Uncategorized

HALIN GIRMA 1-5

   Bud’e masa bayan motar
daya daga ciki yayi, ya russuna kad’an sannan yace

 

 

“We are very sorry sir!”

 

Be tanka masa ba, ya shige cikin motar ya jingina bayan sa da
kujerar ya lumshe idon sa.

 

“Oga Main house zamu?” Yayi tambayar yana tada motar

  

 

“Lamido Crescent!” Yace yana sake rufe idon sa.

 

Chan suka wuce direct, suna isa ya fito ya shige ciki, tun daga
falo ya fara wurgi da kayan jikin sa, ya rage daga shi sai boxer da farar
singlet, kallon kansa yayi a jikin tangamemen mudubin dake tsaye kikam a falon,
ya juya ya sake juyawa sannan ya wuce zuwa cikin bedroom din sa.

   Wanka ya fara yi a
gurguje sannan ya fito ya shirya cikin shigar babbar riga da jamfa da wando
farare kal, sau cikin sa ya jawo ya ajiye a gefe ya fara saka farar socks a
ciki sannan ya saka ya fito rik’e da babbar rigar a hannu.

   Zama yayi sannan ya
danna remote din kofar, da sauri suka shigo su biyu, ya mik’a wa daya babbar
rigar, karba yayi ya taimaka masa ya saka sannan ya dauki abubuwan da yasan zai
bukata ya fita dasu.

 

“Ka zauna anan zan kiraka da zarar na sauka.”

 

Yace da dayan sannan ya tashi ya fice cikin takun da yafi kama
dana jinin sarauta.

   Motoci biyu ne suka
fita daga gidan, shi yana cikin daya su kuma suna bin sa a daya har zuwa
airport.

 

*Muhammad Ahmad Santuraki*          

 

          *(*Captain
Moh*)*

 

 

 

 

 

 

 

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

 

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

 

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*

 

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

 

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

 

*_DEEN MARSHALL👉🏾
Mamuhghee_*

 

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat
rano_*

 

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn
abdul_*

 

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss
xoxo_*

 

*_ÆŠABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

 

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

 

2👉🏾400

3👉🏾500

4👉🏾700

5👉🏾1000

 

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

 

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

 

08184017082

 

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*

 

09134848107

 

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽

#team zafafa biyar

1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA*

 

*_Hafsat Rano_*

 

 

4

 

****

*Adamawa-Yola*

 

Tun daga yanayin manyan motocin da suka cika harabar  ya tabbatar da bakin dake cike da fadar, yana
da yakini dalilin kiran Bubun kenan a kalla zasu ganshi sannan ayi masa maganar
da tafi komai kona masa rai, maganar mulki da yake dukkan kokarin sa wajen guje
mata.

    Be jira an bud’e masa
ba, ya balle murfin motar ya fito bayan hango Aji da yayi yana nufar ciki tare
da tawagar sa, da saurin sa ya cimmusu,domin ya samu su shiga a tare, ko ya
gujewa idanun Bubun daga zuwan nasa. Yasan a cike yake taf dashi

 

“Aji!” Ya kira shi da sunan da yake kiran sa

 

“Hoo d’an nema, na dauka ba zaka zo ba ai.”

 

” Na isa naki amsa kiran ka ko na Bubu? Ai ban isa
ba.”

 

” Dadin baki, idan har da gaske ne ai sai ka amsa kiran da
muka jima munayi maka ko?”

 

Sosa keya yayi ba tare da yace komai ba, suka karasa ciki. Da
ido Bubu ya kafe shi tun shigowar sa, tabbas ya rame fiye da ganin da yayi masa
kwanaki da suka wuce, sannan akwai wani yanayi a tattare dashi da be gamsu ba,
a gabansa ya tare, ya kwashi gaisuwa ya cigaba da bin sa da idon ba tare da shi
ya yarda sun hada ido ba, gefen Ajin ya samu ya rabe yana sake hade fuskar sa
tamau, murmushi kawai Bubu yayi ganin da gaske Muhammad yake har yau yana nan
akan bakan sa, ya rasa dalilin da ya saka shi baya son mulki ko kad’an, tamkar
ba dan naga da ba, kamar wanda aka juyawa tunani kwata kwata akai, gashi da
gaske yake jin ya kamata ace ya huta, yakamata ya karbe shi kamar yadda ya
karbi Aji a lokutan baya. Sai dai d’an nasa sam be shirya hakan ba, abinda yasa
yake dada jan lokacin sosai, burin sa kawai yasa a gaba tun bayan shigar sa
jami’ah, in da ya kwallafa rai akan aikin tsaro, ya kuma samu cikar burin sa
duk da ba hakan ne ya kasanci burin sa ba shi.

