HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6-10


*HALIN GIRMA*

 

  6

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107* 

 

_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR
FAMILY💯💯🙌ðŸ
½â¤ï¸_

 

_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA
KUMA BAR ZUMUNCI_

 

_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR
YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN
ALKUR’ANI MA GIRMA_

 

_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA
KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A
TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN
GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE
KWARAI💯🙌ðŸ
½â¤ï¸_

 

_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_

 

https://youtube.com/c/sudaiskura

 

_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy
Qur’an at a very young age._

 

_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and
liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairanðŸ™
ðŸ»_

 

***

Girgiza kai ya hau yi da sauri da sauri.

 

“Habib aiki na, innalillah wa inna ilaihi rajiun.”

 

“Me ya samu aikin naka?” Mama ta matso da sauri tana
rik’e shi

 

“Wai sun dakatar dani, babu wani kwakkwaran bayani kawai
wai daga sama ne.”

 

“Innalillah wa inna ilaihi rajiun, zo ka zauna, rik’e shi
Habib ya zauna.”

 

Zaunar dashi Habib yayi, yayi saurin dauko masa ruwa ya mik’a
masa

 

“Sha ko zaka ji sauki a zuciyar ka, ba wani abu bane babba
in sha Allah, wata yar matsala ce zasu gyara da yardar Allah.”

 

Jujjuya kansa yake ya kasa magana, shi kadai yasan hakan me yake
nufi, shi kadai yasan yadda yake ji a halin yanzu, tabbas idan suka hana mishi
aikin nan sun yi masifar cutar sa, akan me? Me yayi haka da ya chanchanci
wannan hukuncin? Bayan irin kokarin da yake ganin ya rik’e aikin sa, tsawon
lokacin da ya dauka kafin ya samu aikin, da irin wahalar da yasha kafin ya kawo
matsayin da yake, sai yanzu? Daga sama ta ka kawai ace an dakatar dashi?
Innalillah wa inna ilaihi rajiun. Ya sake maimaitawa.

 

“Kalle ni nan Khalil, karka ce zaka daga hankalin ka akan
abinda kasan baka da iko dashi, kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka, in sha
Allah ba wata matsala bace, kaji?”

 

Gid’a mata kai yayi kamar karamin yaro, ya kwantar da kansa yana
jin kamar ya zubar da hawaye saboda bacin rai. Shiru sukayi kowa yana jimamin
abinda ya faru, ya ma manta da abinda yake shirin aikatawa. Shigowa Zeenat tayi
dauke da wasu manyan ledoji,uwar ta bita da kallo bata ce komai ba.

 

“Daga ina kike?” Habib yace yana bin hannun ta da
kallo

 

“Bashir ne yazo.”

 

Kallon Mama yayi, yaga ta dauke kanta

 

“Mama fa Bashir din nan naji wasu maganganu akan sa marasa
dadi, ya kamata a duba sosai kafin a barta tana fita wajen sa.”

 

“Bana son maganar nan yanzu, dame zamu ji? Da abinda ya
faru da Khalil din ko da naka zancen?”

 

Tsuke bakin sa yayi be sake cewa komai ba, ya tashi ya bar falon
ma,

 

“Me ya samu Uncle Khaly din Mama?”

 

“Babu komai, ki wuce ki bani waje uwar yan magana.”

 

Da sauri tayi gaba da ledojin ta, ta shige dakin uwar ta rakata
da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya tana tuna abinda ya faru daren jiya ita
da Abban su.

 

***

“Ya ake ciki da yaran nan?”

 

“Name fa?”

 

“Akan maganar yaran da suke zuwa wajen su, Yaya yayi min
magana akai yace ya kamata asan abinda ake ciki, kindai san tsarin gidan nan
ba’a wani daukar dogon lokaci ana zance.”

 

“Eh toh, ita Iman akwai wani wanda yazo.”

 

“Zuwan sa biyu kamar ko?”

 

“Ashe ka sani?”

 

“Eh ina sane da komai ai, kinga alamun zasu dai-dai ta ne?
Naga zuwan nasa biyu dududu.”

 

“Toh idan bashi ba waye? Babu kowa ai.”

 

“Khalil din fa?” Yace yana mata kallon mamaki

 

“Wai Dr bar maganar Khalil din nan, ba da gaske yake ba
wallahi.”

 

“Ana wasa a maganar aure ne Hajara?”

 

“Shi dai yayi, gwara a tsayar da magana akan wanda yazo din
dan da alama ba da wasa yazo ba.”

 

“Toh shikenan, Zeenatu fa?”

 

“Eh ita ai Bashir ne dama.”

 

Tashi yayi tsaye yana girgiza kansa

 

“Ban yarda ba sam, ban amince da yaron ba, binciken da nayi
akansa be min dadi ba, kamar ance min ma kuma yana da mata duk da hakan ba zai
hana a bashi aure ba, sai dai na samu labarin bashi da hali me kyau gaskiya, a
wani labarin ma ance min har zaman prison yayi, sai ki fad’a mata nace banda
Bashir ta kawo wani.”

