Uncategorized

HALIN GIRMA 1-5

“Sannu da zuwa, nan akwai rana bari na saka maka a
chan.” Taja kujerar zuwa k’asan wata yar bishiya ta ajiye,

 

” Bismillah.” Tace masa tana nuna masa kujerar, be
zauna ba, ya zaro hannun sa daga bayan sa, ya dawo dasu gaba ya rungume su a
kirjin sa,

 

” Bismillah.” Ya nuna mata kujerar da baki

 

” Zauna babu matsala.” Yace mata

 

” A ah dan Allah ka zauna, be kamata na zauna kana tsaye
ba, ance bakon ka…”

 

” Kyale fadar hausawan nan, zauna dan Allah.”

 

Allah da taji ya ambata yasa ta zauna a kunyace, ya zura mata
ido har sai da ta dan ji wani iri.

 

” Na cika kallo ko? Kiyi hakuri.” Yace mata yana
murmushi,kallon ta kadai yayi jin sa yake kamar yafi kowa sa’a a duniya

 

” Ba komai.” Tace tana gyara wayar hannun ta

 

” Ina wuni?” Ta gaishe shi yana dan zamowa

 

” Lafiya lou, sai kika jini shiru, tafiya nayi zuwa kauye
Baba ya kira ni, naso ma na zo kafin na wuce toh tafiyar ce tazo a gaggauce,
sauka ta kenan ma.”

 

” Allah sarki… Allah yasa lafiya.”

 

” Lafiya lou, sai godiya. “

 

” Ka baro su lafiya?”

 

” Alhamdulillah. Nagode da kulawa.”

 

” Ba komai.” Tace tana wasa da hannun ta.

 

Turo gate din akayi, Habeeb na gaba yana bin sa a baya, wani
irin daukewa yaji ganin sa na neman yi. Iman zaune tare da wani suna hira, a
cikin gidan kuma? Be san sanda ya isa wajen ba, sai ganin mutum sukayi a gaban
su.

   Wani kallo Moh yayi
masa, yayi murmushi yana taune gefen lips dinsa na kasa

 

“Yaya sannu da zuwa.” Yace yana mika masa hannu, kin
bashi hannu Khalil yayi, sai Habeeb ne suka gaisa, ya daki kafadar Khalil din

 

” Muje ko?”

 

” Yi gaba ina zuwa.” Yace masa,

 

“Ok.” Ya wuce ya bar Khalil din a tsaye

 

” Iman shiga gida.” Yace a gadarance, ta dago ta kalle
shi da sauri, ya hade girar sama data k’asa tamau irin ba wasa din nan.

 

“My heart, ki shiga gida ki huta dama naji ba zan iya zuwa
gida ban zo na ganki ba, shiyasa na taho nan kai tsaye, zan kira ki anjima ki
ajiye waya a kusa dake kinji?”

 

Kunya ce ta kamata ta noke, ta mike da k’yar tace

 

“Ka gaida gida.” Sannan ta wuce ciki, tana barin wajen
ya hade fuskar sa sosai.

 

” Da tsakar ranar nan ka taso yarinya, kazo zaka ishe ta da
uban surutu, ku dama talakawa haka kuke, da kunga yar hanya sai kuzo kuce kuna
so, kai kanka kasan ba sa’ar ka bace, ba sa’ar auren ka bace shishigi dai, toh
ita din matata ce, ni zan aureta an gama magana, sai kaja tsumman kafafunka a
koma in da aka fito, ka samu daidai da kai.”

 

” Zaka ga tasirin talaka da talauci kuwa, baka da ikon
tsarawa kowa rayuwa, haka arziki ba wani abu bane face fitina, wadatar zuciya
itace mutum…” Ya dan matso gaban sa

 

” Mark my word, a gaban idon ka, right under your noses,
talaka zai baka mamaki, mamakiin da har ka kare rayuwar ka zaka fita daga cikin
sa ba, count down dinka ya fara daga yanzu.”

