HALIN GIRMA 1-5

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½
#team zafafa biyar
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA*
Hafsat Rano
3
****
Tsaye yayi jikin gate din gidan yana kare masa kallo, tunanin ta
yadda zai fara shiga yake musamman da ba sanin sunan ta yayi ba, ya dai saka
mata suna da zuciyar sa kuma be taba yunkurin tsaidata balle yaji sunan ta ba.
 Lekowa maigadin gidan yayi, ganin mutum a tsaye yasa shi
fitowa gaba daya
“Sannu.” Yace masa yana kokarin daidaita muryar sa
“Yawwa sannu, wa kake nema?” Maigadin ya tambaye shi
yana kare masa kallon cikin rashin sani.
Nan fa ake yinta, shiru yayi kamar me nazari shi kuma maigadin
ya kafe shi da ido yana son jin abinda ya kawo shi.
“Am… Amm nazo wajen…”
“Malam Iliya.” Zeenat dake fitowa ta kirashi tana leko
wa.
“Na’am ranki ya dade!”
“Siyo min kati na 500 kayi sauri dan Allah.”
“Yanzu kuwa, ga wani bako nan bansan wajen wa yazo ba dai
kin tambaye shi.”
Yayi gaba, kallon sa tayi tun daga sama har kasa a wulakanci ta
yatsine baki tace
“Wa kake nema kai kuma Malam?”
“Yar uwarki nake nema dan Allah, wata me zuwa islamiya
kasan layin nan doguwa haka fara.”
“Waye kai a wajen ta?”
Kallon cikin ido yayi mata, ta ja tsaki tana juya fuskar ta
“Ban fiye son kallo ba Malam, ka shigo ciki bari na tura
maka ita dama ai sai dai ita din…”
Gaba tayi tana cigaba da sababi
“A kaf gidan nan wa zai kwaso mutum irin wannman dan Allah!
Ji shi kamar wani mahaukaci.”
Sai ta kwashe da dariya tana sake daga kafa.
A kwance ta tarar da Iman tana danna wayar ta da ba kasafai ta
cika wani amfani da ita ba, yanzun ma wani labari ne yaja hankalin ta a
Facebook take karantawa.
” Kina da babban bako a waje da galleliyar ranar nan.”
” Waye?”
” Idan kika je idon ki zai gane miki shi.”
” Owk.”
  Tace tana tashi zaune, har yanzu bata gama
dawowa daidai ba amma haka ta karfafa jikinta tayi ayyukan ta. Hijab ta saka
madaidaici akan doguwar rigar jikinta ta fito. Daga chan hanyar gate ta hange
shi a tsaye ya rataye hannayen sa a bayan sa, kansa a kasa yana wasa da kafar
sa.
  Dogo ne na ajin farko, jikin sa ko ina a murje
babu alamun rama ko kad’an, yanayin shigar sa bata dace da tsarin zubin
halittar sa ba, kafin ta karasa ta gama ayyana shi a ranta. Da sallama ta isa,
ya dago da sauri a lokaci daya kwayar idon sa ta sauka a cikin ta ta, gabanta
ne yayi masifar faduwa, tayi saurin janye idon ta, ta russuna kad’an tace
“Ina wuni?” Lumshe idon sa yayi ya bud’e, fuskar sa
dake cike da kasumba ta dan yi fadi alamun farin ciki, ya tattaro dukkan
nutsuwa da jaruntar sa yayi gyaran murya yace
“Kina lafiya?”
“Alhamdulillah.” Tace a gajarce ta matsa wajen wasu
kujerun roba guda biyu ta dauko daya ta kawo masa.
“Bismillah zauna kana ta tsaiwa.”
Hannun sa ya dora a saman kujerar ta kalli hannun yayi saurin
janye shi ya zauna sannan yace
“Kefa?”
Wani dan tudu a wajen ta nuna masa da hannu, ta zauna akai tana
jin duk ta takura ganin yadda yake bin ta da kallo da wasu irin idanun sa da
suka sake shiga ciki sosai.
“Na same ki lafiya? Ya gida yasu Mama da yan uwa?”
“Lafiya lou Alhamdulillah.”
“Ban gane waye ba amma?”
“Me sonki ne, me kaunar ki da son duk wani farin cikin ki,
yan kwanakin nan da na dauka banga wucewar ki ba, sun zame min kwanaki mafiya
muni a rayuwa ta. Na kan zauna a duk yini ina dakon wucewarki, ban taba
yunkurin yi miki magana ba, sai dai zuciya ta, ta gaza dauka har sai dana biyo
bayanki, ina fatan ban takura miki ba?”
