HALIN GIRMA 1-5

*_DEEN MARSHALL👉ðŸ¾
Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉ðŸ¾hafsat
rano_*
*_TAKUN SAƘA👉ðŸ¾billyn
abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉ðŸ¾miss
xoxo_*
*_ÆŠABI’AR ZUCIYA👉ðŸ¾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉ðŸ¾400
3👉ðŸ¾500
4👉ðŸ¾700
5👉ðŸ¾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½
#team zafafa biyar
****
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA*
*_Hafsat Rano_*
   *5*
*_Last free page!_*
****
Tana zaune ta idar da sallah, bata tashi daga kan abun sallar ba
taji shigowar sa shashen Gajin, gabanta taji ya fadi, tayi kamar bata ji
sallamar da yayi ba, tayi tsam a kan sallayar tana kallon gabanta. Da kallo ya
bi bayan ta ya samu waje ya zauna a cikin kujerun falon yana kokarin daidaita
yanayin da yake ciki. Gajin ce ta fito,
“Wa nake gani kamar Ibrahim?”
“Nine nan wallahi Hajiya.”
“Lale marhabin, barka da zuwa. Saukar yaushe?”
“Dazu na shigo, mun same ku lafiya?”
“Lafiya lou wallahi, yasu Hajiyan da yan uwanka?”
“Kowa lafiya suna gaida ku.”
“Muna amsawa, sannu da zuwa.”
” Yawwa.” Yace yana yawo da idon sa akan ta,
” Iman ba magana?” Yace yana son Gajin ta tanka
“Kaji sokonci, wai bata gaishe ka ba?” Tayi maganar da
sauri
“Ina wuni?” Tace a gajarce
” Lafiya lou, kina lafiya?”
Shiru tayi bata amsa ba, Gaji ta hau sababi tana mata fad’a,
tashi yayi hannun sa cikin aljihu ya zaro wayar ta
“Gashi na tsince ta a kitchen.”
Ya mik’a mata sannan yayi wa Gajin sallama ya fice yana raya ta
yadda zai bulowa Iman din, ya gama gane yanayin ta ba irin nasa bane, shirun ta
yayi yawa amma duk da haka shi ba damuwar sa bace, yadda ya shiga zuciyar kowa
a gidan nan da hakan zaiyi amfani ya kafa kansa, ba zai wani ja lokaci ba zai
gabatarwa Gaji da kansa, baya jin ma zai wuce gobe, zai sai fara tuntubar Yaya
Hajara idan yaga ba ta goyi bayansa ba zai yi gaban kansa, iya ka tayi masa
fad’a shikenan ya wuce. Be koma shashen ba, sai ya fice daga gidan a
kafa yana adana number da ya dauka a wayar ta ta, so yake ya saka number a
truecaller yaga ko zai samu wani information akai.
 Â
Cikin call log dinta ta shiga ta duba amma bata ga number da aka
kirata ba, taji babu dadi dan bata so yaga kamar tana sane ta bayar aka daga
wayar tasa. Ko da tafiyar su ba zatayi daya ba, ba zata so yaji a ransa dan
yana lacking wani abu bane shiyasa hakan ta faru. Kwantar da kanta tayi a saman
hannun kujerar ta rufe idon ta tana tariyo zuwan da yayi wajenta, akwai wani
abu me girma a muryar sa sai kuma abu daya da ya tsaya mata shine kamshin
turaren da taji yana yi, wanda yayi kama da me tsada ne irin ajin farko, domin
Allah ya hore mata kaunar kamshi, shiyasa ta kan yi saurin ganewa. Sai dai
akwai irin tuurare yan durin nan da suke da kamshi me dadi har ka kasa tantance
su, kila irin su ne, abunda ya kara burgeta dashi kenan, duk da yana cikin
yanayin da zaka ce kai tsaye babu, amma be bar kansa a wulakance ba. Juya kanta
tayi daya gefen ta dora wayar a saman cinyarta ta cigaba da tunani.
***Kiran sallar magriba ya sashi fita daga sashen nasa zuwa
masallaci, achan yayi alwala ya shiga sahun farko sukayi sallar. Bubu na ganin
shi yaji dadi sosai. Bayan an idar ya wuce bangaren nasa domin ya jira shi,
yana zaune sai gashi ko ya shigo, ya tashi tsaye har sai da ya zauna sannan ya
zauna shima a k’asa cikin girmamawa ya sake gaishe shi, ya amsa masa sake yana
nazarin sa.
