Hausa Novels

Lu’u Lu’u 17

*17*

 

Kamar wasa sai kam Bukhatir ya shirya cikin shigar alfarma da take nuna ya fa yi niyyar zama mai mulkin k’asar Egypt na gaba, motoci aka shirya inda ya umarci Zafreen da ta shirya zasu tafi, ba kuma Zafreen kad’ai ba har da matarshi Zeyfi, ita kan ta tayi mamaki dan ba zata iya tuna lokacin da sukayi tafiya tare ba, duk da yanzu ma bai fad’a mata inda suka nufa ba, amma hakan ma ya mata dad’i tunda dai ga ta ga shi, dan kwana biyu kenan ko gidan da take bai kwana saboda zumud’in Zafeera wacce ta ke ganin ta shigar mata hanci a duk’unk’une, tana sunan matarshi ne kawai, amma gangar jikinsa da zuciyarsa sun haukace aka wata wacce bai ko tab’a ganinta ba bayan jiya.

Haka kam akayi inda suka d’auki hanya zuwa babban birnin Texanda, *awa takwas* suka d’auka a hanya kafin suka isa masarautar.

Sanda sukayi oda daga k’aramar tagar dake jikin k’ofar mai gadi lek’o, ganin bak’in motoci yasa shi bud’e k’aramar k’ofa ya fito, motar dake gaba ya lek’a ta madubi yace “Yallab’ai daga ina?”

Dreban dake tuk’a motar da Zafreen take ciki ne yace “Daga Egypt tare muke da gimbiyarku.”

Idonshi ya sauke a kujerun bayan motar, ganin Zafreen ta wurga masa wani kallo yasa shi saurin rusunawa yace “Ranki shi dad’e.”

Da sauri ya juya ya koma ciki ya rufe k’ofar k’arama sannan ya shiga fafutar bud’e k’atuwar k’ofar mai taya wacce turawa ne kawai yake, saida ya bud’esu gaba d’aya sannan hancin motocin suka durfafa ciki, duk tak’ama da ji da kan Bukhatir saida ya tabbatar lallai sarki Musail yana murza mulki a daular nan, irin dukiyar daya zuba wajen k’era gidan nan, shuke shuken dake wurin ka rantse lambuna ne ta ko ina, manya manyan b’angarori ne guda uku, na tsakiyar kuma shi ke shaidawa mai kallo a nan sarki Musail yake rayuwarsa.

Kamar yanda sauran motocin ke bin motar dake gaba har saida suka tsaya daf da b’angaren tsakiya, ganin fuskarta daga cikin farin gilashin motar yasa wasu masu tsoron k’ofar su biyu d’aya a cikinsu ya taho da sauri ya bud’e mata ta fito, juyawa tayi ta kalli Bukhatir da matarshi da suka fito su ma, kallon bafaden nan Zafreen tayi tace “Ina mahaifina yake?”

Da ladabi yace “Shugaba na yana fada.”

Juyawa tayi ta kalli Bukhatir tace “Pah yana fada, zaku same shi a can ne ko zaku jira?”

Wani kallo ya mata yace “Ai mu masaukin bak’i ne ya dace da mu, dan maganar data kawomu babba ce.”

Harara ta galla masa sama da k’asa ta kalli bafaden nan tace “Ka kaisu masaukin bak’i.”

Rusunawa yayi yace “Angama ranki shi dad’e.”

B’angaren dake hagun su ya nufa yana kallonsu alamar su tafi, da kallo Bukhatir ya bita sanda take shigewa ciki da mamakin yanda ta bayar da umarnin a rakasu masaukin bak’i.

Jinjina kai yayi ya kalli Zeyfi ya rik’o hannunta, da sauri Zeyfi ta kalleshi tana sakin murmushi dan hakan ya mata dad’i sosai, gana son mijinta so mai tsanani kuma tana kishinsa, saidai tana tsoronsa da kuma shakkun halayensa, dan tun ranar daya wanka mata mari a kan Zafeera bai sake ko kallon fuskarta ba, ita kamba tasan ya zatayi da Bukhatir ba, wasu lokuta har mamakin irin biyayyar da take masa take, gashi dai tana so ta haihu da shi, amma gaba da gaba ya fad’a mata bata isa ta fara haihuwa ba har sai Zafeera ta zo ta fara haihuwa sannan ita ta biyo baya, tabbas ta ga illar auren tushe, watak’ila da mai son ta ta aura da bata ganin wannan k’ask’ancin, amma dake mahaifinta kwad’ayi yasa shi aura masa ita wulak’anci kawai take gani ta ko ina.

