
Da gudu matan gida suka hankado d’akin,ganin hannunta kam akan mazantakarsa tana lilo, ya firgitasu lalle uwale za ta kashe rai suna Cikin gida
Duka suka rufeta dashi ,kafin da qyar suka qwaceshi
Rikicaaa ya watse can gefe yina ihu yina ,uwale Na sake ki saki uku Ashe dama ke makashiyace ban sani ba…allah ya isana…
Kukan kura tayi tana qoqarin cinmasa ana rirriqesa
“Kubarni da ja’iri bakinsa bai mutuba ai “
Matan gida Koran fata fata sukayi wa uwale ,don su Kansu sunyi murnar rabuwar bello da uwale ko sa samu suyi tarbiyyan yaransu lafiya”
Bello kam saida aka dangana shi da gadon asibiti waje ta salu6e ta kumbura tai sintsir hausi ce me jinya itama tanayi tana allah shi qara tsiyar qarin aure kenan yau wa gari ya waya?akan aurenka da uwale ba tozarcin da bakayimun ba ,yanzu kuwa da nayi haquri gayinan duk allah yayi mun maganin Ku INA kallo”
“Ke dai hausi karki since ladanki,yin jinyar nan kikeyi don allah…
Tuna baya
Tunda bello aka tsaida ranar aurensa da uwale ,hausi take ganin rawan kai nau’i da suffa ,a lokacin suna gida iyayensa mamanshi ta ware masa fili tace yaxo ya danyi ginin qasa a lilli6e da sumunti ya kintsa matansa waje guda
Haka kuwa ya tarkata jarinsa ya qera gini lokacin biki aka sha biki…ranar kuwa da ango zai shiga daki abokansa Na kawosa suka shige d’akin uwargida su gaisa kafin su shigo…shikuma ya shige d’akin amarya ,ya ajiye kazar angwancin zai dawo gurin abokansa .saidai zumbur uwale ta miqe.
” yoooo INA kuma zuwa?
..Wai zan yowa abokaina jagorancine suzo Ku gaisa,kuma a taraku ayi maku fad’a da er uwar zamankii kuma babata da safe zata kuma sasantaku..
Tsidik ta mike ta warware mayafi ta gyara zaman shi aka
“To mu tafi d’akin hausin tare.. yaudai ranana ne ban bari aci min ko minti”
**
Duk nasiha da ban Baki abokansa sunyi masu itadai hausi batace komai ba
Da zasu tafi tayi masu godiya itama ta mike zata shige uwar d’aki
Sigina da ido uwale tayiwa bellon
Saiga bello Cikin rawar murya yina kiran abokansa da hausin wai su daddawo
“Yawwa hausi kwana nawa zanyi a dakin uwale?
” kaji wani rainin aqalu…adadin kwanakin da musulunci ta tsara maka mana kwana bakwai…”
“Haba hausi bansanki da baqin ciki ba. Ke kuwa ba tun kafin auren nan ba kince zaki qara mun kwanaki ba …don allah jama’a Ku bata Baki
Ya juya yina kallon abokansa
Sakin Baki hausi tayi cikeda mamaki
Lallai bello ko yanzu ya nuna mata yayi aure
” hummm shikenan Na qara maka sati biyu aci angwanci lafiya
A tare uwale da bello suka amsa da amin ,uwale harda godiya
Suka miqe suka tafi,itakuma ta shige uwar daki Cikin rad’ad’in 6acin rai
Yanzu shikenan Dan majalisar tarayyar birnin wandon da Nike taqama dashi ya zama mallakin mu mu biyu….
Abun dariya yaro ya tsinci haqori
Tun ranar da bello ya tare da uwale kullum bello akan network yike ,kwana hudu cur baya barci ,dare farai ana abu d’aya . tun yina Na marmari yanzu ya koma yin Na wuya
Gashi ta daina barinsa fita,ko d’akin mahaifiyarsa ya shiga saidai tsidik kiga ta banko labule ta shigo itadai karya Dade yazo a cigaba.