Girgiza kai tayi tana jin wani bawai, wai ita ake karantawa
wannan kalaman, idan har taji daidai wato ya dade yana bibiyar ta, bata ma sani
ba.
” Kinyi shiru!” Yace yana gyara zaman sa
Shirun ta sake yi dan bata san me zata ce masa ba.
” Nasan dama karambani ne irin nawa, ban kai ajin ko da me
wanke miki takalmi bane, kiyi hakuri idan nayi miki shishigi a rayuwar
ki.”
” A ah wallahi, ba haka bane ba, a kalla mutumin da yace
yana son ka ai yafi makiyinka, nagode sosai da soyayyar ka gareni.”Â
Tace da sauri sannan tayi murmushi, ji yayi kamar zuciyar sa zata fito daga
kirjin sa, ya danne sosai ya maida mata murnushin
“Nagode Nuryyy… Nagode sosai.”
Shiru ya biyo baya, ta dinga wasa da gefen Hijab dinta shi kuma
yana satar kallon ta. Nutsuwarta tafi komai tafiya dashi.
“Bari na wuce.”
Da sauri ta mike kamar me jiran kad’an,
“Ka gaida gida.” Tace tana saurin yin gaba
“Ko zan samu number waya dan Allah?”
Tsayawa tayi ta mika masa hannu, ya shafa aljihun sa dukka
“Kinga garin sauri na manta wayar a daki, amma zan rik’e
fad’a min.”
“Ok .” Tace ta karanto masa,
” Nagode sunana Muhammad.”
” Fatima, ka gaida gida.”
Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Sake maimaita sunan Fatiman
yayi, ya saki murmushi a hankali sannan ya juya ya fice daga gidan.
***A zaune a falo ta tarar da Mama na waya, zata wuce ta tsaida
ta da hannu ta cigaba da wayar ta
” Ba za dai ka bar maganar nan ba ko Khalil? Toh shikenan
sai kazo din dai ma sake tattaunata, idan yaso ko a dangi ne sai ka duba sosai
ba za’a rasa ba ai.”
Amsa ya bata daga bangaren sa, ta ja tsaki tace
” Matsalata da kai kafiya wallahi toh sai anjima, sai kazo
din.”
Ta kashe wayar ta dangwarar da ita a gefen ta
” Na rasa shegen taurin kai irin na Khalil wallahi, sam
baya kaunar ya ganni cikin farin ciki, mtsw.”
Ta sake jan tsaki a karo na ba adadi.
” Daga ina kike?”ta jeho mata tambayar bayan ta riga
ta san inda take.
” Wani ne yazo dama.”
” Waye shi?”
” Bansan shi ba nima, wai a bayan layi yake.”
” Toh kina jina? Idan zaki yiwa kanki kiyamullaili ki rik’e
shi hannu bibiyu toh, idan kuma kika yi wasarairai da shi shima ya gudu kamar
sauran, sai ki zauna muyi ta jerawa a gidan nan,tunda dai bakin hali ya hana
samarin zama kowa yazo sai ya tafi.”
Bata dago ba, bata kuma ce kala ba, tana jin Maman tana kuma
ajiye kowacce magana a mazaunin da ya dace, sai da ta gama yi mata cin fuskar
sanann tace
” Khalil zai zo gobe, babu ruwanki dashi da shiga harkar
sa, ko falo bana so naga kina kaiwa da komowa har ya tafi, zan fi so ki tattara
ki koma wajen Gaji da zama aikin ma na yafe miki, idan ya gama kwanakin ya tafi
shikenan, bana son daukar magana dan shi ba kunya magana yake ji ba, kinji dai
na gaya miki.”
” In sha Allah.”
” Jeki.”
Tashi tayi ta bita da kallo ranta na tafasa, da gaske take kishi
da ita dukda bata zauna da mahaifiyar ta ba, amma duk sanda ta kalle ta sai ta
tuno abinda ya faru.
****A guje suka taso ganin ya fito, ya nufi wajen da jerin
motocin ke fake suna jiran sa, ransa a bace yake da kiran amma bashi da ikon
kin amsawa, dole ya ajiye shirin sa a gefe ya kirawo su domin ba zai taba yarda
da shigar masa shirin sa ba. Shiyasa su kansu basu da yakini ko masaniyar
komai, dan ya tabbatar da zasu taimaka wajen lalata masa shirin sa. Dan su din
basu da ikon kansu sai abinda aka gindaya musu.