“Muhammadu!” Ya kira sunan sa, gyara zaman sa yayi ya
tattara hankalin sa waje daya cikin son ganin be yi wani abu a gaban Bubun ba
“Kana ji na Muhammad?”
“Inaji Bubu.”
“Madallah, Muhammad ka san dai a tsarin gidan nan kana
cikin lokacin da ya kamata ace ka ajiye iyalin ka kaima, ka nutsu waje daya a
kalla hakan zai taimaka maka wajen cikar kamalarka.”
Kansa a kasa yana jin Bubun yayi ta bayani yana gida kansa cike
da gamsuwa,
**A kofar ta tsaya tana kallon takalmin Muhammad din dake zube a
wajen, ta samu labarin zuwan sa a wajen Kamal amma bata tsammaci irin wannan
ganawar da Maimartaba ba, shiyasa ta kasa hakuri tazo ta nemi iso wajen
Maimartaba din wajen sarkin kofa amma sai ya nuna mata ba zai yiwu ba, domin an
gargade shi akan barin kowa ya shiga shashen maimartaba din har sai ya kammala
ganawar sa da Muhammad din, ranta a matukar bace ta koma sashen ta tana jin
wani irin tashin hankali, tana tsoron kar Muhammad din ya amsa tayin mahaifin
nasa a wannan zaman da zasuyi.
Safa da Marwa tayi
tayi, har wajen sallar isha basu fito ba, tana hangen bangaren ta cikin nata
shashen, ta kasa zama tana da yakinin ko menene suke tattaunawa haka me
muhimmanci ne sosai.
Tana tsaye jikin window
taga fitowar su, fuskar Muhammad din a sake yana takewa mahaifin nasa baya.
Tsaki taja ta saki labulen tana juyawa zuwa gefen gadon ta, ta zauna tana sake
jan wani tsakin, tsakin haushin Muhammad din da ya zame mata ciwon ido shi da
mahaifiyar sa.
“Ranki ya dade, Maimartaba ya aiko yana da bukatar ganin ki
bayan ya dawo sallar isha’i.”
Bata amsa ba, sai ma juya fuskar ta da tayi wani sashen tana
sake sakin siririn tsaki.
***Bangaren sa ya koma, ya tattaro abunda ya san zai bukata ya
fito, sai kuma ya tuna da maganar Maimartaba ta karshe da suka tattauna, yana
son ganin sa da safe kafin ya fito fad’a, komawa yayi ba dan yaso ba, ya ajiye
komai ya zauna yana kirga lokacin zuwa wayewar gari. Nisan yayi yawan da yake
jin kamar yayi loosing idan har ya kyale shi tsawon wannan lokacin.
Wayar sa dake ajiye a
gefen sa ta dauki sowwa, ya daga ganin kiran da yake ta jira ne tun dazu,
“Oga na duba maka number din, akwai bayanan sa da komai har
da wajen aikin sa, hoton sa da kuma location dinsa a yanxu, na tura maka ta
mail sai ka duba.”
“Ok! Thank you, zan neme ka. “
Ya katse kiran ya shiga mail dinsa, ya hau kan message din ya
bud’e. Hoton sa ya bud’e yayi zooming sosai, sai kuma ya fita ya karanta
information din. Karamin tsaki yaja ya ajiye wayar yana jin a ransa wannan din
karamin kwaro ne be kamata ya hana shi walwalar sa ba, abu daya zai masa ya
kama shi a hannun sa, sai dai ba zai hakan ba har sai ya je ya tabbatar da
zargin sa.
***Anan sashen Gajin ta shirya, ta wuce islamiyya tana tafe tana
satar kallon hanyar ko zata ganshi tunda yace mata yana zama ne domin yaga
wucewar ta, har ta isa makarantar bata ga ko me kama dashi ba, sai kawai ta
share tayi abinda ya kaita. A dawowa ma haka ta sake yi shima bata ga kowa ba,
ta dawo gida ta chanja kayan ta kenan aka shigo aka ce tazo inji Muhammad,
Hijab ta dora a saman kayan jikinta ta fito. A tsaye yau ma ta hange shi wajen
kujerar, ya rataye hannayen sa a bayan sa yana tsaye kyam akan kafafun sa.
“Assalamu alaikum.” Tayi masa sallama tana jan
kujerar.