
Yes ke kikaja ,kuma akan son zan iya qarar da duk abunda na mallaka a duniya
” ai sai ayi mu gani in tusa zai hura wuta ,a gama wahala ya qare ya mace”…
“Ohhhoooo thank you Adama da kika fad’a mun qudurin ki akan son,to wallahi in adnan ya mutu sai nayi qararki, da shedar maita kuma saina tabbatar duk tsatsagun zuri’arki sun wuce jail…
Nnenna(Igbon matarsa) had’e kai da (yaroban matarsa) Abike suna gulmar ita adamar da turanci
” Eh matar so yau Asiri ya karye yalla6ai yayi mata fad’a…
Kallonsu tayi ta tsage da kuka, ba fadar da yayi mata yafi mata ciwo ba ,ya tankacin yarfata da yayi a Cikin kishiyoyi.
.
Kallon su dukkansu yayi ,sannan ya korasu duka waje cikeda sababi yina rokonsu karsu sake zuwa masa kurum.
Alhmdllh ,tafiyarsu madam Nnenna ba jimawa saiga yatsun qafar adnan ya fara motsi ,lokacin quliya yina duqe yina karatun Quran a kusa da kansa ,Cikin nutsatsiyar murya
“Dad helppppp!”
Kalmar da ya doki tympanic membrane dinsa kenan ,Cikin karadi na Wanda baya a hayyacinsa
Hakan ba qaramar tsoratar da quliya yayi ba
Da sauri ya duqo gurin kunnensa yina rad’a masa Kalmar ,Cikin dakiyar rai,ya rigada ya cire masa rai kawai da rayuwa,all his thought mutuwa zai yi
Sosai hawaye ke fita daga idonsa ,yina masa fatan haduwa da malaikun rahmah
Daga office d’in Team b,suna kallon abun da ke faruwa ta system dinsu ,don haka da sauri suka yi rushing zuwa wajen su cikeda murna
Saida ƙuliya ya idar da sallar wadha ,kuma yayiwa allah godiya a sujuda da ya farfaɗo masa da yaronsa cikin ƙoshin lafiya,sannan ya samu damar kunna wayoyinsa ,yina duba duk saƙonnin da aka tutturo masa ta cikin email da sauransu,saida ya ga Amandement ɗin nurses and midwifery council of nigeria ,sannan plate dics ɗin shari’ar su ummi ya faɗo masa a rai.
A nutse ya ajiye wani er ficilan caxbi mai kyau,yina ɗaukan ido ,yaje gaban wani cupboard ya ɗauko disc ɗin,ya jona a laptop ɗinsa dake kan gadonsa ,ya kulla yina kallo daga inda yike zaune akan praying mat ɗin da ya idar da salllah…shariar ya ƙayatar da shi sosai,kuma sosai Tausayin ummi ne yaji yina addabarsa ,wanda ya kasa gane a wani mizani zai ɗaura, Tausayinta yikeji? Ko kuwa soyayyarta ne
Tabbas wannan abunda yikeji ,yafi kama da ace ,soyyayartane ya daɗa tsirga masa a rai,Saidai zullumine ya bai baye masa rai a nan take yaji Zuciyarsa na harbawa fat…fat… tunawa da zallar ƙuruciyarta ,anya zata soni?? Anya zata iya zaman kishi da mata irin mata na??? Kai da kamar wuya gurguwa da auran nesa!!!
Sosai kansa ya ɗauki chaji amma kuma ,yina wani tunani sai yaji sanyi a cikin ransa ,a hankali ya tashi ya rufe laptop ɗinsa ,yina zancen zuci a hankali
This is the right time ,that i ought to tell you who i am,My real feature i mean
**
Sauƙi Alhamdulillah jikin Adnani,sai kyau yike sake yi,saidai komai nasa sabo ya zama ,tindaga cin abinci,tafiya ,magana ,kai komai saida aka koya masa
Ƙuliya yayi farinciki da hakan ,don haka yau ya ɗauki aniyar tafiya Kano don cika daɗaɗiyar ƙudurinsa na kusan shekaru uku da suka gabata…
Ɗorayi ƙarshen waya, kano Nigeria
Yau gidansu ummin ,tsit yike duk ma zauna gidan sunfita Neman abunda zasuci na rana yayi saura daga ummi dake zaune tana dakan qulin da zatasha garin kwaki,sai kuwa bazawara uwale ,Wanda zuwa yanzu ta goge mayukan bleaching take shafawa na mutuwa,tayi fara tarr kamar takarda ,kunnenta huji biyar duk ta jeresu da dan maqale sai can saman kunnen ta huda daya ta saka azurfa ,ita a ganinta gayune batasan en mad’igo ke sakawa ba
Ga hancinta tasa hajara (keken maza) ta 6ula mata huji har biyu a hanci guda d’aya, ta zura masu siraran abun hujin hanci ja da fari
Bakinta kuwa haqorin hajjine sama golden qasa fari,wani mugun qamshine ya doki hancin ummi ,Wanda tsabagen qarfinsa har yina mata d’aci a maqoshi
Fitowa tayi Cikin shirin fita tasha gayu Cikin pencil siket na atamfan roba, ta buga daurin ture kaga tsiya,qafarta takalmi toms saidai ta sakama qafa daya sarqa sai walwali yikeyi
Kallon ummi tayi ,ta kya6e fuska ,sannan ta rataya Jakarta ta sa6a mayafi a kafad’a.