 

” 1,2,3!” Sai na jika.

 

Ya juya ya fice daga gidan cikin takun da ya tsayawa Khalil a
rai, cikin wani irin yanayi yayi cikin gidan yana jin yanzu ba sai anjima ba,
zai yi abinda ya dace, gida be koshi ba, babu yadda za’a yi a bawa dawa.

 

**A tsaye ya tarar da Habib yana ganin shi yace

 

“Kaiko me ka tsaya yi ina ta jiran ka.”

 

“Abinda ka kasa yi, kana ganin kanwar ka da mutum a tsaye,
kana ganin sa kaga mara gaskiya, wa ya sani ma ko dan boko haram ne da wannan
uban kasumbar, amma baka damu ba kayi tafiyar ka, hakan ba daidai bane.”

 

Kallon sa Habib yayi, mamaki na kamashi,

 

” Yaushe hakan ya zama ba daidai ba khalil?”

 

” Habib, maganar gaskiya ina son Iman, son da ni kaina
bansan adadin sa ba, zan iya komai akan na sameta, dan haka ba zan iya jure
ganin ta da kowa ba, musamman mutum irin wannan da ya nuna alamun rashin
gaskiya, gashi fakiri jibi shigar jikin sa, no ba zan iya ba, rakani wajen Gaji
ayita ta kare.”

 

” Idan har kai din jinina ne, idan har na isa da kai babu
kai babu Iman Khalil, na rasa kafiya irin taka, na rasa dagiya irin taka, bayan
maganar nan mun dade da gama ta, na gaya maka ba zai taba yiwuwa ba.”

 

” Akan me? Dan Allah Anty ki gaya min hujja me karfi a
musulunci da ya haramta min auren ta, na daya ni ba muharraminta bane tunda ita
din ba ke kika haife ta ba, toh sai menene? Akan dalili mara tushe?”

 

” Akan duk abinda zaka kira shi Khalil ka kirashi, amma
idan har ina numfashi ba zamu hada jini ba wallahi, ga mata nan bila adadin, me
yasa sai ita, wannan da yazo shi ya dace da ita, shine daidai da matsayin ta,
inaso auren da zatayi ya zama sakayyar aure min miji da uwarta tayi, ta saka
yayana samun yan Uba!.”

 

” Ohh shit! Kin kasa fuskanta ta Anty, kiyi hakuri wannan
karon zabin raina zan bi, zanje na samu Gaji na sanar da ita, gwara kowa ya
sani a san me yakamata ayi.”

 

” Khalil!”

 

Ta k’wala masa kira, ya juya da sauri yayi hanyar fita, wayar sa
tayi kara, ya tsaya chak jin layin da yake ajiye numbers din manyan mutanen sa
ne, ciro wayar yayi sunan Sir ya bayyana a wayar, ya daga da sauri yana
daidaita numfashin sa

 

” Kana ji Ibrahim? Sako ne daga sama ba daga ni bane, an
dakatar da kai aiki zuwa wani lokaci, za’a neme ka idan bukatar hakan ta
taso.” Be jira yace komai ba , ya katse kiran. Da sauri ya dafe bangon da
yake kusa dan ji yayi jiri na neman kadashi, gaba daya rayuwar sa akan aikin ta
dogara, yana da passion sosai a Kai sannan yana iyakar kokarin sa wajen aikin
sa, maganar promotion dinsa ma ake idan har ya kammala wannan assignment din da
ya kawo shi Kano, shikenan sai dakatarwa haka nan ba wani dalili?

 

” Ya akayi?! Habib ya matso ya taba shi ganin kamar ya
shiga coma

 

🔥🔥🔥🔥🔥

*_LAST BONANZA_*

 

*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun
sake rage muku kaso 20 cikin 100_*

 

*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan
800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*

 

*_za’a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_*

 

*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*

 

*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

 

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

 

SAIKU TURA SHAIDAR BIYA

 

08184017082

 

GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA
SHAIDAR BIYANKU

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button