Uncategorized

HALIN GIRMA 1-5

” Shikenan in sha Allah, Allah yasa mu dace.”

 

” Amin ya Allah.”

 

 

***Bangaren Ammin sa ya wuce, yana tafe yana amsa gaisuwar da ya
tsana, ayi ta gaida mutum kamar wata tsiya, hakan na daya daga cikin abinda
yake hada shi da gidan su, ya gwammace yayi guduwar sa waje daya kawai ba tare
da hayaniyar mutane ba.

   Tana zaune ta dora
kafarta a saman dan tumtum din dake falon, kafar na damun ta sosai shiyasa ko
yaushe zaka ganta a mike ana dan mammatsa ta. Yana tura kofar duk suka mike,
har rige rigen gaishe shi suke kowa yasan yadda Ammin ke masifar ji da tilon
dan nata, mace me kirki da sanin yakamata, shiyasa ta karbe kowa a gidan daga
ma’aikata har dangi kowa nata ne, wajen Bubu ma Itace star,itace kuma uwar
gidan sa dan dai Allah be bata yawan haihuwa bane.

 

 

“Barka da zuwa yarima, sarki me jiran gado, uban mara uba
me uban ma kaine gatan sa, shalelen Gimbiya da maimartaba, ka tsare gaba ka
tsare baya, Allah ya kara maka daukaka da girma, Allah ya ida nufi..
sai…”

 

Da sauri ya dakatar da ita, sai ta juya sum-sum-sum ta fice, ya
kalli Ammi yayi mata murmushi kafin ya zauna a daidai saitun kafafun nata ya
tankwashe kafafun sa

 

“Ashe zaka zo.” Tace masa tana murmushi itama

 

” Na isa naki zuwa Ammi? Barka da gida mun same ku
lafiya?”

 

” Lafiya lau Alhamdulillah , shiru daga cewa zaka je wani
aiki Kano shikenan kamar an aiki bawa garin su, su ba labarin su da suka bika
kaima ba labari, gidanka da kake sauka ma an ce min ba chan ka sauka ba.”

 

” Wani babban aiki ne ai Ammi, ki tayani da addu’a kawai in
sha Allah zakuji labari me dadi.”

 

” Allah yasa toh, ya aikin naku?”

 

” Alhamdulillah wallahi, muna ta fama, ba dadi amma haka
dai za’a cigaba da lallabawa.”

 

” Tunda kana so ba.” Tace.

 

 Dariya ya saka kawai be
ce komai ba. Ya dan jima a tare da Ammin tasa kafin ya tashi ya yi mata sallama
zuwa shashen shi, da yake kusa da na Bubu.

   Yana shiga ya tarar da
kayan abinci a jere a falon nasa, sai kamshin turaren wuta dake fita ta cikin
yar karamar burner din dake makale a jikin wani dan karfe.

   Wuce komai yayi zuwa
bedroom dinsa, ya kwanta rigingine a saman gadon ya jawo woyoyin sa, ya shiga
cikin contact dinsa, number farko da yayi saving dinta da emoji din heart da
padlock ya danna kira ya kwanta sosai yana lumshe idanun sa lokacin da ta soma
ringing…

 

 

 

****Da safe ta tashi kamar kullum tayi duk abinda tasan wajibin
ta ne, har zuwa sanda rana ta fito sosai, kayan ta na wanki dana Marwan ta hada
ta zagaya baya ta hau wanke su, daga gefe ta ajiye wayarta tana jin karatun alkur’ani
me girma, tana wankin tana bi har ta gama tsaf, ta tattare su ta shanya sannan
ta dawo ciki ta chanja kayan ta, ta fice zuwa shashen Gaji.

   Fitar ta kenan Khalil
ya shigo, maigadi na bin sa janye da katotuwar trolly din sa a baya. Da Habib
suka ci karo yana kokarin fita, ya bashi hannu suka chapke cike da murnar ganin
juna

 

“Welcome welcome.” Yace masa yana juyawa suka shiga
ciki. Da sauri Mama ta fito jin hayaniyar su..

 

“Wa nake ji kamar Khalil, inyee lallai yaron nan Ashe dai
da gaske kake.”

 

“Gani dai, ai dama na gama shirin zuwa kawai ban sanar dake
bane sai jiyan.”

 

“Maraba lalle da manyan yan jarida.”

 

Zama yayi a cikin kujerun falon, itama maman ta zauna tana gyara
dan kwalin kanta.

