba Kabir.

   Dr Ibrahim dan boko ne sosai dan har ya kai
matakin associate professor in da yake lecturing a halin yanzu. Matar sa daya
ta aure Maama wanda zamu iya cewa kaf family din babu wanda baya kaunar ta
saboda kirkin ta. Yaranta uku da Dr, Habib ne Babba, sai Zeenat sai karamin
kanin su Marwan. Sai dai shi yana da ya daya daban wadda suke haifa da matar da
ya aura a lokacin da yaje karatun sa na Masters a University of Michigan, anan
suka hadu har sukayi aure suka haifi ya daya me sunan Gaji (Fatima-Iman) a
lokacin ne kuma suka rabu saboda wata babbar matsala da ta taso tsakanin shi da
family dinta, dan dama basa son auren, yana ji yana gani ya rabu da ita, ya
dawo gida. Fatima na yin wayo suka kawo masa ita inda ya dauki rikon ta ya
damka a hannun Maama wanda a lokacin take goyon Zeenat itama. Bata taba nuna
masa komai ba ko a fuska kuma be taba ganin wani banbanci tsakanin Fatima da
Zeenat ba, shiyasa ya kara bata mazauni me girma a zuciyar sa.

 

***Daidai layin su ta hangi Zeenat tsaye da Bashir, dan dam taji
a zuciyar ta kasancewar ba wannan ne karo na farko ba, duk wanda yace yana son
ta in sha Allah ba za’a dau lokaci ba zata same shi tare da Zeenat shikenan
kuma ta ta maganar ta sha ruwa. Zeenat yar uwarta ce amma duk da haka tana jin
babu dadi, sai dai bata bar hakan yayi tasiri a zuciyar ta ba, ta dau hakan a
matsayin wata jarrabawar rayuwar ta. Daidai in da suke tsaye tazo zata wuce
Zeenat din ta kira sunan ta

 

“Iman!” Tsayawa tayi chak, ta kalle su kad’an sannan
tace

 

“Sannun ku.”

 

Murmushi Bashir din yayi mata sannan yace

 

“Malamar islamiyya, sannu da zuwa.”

 

Bata amsa masa ba dan yadda yayi maganar taji akwai alamun
rainin wayo

 

“Ya akayi?” Tace tana kallon Zeenat.

 

“Babu!” Ta dage kafadar ta.

 

“Ok!” Tace tana cigaba da tafiyar ta, tana jin sanda
suka kwashe da dariya, ta dan ji babu dadi a ranta amma ta danne, ta karasa
gidan duk ranta babu dadi. Da gaske ta ji zuciyar ta, ta amince da Bashir
farkon magana da yayi mata har tana addu’ar Allah ya tabbatar mata dashi, sai
gashi tun ba’a je ko ina ba, ya koma wajen Zeenat wadda ko da ace da wasa yaje
wajen Zeenat din toh babu ita babu shi har abadah.

  

A gate taci karo da Maryam, a kalla ba kamar sauran ba, Maryam
ta fuskance ta, shiyasa tasu tazo daya sosai, duk da ba wata doguwar hiraa ce
ke hada su ba amma ta kan sake da ita fiye da kowa. Bikin su za’a yi su hudu a
gidan. Maryam din sai Bilkisu, Aysha da Amina. Daga su sai ita da Zeenat da yar
gidan Abba Musa Rabi’ah sune a layi, duk cikin su babu wanda bashi da me son
shi amma banda ita da ta gagara samun wanda ma zai tsaya din.

    Bangaren Gajin suka
wuce tana mata hira akan shirye shiryen bikin, rabin hankalin ta baya kan
Maryam din har suka karasa, suna shiga ana kiran sallar magriba sai kawai suka
wuce sukayi alwala.

   Bayan sun idar ne Gaji
ta kalle su tana kan abun sallah kamar zatayi magana sai kuma ta fasa. Sai da
ta gama ta tashi sannan tace

 

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button