Labarai
Ina biyan mai min wanka N3.5m duk wata, bana iya yi da kaina, ‘yar kasar Tanzaniya
Aisha Feruz ta bayyana yadda take kasa yi wa kanta wanka hakan yasa take nemo ma’aikatan da su ke yi mata, Legit.ng ta ruwaito.
‘Yar kasar Tanzaniyar, ta bayyana yadda bata dade da korar mai yi mata wankan ta dindindin ba, inda yanzu take daukar mutane daban-daban na kwanaki don su yi mata aikin.
A cewarta, tana biyan tsohuwar mai yi mata wankan N3.5m (KSh 1,000,000) a ko wanne wata yayin da take biyan duk wanda ya yi mata wanka na rana daya N178,000 (KSh 50,000).
Feruz ta janyo cece kuce a kafafen sada zumunta bayyan ta bayyana wannan batun.
Daga namiji har mace ko wanne zai iya yi mata aikin
A cewarta, ba ta kebe aikin ga wani jinsi, duk wanda ya nema kuma yana da bukatar sannan ta ga ya cancanta zai iya samu.
A cewarta:
“Idan na falka da safe, ina kiran wani don ya wanke min jiki saboda ina matukar wahala idan ni zan yi wa kaina wanka.”
Ga bidiyon tattaunawar wanda globaltvonline ta wallafa:
[ad_2]