HARIJI COMPLETEHARIJI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

HARIJI BOOK 1 COMPLETE

HARIJI BOOK 1 COMPLETE

Tunda ya fara magana kanta ke sunkuye ranta na tururi,kowa ya tashi zagi! ,zagi dai akan iyayenta da danginta,basu tunanin duk lalacewarsu ina sonsu a hakan? .
Saida ya ƙare ɗiban Arziƙinsa ya wuce,itakuma kamar yanda ya bata umurni ta shiga gida ta ɗauko wata tsohuwar tabarma ta shimfuɗa masu a zaure,jimawa kaɗan sai gashi ya dawo bayansa ,wani ƙasurgumin Alhaji cikin wata ɗanyar shaddar gezna dark blue sai ƙamshi takeyi.
Can daga bakin ƙofar shiga gida ta zauna gamida rafka tagumi
A haka take gaishesu kanta a sunkuye,saida suka gaisa sannan baaba mai unguwa ya fita ,shikuma yayi gyaran murya.

“Malama Oummu” bata samu zarafin iya amsawa ba,sakamakon yanda muryarsa ya haifar mata da jin nauyinsa gamida ninkuwar kwarjininsa,don haka a nutse ta watsa lulun Eyes ɗinta a kansa a karon farko tun zuwansa.

“Kin ganeni?” da sauri ta girgiza masa kai “ban sanka ba yalla6ai”
Murmushi yayi irin tasu ta girma
“In tuna maki ko ni wanene?” Gyaɗa kai tayi shaye da mamakinsa

…..3 years back
Dambene ya kacame tsakanin Hajjo(Hajara keken maza ) da Uwale (Jamila) duk akan saurayin Jamila da yaga hajara yaci amanar uwale ya koma yina nemansu gabaɗaya,shine a ranar asirin su ya tonu ta kamasu a ɗakin saurayin tana kwance akan katifarsa da shi,itakuma tun a ɗakin bala’i ya ruguntsume shine har gida…Bala’i yayi bala’i har maƙota saida suka shigo sasanci,saidai ba ko kunya ana tambayarsu abunda ya faru sai tace wai daga ta ganni akan katifar saurayinta,to shiɗin aurenki xaiyi,ai gwara kowa ya yaga rabonsa…”
Itama umma ba kunya take bin bayan uwale,wai hahara ce ba gaskiya tinda ai ba saurayinta bane

Kuka sosai ummi takeyi a lokacin tana shekaranta na farko a makarantar midwifery ɗinta,kwata kwata shekaranta sha shida
Haƙurin duniya ta basu sunƙi haƙura saima duk suka juyo da akalar faɗar kanta

“To Algunguma,ina kika fito school,ina zaki makaranta,ai yanzu kema kika fara tasowa,duk muna kamar ki bamusan daɗin maxa ba ,amma a juri zuwa rafi,don indai ke jinin abbah da ummah ne to harijanci a jininmu yike,Alfarma ɗaya zakiyiwa kanki ki samu miji kiyi aure,saidai kuma kashh har yanzu ba mashinshini…”

“Ya isa uwale,kiyimun duk tujaranki ,allah na gani,kuma inshallah yau ɗinnan zan fita ,zanje duk namijin da na fara haɗuwa dashi,shi xan aura…wannan alƙawari na ɗaukarwa raina da ziciyata,don bazan ta6a yarda in lalaceba,koda kuwa kwartanci a jininmu yike…”

Tana kaiwa nan ta fice da sauri tana sharar ƙwalla

Titi ɗoɗar ta ɗauka ,tana faman waige² jiri na ɗibarta,har tahau babbar titin da zai kaika babbar titin gidan sarkin kano

Wata ƴar ƙumbular mota ne ta shararoo da gudu,saidai tundaga nesa ya fara jan ham,saboda yanda ya hangota tana shiga ma titin,hakan mai makon ya ankarar da ita saima kamar ya ƙara tsoratar da ita.,haka kuwa ta daɗa shigewa titin…ƙiiiiiiiiiii yaja burki ,tareda ɗan ƙurzan ta a hankali ta faɗi ƙasa rikica…aikuwa taba faɗi,ta miƙe da sauri ta tattare siket xata fyalla da gudu ,sosai ya kawo tanada psycho problem ,don haka cikin zafin nama ya damƙeta
Ya turata a motarsa ,ya kewayo zai tuƙa ta kallesa

“Alhaji”
“I haƙuri,yanzu zan kaiki asibiti daga nan”
“Alhaji zaka aureni?”
A mugun bazata kalmarta yazo masa
“Ke kinada lafiya kuwa?” kuka ta fashe masa dashi,tana bubbuga masa gaban mota ,wajen fitar sauti
“Ka saukeni ni lafiyata ƙalau ,damuwata mijin aure kuma kai nikeso,ni ka saukeni in baka yarda da tayina ba”
Ƙare mata kallon ƙurilla yayi,yarinya kyakyawa black beauty,hancinta ɗan gajere da ya dace da faffaɗar fuskarta mai ɗaukeda dimple a kowani ɓangare,idonta dara dara,masu haske kamar madara,wanda kuka da damuwa suka surkasa zuwa ja ja…Ɗan nazartan ta yayi,gadai ta yarinya dake kan ƙuruciyarta da bazata wuce sa’oinsu rufaidah ba(ɗiyarsa) ,wanda suke just in their midst ,a sweet sixteen ,to meye haka??

