HALIN GIRMA 1-5

“Maryama daga ina haka ke da alhuda-huda?”
“Daga islamiyya Iman take ni kuma na fito zan taho nan muka
hadu.”
“Toh ku tashi ku dubo min ko an gama tuwo dan cikina ya
soma kiran chiroma.”
“Wai Gaji wasa wasa fa kina da ci wallahi.”
“Saukin ta ba kowa ke siyan kayan abincin ba ‘yaya na ne,
ko zaku hana su bani ne?”
Rik’e baki Iman tayi tana dariya Maryam tace
“Bamu isa ba ai Gaji, aci dadi lafiya lokacin ki ne.”
” Yafi muku sauki dai, kema alhuda-huda kin fara zama su
balki ko? Kika biye musu baki da bakin da zaki iya karawa dani atau.”
Shiru tayi bata ce komai ba, suka zagaya kitchen din Gajin da ke
baya suka hado mata abincin suka kawo mata sannan suka zauna suka ci tare,
lokaci lokaci Maryam na tsokanar ta, ita dai Iman jin su kawai take har aka
gama suka tattare kayan sannan Maryam ta tafi ta barta a nan, sai kawai ta zame
tayi kwanciyar ta a saman doguwar kujerar ta fad’a kundin tunani kamar yadda ta
saba.
“Yaya Iman kizo inji Maama, zamu ci abinci kar ya huce baki
ci ba, kiyi sauri.”
Muryar Marwan ta iso daidai kunnenta, da sauri ta tashi zaune,
sai kuma ta mike da sauri tana jin sanda Gaji tace
“Hajara ba dai kirki ba, yadda kike kula da yarinyar nan
ubangiji Allah ya kula miki da naki yayan.”
Wasu guntayen hawaye ne taji suna neman zubo mata, tayi saurin
maidasu ta kara sauri zuwa shashen nasu domin amsa kiran Maama.
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
*_KASHI NA BIYAR_*
_*SABUWAR SHEKARA, SABUWAR TAFIYA, SABON SALO*_
🔥🔥.
🔥🔥. 🔥🔥.
_*ZAFAFA BIYAR!! KASHI NA BIYAR!! SINADARIN ZAFAFA5 (BEST TOP
5)*_
_*INA MASOYA KUMA MAKARANTA, MABIYA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR? KU
MATSO DOMIN NESA TAZO KUSA, KU SHARE HAWAYEN KU, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE DANNOWA
DA TURURUN SU, MASU ZAFAFAN FADAKARWA, NISHADANTARWA HAD’I DA ZAFAFAN KAUNA
MARAR GAURAYE.*_
_*YAN BIYAR DIN NAKU KAMAR KO DA YAUSHE SUNE:*_
_*SAFIYYAH HUGUMA*_
_DABI’AR ZUCIYA_
2-_*BILYN ABDULL*_
_TAKUN SAK’A_
_*3- MAMUH GEE*_
_DEEN MARSHALL_
_*4-HAFSAT RANO*_
_HALIN GIRMA_
_*5~NANA HAFSAT (MISS XOXO)*_
_SO DA ZUCIYAâ¤ï¸_
1
_DAGA TASKAR *SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI;
DAURIN BOYE, ALKAWARIN ALLAH, ALKIBLA, SIRADIN RAYUWA TA SAKE ZUWA DA WANI
RANTSATTSE MAI SUNA:_ *_ÆŠABI’AR ZUCIYA_*ðŸ˜
2
_DAGA ALKALAMIN *HAFSAT RANO* , MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAZO MUKE
A BAYA DA, DAURIN GORO, ABINDA KE CIKIN ZUCIYA, SAUYIN KADDARA, MABUDIN ZUCIYA.
WANNAN KARON TAZO DA WANI SABON SALON MAI SUNA:_ *_HALIN GIRMA_*
3
_DAGA SALON TAFIYAR *MAMUH GEE* ,WADDA A LITTATTAFAN TA NA
ZAFAFA TAYI; MIN QALB, BURI DAYA, KAUNAR MU, UBAYD MALEEK. WANNAN TAFIYAR TAZO
DA WANI DADDA’DA MAI SUNA:_ *_DEEN MARSHALL_*🥰
4
_DAGA TAFIYAR RUBUTUN *NANA HAFSAT (MISS XOXO)* WADDA A ZAFAFAN
BAYA TAYI WASU KAMAR SU: KAI MIN HALACCI, KIBIYAR AJALI, DALAAL, IGIYAR ZATO.
WANNAN NEXT LEVEL DIN TAZO DA WANI MAI TAKEN:_ _*SO DA ZUCIYA*â¤ï¸_
5
_DAGA SALON RUBUTUN *BILYN ABDULL* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI NA
BAYA IRIN SU: WUTSIYAR RAKUMI, SARAN BOYE, MAKAUNIYAR KADDARA, GUDU DA WAIWAYE.
WANNAN SABUWAR TAFIYAR TAZO DA WANI MAI SUNA:_ *_TAKUN SAKA🔥_*
☄ï¸ðŸ’«ðŸ’¥âœ¨ðŸ”?