Zafreen na shiga duk hadimai suka kama jikinsu, d’akinta ta shiga da sauri sauri ta shiga cire kayanta inda hadimar ta shiga ban d’aki dan had’a mata ruwan wanka, tana kammalawa ta fito ita kuma ta shiga d’aure da k’aramin towel tace “Ki kawo min madara mai sanyi.”

“To shugaba ta.” Ta fad’a tana ficewa a d’akin, bata wani jima a wurin wankan ba ta fito dan dama ta shirya a can, madarar data samu ajiye ta d’auka tana kurb’awa tana kallon kan ta a madubi, dafe k’ugu tayi tana shan madarar tana ayyana _”Ashe dama ita ce Zafeera? Tana da abun al’ajabi yarinyar? Shi yasa ta iya d’aga hannu ta mare ni a fuska? Ai kam zatayi nadama, zan samota sannan na hukunta ta, zata san ni ce gaba da ita ko a haihuwa ma.”_

K’wafa tayi mai k’arfin gaske tare da aje madarar ta shiga shiryawa a tsanake, cikin shigarta ta alfarma na kayan sarauta ta shirya inda ta fito fes da ita ta gama kyau, fitowa tayi daga d’akin tana ta k’amshi abun ta, jakadiyar da suka had’e da ita yasa ta tambayar “Ke ina Mah?”

Da sauri ta d’aga kai ta kalleta tana rarraba ido da tunanin ta inda zata fara fad’a mata, sunkuyar da kai tayi tace “Ranki shi dad’e sarauniyata bata nan.”

Yatsina fuska tayi tace “Ina kuma ta tafi?”

Kad’an ta ja baya dan tsoron mari take idan ta bata amsar, girgiza kai tayi dan kare lafiyarta tace “Ni ma ban sani ba gimbiya.”

Tsawa ta daka mata tace “Kamar ya baki sani ba? A gidan nan fitar Mah tana b’oyuwa ne ko dan yan rakiyar da Pah yake had’ata da su, zaki fad’a min ko sai na wulak’antaki?”

Jiki na b’ari ta durk’ushe k’asa tace “Ranki shi dad’e ai sarauniya ta kwana biyu a gidan kurkuku na sabah.”

Da k’arfi tace “Me? Kurkuku?”

Da sauri ta taka zata bar wurin sai kuma ta juyo ta kalleta tace “Akan me wai?”

Shiru tayi hakan yasa Zafreen fita da sauri kamar zata tashi sama, b’angaren damansu ta shiga inda anan fadar take, sosai ke da banbanci tsakanin babban b’angaren da kuma nan d’in, inda kujerarshi take cikin sauk’i Zafreen ta hangeshi, fadawan kuma duk suna zazzaune suma a kan kujeru cikin shigarsu ta alfarma.

Tunda suka ji an bud’e an shigo babu neman izini suka maida hankulansu kan k’ofar, ganinta yasa kowa mamaki har sarki Musail da waziri Khatar suka mik’e dan suna tsaka da maganar inda ta shiga ne ita ma, da sassarfa sarki Musail ya sauko a matakalar ta fari da ta biyu har zuwa ta uku wacce ita ce ta k’arshen dake sadashi da kujerar mulkinshi, bud’a hannayenshi yayi da farin cikin ganinta yace “Gimbiya Zafreen, yaushe kika shigo? Ina kika shigo haka?”

Ja baya tayi cikin d’aga murya tace “Pah, me Mah tayi haka da zafi daka zab’i kulleta a kurkukun sabah? Kurkukun da kake rufe manyan masu laifin daka kama ko kuma kake son horar da mutum dan nuna masa ikonka.”

Sauke hannayenshi yayi ya dogara sandar shi a k’asa ya k’ura mata ido, shiru yayi bai da niyyar amsata, cikin jin haushi ta sake maimaita” Pah, mahaifiyata fa ka rufe a kurkuku, ina so nasan me tayi haka? Ka daina son ta ne?”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button