Tsaida tunaninsa yayi waje guda,yaja burki ya tsaya ,akan kwaltan gefensa ya dauke idonsa cikin rashin kula ,yace “Fita!”
A tsorace ta fara dambe da mirfin ƙofar saidai ta kasa buɗewa
Wani dabban tsawa ya buga mata
“I said out!”
Da sauri ta fita ,sannan ta ƙara da gudu har tana tuntu6e….

….Sunkuyar dakai ummi tayi ,saboda tunowa da abinda ya faru tsakaninsu ,sai yanxu ta ganesa,kunyane ya lulluɓeta
“Alhaji wautace da ƙuruciya kayi haƙuri bansan ko kai wanene ba”
Murmushi yayi irin tasu ta manya

“Nasan hakan,saidai yanxu na bibiyi tarikhin ki,kuma na gano abunda kikayi daidai ne,saidai bakiyi ta hanyar da ta dace ba,a lokacin ina saurine zanje wajen aminina sarkin garin nan,sai daga baya nadamar wulaƙancin da nayi maki ya kamani,saidai abun takaicin bansan inda zan ganki ba,sai sanadiyyar shari’arki da aka sanya a gidan talabijin NTA…A ƙarshe gani nazo a wannan karon badon amsa tayinki ba,A’ah saidai don na hango wasu charisma a tare dake oummu,kuma ni a shirye nike in aureki a duk ranar da kika shirya ,Ni namijine mijin mata uku,matana akwai bayarbiya,banufiya da inyamura,zaki yarda in cike ƙofa dake matsayinki na yarinya jinin Hausa /Fulani?…


Hariji @#200Regular group @#400 vip group ta 7782217014 ,muhammed Hassana,fcmb ko mtn card ta 09065990265….ga masu son duk littafaina zasu sameshi akan kuɗi #1000 only a matsayin sauke farashi,amma banda na wannan littafin,don Allah in baki shiryaba karki biyoni

Uwale daga gidansu gidan saurayinta da ya kirata a waya ta wuce wato maiwada,saida ta sauka akan mashin sannan ta daɗa kiransa a waya
“Gani a bakin kwanan gidan kazo ka sallami ɗan Acaɓan”
Minti kaɗan ya fito cikin shigar kamala,rigan yadi tazarce,inka gansa bazaka kawo mai fajirciba.
Makullin ɗakin matarsa ya bata,shiga gidan ki buɗe ɗakin ,gafaƙar an tafi yawon ta zubar,kinga muma sai mu murje gyaɗarmu son ranmu,tace kwana zatayi,iba fatan dai kin zo da shirinki,kinsan dai banda sauƙi
“Ai daɗinta nima kasan ba sauƙi garenba,nidai kamun ka shigo ka taho mun da abun motsa baki kurum”
“Angama ranki ya daɗe,uwale kenan kankana gidan ruwa???? ai namiji yayi maki komai don juriyarki ga ruwa da an ta6aki kin hau tsiyaya kenan”
“To ai sai ka tona muna asiri ,adai kan hanya muke”
Sosa ƙeya yayi kamar me kunya
“Santin kine tawan”

Kar ku damu daga gobe zamu fara abubuwa????,Sis akwai raraka da zungura ,daga gobe xa’a fara book ɗinnan ma zance,kuma inshaallah fejin gobe shine zai zana na ƙarshe,in baki biyaba ,maza ki biya kar ayi maki ta leƙo,ta koma????09065990265
Typing ✍????

    *HARIJI*

(Original Romantic love story)

LAST Free page 19&20

Alheri writers Asso.

By…Oum Aphnan

Daga page ɗinnan na kyauta ya ƙare,saura na kuɗi,sai kiyi gaggawar biyan kuɗinki ta 7782217014,muhammed Hassana ,Fcmb bank…ko MTN card ta wannan number 09065990265 Ga masu buƙatar Duka littafan marubuciyar,zaku biya naira dubu ɗaya kacal,#1000 tahanyoyin biya na sama

Gaisuwa da jinjinan ban girma ta bazasu yanke ba ga tarin masoyana…kuma masoyana littafaina,kamar su
Maman teddy
Oum Afnan
Oum Hanif
Maimoon
Oum ilham
Oum laylerh
Oum yusrah
M.sadiq
M.sajida
Ummi minnah
Aisha kd
M.zahrah Mubi
Faty kano
Su’udiyya Abuja
Adabiyya
M.samha
Cise
Hajiya Atika
Hajiya fatima
Hajiya Nafisa
Hajiya xainab ,bammanta da karramwarku ba,sannnan ina jinjina ga ku readers ɗina da kuke biye dani tundaga farkon littafina wato RAYUWAR AFREDARH Har zuwa tsayin littafaina goma sha…. Baku taɓa rashin bin ko ɗaya ba,Tabbas wannan ba komai bane face ƙauna…
Mutane na ƴan comments group ɗina wanda baku gajiya wajen yimun comment,zan bibiyi sunayenku rankatakaf zan rubuceku a ƙarshen littafina don ku gane na damu daku nima kamar yanda kuke sona
Zazzagawa mutane na ga irin naku✊
Kanawa Abokan wasanmu ina jinjinawa lukutar qaunarku a gareni???? Mutanen ƙasar niger,saudiyya,ghana ,Oum Aphnan takuce har kullum
Da sauranku wanda lokaci bazai bani damar ambatanku duka ba,saidai in a nutshell ince ƴar mallawanku ,nayi maku zunzurutun so ,maras Algus????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button