_*KADA KU BARI AYI BABU KU, KUZO A DAMA DAKU A SABUWAR TAFIYA
MAI TAKEN SABON SALO, SINADARIN ZAFAFA BEST TOP 5, MASU ZAFAFAN DARUSSA, NA
RAYUWA, WANDA DUK WANI MAKARANCI BA ZAI RASA DARUSSAN DAUKA ACIKI BA.*_
_*GUDA DAYA: 300*_
_*BIYU 400*_
_*UKU 500*_
_*HUDU 700*_
*_BIYAR DUBU DAYA (1k)_*
*_YAN TALLAH SAMAN SHAFI NAIRA 300, ‘KASAN SHAFI KUMA 200 NE_*
_*YADDA ZAKU BIYA*_
*_ZAKU TURA KUDINKU ACIKIN WANNAN ASUSUN NA
BANKI_*👇👇👇👇
*6019473875*
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai katura shedar biyanka ta wannan number*👇👇👇
08184017082
_*IDAN KATIN MTN NE, KO VTU SAI ATURO ZUWA GA*_👇👇👇👇
09134848107
_#TEAM ZAFAFA BIYAR_🔥🔥
 Â
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA!*
©®Hafsat Rano.
FREE PAGE
(2)
*****
Takalmin Abban su da ta gani a kofar shiga falon yasa ta sauke
ajiyar zuciya, ta bud’e labulen hade da sallama, idonta ya sauka a cikin na
Mama da take kallon kofar, tayi mata wani kallo me cike da ma’anoni da ba kowa
ne zai gane ba sai ita kadai da ta san manufar sa.
“Abba barka da gida.” Tace tana zamewa k’asa
“Yawwa Uwata, kina ina haka mamanki na ta neman ki kinsan
bata so kici abincin da ya huce ko? Ga yanayi na sanyin nan ba komai ne yake
rik’e zafin sa ba.”
“Ina wajen Gaji ne.” Tace tana sake yin kasa da kanta.
“Toh dai a dinga kula ana abinda ya kamata kinji? Allah
yayi muku albarka.”
“Amin.” Tace tana mikewa ta shige dakin su da dan
sauri tana avoiding idon Maman da ta rakata dashi. D’are-d’are ta tarar da
Zeenat a saman gadon tana waya, wuceta tayi ta bud’e jakar kayan ta, ta sauya
kayan jikin ta da wasu ta ninke Hijab din sannan ta dawo ta saka abun sallah a
k’asa ta zauna ta ciro littafin da akayi musu a islamiya ta soma karantawa a
hankali.
“Malama kina distracting dina.”
Ta zare wayar daga kunnen ta tayi maganar a chunkushe. Banza
tayi mata ta cigaba da karatun ta ba tare da ta daina ba.
“Mtsww!.” Ta ja dogon tsaki
“Baby bari zan kiraka ina zuwa.*
“Owk dear, ina jira.”
Katse kiran tayi ta zuro kafafunta daidai wajen da Iman din take
zaune
“Malama duk karatun da kikayi a islamiya be ishe ki ba, sai
kinzo kin cika mana kunne mu san kina zuwa makaranta, bayan kowa yasan dalilin
da ya saka kika nace da zuwa ko kya samu ya sayyadi ya ce yana so.”
Bata tanka mata ba, hakan ya sake kular da Zeenat din, ta saka
hannu zata warce littafin tayi saurin janyewa ta mike tsaye,
“Wallahi sai dai ki hakura da karatun ko kije chan kiyi,
naga ma aiki ne gaban ki kin sani tsabar kinibibi so kike sai ya jiyo ki kina
karatu. “
” Kinga duk abinda kike yi bana taba tanka miki, ba wai don
ina tsoron ki bane ko wani abu, kawai bana son tashin hankali ne da hayaniya.
“
” Toh ki tanka min ma mana, wallahi yanzu zanje na hado ki
da Mama.”
Bata sake magana ba ta fice daga dakin dan ba karamin aikin
Maman bane ta hanata zuwa makarantar na wani lokaci, sai kawai ta zarce kitchen
ta tarar da kayan wanke-wanke tuli guda, ta nannade hannun ta tasoma wankewa.
Abincin da ta gani a tukunya ta san nata ne, yayi mugun sanyi ita kuma a
ka’idar ta bata cin abinci me sanyi, ko ruwan sanyi bata sha a rayuwarta balle
yanzu da ake zuga sanyi sosai., gudun ta barshi bata ci ba gobe a hanata yasa
ta samu leda ta juye a ciki ta wanke tukunyar ta goge gas da k’asan kitchen din
ta gyara komai tsaf sannan ta fito da ledar ta zagaya ta kofar baya ta fita
zuwa part din Gaji, ta samu me aikinta ta bata sannan ta dawo ta dauko katifar
ta a store ta wuce dakin.
  Har lokacin Zeenat bata gama wayar ba, toilet ta
wuce ta dauro alwala tazo tayi shafa’i da wutri sannan ta kwanta ta rufe kanta
gaba daya da dan yalolon zanin gadon da duk ya yayyage ta gefe da gefe ta
kudundune da haka bacci ya dauke ta.
  Da safe ta tashi kamar kullum tayi ayyukan da
suka zama wajibi akanta, kasancewar litinin ce sai ta yi wanka kawai ta wuce
shashen Gaji bayan ta tabbatar da fitar Mama tun sassafe, a chan taci abincin
ta sannan ta kwanta bacci. Sai da rana ta soma dagawa sannan ta koma ta daura
girkin rana,ta gama kafin lokacin tafiya islamiya, ta dauki na Gaji ta kai mata
ta sake zama tana jiran lokacin ya cika.