    Kamal ne ya shigo
wajen, ya gaida kowa cike da girmawawa sannan ya samu gefe ya zauna yana
fuskantar Muhammad din, kallon juna suka yi ba tare da wata magana ba, murmushi
kawai Kamal din ya sakar masa wanda ya kasa maida masa domin ya san ma’anar sa,
be damu ba ko kad’an, da ace Bubu zai ji shawarar sa da ya jima da yiwa Kamal
din abinda yake muradi, amma shima kemaimai yaki, ya kwallafa rai akan Muhammad
din, ko me yasa? Oho. Ya dage kafadarsa alamun baya da bukatar ya sani ma dai.

 

 Duk batutuwan da aka
tattauna a wajen be tsinci komai ba, zuciyar sa ta lula chan zuwa in da ya
baro, tunanin halin da take ciki ko abinda take aikatawa kawai yake har kusan
kowa ya gama ficewa ya zama na daga shi sai Aji, da Bubu.

 

“Muhammadu.” Yayi firgigit sai kuma ya hau sosai kai
yana murmushi

 

“Barka da rana Bubu.”

 

“Kalli shigar ka fa Muhammad, kalle ka? Hakan ya dace a
matsayin ka da gidan nan? Haka kaga dan uwanka Kamal yayi shiga irin ta
masarauta?”

 

“Wallahi Bubu garin sauri ne, kuma gashi ba wani iya nada
rawanin nan nayi ba wallahi, infact ciwon kai wallahi yake sani, amma za’a
gyara ba za’a sake ba.”

 

Murmushi Aji yayi me dan sauti, ya kalle shi yana sake fadada
fara’ar fuskar sa.

 

“Ayi hakuri ranka ya dade munyi kuskure ba zamu sake
ba.” A duk sanda irin hakan ta faru Ajin ne ke yin uwa yayi makarbiya ya
hana ayi masa fad’a, hakan yasa ba kasafai Bubun ke korafi gaban Ajin ba, sai
ya tsuke bakin sa kawai be sake cewa komai ba.

 

Tashi yayi, ya dan russuna a gaban mahaifin nasa

 

“Zan shiga ciki Bubu!”

 

“Ka same ni a shashe na bayan sallar magriba.”

 

” In sha Allah. A tashi lafiya.”

 

” Aji sai na shigo wajen yar tsohuwa ta.”

 

” Tana nan tana jiran ka da manshanun ta da yajin
daddawa.”

 

Murmushi yayi, ya fice suka raka shi da ido. Yana fita Bubu yaja
tsaki

 

” Na rasa me yake damun yaron nan wallahi, ace yaro ya taso
a cikin abu amma sam ya tsane shi? Wannan wanne irin abu ne?”

 

” Mu cigaba da hakuri kawai Ahmadu, komai zai wuce
ne.”

 

” Allah yasa, kowa jira na yake, mutanen gari da manyan
mutane kowa ya zuba ido yaga me zanyi akai, ga Kamal da gaske yake son mulkin
nan, gashi sam be chanchanta ba, na rasa yadda zan.”

 

“Shima ka barni dashi kawai, ayi masa abinda yake so din,
yanzu dai a zaman da zakuyi sai kayi masa maganar auren muji, a kalla auren zai
taimaka masa ya zauna a cikin mu, kaga dole ya koyi komai.”

 

” In sha Allah, idan ma bashi da yarinyar da tayi masa ni
zan nemo masa.”

 

” Kul, Muhammad ba irin yaran da za’a yi musu haka bane, mu
da muke son amfani da soyayyar shi ga yarinyar, abi dai komai a sannu.”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button