“To hajiyan en gida mu mun fita bid’a addu’ar babban mutum ,mai babban aljihu
Kallonta ummi tayi taja tsaki
” allah ya tsari gatari da saran icce wallahi da in maki addu’ar Neman kwarto mai kudi gwara in yiwa kaina fatan cholera”
“To dussa rufe mana massai(bakin ummi take nufi da toilet)
Sai naga ke da kika qi wayewa ,sai an magana kice heeeeee aure zanyi…banza haryau ba mashinshini kinyi badago kamar daddawa a kasuwa…
” Anty uwale don allah kije abinki”
Yanzu kuwa ,aini fita ta gani ,kinga alhaji maiwada ma ke kirana ..
Ta soma magana da kanta tana latsa wajen green na qaramar Nokia ,alamar dauka
“Rabin raina.. Antashi lafiya,ya kwanan kud’ad’enka…
Da sauri ta yi hanyar waje tana d’agawa ummi hannu alamar ta tafi ,tana cigaba da waya da Wanda ta kira da alhaji mewada
Wannan shine page din kusa da qarshen na kyauta ,in baki biya kudinki ba hanzarta biya ta 7782217014 ,fcmb, Mohammed hassana ko vtu da MTN card ta 09065990265,nagode masoyan Amana
Typing ✍????
*HARIJI*
(Original Romantic love story)
Free page 17&18
Alheri writers Asso.
By…Oum Aphnan
Marubuciyar
Bagidajiya
Laylerh
Jarababben Namiji
Indo maqata
Ramuwar gayya
Qasaitattun mata
Rayuwar Afredarh
Namijin kishi
Akan dadiro nah
Jinin sarauta
And now
°•°•° Hariji °•°•°•
Like father like Son
Gama duk aikinda ummi takeyi, tayi. sannan tasa tsintsiya ta share gaba ďaya dandaɓaryan ƙasan gidan,wanda ya daɓe kamar sumunti,saboda tsabagen gyara da shara da yike samu a wajen ummi,duk ƙurar ya kwanta,ta gama sharesa…daganan janyo ruwa tayi a daga kwakwareren rijiyarsu,datake a bude kasa na zabtarewa yina komawa ciki,haka ta gama zuba ruwan a bokati ta saka a inda rana yike fitowa,da nufin yayi dumi taje tayi wanka dashi,itakuma kafin nan ta kewaya bayan gidan tana gyara wajen shukan ɗatan ta(shuwaka).
Wulƙawar ummi baya keda wuya ,hajara ta shigo gidan ,da sauri ,sauri ta fara jan ghana must go ɗinta na suturu tana fitar dasu ƙofar gida.
Ta janyo na ƙarshen ummi ta kewayo,anan sukayi kici6is
“Anty Hajjo,ina zuwa da kaya haka”
Ɗan sassauta muryarta tayi ,kamar mara gaskiya
“Shishhh ,ki magana a hankali tareda wani gaye nike a ƙofar gida ,da dalleliyar motarsa ,ya rakoni ne in kwashe kaya ,bayan naje gidan uncle ɗin GRA ba roƙeshi Arziƙi zan koma can da zama ,don gaskiya ina mugun kunyata ,idan samarina sukazo ,sukaga wai wannan buscuit house ɗin shine gidan mu,a take nike ganin alamun raini a ƙwarar idonsu,don haka in umma tazo kice mata na koma GRA zan ringa zuwa muna gaisawa,don yanzu haka ma nacema wannan gayen ne,nan gidan da nike kai wanki ne nazo in kwasa kayana..”
Tunda hajjo ta soma magana ,ummi tayi mata sakatata da baki ta kasa furta ko 1 kalma,itakuwa taja jakar kayanta tayi ficewarta
“Ohni oum kulthoom ,inaji da yayyu,In baka mutu ba zakaga abu ,Allah yasa mufi ƙarfin zukatanmu”
Daganan taje ta ɗauki ruwan wankanta ta wuce banɗaki abunta.
**
4 Pm
Sallama ummi taji daga ƙofar gida,itakuma a daidai tana ƙoƙorin saka safa zata wuce Islamiyya,ɗan ɗaga murya tayi kaɗan,tana amsa sallamar ,sannan tayi hanyar fita da sauri,gabanta na faɗi, ko da wanne yau a kazo ohoo?
Turus tayi ganin baba mai anguwa a bakin ƙofa.
“Sannu baba ,ina wuni”
“Lafiya lou,ummulkaltume ƴar Albarka anyi shirin islamiyyar?”
“Eh baba me unguwa,wani kake nema ne?”
“Eh to,da babanki naso gani,amma dai tunda na ganki zance ya ƙare,tunda dama mune almuhimmun kuma zancen ta kanmu ya biyo,watakon ALƘALIN ALƘALAI NA ƘASA Ne takanas ya taso don ku gana akan magana mai muhimmancin gaske ,dikda bai faɗa mana ba,to nasan yanzu mara zuciyar ubanki baza’a samesa a gidaba ,wataƙil yina bakin tasha ,to don haka na taso in shaida maki zuwansa ,wataƙila akan bai rasa nasaba da shari’arku .A don haka,yayi maki saura ki ɗauko tabarma ki shimfiɗa masa a soro ,ko kuma ki masa tujara irin na gantalallun ƴan uwanki,da suka saba,kedai kin fice masu zakka! Don haka Ki riƙe matsayinki Ato”