 

“Wai dama kinsan zaizo Mah?”

 

“Nima sai jiya na sani, na zata kuma halin nasa ne Ashe da
gaske yake shiyasa ma ban fad’a ma kowa ba.”

 

“Ina wuni Anty?”

 

” Lafiya lou Khalil, yaso Hajiya da kowa da kowa?”

 

” Duk suna nan lafiya, itama tayi mamaki da nace zanzo,
gashi kuma zan dade sosai dan aiki ne ya kawo ni.”

 

” Ahaap ko da naji, Ashe zuwan dai da dalili, jairi dama
nasan akwai abinda ya kawo ka.”

 

” Abubuwa dai Anty, karki manta da wannan maganar tamu
hadda ita ma.”

 

Tsaki taja ta harare shi

 

” Zaka fara ko?”

 

” Nayi shiru.” Yace yana dora hannun sa baki

 

” Yafi maka dai.”

 

” Ina su Zeenat ne? Banji duriyar su ba.”

 

” Zaka ji su ne ai ba dai kananan ba, ka tashi ku shiga
ciki ka huta kaci abinci, sannu da zuwa.”

 

Tashi yayi, yabi bayan Habeeb suka wuce dakin sa suna hirar yaushe
gamo, idanun sa da kunnuwan sa na jiran yaji ta inda zasu bullo, he can’t wait
to see her beautiful face, ko me Anty zatayi masa kuwa ba zai fasa bawa zuciyar
sa abinda ta dade tana so ba. Kishin ta daban soyayyar sa daban. Period!

 

 

 

****Zaman ta a bangaren Gajin yafi komai yi mata dadi, abu daya
ne kawai yake dan takura ta yawan maganar Gajin, duk da haka take daurewa tana
amsa mata, gashi ta manta wayar ta a kitchen bayan ta gama wankin nan, gashi
taji alamar Khalil din yazo ta tabbata idan taje dauka zasu iya haduwa, ta kuma
san me hakan ke nufi a wajen Mama.

   Zaman ta ta cigaba
kawai har sanda taji ana kiran sallar, alwala tayi ta zauna ta jira a tayar,
tana jin sanda za’a tada sallar ta fita zuwa bangaren nasu, lokacin tasan sun
tafi sallah Maman ma kuma ta shiga ciki tayi sallar itama, ta baya ta bi, ta
shiga kitchen din a daidai lokacin da ya saka wayar a kunnen sa

 

“Waye?”

 

Yace yana gyara rikon da yayi wa kofin hannun sa, tashi zaune
Moha yayi da sauri, ya kalli screen din wayar ko be kira number daidai ba? Kai
Anya? Daidai yadda ta fad’a masa ne

 

“Fatima nake nema, ko tana kusa?” Yace jin me maganar
ya sake tambayar waye a karo na biyu.

 

“Fatima? Malam Waye kai din da kake neman ta?”

 

“Sanin waye ni ba zai taba maka dadi ba, idan tana kusa ka
bata zanyi magana da ita.”

 

” Ba zan bata ba, abun yar karfi ne kazo ka karba idan kana
dashi, mtsw.”.

 

Yaja dogon tsaki hade da kashe wayar, kafar ta ta sako a kitchen
din zata shigo domin ta karbi wayar ta da ya daga mata ba tare da izinin ta ba,
muryar Mama ta dakatar da ita, ta juya da sauri ta bar kitchen din.

 

” Kai kuma me kake anan kana jin an tada sallah?”

 

“Ruwa nazo sha.”

 

 Yace yana juyawa ya bar
kitchen din, kofar bayan ta leka ta tabbatar babu komai a wajen, tayi kwafa ta
juya bayan ta jawo kofar ta ciki.

 

Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce shi, ya tashi da sauri
yana jawo dayar wayar tasa, cikin kankanin lokaci ya birkice ya koma Captain
Moh din sa na ainihi, a yau ba sai gobe ba zai juya, dan ba zai taba daukar
rainin hankali ba, ba dan ganin da zai wa Bubu ba, da babu abinda zai hanashi
daukar hanya a yanzu, amma dole ya hakura zuwa lokacin da ya dauka masa duk da
yana ganin yayi masa masifar nisa.

  Kaiwa da komowa ya dinga
yi a tsakanin dakin, zuciyar sa tamkar zata hudo daga kirjin sa saboda tsabar
kishi.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

 

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

 

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*

 

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

 

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button