AtikuAureLabaraiSiyasa

Ina Bukatar Takardar Saki Daga Wajen Ka, Cewar Matar Atiku Abubakar Jennifer  

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Daya daga cikin matan Atiku Abubakar, Jennifer Douglas Abubakar, ta bukaci takardar saki daga wajensa.

Jennifer Douglas Abubakar wacce ita ce matar Atiku ta uku, ta yi ikirarin cewa tana fuskantar barazanar kisa sakamakon shirinta na rabuwa da Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Nijeriya.

Jennifer, wacce lauya ce a kasar Amurka ta musanta zargin cewa tana yunkurin rabuwa da Atiku Abubakar ne saboda kwanan nan ya auri sabuwar amarya ba tare da ya sanar da ita ba kamar yadda al’adar Arewa da Musulunci suka tanada, inji rahoton The Cable.

Jennifer ta yi kukan barazanar kisa da ake yi mata a wata hira a baya-bayan nan ta ce barazanar ta fara ne bayan ta bayyana shirinta na rabuwa da Atiku Abubakar.

A maimakon haka, Jennifer ta bayyana cewa aniyar ta na neman sakin yana da nasaba ne da shawarar zama a Amurka don kula da ‘ya’yanta wadanda a cewarta, sun dade ba tare da iyayensu ba, in ji PM News.

Ta kara da cewa akwai batutuwan da suka dade a gamayyar auren nasu wanda kuma shi ne dalilin da ya sa ta yanke wannan shawarar ta rabuwa da Mijin nata.

Da take karin haske, matar dan takarar shugaban kasan ta ce a yanzu haka tana samun barazanar kisa daga jami’an tsaronsa tun bayan da ta bayyana shirin ta na rabuwa da shi.

A kalamanta: Tace Mai Martaba ya auri amarya ba shi ne ya kawo matsala tsakaninmu ba kamar yadda mutane da yawa ke cewa.

Mai Martaba Musulmi ne, ban taba tambayarsa game da matansa ko nufinsa ba.

Babban dalilin neman kashe aurena shi ne rashin jituwa game da ci gaba da zama a Burtaniya, don kula da ’ya’yana da wasu batutuwa da suka dade a kasa.Tun da wannan lamarin, ina jin tsoratarwa kaina da na ‘ya’yana.

Jami’an tsaronsa na musamman Ibro da sauran su suna ta barazana da kiraye-kirayen ‘yan uwa da abokai da ma’aikata suna neman kadarorina su kwace.

Saboda haka, na fice daga tawagar lauyoyi na, na sayar da dukiyoyina kuma na koma kasar waje har zuwa lokacin da zaman lafiya ya samu.

Ban yi wani laifi ba face na nemi a raba aurena kuma abin ya min zafi da har nayi amfani da wannan kafar wajen magance matsaloli masu sarkakiya amma ina fargabar cewa a wannan lokaci zan sanya bangarena a rubuce.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button