 

Hankalin ta a tashe tace

 

” Amma baka ganin sharri akayi masa? Don a hana a
bashi?”

 

” Akan me za’a masa sharri? Akan wanne dalili kenan?”

 

Ya tsare ta da idanun sa, sunkuyar da kanta tayi bata ce komai
ba, tsoron yadda za’a kwashe da Zeenat din take domin ta san yadda ta saka
Bashir din a ranta, gashi babu laifi yana mata hidima sosai, hakan ya saka
Maman sake yarda dashi da yar ta ta.

 

“Bari na shiga ciki Anty.” Khalil yace yana mikewa, ta
daga masa kai kawai ya wuce ya barta tana cigaba da tunanin yadda zata bullowa
al’amuran.

 

***Tana zaune a falon Gajin tana tunanin abinda ya faru tsakanin
shi da Uncle Khalil, wayarta dake saman cinyarta tayi kara, ta kalli wayar
ganin bakuwar number ya saka ta tashi, ta wuce zuwa bedroom din Gajin ta daga
tana zama a gefen gadon ta

 

“Assalamu alaikum.” Tayi sallama cikin muryarta da
tafi komai tafiya dashi, lumshe idon sa yayi ya bud’e a hankali ya amsa
sallamar ta ta

 

“Wa alaikisalam…”

 

“Ina wuni?” Ta gaishe shi jin muryar sa

 

“Lafiya lou Mi Love, na barki lafiya?”

 

“Alhamdulillah.” Tace a kunyace ganin shi kai tsaye
yake maganar sa.

 

” Kina jina Zahraaah na? “

 

” Na’am?” Tace tana mike kafafunta

 

” A zahirin gaskiya ba da wasa nazo ba, da gaske nazo neman
auren ki ba kuma naso a dauki wani dogon lokaci in sha Allah, ni din dai ba
wani bane kin dai ganni, bawan Allah ne me neman amincewar Fatima Zahra, ina
fatan zaki bani dama dan Allah!”

 

” Hmm…” Ta sauke ajiyar zuciya maganganun sa na taba
ta, me zata ce toh? Da gaske take jin ya kwanta mata duk da taga alamun ba wani
shi nne dashi ba, amma sai taji yadda yake abu kai tsaye ya birgeta sosai, babu
karya straight kawai yake maganar sa, bayan haka da gaske take son matsawa daga
wajen Mama, ko ba komai ta samu yanci itama.

 

“Baki ce komai ba?”

 

“Allah ya shige mana gaba, Allah ya zaba mana abinda zai
zamar mana alkhairi gaba daya.”

 

Wani irin dadi yaji ya shige shi, ya rufe idon sa, ya dau yan
sakanni yana jin sonta na sake ruruwa a zuciyar ta, yana tuna tsawon lokacin da
ya dauka yana dakon soyayyar ta, a lokacin da shi kansa be san me ake nufi da
so din ba.

  Mahaifiyar sa ‘ya ce ga sarkin Kano kuma shi jika ne a
gidan, hakan ya saka yake da alaka me karfi da garin na Kano duk da mahaifin sa
da mahaifar sa Adamawa-Yola ne, rayuwar sa bayan ya tasa yayi ta ne tsakanin
Kano da Adamawa, shiyasa babu in da be sanin a Kanon ba, yake kuma jin kamar
yafi zama comfortably a Kanon, musamman da bashi da son hayaniya sosai sai nan
din yafi zamar masa peaceful wajen hutawar sa.

   Akwai ranar da ya fito shi da abokin sa Musaddik,
suna tafe a mota hanya ta biyo dasu ta area din su Fatima, a lokacin ya ganta
duk da lokacin ba ta kai yanzu ba, be kuma taba jin abinda yaji akanta, shiyasa
ya nace a lokacin suka yi ta bin ta har suka ga gidansu, suka kuma yi tambaya
akan ta da komai. A lokacin yaso ya shigo da karfin sa, sai dai wani labari da
ya samu ya sauya masa tunani da shawara, ya kuma yanke ma kansa shawarar da
yake ganin itace zata daga masa darajar ta, a ranar da gaskiya ta bayyana.

  Musaddik be aminta da shawarar ba duba da gidajen da
Muhammad din ya fito, amma haka ya kafe akan bakansa, shiyasa ma kawai Musaddik
din ya kyale shi amma fa kullum cikin masa korafi yake.

   Bangaren aikin sa zai iya cewa yana cikin yan
gata da sai abinda suka zaba da inda suka zaba zasu zauna, kasancewar gaba daya
k’asar babu in da kakan shi mahaifin Ammi zai nemi alfarma ba’a masa ba, sannan
gefe guda mahaifin sa yayi sunan da zaka yi mamaki sosai.

  Duk da hakan be daina aikin sa ba, sai dai babu wani
matsi ko takura tun ma be kai matakin captain ba, balle yanzu da yake da rank
me girma.

 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button