Bello kam ya shiga tashin hankali kullum yawo da zariyar wando kacau kacau a hannu ko daurewa baya iyawa
Hutu daya yike samu lokacin sallah..aikuwa lokacin zai gofana sujuda yina rokon wa uwale barci ko ya samu ya huta
Shedanci da karuwanci kuwa iri da kala
A baya babansa ita tasa yayiwa hausi kishiya saidai yanzu duk inda ta zauna sai tayi gulmar su
littafin kud’i at regular 200 VIP 400 ,plz serious buyer kadai zasu biyo mu din jin yanda zaki biya plz. ,09065990265
“Allah ya hada Dana da me farar qafa duk ya karkad’ar da komai nasa ya aurota bata tsinana masa komai sai karuwanci da suke isana dashi.. Na qwace huwaila ersa a hanun uwarta na bata kyauta amma da shike ba diyar arziki bane dare nayi zata turo mun ita su rife qyaure garamm
Bazakiji motsinsu ba sai wajen shad’aya shaura na safiya sannan zakiji qoshiyoyi suna qara a cikin faranti a dole suna karyawa
Da murya qwarqwar irin na soyayyun nan da suka tsofe a gida zakiji tana gardama dashi
Ahh ni Wallahi na fika loma…Ah lomana yafi naki
To wannan tsinewar yazo qarshe yanzu nan zanje inyiwa tufkar hanci”
Ta dasa aya tana kallon qawarta sala mai waina,ta zura mata ido mai ma’anar domin gyara ko shawara…
Typing ✍????
*HARIJI*
(Original Romantic love story)
Free page 11&12
Alheri writers Asso.
By…Oum Aphnan
Masu zagina na barku da illalah akwai madakata ,so if u lyk ki cigaba da zagina ohum bayi tsiro ????♀️Amma ki sani Bana fada a social media ,don’t allow me to start ta kanki….oh allah is it by force ehennn?so oum Aphnan ta dasa alkalaminta no going back ,so don’t exhaust ur time jareee????
Ana qare qarar su ummi ,en sanda suka taho da Ankwa suka umurceta da ta miqo hannu,a sagala mata a wuce da ita gidan yari zuwa lokacin zaman kotun na gaba….
hawayen bakin cikine ya fara tsatstsafo mata a kwarmin idon ta,talaka! Talaka bawan allah ,ace yau duk bautar da tayiwa likitocin asibitin nan ba Wanda zai tsaya mata? Haba wato kowa yina tare da Kaine zuwa wani lokacin gazawa.
Girgiza kai tayi kurum ta miqa masu hannun suka saqala mata ,er sandar haka ta shiga ingixa qeyarta tana tangadi ,tamkar zata kifa
A tarikhin rayuwar ummi in ance mata wani rana zaizo da za tayi abunda za a kaita koda police station to zata qaryata,to bare wai gidan yari ! Ya ilahy????
Quliya ,bai cire idonsa akan talabijin ba,saida aka nuna inda aka hankada keyar ummi cikin motar en sandan
Wani kakkauran numfashi ya furzo zuwa waje mai d’umin gaske
A take ya d’auki wayar salulansa commissioner of police ya kira ,bugu biyu ya dauka ya soma gaishesa cikeda girmamawa
A gaggauce ya bashi umurnin dakatar da yaransa ga maltreating din ummi da sukeyi
Kuma a wuce da ita headquarters dinsu,yanzu nan zai turo lawyansa na musamman don a daukaka qaran zuwa federal ,inyaso sai idan sun nadi sahihan bayanai a bakin ummy a maida ita gidansu safely
Qarfe biyu da rabi na dare a birnin Abuja, Nigeria
Matasane kusan su biyar suka fito daga cikib wani club da naga daga sama an rubutun sunan da golding blue light kamar haka Recreation club
Wani matashin yaro da bazai Gaza shekaru ashirin da tara ba ,ya fara danewa Bayan wata d’irmemiyar mashin Wanda ake tseran gudu da ita ,A qiyasin kudin Babur d’in kuwa takai miliyon takwas
Sanye yike cikin gajeran wando da singlet mai roba roba da ya dace da hadadden fatar jikinsa mai dauke da lufluf din kwantaccen gashi,kai da gani ba tambaya kasan yaron inba balarabe bane to tabbas ya had’a tsatso da larabawa ,tun a yanayin layalayan gashin kansa da akayi masa askin funck ya saisaye wajen qeya ,ya tarashi cukus ta gaba
Sai gashin gemu da ya Tara cunkus har kusan saman kirjinsa tamkar jikan sheqau
Da gaske kallon farko xaka aza cikakken mutum ne da zai kai shekaru talatin da biyar haka,duba da tsuvurin gemun da ya bari ,sai yana taqadaranci ne ko kuma yina zubo wauta zaka gane yarone danya sharaf
Da fofoti suka fito club din shida abokansa, alamu ya nuna su din gayune kawai amma basa shan komai ,inma da abunda ya kaisu club din to bai wuce kallon rawa ba da rashin ji irin na yaran manya da suka saba da rayuwar qasar waje
Wata wargajejiyar mashin mai fad’i da yawan fitillu ya hau ,sannan ya maqala hulan kwanon dake sagale da hannun mashin din